Zafafa 2023

Cuta Ta Dau Cuta Chapter 42 By Billyn Abdull Complete Novel

*_Typing📲_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

 

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

 

_Shafi na arba’in da biyu_

 

*_WAI KINA SHIRIN WUCEWA NE BAKI KARANTA BA😨._*

*_TO MAZA DAWO BAYA KI DUBA. IN BA HAKA BA ZA’AYI BABU KE NE_*

*_INA KUKE MASOYAN ZAFAFA BIYAR DAMA WANDA BAZU TAƁA SIYA BA SAI DAI SU KARANTA A HANYA_*.

*_MAZA KU MARMATSO KU MALLAKI NAKU DAN GAB JIRGIN YAKE DA BARIN ƘASA. MA’ANA GAB ZAFAFAN SUKE DA FARA SAKAR MUKU ZAFAFAN LITTATAFAN SU NA SABUWAR SHEKARAR 2024_*

*_KAR KUYI MAMAKI IDAN NACE MUKU TAFIYAR FA TA BANBANTA DA BAYA. SABODA SALON NA DABANNE, NA KUMA MUSAMMAN NE_*.

*_TSUTSAR NAMA….!!_*
_(Bilyn Abdull)_

*_AMEENATU_*
_(Mamu gee)_

*_KWANKWASON JIMINA…._*
_(Mss xoxo)_

*_GUDUN ƘADDARA_*
_(Safiyya Huguma)_

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

 

🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥

_______________

……..Cikin jinjina kai Ministar ya ce, “Wlhy ka birgeni, kuma hukuncinka yamun dai-dai. Aure kuwa tare da shi daya hure mata kunne zamu musu in sha ALLAHU. Suje su ƙarata dan ni dai babu ɗan da zai bani ciwon kai in sha ALLAHU Alhaji Abaan. Na kuma gode da wannan karamcin naka. ALLAH yabar zuminci. In sha ALLAHU zuwa weekend zamu shigo mu ganka. Sannan ina sake bada haƙuri da neman afuwa dan ALLAH”.
Murmushi Daddy yay da ɗan harararsa. Daga haka sukai dariya irin tasu ta manya. Cikin kuka Yazeed ya rarrafa kusa da Daddy. Haƙuri ya rinƙa bashi da cewar ya yarda yayi kuskure. Amma dan ALLAH Daddy da Abban nasa su yafe masa. Kuma shi wlhy ba laifin Mimi bane laifinsa ne. Murmushi kawai Daddy yay da shafa kansa da faɗin, “ALLAH yay muku albarka. Ya shirya mana ku baki ɗaya.” daga haka ya miƙe abinsa.

Har mota Ministar yay masa rakkiya. Har lokacin Mimi kuka take na fitar hankali Ministar dake riƙe da hannunta na lallashinta. Shi ya sakata a mota da kansa, yayinda Daddy ya shiga mazaunin driver abinsa. Ko a hanya duk kuka da magiyar da take masa baice da ita uffan ba. Makaranta ya maidata. Ta fashe da kuka zata fara roƙonsa ya daka mata tsawa da faɗin, “Get out of my car my friend!!”. A rikice ta fita jikinta na rawa. Ko kallonta bai sake yi ba yay reverse ya fice ya barta anan tana kuka. Office ya nufa bayan yay kiran Awwal ta waya yace ya samesa can. Dan dama da safen ya kira shi akan basai yazo kaisa Office ba zaije wani waje da kansa…

★★★

Kuka sosai Khadijah keyi da jin hukuncin da mijin nata ya yanke akan tilon ƴarsu mace. Cikin sake ƙarfin kukanta ta ce, “Hamma dan ALLAH kada kamin haka na roƙe ka. Wlhy zai iya zama fiye da Dafeeq a gareta. Ƙarya yake ba sonta yake ba ƙuruciya ke ɗibarsu. Wlhy daga ita har shi basu da hankalin tantance dai-dai da akasin sa. Hamma zai cutar mana da yarinya ne kawai amma ba sonta yake ba…..”
A fusace, matuƙar fusace Abaan ya katseta da faɗin, “To yaya kike so nayi ne Khadijah! Na barsa ya lalatamin rayuwar yarinya a saman titi ne ko mi? So kike na matsa na hanasu tarayya wataran ya jata su gudu. Tunda har Fatima zata iya fita a gidan nan a dalilin namiji yaya kike tunani idan nace sai sun rabu. Kima kanki adalci mana dan ALLAH Khadijah. Wlhy idan yarinyar nan tabi yaron nan suka gudu zuciyata zata iya bugawa. Na fiki jin wannan tsoron, dan tun daga jiya zuwa safiyar yau hatta da bugun zuciyata ba dai-dai yake ba. Ni bazan iya jure abinda su Baba suka jure akanki ba Khadijah, dole ne na ɗauki matakin da zai zame min masalaha dan bazan iya jurar rasa yarinyata ba, zan aura masa ita, suje hakan zai fi bani kwanciyar hankali akan ace sun bijire mana zuwa wata duniyar..” hawayen dake neman zubo masa ya sashi kasa cigaba da maganar. Sai kawai ya juya ya shige bedroom dan dama a tsaye yake, ya shige yana ƙoƙarin maida hawayen.
Da kallo Khadijah da tun furucinsa na (Ni bazan iya jure abinda su Baba suka jure akanki ba Khadijah) hawayenta suka tsaya cak. Illahirin jikinta ya shiga rawa. Dan ba ƙaramin ratsata waɗan nan kalaman sukai ba. Sai zuciyarta ke gaya mata kamar fa gori mijin nata ya mata. Gori yake mata akan abinda ta aikata da ya zama ya shafi ƴarsu a yanzu. A take ta sake fashewa da wani matsananci kuka. Domin wannan shine karo na farko da irin wannan babban saɓanin ya shigo tsakaninsu. Bawai basa samun saɓani ba. Wannan dole ne a gidan kowane aure na kowace ƙabila. Amma a tsahon shekaru goma sha takwas da aurensu bata jin Abaan ya taɓa ɗaga mata murya irin haka, dan shi ko faɗa zaiyi yakanyi ne cikin yanayin sanyinsa da rashin hayaniya. Amma a yau yanda yake ihu mata akai ta tabbata hatta yaransu dake ƙasa duk suna jiyosu…
Ilai kuwa hasashenta yay dai-dai, dan ta iske Auta da Fharooq na kuka sosai a falon ƙasan. Yayinda take jiyo muryar Muhammad a ɗakin Mimi yana mata masifa yana kuka da ƙalibalantarta akan yau a dalilinta ga iyayensu suna ɗagama juna murya. Yayinda ita kuma take kuka kamar ranta zai fita. Ji Khadijah tai hajijiya na neman kwasarta, dan komai ya gama rikice mata tama rasa ina zata dafa.

Al’amarin kamar wasa sai abu ya zama babba. Dan gaba ɗaya a cikin satin gidan dake kamar aljannar duniya ha ma’abota rayuwar cikinsa ya zama kamar wani gidan mutuwa. Magabatan Yazeed sunzo. Dan Ministar da kansa tare da vice president da ƙanensa biyu sunzo neman auren Mimi kamar yanda Alhaji Abaan ya basu dama. Bai kuma ja komai da nisa ba duk da raɗaɗin da yake ji a ransa na rabuwa da yarinyarsa da bata gama mallakar hankalinta ba suka gama komai hatta ranar ɗaurin aure. Dan gaba ɗaya wata biyu kacal ya saka musu a lokacin su Mimi na cikin hutu. Aifa ranar sosai Khadijah ta birkicema Alhaji Abaan akan itafa bata yarda ba, bata amince ama Mimi aure a wannan shekarun ba. Dan tana matuƙar tsoron ɗiyarta ta faɗa a makamanciyar rayuwar data faɗa itama. To anan nefa rikici ya ɓarke. Alhaji Abaan yace bata isa ba. Babu fashi zai aurar da Mimi dan haka shine kwanciyar hankalinsa. A gefe kuma Mimi na kuka da roƙon Daddyn nata akan yayi haƙuri kada yay mata aure. Ita wlhy bata son aure a yanzu. In dai Yazeed ne ta rabu da shi har abada. Ko saurarenta ma Daddy baiyi ba. Ranar ma data ishesa da magiya da kuka a karo na farko na tarihi ya faffaleta da maruka biyu da suka matuƙar gigita mata rayuwa. Dan abu ne da bai taɓa faruwa ba. Duk rintsi Alhaji Abaan baya dukan yaransa. Wani lokacin ma idan suka ƙure Khadijah ta dakesu har haushi yake ji. Yafi gane ya zaunar da yaro ya masa nasiha idan yayi ba daidai ba. Amma a ranar sai da Mimi ta samu rabonta har ana ganin shatin hannunsa a farar ƙyaƙyƙyawar fuskarta mai tsananin kamanni da tashi. Aunty Noor ta shiga zancen itama tana beging yayan nata. Amma a karo na farko yaƙi saurarenta akan shifa babu fashi akan aurar da Mimi. Idan sunga zasu je su fara shiri matsayinsu na iyaye suje su fara. Idan kuma bazasuyi komai ba daga an ɗaura aure zai ɗauketa shi kaɗansa ya miƙata gidan miji ne.
Komai ya caɓe, ƙura ta tashi sosai da ya kai har rashin jituwa yasa a karo na farko Khadijah tai shiri ta wuce Kano. Kai tsaye kura ta nufa wajen dangin iyayensu. Inda takai ƙarar Abaan wajen kawunan ta. Aranar ta dawo cikin Kano ta yada zango a gidan Ni’ima. Inda suka tattauna tare da ita da Zuhrah da mazajensu dake tamkar ƙanne ga Alhaji Abaan ɗin. Basu ɓoye mata ba sun fito fili sun sanar mata kuskurenta na tun farko ko muce maimaita mata tunda kowa ya daɗe da tabbatar mata wannan tun iyayensu nada rai. Suka kuma nuna mata kar taga laifin Alhaji Abaan da yawa a tsorace kawai yake dan yana ganin tarihi zai fa iya maimaita kansa Mimi tabi Yazeed su gudu kamar yanda itama tabi Dafeeq a wancan shekarun. Bata ko musa ba wajen amsar laifinta, ta kuma yi kuka ta sake nadama da roƙon gafarar iyayensu da suka jima da kwanta dama. Haka dai washe gari suka ɗunguma suka koma Abuja wajen Alhaji Abaan, sai dai ita bata bisu ba nan suka barta a Kano ɗin.
Suma dai sun je sun zauna da Alhaji Abaan tare da lallashinsa da ban haƙuri musamman ganin yanda Mimi itama ke kuka da magiya da roƙon yay haƙuri ta tuba. Dan yanda yarinyar ke a firgice har asibiti aka kwantar da ita na kwana biyu. Duk ta zabge ta rame ta sake yin haske abin tausayi. Ga ƴan ƙannenta ababen farin cikinta sun juya mata baya gaba ɗaya. Musamman ma Muhammad da yafi kowa ɗaukar zafi da ita kasancewar yafi sauran ƴan uwansa wayo. A su ɗin ma dai Alhaji Abaan ya murje idonsa, sai ma haƙuri da ya basu akan shifa yana akan bakansa dan babu fashi. Garama su faɗama Khadijah ta dawo in zata dawo. In ko ba hakaba za ai bikin Mimi ko bata nan. Waɗan nan kalamai nashi sun sake tada musu hankali. Dan dole fa suka komo Kano jiki a sanyaye. Sunta lallashin Khadijah akan ta haƙura kawai ta koma ta barsa yay abinda ya tsara akan ƴarsa. Dan ya riga ya hau sama irin yanda kowa bai san ya iya fushi haka ba. Kuka ta dinga musu dan gani take ita kowa fa baya hango abinda take lurar dasu. Tana tsoron a aurar da Mimi Yazeed ya dawo yaci dunduniyarsu kamar yanda Dafeeq ya mata. To bayan dai sun sake tattaunawa dabarar zuwa ga Baba Hakimi ta zo musu. Haka sukai shiri suka ɗunguma garin Adamawa. Inda suka je suka tattare komai suka sanarma Baba Hakimi daya ƙara tsufa sosai. Haka dai badan yana jin ƙarfi ba suka kwashesa zuwa Abuja. Shine yay zama da Khadijah da Abaan da Mimi, sai da ya gama jin komai sannan yay murmushin su na manya. Sannan ya sallami Mimi ya fara magana da Abaan da Khadijah. Sun tattauna sosai inda daga ƙarshe ya sa Alhaji Abaan ɗin kira masa Ministar da ɗansa Yazeed aka sake sabon zama harda Mimi. Wannan zama shine ya kawo masalaha a tsakani. In da Baba Hakimi ya kawo masalaha akan komai. Yazeed zai yi haƙuri Mimi ta kammala secondary ɗinta. A lokacin shima karatunsa yay nisa. Amma da sharaɗin bazai sake zuwa ya ɗauketa a school ba ko ya fiddata daga gida bada sanin iyayenta ba. Zai dinga zuwa hira wajenta akowane ranar juma’a da yamma, zakuma suyi hirar ne a nan falon gidansu.
A take Yazeed ya amince. Dan shima hankalinsa a tashe yake sosai da yanda Mimi ta birkice masa tamace su rabu, ta kumayi blocking nashi a waya da kowanne account nata na media. Shi kuma harga ALLAH so da ƙaunarta yake na gaskiya. Ya kuma fahimci wawtarsa da kuskurensa saboda mahaifiyarsa ta masa faɗa sosai kasancewarta mace mai dattako. Anan dai aka sasanta komai aka dai-daita zancen biki ya fasu…

Bayan ɗan fushi da shashshare juna na kusan sati guda bayan sasantawa Alhaji Abaan da Boddonsa suka shirya kansu. Suka kuma sake ɗaura ɗammarar jan Mimi jikinsu. Yayinda a ɓoye Alhaji Abaan yay mugun sakama Mimi ƴan leƙen asiri ako ina da zata iya kasancewa. Haka itama Dr Khadijah ba’a barta a baya ba wajen sakama ƴar tata idanu. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har Mimi ta kammala karatunta na sakandare. Yayinda Yazeed ma ke cigaba da nasa karatun. Abin kuma birgewa bayan ta kammala ɗin koda aka tada batun aurensu sai sukace ba yanzu ba sai Mimi ta fara karatunta na Jami’a, shi kuma ya kammala nasa. Hakan yayma iyayensu daɗi sosai, musamman kasancewarsu duk ƴan boko dama. A haka Mimi ta fara karatu a jami’ar, tana lavel 200 Yazeed ya kammala nashi karatun. Ya shiga hidimar bautar ƙasa. Yana kammalawa Babansa ya sama masa aiki mai tsoka, bai zauna ba ya sake shirin joining masters nashi. Zuwa lokacin soyayya ce mai ƙarfi da shaƙuwa a tsakanin Mimi da Yazeed. Ga zuminci ya sake ƙulluwa a tsakanin iyayensu fiye da da. Dan yanzu in ma baka sani ba saika ɗauka Yazeed ɗin ɗan gidan ne. A dalilin Masters da Yazeed zai wuce abroad aka yanke shawarar saka bikinsu. Daya dawo za’a sha biki Mimi ta ƙarasa karatunta a ɗakinta.
Haka kuwa ne ya faru, dan shekarar Yazeed ɗaya da wasu watanni ya dawo gida Nigeria. Inda aka shiga shirye-shiryen biki na ƴan gata. Dan daga ango har amarya iyayensu duk masu hannu da maiƙo ne. Kafin kace mi zance auren waɗan nan iyalai biyu ya karaɗe shafukan sada zumunta. Inda aka shiga biki na nunama tsara. Amarya da ango duk sun sha ƙyau. Komai suke zaka fahimci cike da so da ƙaunar juna ne. Hakama iyayensu na a cikin matuƙar farin ciki da ganin wannan rana a gare su. Dan Khadijah tayi kuka har bata san iyaka ba. Ansha shagali amarya ta tare ɗakinta. Inda tabar iyayenta da ƙannenta da kewa. Duk da ma zuwa yanzu duk ba zaman ƙasar yaran suke ba saboda karatu. Auta ne kawai a gida sakamakon bana ya kammala nashi secondary ɗin shi. Shima dai ana shirye-shiryen miƙashi abroad ɗin ne……..✍️

Click Here To Read Cuta Ta Dau Cuta Chapter 43 By Billyn Abdull

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

 

🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥

 

 

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

 

Back to top button