Novel Document

Mr Romantic Complete Hausa Novel

Description/Story:

Mr Romantic Complete Hausa Novel 

Written By Maman Teddy

 

Description Of Mr Romantic Complete Hausa Novel

RUGAR DAALA

Wani irin Gudu matashiyar bafullatanan keyi a tsakanin dajikan tana ƙara nitsawa cikin garken shanayen da ta fito kiwo dasu, cikin ƙaraji da kuma siririyar Muryar ta a maƙale irin na Fulani take kwaɗa kiran Sunan tumakan da suka shigo ma wurin kiwon ta suna mata ɓanna …. Aradu Wannan Dabba anyi Banza, na kama Wannan Dabba sai na kusa Karya ƙafan sa ko da kuwa na liman ne ba zan raga masa ba. Bin ɗaya daga cikin akuyan da yafi mata ɓarna ta Cigaba da yi tana gudu iya ƙarfin ta a Wannan jejin Fulanin tana tsallake Shanayen ta da ta fito kiwo dasu.

Wani irin ƙatuwar Ƙwazanzama tazo tsallaka wa, wanda sam bata tare da Hasile ta lura ba zanin yayi na ƙasa. Kun san to zanin Fulani musamman na jeji irin Daala Zanin ma a can sama yake kuma ɗan ƙarami.

Cikin wani irin ƙaraji da Hauka irin na Hasile ta yanka ihu tana furta “Yau dabban nan kashe sa zanyi Aradu kowa ya huta”.

Hasile!

Taji Muryar Lamiɗo ya katse ta, cikin sauri Hasile ta Juyo tana kallon Lamiɗo kana tayi saurin kai hannun ta tana gyara zanin jikin ta. Amma gaskiya Lamiɗo ka cika ɗan iska, dama bibiya ta kake yi? Kaine ka turo mun akuyar ashe? Tabbas yau sai na sanar ma liman. dama ana su rabe suna bani labarin zuwan ka binni ka zama ɗan iska aradu.

Cike da gurɓatacciyar Hausan sa irin na Fulani ya fara cewa “A’a Hasile, Ni ban ga komai ba Aradun Allah, yanzu fa zuwa na kenan .! Aradu karya kake yi, tun da kace baka gani ba, to ka gani kuma sai na sanar ma jauro da liman. Juyawa tayi ba tare da ta jira jin mene lamido zai ce ba, shi kuwa lamido gaba ɗaya Hankalin sa ya gama tashi, don har ga Allah bai ga komai daga jikin Hasile ba, sannan ba shi ya turo tumakan ba.

Hasile ..! Ya ƙara kiran ta amma ina ko waiwayon sa ba tayi ba, tuni ta juya tana fara kada shanayen ta tare da masa nisa.

Matsala ta dake kenan ,yarinya bata san komai ba sai Masifa, duk yan matan Fulanin rugar dala babu me kyaun ki, amma Babu saurayin da kike dashi ko guda daya.

Shiru yayi yana kama hannun sa tare da yi kaman mai tunani ne, cike da sakarci irin nasa yace “Oho yanzu na fahimta dalili ashe sharrin ki suke tsoro. Aradu to baki isa ba, sai dai muyi ma juna. Da sauri ya juya yana ɗaukar sandar sa tare da biyo bayan Hasile .

America
1:00am.
Atk massage center!

Wani kyaƙyƙyawan matashin Saurayi ne na hanga ƙwance a gyefen Swimming pool idanun shi a Lumshe suke a wannan tsawon daren yayin da ya Datse laɓɓan sa ta hanyar ɗaura Fararen Haƙoran sa akan su yana ɗan cizawa da’alama yana tunanin Wani Abu mai matuƙar muhimmanci a rayuwar sa. Ko ina na wurin haske ne tamkar rana, haka kowa ke Sharholiyar sa tamkar Rana, Wanda ko ba’a faɗa maka ba a yanayin yanda fuskar sa ke fidda annuri zaka fahimci yana tunanin Abu mai daɗi ne a tasa Rayuwar. Duk da a kwance yake amma hakan bai hanani fahimtar dogo ne ba shal sannan kuma yana da dan ƙiba, sannan fatan shi yana da dan duhu we called him “Tall and black guy”. wanda a hausance mukan kira irin su da Ingarma.

Sunan idanun sa a Lumshe suke amma tun kamin ya buɗe su na fahimci yana da manyan Idanu lulu, Gyefen Kuncin sa da fuskar sa ya aje Saje kaman malam Sheikh, tamkar kuma Wanda yake ba a Ƙasar Turai ba don su basa tara suma haka, wannan ya nunar mana da cewa “Shi mutum ne mai tsayuwa akan ra’ayin kan sa. Choco skin din shi Yafi komai kara masa kyau da kuma jan hankalin yan matan nashi Wanda a cewan sa har yanzu bai ga Wacce zai amince da ita a matsayin Budurwar da ya shirya aure ba. A yanayin sa kaɗai zaka fahimci irin shaiɗanun mazan nan ne masu wahalar da zuciyar yammata da rayuwar su. Duk da kuma kasancewar shi Choco laɓɓan sa Pink ne sosai wanda har tiri suke ƙara yi don yasha fuskantar Hukunci a wurin malaman sa a lokacin da yana matsayin secondary a cewan su Lipstick yake sawa irin na wasu samarin turawan don a kasan Turkiyya yayi primary and secondary school ɗin shi. Daga baya ne ya dawo kasar America da zama tare da iyayen shi… Doctor Maleek Jibo kenan!

Ɗaga kaina nayi ina ƙara ƙare ma wurin kallo bin don sam bai kama da Gida ba sai dai Wurin hutuwa ko sauke Gajiya.

Idanu na ne suka sauka akan wani bord Wanda yake Walwali wasu irin Golden gloves na haskawa tare da rubutaccen harufa din da suke a rubuce kaman haka “Atk massaging Centre”.

Wannan shahararren wuri ne a kasar America da manyan mutane ko matasa ke zuwa don watstsakewa. Inda a hausance zamu iya kiran Wurin da Wurin sauke Gajiya da matsa jiki.
Gyefe kuwa daga bayan Maleek na kalla inda Wata mace ke tsaye a daga bayan shi tana kama Ƙafadunn sa tana matsawa zuwa Bayan sa tana wani irin shafa taffan Hannun ta akan skin din shi. kun sani dama daga massage karuwanci ke shigowa ciki, don asali matattara ne na lalata duk da a irin wannan wuri basu dauki sex a bakin komai ba… Muryar matashiyar baturiyar ne ya katse Ni inda take cewa “I love You Maleek!

A natse ya fara ware Lulun Idanun sa akan fuskar Jenny Wacce take tsaye a gaban sa daga ita sai Pant da bra, Baturiya ce yar kasar London aiki ya kawo ta America. Komawa yayi yana kwantar da kansa akan Resting chair din Wurin yana kai Hannun sa tare da shafa baƙin Suman kansa wanda ya cika yayi Wani irin askin su na matasa gaban yafi bayan cika. Ka rantse da Allah a kasar aka haife shi wato Black America ne. Ganin yasa hannun sa akan Suman kansa yasa Wata da ake kira da Katrina saurin Isa inda yake tana kama hannun nasa tare da matsa masa a hankali don dama aikin su ne yin hakan. Tana wani bin sa da wani abu mai kama da oil perfume.

Lumshe idanun sa yayi yana magana da Hausa ba tare da sun san me yake fadi ba. Wannan itace Ƙaddara ta, tun da na taso mata ke bibiya na, ban taɓa jin Soyayyar kowa ba sai yarinya Ɗaya tak a rayuwa ta…….!

Muryar Jenny ne ya katse shi tana cewa “Maleek please…

Kallon ta yayi yana Ware mata hannayen sa, wanda cikin sauri ta nufi jikin sa tana Hugging din shi tare da kai bakin ta tana Ɗaurawa Bisa laɓɓan sa tana tsotsan lips ɗin shi a hankali, hannun sa yasa yana kama bra ɗin ta tare da matsa tudun su ba tare da ya saka Hannun sa ciki ba. Ashh… ta furta tana sauke wani irin numfashi tare da Furta i really love you maleek Please… Saurin katse ta yayi yana Cewa “Na sani Jenny, nasan kina SO na, amma matsalar Ni ban taba Son ki ba ko sau Ɗaya ban taɓa jin Ina son nayi Rayuwa dake ba.

Idanun ta ne ya taru da ƙwallah. Wanda Ganin yana yunƙurin miƙewa yasata saurin danna Jikin ta bisa nasa tana shafa Ƙirjin shi tare da kallon Ƙwayar idanun sa. Maleek please ka Aure Ni, a shirye nake nabi Addinin ka Indai zaka Aure Ni, zan biyo bayan ka, zan bar kowa nawa don na zauna dakai na rayu da kai har Abada…!

Mr Romantic Complete Hausa Novel txt

File Name   Mr Romantic… Hausa Novel Doc.
Title   Mr Romantic Complete Hausa Novel
Author   Maman Teddy
Group    Ai  Hausa Novels
Genre   Romantic & Luv Story
Published Date    23/10/2024
File Size    300KB
Format Size    TXT
Book Price    ₦500
Phone No   09061466409
Download Mr Romantic Complete Hausa Novel By Maman Teddy

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog

Back to top button