Hausa novels

Hajar Page 5 Complete Hausa Novel

💛 HAJAR 💛

Hajar Hausa Novel Document txt

By Feenerh_feeche

 

{ 5…}

Noor ta koma kan kujera tana murmushi tace “Allah kam sai naga kamar rigar ce”, shiru yayi mata ya buɗe lemonsa ya zuba a glass cup ya fara sipping, Noor ta tashi ta haye stairs ta kara wayarta a kunne tana murmushi. Mami ta kallesa tace “Nurain”, ya ɗago yace “na’am Mami”, Mami ta sauke ajiyar zuciya ta mayar da hankalinta kacokan akansa tace “you have to move on dear, me ake ciki ne maganarka da Ruqayyah??, ka riga da ka gama gini to mai kake jira, gaskiya ya kamata ka motsa kar iyayenta su ɗauka playing daughtern su kake”, Nurain ya sauke sassanyar ajiyar zuciya ya dire cup ɗin hannunsa yace “yeah Mami daman ina so na gaya miki ki sanar da Abba, I’m ready a kai kuɗin, kuma…” sai yayi shiru yana shafa lallausar sumarsa, Mami tace “kuma me??”, yace “kar a saka lokaci mai tsaho tinda dai mun gama fahimtar juna, kuma maganar lefe shima ba wata matsala Insha Allah”, Mami tayi murmushi tace “idan kai a shirye kake toh iyayenta fa, nima kaina ban shirya ba”, yace “Amma nasan kafin lokacin kin shirya aii”, tace “maganar lefe mai za a ƙara nasan dai akwai wasu kayan wajen zulaiha, abinda ya rage bashi da yawa”, yace “yeah munyi maganar da ita tace 2million sun isa a cike ragowar kayan”, Mami tace “toh shknn zan sanar da Abbanku idan ya dawo”, Nurain yace “ohk, bari na fita masallaci”, ya miƙe ya fita daga palourn. Da daddare Mami ta tari Abba da maganar ta sanar dashi komai, Abba yana zaune a palournsa ya kalli Mami yace “ohk, kika ce yace he is ready??”, tace “uhmm haka yace”, yace “ohk then, bawai na rabu da Nurain yayi komai na aurensa yana nufin bana sonsa bane, abinda yasa ina son ya martaba matarsa ne kuma ya kula da ita, nafi so yayi aure da dukiyarsa yadda zaifi kula da matar da haƙƙoƙinta, though banida doubt akan Nurain amma i have to do this”, tace “na fahimceka my prof”. Abba ya ɗauki wayarsa yayi dialing numbern Nurain ya kara a kune, Nurain a lokacin yana balcony yana waya da Ruqayyah, ganin kiran da yake shigowa wayarsa yasa yace “ina zuwa bari na ɗauki kiran Abba zan kiraki if I’m done”, Ruqayyah tace “ohk” ta katse kiran, yayi picking kiran Abba, ba tare da ɓata wani lokaci ba Abba yace masa ya samesa a palourn sa ya katse kiran, Nurain ya sakko down stairs ya wuce part ɗin Abba, ya murɗa tsadadden handle ɗin ƙofar palourn ya shiga da sallama, Mami ce ta amsa ya ƙaraso ciki ya zauna kan carpet yace “Abba gani”, Abba ya nuna masa sofa yace “zauna”, ba musu ya koma ya zauna inda Abba ya nuna masa, Abba yace “naji saƙonka wajen Maminku, naji daɗin hakan, kace kar a saka lokaci mai tsaho amma baka tunanin ɓangaren ita yarinyar zasu iya cewa lokacin ya musu ƙaranci, kamar month nawa kake so ayi fixing date??”, Nurain yace “Amm kamar three months haka”, Abba ya jinjina kai yace “ohk, kaine ai me aure shiyasa nake tambayarka, amma bazan yi assuring dinka three months ba idan sun nemi a ƙara musu lokaci za a mayar five months, idan kuma basu nema ba za a barshi a three months din da kake so, Insha Allah gobe zan samu uncles ɗinka next tommorow sai aje gidan nasu”, Nurain yace “okay”, Abba yace “ka iya tafiyarka”.

 

★Umma na fita bakin titi ta tari napep ya kaita har ƙofar gidan Anty Jamila dake a unguwar Goron dutse, Umma ta shiga ɗan madaidaicin gidan mai ɗan ƙaramin gate da wajen parking mota ɗaya matsayin tsakar gida, Anty Jamila baki har kunne ta tarbi ƴar uwarta cike da murna, suka zauna a ɗan matsakaicin palourn Anty Jamila da yasha ado ba laifi, Hafsa ce ta shigo wacca itace second born ɗin Anty Jamila da jug mai ɗauke da zoɓo mai sanyi da ruwa ta ajiye a gaban umma, Umma tace “kai alhmdllh jiki yayi sauƙi, Allah ya ƙara afuwa”, Hafsa tace “umma ina wuni, ya baki tahomin da Hajar ba?”, Umma tace “lafiya lou, Hajar tana nan tafe zata zo aii”, Hafsa tace “tom Allah ya kawota” ta fita ta basu waje. Anty Jamila tace “wllh Adda dama baki wahalar da kanki ba ai na gaya miki Hafsa taji sauƙi, amma naji daɗin zuwanki”, Umma ta tsiyayi zoɓon a cup ta ajiye gefenta tace “akwai wani dalilin da ya kawoni bayan duba Hafsa aii”, Anty Jamila ta gyara zamanta ta ɗauki remote ta kashe ƙarar Tv tace “ai da kin gaya min sai nazo can ɗin ma Adda ba sai kin wahalar da kanki ba”, Umma ta sauke ajiyar zuciya tace “babu komai nan ɗin yafi”, Anty Jamila tace “toh Adda Allah yasa dai lafiya”, Umma tayi sipping zoɓo tace “Jamila babu abinda baki sani ba akan rayuwar gidan da nake, toh a da dai abin bai fiya damuna ba sai yanzu da Hajara ta fara mallakar hankalinta, yanzu fa gidan kullum cikin tashin hankali ake, ga Hajara ba zata taɓa gani ta kyale ba, in ƙarƙare miki zance har dambe ake yi dani”, Anty Jamila ta riƙe baki ta zabga salati tace “Adda dambe..”, Umma tace “da zarar sun tsokani Hajara saita rama, to sai su haɗu su lakaɗa mata duka, ni kuma idan naga zasu kassaramin ƴa saina shigar mata a haka abin yake zama dambe, babu irin faɗan da ban yiwa Hajara ba akan ta dena biye musu amma kuma taƙi ji saboda na lura da ita tanada zuciya kuma bata son wargi, toh yanzu gaba ɗaya lungun mu an riga da an canfa mana gida wai mu ƴan bala’i ne kullum cikin dambe muke, kinsan mutane wallahi harda nasu gishiri da magin suke ƙarawa, ni dai yanzu na yanke shawara zan mayar da Hajara wajen Iya ko a samu sauƙi, jira nake suyi sauka a islamiyya saita koma gaban Iya, ko ya kika gani??”, Anty Jamila tace “Eh toh me zai hana ki kawomin ita nan saina haɗasu da Hafsa”, Umma ta girgiza kai tace “gara dai na kaita wajen Iya kinga ta ringa taimaka mata da wasu abubuwan, amma kuma bansan ta yadda zan shawo kan Mal ba kinsan yadda yake jin Hajara duk cikin ƴaƴansa”, Anty Jamila tace “indai kikai masa bayani ai zai gane”. Umma bata baro gidan Anty Jamila ba sai bayan sallar la’asar.

 

★Wata numfasasshiyar Mota ce tayi parking a daidai lungun ƙunshi, saida motar tayi minti ashirin da tsayuwa sannan Sa’adatu ta buɗe ƙofar mai zaman banza ta fito, hannunta riƙe da ledoji ta fara tafiya tana rangwaɗa ta shiga lungunsu, Naseer na zaune akan benci gaban shagon Iliya kuma akan idonsa aka sauketa daga mota tazo ta wuce, iliya da Munkaila suka haɗa ido suka kasa cewa komai saboda kasancewar Naseer a wajen, ita kam Sa’adatu bata ma lura da yayan nata ba saboda duhun dare na damuna, saida Naseer ya bari tayi nisa sannan ya biyo bayanta, tana shiga soro shima ya shiga ya sakawa ƙofa sakata, ya saka ƙafa ya kwarfeta ta zube a ƙasa har saida bayanta ya amsa, beyi wata-wata ba ya zuge belt ɗin wandonsa ya fara zabga mata ta ko’ina, Sa’adatu ihu take tana neman ceto gashi ta kasa tashi ƙugunta ya riƙe, da iya ƙarfinsa yake sauke mata ruwan belt ajiki. Maama da Maimuna da kuma Nabilah da suke tsakar gida suka jiyo ihu a soro, Maama ta miƙe da sauri tana gyara zaninta da yake shirin kwancewa tace “ke Sa’adatu ce fa” tayi hanyar soro cikin sauri Maimuna ta bita a baya, Nabilah kuma ta rarumo wayarta keypad tana ƙoƙarin kunna fitila wayar ta suɓuce daga hannunta ta tawarwatse a ƙasa. soron duhu dunɗum Maama cewa take “Nasiru ka rabu da ita nace maka”, Naseer kam dukan Sa’adatu yake da iya ƙarfinsa yana cewa “uban waye wancan da ya ajiyeki a mota??”, Sa’adatu da azaba ta hanata magana sai gunji take, Maama ta kwalawa Nabilah kira tace “ki ɗakko min kyandir a ɗaki”, kafin Nabila ta kawo kyandir ai Sa’adatu ta faɗawa ƴan garinsu, a matuƙar fusace Naseer ya wuce cikin gida Maimuna da take kan hanya itama saida ta samu rabonta, domin kuwa saida ya cije ya zabga mata belt ɗin hannunsa ta ɗaureta ya zuge mata ita ajiki tayi mata wankan jego, da mugun gudu Maimuna ta kyalla cikin gida tana soshe-soshe, batama san lokacin da ta bangaje Nabilah ba kyandir ɗin hannunta ya liƙe mata a wuya har saida fatar wajen ta kwaile, Nabilah da zafin wuta ya ratsata ta mulmulo ashar ta danƙara mata, a banza dan Maimuna batama san me ta aikata ba ji take tamkar an zuba mata tafasasshen ruwan zafi a fatar baya. Maama ta tallafi Sa’adatu ta shiga da ita cikin gida, gaba ɗaya jikinta yayi ruɗu-ruɗu da shatin belt, ga wani shaɗi da yayi mata a fuska wajen har ya kwaile, Nabilah ce ta tsaya ɗakko ledojin da Sa’adatu tayi wurgi dasu tin lokacin da Naseer ya kwarfeta, shawarma ce da pizza gaba ɗaya sun gama baɗewa da ƙasa babu ta yadda za ai su ciyu, ice cream kam kifewa yayi a ƙasa. Maama ta shiga ɗakinsu Naseer tace “Nasiru banyi maka gargaɗi akan dukar min ƴaƴa ba?”, Naseer ya dafe kai yace “Maama dan Allah ki barni da yaran nan, wllh a wata ƙwatuwar mota aka sauketa, ki duba fa irin suturar jikinta sai kace ƴar arna”, Maama tace “nima tashi ka dakeni Nasiru tinda har agaban idona kake kiran ƴata arniya”, Naseer ya fice ya bar ɗakin yayi soro da sauri. Washe gari tinda Hajar tayi sallar asuba bata koma bacci ba, tana zaune tana tilawar Al’qurani har saida gari ya fara washewa sannan ta rufe karatun ta matsi toothpaste a brush ɗinta ta fita tsakar gida, saida ta kusan wurgi da brush din hannunta ganin Sa’adatu da take fitowa daga ɗakin Maama da ɗingishi, fuskarta ta kumbura idonta na hagu ya lume da taruwar jini a gefensa, gefen kumatunta ya kumbura suntum sai kace ta ajiye kwallon goruba a baki, duk da irin saɓanin da suke samu saida ta tausaya mata, jiya da daddare tana jin lokacin da Naseer ya lakaɗa mata na jaki, Hajar ta taɓe baki ta saka slipers dinta ta wuce gaban tukwanen ruwa, ta ɗebi ruwa a buta ta saka kujera ta zauna ta fara goge bakinta, kamar daga sama taji saukar wani mugun ɗaɗe a gadon bayanta, ta gantsare saboda azaba brush ɗinta ya suɓuce daga hannunta……….✍️

Download Hajar Hausa Novel Document By Nafeesa Yusuf Nagoda 

Click the below green button to read the novel online

 READ HAJAR PAGE 6 COMPLETE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button