Kannywood

Fatima Mai Zogale: Fikirar Rarara da ta yi kama da ta Shata

Watarana ina sauraren wata hira da aka yi da Marigayi Mamman Shata (ba zan iya tuna kafar yada laban ba) na ji yana cewa “idan wakar ta zo, zan yi, idan kuwa ba ta zo ba, ba ni iyawa” (ba hakikanin kalmomin da ya furta ba kenan, amma kusan sakon abin da ya ke nufi kenan). Bayan na saurari tsakuren sabuwar wakar mawaki Dauda Adamu Abdullahi da aka fi sani da Rarara mai taken Fatima Mai Zogale, sai wadancan kalaman na Marigayi Shata suka dawo min a rai.
Na kara tabbatarwa cewa waka ga duk wanda Allah Ya ba ilhamarta, to tana zuwar masa ne a daidai lokacin da Allah Ya so, ba lokacin da shi mawakin ya ga dama ba. Kamar yadda Adam Zango ya furta a wata wakarsa cewa “…..Waka ai baiwa ce,
            In ka iya ta ko, ka dace,
        Don jahili, ba ya waka”……..
Wannan dan waka na Adamu, na nufin Allah ne ke ba bawanSa baiwar waka, ba kuma kowa ne mutum ne ke da irin wannan baiwa ba.
Na tuna lokacin da muna jami’a, muna karatun digiri na farko, malaminmu (Allah Ya kara masa lafiya) Prof Haruna Abdullahi Birniwa, ya ba mu aikin gida cewa kowa ya kawo masa baitukan rubutacciyar waka biyar, sabuwa, wadda ba a taba yin irinta ba, ma’ana kada a kwaikwayi wani ko wata a wakar, a cikin mako daya. Amma cikin mu (dalibai) kusan 30, babu wanda ya iya kawo wannan aikin gida yadda ya kamata, (wataqila saboda duk a cikinmu babu wanda Allah Ya hore wa baiwar waka).
A hirarrakin Marigayi Shata daban-daban da na samu damar saurara ko kalla, na sha jin yana fadin cewa wani mutum ko wasu gungun mutane sun so ya yi musu waka, wasu har kudi sun sha bashi, amma idan wakar ba ta zo ba zai yi ba. Har yana cewa wasu na ganin kamar girman kai ne ko wani abu makamancin haka, amma ba girman kai bane, wakar ce ba ta zo masa. Amma idan wakar ta zo, to ko me ya tarar, zai wake shi, ko min kankantar darajarsa kuwa. Misali, wakar Marigayi Shata ta Dajin Rugu, Hawwa Mai Tuwo Matar Lado, Sarki Bakwai Na Sabon Birni da sauransu.
Wani zai yi mamakin jin Dauda Kahutu Rarara ya yi wa Fati Fatima Mai Zogale waka, ba sabon abu bane idan duk muka yi duba da irin abubuwan da suka faru da magabata a waka irinsu Marigayi Shata. Ko Marigayi Salihu Jan Kidi na taba karantawa a wani wuri (ba ni iya tuna littafin) yana cewa akwai lokacin yana bacci zai ji wakar ta zo, sai yi furgigit ya tashi, ya rubuta, ta yadda zai gabatar da ita idan gari ya waye ko kuma duk lokacin da ya bukace ta.
Sannan masu sukar diyan sabuwar wakar Dauda Kahutu Rarara cewa wai kalmomin ba su hau daidai ba, ai dama na daga cikin ka’idar waka ta karya dokar nahawu muddin kafiya za ta fita yadda ya dace.
Akwai wasu wurare a waka da aka hadu tsakanin Marigayi Shata da Dauda Kahutu Rarara, misali Shata na yin wakoki mabambanta a lokaci daya, ma’ana da ya kammala wannan ya dora kan waccan. Haka Dauda Kahutu Rarara ke kokarin yi, a zama daya yana iya waka daya mai hawa biyu ko uku. Misali lokacin da Shata ya yi wakar Malam Sidi Mijin Hotiho, bayanai sun ce ba ita ce ya zauna ya yi ba, ya yi wasu wakokin kafin Sidi Mijin Hotiho ya zo, bayan ya zo ne, sai Shata ya rero masa tasa.
A bangaren Dauda Kahutu Rarara a misalin wakar Sani Aliyu Danlami
Amshin hawa na farko na cewa’
“…..Hajji Sani dawo Danlami,
Dawo ba mu sake zabe na tumun-dare, hoto….”
Amshin hawa na biyu na cewa’
“…….Mai Raba Alkhairin nan,
Katsina dawo-dawo,
Sani Danlami mun gamsu da alkhairinka…..”.
Kada ku yi mamaki, akwai mutane da yawa (wataqila) da har gobe suke so Dauda Kahutu Rarara ya yi musu, wataqila sun ma bashi kudin, wasu ya amsa, wasu ya ki amsa, amma har yanzu wakar ba ta samu ba, saboda wakar irin tasu ba ta zo masa ba, sai su ga kamar girman kai ne ko raini ya sa bai yi ba. Amma ga shi ya buge da wakar Fati Fatima Mai Zogale da har wasu ke ganin kamar Alkiyamar wakokin Rarara ce ta tsaya. A iya fahimtata, ci gaba ne Rarara ya samu, tun da idan ka tsaya falen daya wato a wakar siyasa kadai, a irin wannan lokacin da ba a buga gangar siyasa ba, sai mawakin siyasa ya ci me? Ko so kuke yi ya koma bara/roko? Idan bai yi irin waɗannan wakokin ba, za a ce ai wakar siyasa kadai ya iya, don haka an gama da shi idan siyasa ta wuce. Amma ko Bahaushe na cewa “gida biyu maganin gobara” kuma idan hagu ta kiya, ai sai a koma dama.
Abdullahi Garba Jani
07034656392
agarbajani@gmail.com
25/04/2024

Back to top button