Hausa novels

Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 36 By Hafsat Bature

💋KURKUKUN ƘADDARA💋

E36

Daga alƙalamin Boss Bature writer of Abban sojoji

Angel ce ta fara farkawa, A hankali ta É—ago da kanta daga saman Æ™irjinshi, ras taji gaban ta ya faÉ—i ganinta ajikin danish, sam ta manta meya faru jiya, waro ido ta É—anyi tare da sanya tafin hannunta ta rufe bakinta, Gyaran miryar Da haris yai mata ne yasa tayi wuff ta sauka daga saman jikin danish ta koma gefe É—aya, Ta yi tunanin zata ga haris shi kaÉ—ai amma sai ta gansu kaf É—insu kewaye dasu, Tawaga guda, sun baza na mazurinsu suna kallon Ikon Allah, Muryarta na in ina tace”Am..kun..gane..jiya..um” bata Æ™arasa maganar ba, Batool tace”Ai mun riga mun gane komai ba sai kin yi mana bayani ba,” azeeza tace”Æ™warai kuwa, Aljanu ne suka kawo ku nan, koba haka ba”? Ta yi tambayar tana kallon faces É—insu Hannah, har suna haÉ—a baki wurin cewa eh, wani kallon rainin wayau taga suna Yi mata, Kafin ta Æ™ara furta wani abu, danish ya farka yana kokarin buÉ—e idanuwanshi, Biji biji yake iya ganinsu, Haris yakai hannu ya bugi Æ™afarshi”tashi ka yi mana bayani, meya faru a daren jiya,” gaba É—aya jikin shi kasala yake Ji, YunÆ™urawa Yayi tare da miÆ™e wa zaune, a lokacin idanuwan nashi sun washe yana ganinsu, One by one ya dinga binsu da kallo, sai wani sakin murmushi suke Yi kamar sabbin mahaukata, É—auke eyes É—inshi yae daga kan fuskokinsu, Ya mayar dasu kan angel da tayi wuÆ™i wuÆ™i da ido, Suna haÉ—a ido dashi, ta fara zazzaga mashi masifa”Duk kai kaja mini ina zaman zaman lafiyata, Tun farko basai da nace Ka koma É—aki ka kwanta ba amma saboda kafiya irin naka kaÆ™i jin maganata, Ka nace saika kwana anan, Ni banma yarda dakai ba, kaine ka janyo ni jikinka, har bacci ya É—auke ni, saboda rashin tsoron Allah, gashi kaja min zunubi,” tun da tafara faÉ—a suka zuba mata ido suna kallonta, Ita fa gani take kamar suna zargin wani abu, yayin da su kuma basu kawo komai aransu ba, saboda ilminsu bai kai nan ba, Abun ma burgesu Yayi, don su a wurinsu ba wani bane don mace ta haÉ—a jikinta dana namiji, sun saba ba tun yanzu ba, saboda haka suka taso suna rungumar junansu, abu É—aya ne basu yi neman junansu, shima saboda basu da shauÆ™in sha’awa kwata kwata, an cire masu shi, amma fa suna Æ™aunar junansu sosai, sai ma mutun ya yi tsammanin akwai soyayya asakaninsu, Alhalin nan kowa babu wannan aransu, Kawai Æ™aunar juna ce,

“Angel ki daina Æ´an kame kame, Mun riga mun san komai,” harara ta jefa ma hanna da ta yi maganar tace”Me kuka sani? Idan ma wani abu ku ke zargi to shine ke da laifi ku tambaye shi ku ji,”a Æ™ule tayi maganar, shi dai baice komai ba, idonshi na akan fuskarta,

Parveen tace”danish ka faÉ—a mana gaskiyar abunda ya faru? Dagaske ne Kaine silar komai? ÆŠaga mata kai yayi alamar eh, saboda gudun jarabar angel,

Javed yace”Ni ban yarda ba, Nafi zargin Angel, Cos danish bazai ta6a kawo ki nan ba, sai dai ko kece kika biyo shi, wama ya sani ko faÉ—a ne ya haÉ—a ku, ” miÆ™ewa tsaye angel tayi”Ni kun ga tafiya, Ina da abun yi” Takai karshen maganar tare da Juyawa ta Nufi toilet ta buÉ—e ta shige, Jamlock ta sanya ta datse Æ™opar, kafin ta le6e tana sauraron me suke cewa,

“Danish faÉ—a mana gaskiya, Meya faru daren Jiya a tsakaninku? Ya akai kuka baro É—aki kuka dawo nan”? Batool ce ta jera mashi tambayoyin, angel dake la6e ta yatsina fuska aranta tace”Wannan batool É—in sai kace Æ´ar jarida, ko ina ruwansu da abunda ya faru adaren jiya in ban da gulma da son jin kwakwaf mtsww”taja tsaki daga Æ™arshe,

Tana Jinsu suna ta tambayarshi ya faɗa musu, Amma yaƙi basu amsa sai dai ce musu ya yi, ya manta komai, bazai iya tunawa ba, dole suka haƙura da tambayarshi, Ajiyar zuciya angel ta sauke, a fili tace yayi ma kanshi ƙiyamul laili, dama Bata son ya faɗi ne don kada ajinta ya zube, su ji cewa itace ta biyo shi don ta ba shi haƙuri,

Bata fito daga Cikin toilet É—in ba, sai da ta yi wanka, A waje ta samu Su haris suna Jiran Na cikin toilets É—in su fito su ma su shiga ko sun samu su yi wanka, Wuce su ta yi zuwa Cikin É—akin, Babu kowa duk suna a can sai ita kaÉ—ai, daga gefen gadonta ta zauna, bakomai ya faÉ—o mata acikin ranta ba face Deeja, Ko awani hali take ciki yanzu Allah wa’alamu, É—aga hannayenta sama tayi cikin harshen labarabci ta soma jero addu’o’i tana karanto da niyar Allah ya tsare musu Æ´ar uwarsu, tana Cikin Yin addu’ar taji yo motsin buÉ—e Æ™opar É—akin tsohuwa, da sauri takarasa shafa addu’ar, Ta juya tana kallon Æ™opar, tsohuwa ta fito daga cikin É—akin, hannunta ruÆ™e da sanda, fuskarta a harmutse baka Iya gane awani yanayi take, haÉ—a ido su ka yi da angel, da buÉ—ar bakinta sai cewa ta yi”Ba zaki zo ki gaishe ni ba”? MurguÉ—a mata baki angel ta yi tare da cewa”Mutanan kirki nake gaisarwa, ba masu matattar zuciya ba” bazawarin murmushi tsohuwa tasaki, haÉ—i da girgixa kai tace”kin tsane ni kamar mutuwarki” angel tace”fiye da haka” dariya tsohuwa tayi,
“Idan ba ki son ganina to ki kwantar da hankalinki, nan badajimwa ba, Zaku daina gani na,” babu yabo ba fallasa angel tace”Da munji daÉ—i wlh, kwara mu daina ganinki, tun da dama babu amfanin da kike yi mana, sai sai kawai kullum ki leÆ™o da Æ´ar sanda a hannu,” wannan maganar ta angel ba Æ™aramar dariya ta bata ba, Musamman data kwatanta yadda tsohuwa ke leÆ™o wa da kanta,

“Ba zaki yi kewata ba”? Ta jefa mata tambaya, angel tace”Kin ta6a ganin anyi kewar maÆ™iyi? To idan ma ana yi ni bansani ba, Ni dai burina shine ki fita arayuwar mu, saboda baki da amfani, ” hannu takai ta É—auki pillow Ta É—ago dashi tana nuna ma tsohuwa tace”Kinga wannan matashin kan na hannu na? wlh yafi ki amfani yafi ki daraja da Æ™ima a wurin mu, ai ke dake da waccan tukunyar fulawar ta Cikin toilet É—in mu baku da banbanci,”

Tuntsirewa tsohuwa ta yi da wata irin mahaukaciyar dariya hhhhhhhh, da gudu su Hannah suka shigo cikin É—akin sakamon Jin sautin dariyar tsohuwa wanda yajawo hankalinsu, A tsakiyar É—akin suka tsaitsaya suna Kallonta, ÆŠauke ido tsohuwa tayi daga kan angel ta mayar dasu kansu Batool tace”Kuma bazaku gaishe ni ba”? Maimakon su gaishe ta, Sai suka juya suna kallon angel, Tsohuwa tace”ba shakka, Uwarku kuke Jira ta baku Umarni kenan”? Shiru suka Yi basu ce mata komai ba, Still idonsu na akan angel data maÆ™e musu kafaÉ—a alamar kada su gaishe da ta ita, Shigowa cikin É—akin mazan su ka yi gaba É—ayansu duk sun yi wanka, Suna Æ™arasowa inda tsohuwa take, cikin girmamawa Danish Ya É—an russuna tare da gaishe da ita, hakan ba Æ™aramin fusata Angel yayi ba, har saida taja dogon tsoki,

Dogara sanda tsohuwa ta yi zuwa inda danish yake a tsaye, Ta miÆ™a hannunta É—aya ta shafa sumar kanshi tace”Albarka zata tabbata akanka, Yarona, ina matuÆ™ar alfahari dakai, Saboda kai na musamman ne, Zan yi kewarka sosai” Cikin sanyin murya danish yace”meyasa kika ce haka”? gajeran murmushi tsohuwa tasaki kafin tace”Bakomai,” ta ambaci hakan tare da kallon su Batool dake a tsaitsaye cirko cirko tace”Ko kaÉ—an banji haushi ba da kuka Æ™i gaishe ni, Saboda bancancanci hakan ba, Naji daÉ—i da ku ka nuna min cewa Kun girma kun mallaki hankalin ku, zaku iya tafiyar da rayuwarki even without me,” tana kai karshen maganarta, A sukwane ta juya tana dogara sanda ta nufi É—akinta, Har ta kusa shiga sai kuma taci burki, kamar an dakatar da ita, a hankali ta waiwayo baya ta kalli angel dake zaune tana hura hanci, tace”me ma ki kace? Dani da tukunyar fulawar dake acikin makewayin ku bamu da banbanci”? ÆŠaga mata gira angel tayi alamar eh, dariya tasaki tana girgiza kai tace”Tukunya fulawar dake a makewayinku tafi ni mahimmanci Angel, Ku dage da bata ruwa akai akai, Furannin dake Acikinta zasu Yi tsuro su girma, gwanin ban sha’awa,” tana faÉ—in hakan ta juya ta karasa shigewa cikin É—akinta, taja Æ™opa ta rufe,

Ta6e baki angel ta yi tare da watsa hannayenta tace”Abanza” batool tace”bansan meyasa naji jiki na yayi sanyi ba, sai naga kamar bamu kyauta ba da muka Æ™i gaishe da tsohuwa” Harara angel ta watsa mata”Ae sai ki bita cikin É—akin ki gaishe da ita, Ni ko me matar can zata yi wlh bazan ta6a girmamata ba, muguwa azzaluma macuciya kawai da ita,” Cikin sanyin murya danish yace”Ki daina angel badai dai bane, ita tamkar mahaifiya ce agare mu, koda ace kuwa muguwace ita, saboda tafi iyayen mu, idan har dagaske suna araye kuma su ne suka yi silar zuwan mu nan” daÆ™yar ya kai Æ™arshen maganar, ganin tana nuna shi da yatsan hannunta”Kai ka kiyaye ni! Wato raini ya fara shiga tsakanina dakai saboda jiya mun kwana a shimfiÉ—a É—aya ko”? yadda tayi maganar ba Æ™aramin dariya taba su batool ba, Haris yace”Da alama Jiya kunji daÉ—in baccin nan, shiyasa muka taras daku a manne da juna, Yadda kasan ANTA da JINI,’ dariya su hanna suka saki, Angel kuwa tasha mur, tana jifar danish da harara, murmushi ne ya bayyana akan fuskar danish, tana Æ™unÆ™uni tace”zamu haÉ—u” juya mata Æ™eya ya yi, batare da ya tanka mata ba,

Azeeza tace”Ni dai bari naje toilet, In zuba ma fulawar nan ruwa, Saboda tsohuwa tace mana tana da amfani” ruÆ™o wuyan rigar azeeza haris Yayi”Zo nan Sullu6iyo, Ke har kin yarda da maganar ta? Bayan irin Æ™arairakin da take gaya mana? Shin idan kin bama fulawar ruwa ta girma, wani amfani zata yi mana? Ko É—ibarta zamu dinga yi muna ci ne”? Yayi tambayar yana LeÆ™en fuskarta, Gatsina mashi hanci ta yi, tare da cewa”Oho, Nima bansani ba,” ta faÉ—i hakan tare da buge hannunshi, Ya zame daga ruÆ™on da yayi mata, Hanna tace”Dama ita mashiririciya ce narasa me ke damun azeeza, Kwakwalwarta gaba É—aya shirme ne acikinta, saboda rashin aikin yi flower zaki je ki zuba ma ruwa? bubbuga Æ™afa azeeza tayi rai a6ace tace”To wai ina ruwanku dani ne? Bani naji zan iya ba, Sai ku Æ™yale ni,” Da É—an tsoki ta Æ™arasa maganar,

Parveen dake ta faman Yin hammar yunwa tace”Dan Allah ku yi shiru, Surutunku Yana Æ™ara HarzuÆ™a Yunwar Ciki na,”

Rubina tace”damuwarki kenan, abinci abinci, Kowa dai da abunda ya ishe shi,” Haris yace”Ni kuma damuwata deeja, ” Yana faÉ—in hakan gaba É—aya walwalar dake akan fuskar kowannan su ta canza zuwa damuwa,

“Ba kai kaÉ—ai ba haris, Gaba É—ayan mu mun damu da deeja, tana acikin ran mu, Mun yi shiru ne saboda bamu da yarda zamu yi, damuwa ko yin kuka bazasu ta6a dawo mana da ita ba, HaÆ™uri Shi ne yakamata mu yi, Sai kuma mu bi ta da addu’a, Allah Ya tsare mana ita aduk in da take” Angel ce tayi maganar a yayin da ta miÆ™e daga saman gadonta, walking Slowly Ta nufi inda suke a tsaitsaye itama ta tsaya, Jikin kowannan su Ya yi sanyi, shessheÆ™ar kuka azeeza ta fara, aikuwa haris ya daka mata tsawa tare da cewa”Zaki yi shiru ko saina buge maki baki? Ƴar rainin wayau, yanzu kika gama zancen bama flower ruwa amma daga jin anyi maganar Deeja kin wani 6are baki zaki ma mutane kuka ke da kika fi kowa Æ™aton baki acikin mu” idamuwanta cike tab da kwalla take kallon haris, sai kuma ta duÆ™a Æ™asa ta É—aura kanta saman guiwowinta ta fashe da kuka, girgiza kai danish yai idonshi akan na haris, Shi ma haris din kallon nashi yake yi, don yasan dole ya tanka mashi, Saboda sanin halin shi na rashin son ana 6ata musu rai, musamman azeeza kodan yana ganinta Æ´ar Æ™arama ne acikinsu,

Tunkafin danish yace wani abu haris ya riga shi cewa”Its ok Bazan Æ™ara ba, amma itama ta daina Yi mana kuka” Azeeza dake a tsugunne tana kuka ta É—ago da kai Cikin shessheÆ™a tace”Bazan daina ba, In ka tashi ka kashe ni, Kuka yanzu na fara” yanayin yadda ta yi maganar taso basu dariya,

Matsawa angel tayi kusa da azeeza, Ta sanya hannayenta biyu ta É—ago da ita, tare da rungumeta ajikinta, tana lallashinta, Cikin Æ™anÆ™anin lokaci azeeza ta yi shiru, kamar wadda ta samu jikin mahaifiyarta, ta lafe ma angel, hada zagayo da hannayenta biyu abayan angel ta Æ™anÆ™ame, Batool dake kallonsu ta saki murmushi, tare da cewa”gwanin ban sha’awa,” angel tace”kema idan kinaso kizo in rungumeki” kafin batool ta bata amsa, Hanna tace”Ni baki ta6a rungume ni ba ajikin ki” Tun da hanna tace haka gaba É—aya sauran Ƴan matan suka ce suma bata ta6a yin hugging É—insu ba, Lokaci É—aya ta ji gabanta ya faÉ—i rass! Da sauri ta sanya hannayenta Biyu ta janye azeeza daga Jikinta, Hannunta na dama ta É—aura saman Æ™irjinta a saitin zuciyarta, Yayin da la66anta suke kerma, Hankalin su Hanna ba Æ™aramin tashi ya yi ba ganin irin canzawar da angel ta yi, Ji su ka yi ta fara ambaton”Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un”! har suna haÉ—a baki wurin tambayarta lafiya, Girgiza kai ta É—anyi tare da cewa”Bakomai kawai bana Jin daÉ—i,” Tana kai karshen maganarta, Jiki na kerma ta koma gefen gadonta, duk sunata kallonta,

Haris yace”Yakamata Mu je mu zauna, kafin giants su kawo mana abinci,” hibba tace”Yau bazamu motsa jiki ba”? Parveen tace”Sai mun ci abinci tukunna,” Basu kai ga zuwa sun zauna ba, Sai ga Giants sun shigo kawo musu abinci, Bayan sun sauke abincin Jiki na rawa kowannansu Ya samu wuri ya zauna saman dining carpet, Suna tsaka da cin abincin Angel ta miÆ™e suka tambayeta Harta Æ™oshi sun ga bata Ci dayawa ba, tace masu ta Æ™oshi, gaba É—aya sun lura da yanayinta, kamar bata Jin daÉ—i, ko bayan da suka kammala Cin abincin giants suka tafi, Agaban Gadon angel suka je suka tsaitsaya Suna kallonta, Ta kwanta idanuwanta na fuskantar ceilling, cikin nuna damuwa suka tambayeta ko lafiya tace musu babu komai su kwantar da hankalinsu, Badan sun yarda da maganarta ba suka Æ™yaleta kowa ya koma saman gadon shi ya zauna, Yau ko motsa jikin basu samu sun yi ba, saboda canzawar da angel ta yi musu, tana daga kwance ta kasa kunne tana jin muryoyinsu suna fira, parveen tace”idan angel ta gudu damu, zuwa gidansu, Shikenan mun huta da ganin giants, Zamu sakata mu wahala, Kuma zamu dinga fita yawo, Wlh ni duk na Æ™osa inga ya wajen kurkukun nan yake, Nasan zaiyi kyau sosai, kuma zaifi daÉ—i,” Azeeza tace”kuma ta faÉ—a mana cewa daddynta zaiso mu kamar ya’yanshi, hada sauran Æ´an uwanta ma, mu ma zamuyi rayuwa kamar kowa, ” can kuma tajiyo muryar javed yana cewa”dama kun daina wannan mafarkin da bazai ta6a zama gaskiya ba, In banda abunku taya za’ai ku fita daga Cikin kurkukun nan? kuna tunanin Giants zasu Barku? haris yace”faÉ—a musu dai, Nima jinsu nake kawai, Ni bana so ma suna Æ™wallafa rai akan son Yin rayuwa awaje, saboda suna wahalar da zuciyoyinsu ne, ita kanta angel É—in da take Sanya musu rai, bata da hanyar da zata Iya ku6utar dasu” Hanna tace”Amma ae ta faÉ—a mana cewa, Idan muka dage da addu’a, muna kai kukan mu wurin Allah, Zai ji Æ™anmu ya taimake mu, Mu fita cikin kurkukun” koda tayi wannan maganar sai haris Ya tuntsire da dariya tare da cewa”Taya kenan hakan zata Iya faruwa? Wannan fa ba gaskiya bane…..” Bai Æ™arasa maganar ba, sakamakon Tsawar da angel ta daka mashi, a yayin da take Æ™oÆ™arin miÆ™ewa daga saman gadonta, Hankalinsu duk ya dawo kanta, Harara ta wurga mashi tamkar Æ™wayar idanuwanta zasu faÉ—o Æ™asa, Muryarta da rauni tace”Ya isa haka haris! Bana so kana shiga hurumina, kuma Ka daina Æ™aryata magana ta! Idan kai baka Yi imani da Allah ba, Su sunyi, Kuma in sha Allahu zamu samu mafita ne bi’iznillahi, ka zuba ido ka gani” Jinjina kai haris yae fuskarshi É—auke da murmushin rainin wayau, yaso ya mayar mata da martani, Amma danish ya dakatar dashi ta hanyar yi mashi magana, gyaÉ—a kai ya yi tare da jan baki Ya yi shiru,

ÆŠakin Ya yi tsit babu mai magana, wuraren marece, Duk sun kwanta saman gadajensu, wasu sun fara bacci, yayin da wasu kuma sun lumshe idanuwansu ne badan suna jin bacci ba,

Damuwar duniya ta ishi angel, Ga wani irin faÉ—uwar gaba da take ji, tarasa gane dalilin hakan, addu’o’i kawai take janyowa Acikin zuciyarta, Tana ji aranta kamar wani abune zai faru, wasa wasa suna kwancen nan har dare Ya ratsa hasken É—akin Ya yi duhu, tun tana iya jiyo hirarsu suna faÉ—in har yanzu ba’a dawo da deeja ba, har tadaina Jin surutunsu alamun sunyi bacci, Aranta tace”ita kuma wannan Makauniyar rayuwar haka zata Æ™are? Kullum muna Æ™unshe a É—aki ÆŠaya tsawon shekara da shekaru, Gaskiya bazai yiyu ba, Nifa ina da burikan da nake son Cimmawa don haka bazan zauna in zuba ido ba, dole in nema ma kaina mafita, tana karasa zancen zucin nata, ta yunÆ™ura ta sauko daga saman gadonta, Cikin duhu ta shiga laluban Fitilun É—akin su, ko da ta É—auko fitilar bata kunnata ba, saboda gudun kada Danish ya farka daga bacci Ya bi bayanta, Cikin sanÉ—a taci gaba da tafiya ko sautin tafiyarta baka Iya ji, tana shiga sashen toilet É—in Abakin door ta kunna fitilar, Ta buÉ—e toilet ta shiga ta zura jamlock, A Æ™asa ta sauke fitilar, Ta É—auko bokitin Æ™arfen nan, ta Ajiye shi jikin bangon da tagar Nan take, saboda ta sa mu tsawonta yakai, Daddagewa ta yi tare da haye saman bokitin, tana yunÆ™urin kai hannu ta zame glass É—in muryar danish Ta ratsa kunnata
“Angel!” ras taji gabanta Ya faÉ—i, gaba É—aya jikinta ya hau kerma, tsantsar 6acin rai ne ya bayyana akan fuskarta, a tsiyace ta juya saitin Da yake tana kallonshi, A tsakiyar toilet É—in taganshi A tsaye, tun kafin yai magana ta riga shi cewa”kai nifa nagaji, Don me zaka dinga faÉ—o mini cikin toilet? Bayan ka yi mini alÆ™awarin cewa bazaka Æ™ara shigowa ba?

Cikin sanyin murya yace”Ina Bibiyarki ne saboda sanin Æ™udirin da kike dashi na son shiga Cikin prison, wanda yin hakan zai iya haddasa mana shiga mummunan haÉ—ari, ” Har saida taji gabanta Ya faÉ—i, jin abunda yace, Da mamaki tace”Oh dama kasan abunda nake son yi kenan? Taya akai ka sani?

“kawai naji araina ne, kina son ki dura ta tagar, ko last time dana Sauke maki glass, Ban yarda da abunda kika faÉ—a mini ba, na cewa bakya son kallon glass yana affecting É—inki, da ace dagaske ki ke, to da tun lokacin kin kawar da shi daga Cikin toilet É—in amma sai baki yi hakan ba, ” Ya Æ™arasa maganar a yayin da yake tunkararta, Runtse ido ta É—anyi tare da cizon lips É—inta, Rai a6ace tace”wlh duk bala’in ka baka isa ka hana Ni yin abunda nayi niya ba, kada ka kuskura kace zaka ma dakatar dani, idan har ba so kake In yi maka Illa ba”

“Angel Na roÆ™e ki kada ki je, Zaki jefa rayuwarki da tamu Cikin hatsari, Ba’ayi musu leÆ™en asiri, Ki fahimce, yafi muyi rayuwarmu Cikin duhu akan musan ainihin abunda ke faruwa acikin prison, amma daga ranar da kika haura tagar nan, xaki ja mana ne gaba É—ayan mu ne”… Tamkar zai fashe da kuka Yake yi mata magiya akan karta dura, A Æ™arshe daya ga ta kafe tasa naci akan saita dura, ai kuwa da Æ™arfi Ya sanya hannu ya janye bokitin da tahau sama, Gaba É—aya ta tafi zata kife Æ™asa da sauri ya sanya hannayenshi biyu Ya tarbo ta, ta faÉ—o saman jikin shi, Suka rubza Æ™asa atare, kanshi ba Æ™aramar buguwa yai ba, ita kuwa kamar jira take yi su faÉ—o aikuwa ta daddage ta dunÆ™ule hannayenta, Ta shiga kai mashi bugu a Æ™irjinshi, Ya yi shiru batare daya dakatar da ita ba, zuciya ce ta fusgeta, a karshe ta kifa kanta saman Æ™irjinshi tana kuka tana faÉ—in”Ya rabu da ita taje, Ita ta gaji da rayuwar kulle, Bazata Iya jure azabtar da Æ´an uwansu da ake Yi ba, ” HaÆ™iÆ™a Danish yaji tausayinta, Sai dai bazai Iya barinta taje yin leÆ™en asirin ba, saboda shi ya fita wayau da hankali, Ya kuma san Abunda sai biyo baya, Idan har ta dura ta tagar nan,

Tuntana yin kukan har tagaji tadaina muryarta ta disashe, Sai lokacin ya samu damar yunƙurawa Ya ɗago da ita a jikinshi, A saman kafaɗarshi ya kwanto da ita, ranƙwafa yayi tare dakai hannu ya ɗauki fitilar da tazo da ita, Ya juya ya fuce daga cikin toilet ɗin, Yana shiga ɗakinsu Ya kwantar da ita saman gadonta, Daga ƙasa ya ajiye fitilar hannun shi, Ya zauna daga gefenta yana kallon fuskarta, Wadda ta yi jaga jaga da hawaye, hannayenta ya ruƙo acikin nashi, ya soma lallashinta, ya ɗauki tsawon lokaci Amma ko kallo bai isheta ba, Sai da ya gaji don kanshi tukunna Ya ƙyaleta, Ya koma nashi gadon Ya kwanta, A daren ranar daƙyar bacci ya ɗauki angel,

Ranar da Deeja ta Cika 4 days da aka É—auketa, A daren Ranar Giant Ya dawo da ita, Babu wanda ya sani duk sunyi nisa a cikin baccin su, A tsakiyar É—akinsu Giant Ya sauke ta, Baiwar Allah duk ta fita hayyacinta ta rame ta fige, kamar wadda aka É—ibi naman jikinta, kasancewar sun kunna fitilun É—akin su, Hakan ya bata damar bin Cikin É—akin, Bata nufi ko’ina ba sai bakin gadon angel, a gefe gadon ta zauna, fuskarta sharkaf da hawaye, hannu takai saman shimfiÉ—ar angel ta É—an bubbuga kafadarta, Ƙasa kasa da murya take ambaton sunanta don kada ta takura ma masu yin bacci, koda angel taji muryar deeja acikin baccinta, a matuÆ™ar ruÉ—e ta yaye bargonta, muryarta na kerma tace”deeja! Dagaske kece? Ko dai mafarki nake yi,” jinjina kai deeja tayi cikin shessheÆ™ar kuka tace”its me angle, am back, Giant ne ya dawo dani, na same ku kuna bacci, bana so na tashi kowa shiyasa nazo wurinki, saboda akwai abunda nake son faÉ—a miki,” Tun da angel taji haka, Sai ta yaye bargon dake a jikinta, Ta kalli fuskar deeja da kyau, Gaba É—aya ta zabge Duk ta bushe, janyota tayi zuwa jikinta ta rungumeta sosai, kamar zata maida ta cikin cikinta, Tayi matuÆ™ar yin kewarta, Sun É—auki tsawon lokaci, Kafin angel ta raba jikinta daga na deeja tace”Ki faÉ—a mini menene? Deeja tace”za’a iya jin mu idan muka Yi magana anan, amma zan shiga toitet, sai ki biyo ni” angel ta amsa mata da toh, MiÆ™ewa deeja ta yi jiki duk ba Æ™wari ta shige toilet, angel ta miÆ™e ta bi bayanta, bayan sun shiga, deeja ta sanya jamlock ta datse Æ™opar, ta juyo suka fuskanci juna ita da angel,

“FaÉ—a mini menene kikeson Gaya mini? Duk na Æ™agara inji” Cikin shessheÆ™ar kuka deeja tace”Angel yanzu na Æ™ara yarda da maganarki na cewa ana cutar da rayuwar mu, wani iko na angel, Duk da bakomai zan iya tunawa ba, Amma lokacin da giant ya tafi dani, ina Cikin hayyacina, Inata karanta addu’ar nan da kika koya mana acikin zuciyata, Har yakai ni wani part inda wasu jerin daÆ™una suke, Bayan ya shiga dani É—aya daga cikin su, duhu ya mamaye idanuwana, ban iya ganin komai sai dai biji biji nake gani, Har lokacin ban fita hayyaci na ba, Sai dai bana iya gani da kyau, Naga mutun shida wanda ba baÆ™aÆ™en kaya bane ajikinsu kalar na giants, naga launin Ja a Æ™ugunsu, angel daga nan ne na fita hayyacina, bansan me akayi mani ba, Sai dai naji ajikina an cutar da rayuwata, nayi kukan mutuwa, Na azabtu iya azabtuwa, ” Deeja nakai karshen maganarta, Ta zube saman gwiwowinta, tare da fashewa da matsanancin kuka, kamar ranta zai fita, Hankalin angel yayi matuÆ™ar tashi, duk da bata ji me mutun shiddan nan suka Yi mata ba, amma tana ji aranta cewa Lalata suke yi dasu, idan har zata iya tunawa, can lokacin baya,Ta ta6a yunÆ™urin guduwa daga islamiya zata je gida, Tazo giftawa ta ofishin head master É—insu, Tajiyo shessheÆ™ar kuka, da kuma maganganun mutane, duk da Æ™arancin shekarunta a time É—in tana dab da shiga 11 years, Har zata wuce ta la6e ta kasa kunne tana sauraronsu, É—aya daga Cikin É—aliban makarantar ne aka samu wani malami yayi ma fyaÉ—e ya kuma cigaba da lalata da yarinyar da bazata wuci shekara sha bakwai ba batare da sanin kowa ba, idan tazo islamiya aka tashi sai ya É—auketa saman mashine É—inshi zuwa gidanshi da ya gina da niyar yin aure, amma sai ya 6uge dakai yara yana 6ata musu rayuwa tare da yi musu barazana, Mahafiyar yarinyar ce ta fara lura da canzawarta, Bata iya tafiya Æ™afafuwanta sun gwame, ga yawan yin amai, da su ka kaita asibiti likita ya tabbatar musu cewa Æ´arsu Cikine da ita, iyayen yarinyar sun shiga damuwa, bayan sun baro asibiti sun dawo gida, mahaifiyar yarinyar ta É—auko wuÆ™a ta É—aura akan wuyan yarinyar tayi mata barazana akan ta faÉ—a musu wa yake yin lalata da ita har ta samu ciki, in ba haka ba zata kashe ta, atsananin tsorace yarinyar ta faÉ—a musu cewa malaninsu ne na islamiya, Koda jin haka sai suka tasa Æ™eyarta gaba suka zo makarantar don su tabbatar da abunda ta faÉ—a musu, A lokacin angel bata fahimci komai ba, amma ta naÉ—i komai a acikin kanta, sai yanzu da Deeja ke faÉ—a mata wannan maganar ta soma tariyo abunda ya faru da É—alibar nan ta makarantar islamiyarsu, duk da bata da tabbaci akan hakan amma tana zargin Suma lalatar ake yi dasu, ‘ ZuÆ™unnawa ta yi agaban deeja, Ta sanya hannayenta biyu ta rungumota ajikinta, Lokaci É—aya ta fashe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, itama deejan kuka take yi sosai, ta Æ™anÆ™ame angel da hannayenta, Abun da ciwo idan har ya tabbata cewa lalata ake yi dasu saboda rashin imani kuma a lokacin da suke Yi jinin al’ada, 😭😭😭

(Akwai Sauran free pages amma yakamata ku fara yin payment, nayi kokari dai na baku book one kyauta, nima sai ayaba mini, Masu son shiga paid group na Facebook sun tuntu6i 08169856268, for whatsapp 08103884440) kuÉ—in book É—in 500 ne, ta bank ake turawa koda pos, in mutun baida account, idan Æ™aramar wayace in ka tura kuÉ—in zaka fadi sunan me banki ko mai pos din za’a duba. alert,*3196407426*
Bature Hafsat Muhammad
First bank

*Zaka tura da shaidar Biyanka ta wannan Numbers É—in (0816985 6268) ko kuma ta (08103884440)

Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete

 

 

( mu hadu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya, masu yi mun ya jiki ina godiya)

Back to top button