Hausa novels

Fatalwar Delu Part 5

Fatalwar Delu Part 5

🤡 FATALWAR DELU 🤡

 

Part 5

 

Kingboy Isah 👑

 

Short story

 

 

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION

 

 

Aa abu kamar wasa daga karshe ma mashin din kwata-kwata ya daina tashi, kuma mai mashin din ya duba ya kuma tabbatarwa akwai mai. Har turashi sai da mukayi amma dan banzan mashin din nan yaki tashi. Daga karshe dai ya yanke shawarar turashi zuwa wajen wani a garin domin ya duba masa. Tare da Bukar suka tafi gyaran ni kuwa na zauna na cigaba da latsa waya ina jiran dawowarsu. Amma me ba’a fi mintuna biyar ba sai gasu sun dawo a kan mashin din wai suna shan kwana ko wajen mai gyaran basu karasa ba mashin din ya tashi. Cike da farin ciki na tashi na dau jakata a karo na barkatai na sake hawa, ina hawa mashin din ya mutu. Nan take muka fara kallon-kallo tsakanin ni da mai mashin da Bukar. Kowa a wajen da abinda yake sakawa a ranshi, ni dai abun da zuciyata take fada sam ban yarda da shi ba. Wato kenan ni ne idan na hau mashin din yake mutuwa?.

 

 

Yana ta kokarin tayarwa mashin yaki tashi, Bukar yace, “Gaskiya karfen nasara baya da tabbas, dubi fa yanzu ma a kanshi muka zo amma ya mutu yaki tashi, Dan Ladi yi hakuri mu sake turawa zuwa wajen mai gyaran nan a duba mana”. Dan Ladi dake leke-leke a jikin mashin din ya ce, “Ni fa abun nan har ya fara daure mun kai, mashin din nan lafiyarsa kalau babu wata matsala a injin ko wani wajen amma dai muje”. Haka suka sake tura mashin din ni kuwa na sake neman waje na zauna ina jiran dawowarsu. Hallau dai ba’a fi minti biyar ba sai gasu sun dawo a kan mashin din yanzu ma sun kara tabbatar min suna barin wajen ya tashi. A wannan karon na hau ya murza zai tafi kenan mashin din ya mutu. Mai mashin din wanda naji Bukar ya kira da Dan Ladi ya juyo hade da cewa, “Kai Bukar anya kuwa wannan bakon naka ba a jikinsa abun yake ba? Ko ka lura wannan shine karo na ba adadi da sai ya hau mashin din yake mutuwa?”.

 

 

Bukar ya ce, “Wallahi nima na so in fahimci haka, amma sai dai abu ne da hankalina ya kasa dauka”. Ni kuwa sakin baki nayi ina kallonsu, kafin daga bisani nayi wata yar dariya hade da cewa, “Ni bangane me kuke nufi ba, shin mashin din mutum ne da zaiyi zaben wanda zai dauka har ma ace wai nine in na hau yake mutuwa?”. Dan Ladi yace, “Gaskiya ni kam na gaji wallahi dama kasuwa zani ku nemi wani ya kaika hayin gada bakin titi din”. Muna tsaye ni da Bukar ya juya mashin dinsa yayi gaba. Bukar ya ce, “Lalai an sama matsala su uku ne kacal fa masu mashinan haya a garin nan, amma bari muje neman Zubairu idan anci sa’a yana gida sai ya zo ya kaika”. Na amsa mai da to, ni sam ban yarda da abinda suka fada ba na cewa dalilina mashin din ke mutuwa, kawai dai watakil wata damuwar ce a jikin mashin din basu sani ba. Bayan kamar mintuna ashirin sai ga Bukar da mai mashin, bayan mun gaisa da mai mashin din nan take na dau jakata na hau, ai kuwa mai mashin yaja muka tafi, ganin mun fara tafiya na ce, “To Bukar yanzu kuma me zaka ce? Da kuke cewa wai nine idan na hau mashin din can yake mutuwa”.

 

 

Bukar ya danyi dariya hade da cewa, “Ah to wallahi abun ne kusan kamar haka, kai kanka ka lissafa mana sau nawa ne da ka hau sai mashin din ya mutu”. Nan Zubairu mai tukun mashin yake tambayar abinda ya faru na kara masa da bayani shima ya ce sam bai yarda cewa hawana ne yake sawa mashin ya mutu ba, a cewarsa abun hankali ma ba zai dauka ba. Kafin ya rufe baki tayar mashin dinsa ta fara sacewa, nan take yayi parking yana fadin, “Ai kuwa in ba sa’a ba munyi faci”. Haka kuwa akayi muna sauka aka duba tayar gaba tayi faci. Ba shiri muka turo mashin din aka dawo cikin gari domin a face, ni dai raina bai so ba ko kadan. Yanzu har wajen karfe goma da rabi ni da na so ace zuwa yanzu har mun dau hanya, Kauyen Tokulo zuwa Kano ai tafiyar da nisa. Nan dai tare mukaje gun mai facin ya gyara mana muka sake hawa, bamuyi nisa ba mashin din ya mutu. Matsaloli dai kala-kala mune har wajen karfe biyu daga karshe shima mai mashin din ya gudu.

 

 

Tun ban yarda ba har na fara zargin lalai akwai abinda ke faru ba haka kawai wannan mutuwar mashin din ba. Ni dai na ki yarda in mayar da jakata domin na sa ran tafiya gida, dan tun dazun mahaifiyata ke kira ta ji ko na ta so, na ce mata ban samu tahowa ba tukun. Mun sai kunu muna sha na dubi Bukar hade da cewa, “Bawan Allah kasan yadda zakayi da ni fa, kasan dai yau ba kwana zanyi a garin nan naku ba, duk dare sai na tafi gida”. Yayi murmushi hade da cewa “Ai kuwa yau kwana ya kamaka a garin nan, da alamu aljannun da ka kwaso jiya ne basa so ka bar garin nan sai ka kara kwana”. Na kai ludayin kunu baki tukun na dan murmusa na ce, “Kaji ka da wani batu, ni har na manta da batun nan amma kai gashi dake kasa a rai har yanzu kana tune. Amma a ajiye maganar wasa Allah so nake na tafi”. Bukar ya ce, “Ah to ko kana so ka tafi ai ba a kasa zaka tafi ba ko? Tunda dai kaga tunda safe munyi iya kokarinmu masu mashinanma sunyi mana kokari amma abun yaki yuyuwa”.

 

 

Ba yadda na iya haka zancen tafiyata ta shiririce domin Bukar ya tabbatar min idan nace zan tafi a kasa zuwa garin da zan sama motar Kaduna ko Zaria sai nayi tafiyar da ta kai awa daya da rabi a kasa. Ni kuwa na tabbata a rayuwata ko tafiyar awa daya ban taba yi ba, don haka ba zan fara ba yau. Ina ji ina gani har dare yayi ba’a samu wani mai mashin din ba, domin su Dan Ladi kam sun ce ba zasu daukeni ba, duba da matsalolin da mashinansu ke samu idan na hau. Bayan munyi sallar isha’i munci abinci Bukar yace shi wallahi ba zai kwana a dakin nan ba, har nima yake bani shawara wai in bishi dakin abokinsa mu kwana can saboda jaririn jiya. Nayi dariya hade da cewa ni kam ba inda zani ina nan a dakin zan kwana. Ba yadda baiyi dani ba amma naki yarda don haka ya tafi ya barni ni kadai a daki.

 

Fatalwar Delu Part 5

 

Kamar jiya tun kafin karfe tara ta karasa yi naji ana t guje-guje a garin, ni kuwa sallaya ma na fiddo na shimfida a waje ina ta mamakin shegen tsoro irin na mutanen wannan gari. Sai ma da na kalli kudu da yamma gabas da arewa, babu kowa duk sun shige gida sun rufe. Ba abinda nake tunowa sai katti maza abokan Bukar da muka dinga gaisawa da da rana, wato suma harda su a cikin masu gudun fatalwar kenan. Ni dai ba abinda ya sha mun kai na kunna india hausa a wayata sai kallo nake. Can wajen karfe 10 na fara jin sawun tafiya an doso inda nake zaune, nayi saurin juyawa na zata mutum ne ma amma sai naga ashe dabba ne kamar rago kamar akuya duk da akwai farin wata amma ban tabbatar da ko miye ba, don haka na haska da fitilar wayata. Abinda na gani sai da na dan zabura, wani katon bakin karene baki daya baya da kyan gani sai zaro harshe waje yake.

 

 

Yana zuwa saitin inda nake kamar zai wuce sai kuma na ga ya tsaya cik ya juyo yana kallona, idan na ce ban tsorata ba nayi karya, amma a zahiri ko kadan ban nuna tsoro ba sai ma cigaba da haskashi da nayi. Abinda kawai nake tunani, ni da nake cika baki a kan fatalwa idan ya kasance wannan karen ya bani tsoro ai na zama ba namiji ba ma kenan. Don haka na dake, jimawa can karen nan baiyi gaba ba, kuma baiyi baya ba. Ni kuwa ina cigaba da haskeshi da fitila. Da na ga haka sai na dauki takalmi na dan yi barazanar zan jefeshi hade da cewa, “shiiiit”. Haba ai da naji yayi wani irin haushi bansan lokacin da na mike tsaye ba, domin kuwa nasha jin kukan karnuka amma ban taba jin kukan kare mai matukar ban tsoro irin wannan ba. Ga kukan nashi da karfi, nasan dai ko wane kare tsoron jifa yake, amma wannan da nayi yunkurin jifarsa maimakon ya gudu sai na ga yana kokarin yowa kaina.

 

 

Mun dan dade a haka yana yin haushin nashi marar dadin saurare, yayin da ni kuma na tashi tsaye a ta saitin bakin kofa ina haska shi. “Ka ga dan iskan kare, ka tafi uzurinka mana ina ruwanka da ni”. Na fada a lokacin da na dauki sallayar na rike a hannnu sannan na zura takalmina. Dutse na fara dubawa a kasa, ai kuwa nayi sa’ar samun wani a kusa d ni. Barazanar jifa na shiga yi ma karen, shi kuwa duk lokacin da nayi yunkurin jifawa sai ya kara karfin haushin kamar zaiyo kaina. Daga karshe dai na jefe shi da dutsen, amma maimakon ya gudu ai sai yayo kaina a guje. Bansan lokacin da na fada shago a million na turo kyaure na saka sakata ba. Na dan jima a tsaye, ina jin haushin karen yana dukan kyaure amma nayi banza da shi. Ganin ina huci kamar wanda yayi dan banzan gudu, wata zuciyar ta ce wato kare ne ya tsorata ni. Amma wata zuciyar kuwa ta ki amincewa tsoro ne, a cewarta bana so kare ya cijeni ne gashi babu mabugi a tare da ni amma na tabbata karen nan bai isa nayi masa gudu ba. Nan take na fara dube-dube a cikin dakin Bukar, cikin sa’a kuwa naga fartanya a bayan kyaure. Na dauketa na jinjina, kai tsaye naji karfin gwiwar fita waje domin in koyawa karen nan hankali duk da kuwa naji ya daina haushi da bugon kyaure da yake yi……….

 

 

Zan cigaba

Back to top button