Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 60 The End Hausa Novel

Zaune suke a cikin ƙayataccen hall ɗin da ake shan hidimar bikin Autan Mammi da Autar Ammi waenda duk yanzu suka zama shalelen Ammi kuma angwayen ma duka ‘ya’yanta, Ryan na zaune bisa wani table riƙe da hannun Afeefah sun yi azabbaben kyau cikin outfit ɗinsu na Soire party wanda english party ne duk mazan shigar suite suka yi matan english dress, Farin suite ne jikinshi da baƙin shirt daga ciki bakin takalmi da baƙin hankey da ya ɗan leƙa bakinshi daga aljihun, gashin shi ya sha gyara ainun fuskarshi sheki yake kowa ya ganshi ya ga cikakken namijin da yake cikin kwanciyar hankali da jin dadi.Tana sanye da wani doguwar riga na tsadadden sugar lace da ya bayyana cikinta da ya taso yayi mata kyau ainun, ta saka gyale da ya tafi da kayan tayi wrapping kanta ta sha make up da ya matuƙar zama mata wanda mijin nata ke ta bacin rai akanshi don kishi ya sa ko motsi tunda suka zauna basu yi ba su Saleem sun ta kiranshi ya ƙi zuwa sai Sulaiman ne yake representing ɗin shi, gabansu Suhail da Suhaila ne shigan ryan shine irin na Suhail haka Suhaila ma irin na Afeefah sai suka ba da wani kyau mai ma’ana. Zarah ce da yanzu ta sake saboda janta da su Abeeha ke yi a jiki kuma tayi tuban gaskiya ta zo ta ja su Suhaila don tana kaunarsu su ma kuma sun sonta, Afeefah ta kalli Ryan “Ya Saraki..!”A Shagwaɓe tayi maganan ya kalleta “Matar Masu Sarauta ya aka yi?”Yayi maganan yana ɗage mata gira tace “Eyyaa dubi ana yi wa Adda Abeeha barin kudi in je in manna kaɗan mu yi hoto?””Wanda kuka yi kan ku zo nan ya isa ba za ki shiga cikin maza ba”Ta ɗan ɓata rai har ma nadamar Kwalliyar take ji yadda ya kasa ya tsare dama bikin duk ya hanata wani hidima yadda ta so cin uwar sabada sai dai ta ga su Samha na yi don duk Fombina suka zo har Sadiqa da ake hidimar aurensu tare sun zabi su zo nan in za’a ɗaura aurenta sai ta koma tunda sai an ɗaura na Saleem an kai mishi matarshi zai ba da nata.Har su kawu sun zo bikin da Inna Asabe sun bar inna Larai a gida, kawu ya sauya ƙwarai natsuwa ta shige shi haka Inna Asabe da inna Larai babu wannan rawan kan da son zuciyar sam sam sam.A bikin ne ma take samun labarin Sabrina da iyayenta inda ta kwaso HIV da ya kasa warkewa ga talauci da yayi musu katutu ita Gaje garin zuwa boka nema mata waraka ta faɗo daga tsauni sai gawa aka ɗauka Yaya ne ya zo neman tuba wurin mommy kuma ta yafe musu.”Assalamu Alaikum warahmatullah”Wata ƙawar Aisha ce ta yi musu sallama, Afeefah ta kalleta da mamaki don ta kula yarinyar na ji da uban ta wani ne tun fara bikin sai rawar kai take bata zaci Rayyan zai wani kula ta ba sai ta ji ya amsa, a take wani abu ya taso mata zuwa wuya wato ita ce bata da kishi shi ya hanata tashi saboda maza ita kuma tana kallonshi yana magana da wata macen.”Yayanmu barka dai, mun jima muna kallon irin kokarin ka akan rayuwar matasanmu a koyaushe His Excerllency ba shi da zance sai taka gaskiya samun shugaba irinka abin alfahari ne in kuwa da irin ku rayuwar matasanmu ba zai taɓarɓare ba”Ya san mahaifinta Gomna ne mai ci a yanzu don haka yana martaba gidansu sai ya ɗan murmusa”Thank you””idan ba damuwa ga wannan na jima ina so na baka ban samu ganinka ba Its a small gift don Allah kar ka ce a’a”Ta ajiye wani karamin paper bag tayi murmushi ta juya ta wuce.Kaman an ce ya kalli Afeefah ta haɗa gabas da yamma kudu da arewa, idanunta har shekin kwalla su ke, hannunshi dake cikin nata ya ɗan murza don ta kalleshi amma ta ɗauke kai sai ma ta miƙe chadak ta nufi waje, da sauri ya bi bayanta yana dan kiranta amma bata waiga ba dab wurin mota ya riƙo damtsen hannunta a hankali ya janyota bayanta ya sauƙa kan kirjinshi yana dan lekan fuskanta yace “Tsaya mana Boɗɗi fushi kika yi?”Fuskarta babu walwala ta janye tare da Juyowa ta kalleshi “No, Meyasa zan yi fushi?””Me yasa kika fito to ina ta magana kin ki kulani?”Ta kalleshi “Gashi na kula ka, ina jinka”Numfashi ya sauke “It seems kin gaji mu tafi gida”Ta juya ta nufi motarshi bata ce komai ba, numfashi ya sauke yana ɗan shafa gira ya nufi motar tuni ta buɗe ta zauna ya shiga shima drivern shi ya ja suka nufi ɓangaren su tunda akwai tafiya sossai, hannunta ya riƙe ta zame tare da juyawa tana kallon Window.”Akwai abinda ya faru ne? Ko na miki ba daidai bane?””Babu, me kuwa zai faru?””Ta ya zan sani Afeefah na ga kina fushi”Ta ɗan bashi side eye tana sake juyawa”Ni ba fushi nake ba”Lip dinshi na kasa ya ɗan lasa har ga Allah bai zaci wai kishi take ba a hankali yace “Ok”Ya kalleta sai ya ga ta sake haɗa rai ya sauke numfashi har suka isa ta sauƙa tun kan ya zagayo ya buɗe mata.Ɗakinshi kai tsaye suka nufa don suna shiga parlorn ya riƙo hannunta, bata ga amfanin make up ɗin ba bayan hotunan da suka yi musamman nata dashi da yayi kyau ainun hannunshi kan cikinta yana murmushi yalwatacce ita kuma tana kallon hannun nashi tana murmushi wanda har ta mayar wallpaper to bayan shi bata ga amfanin adon ba.Wanka ta shiga bayan ta goge Kwalliyar shima ya kwaɓe ya bi bayanta, tana tsaye shower ta ji ya manne da ita yana bin wuyanta da tafiyar tsutsa, zamewa take har ta gama ɗauraye jikinta ta fice ta bar shi ya bi bayanta da kallo, bata wani tsaya drying kanta ba ta duba shirt din shi ta saka don tana jin daaɗinsu sossai ta zame towel ɗin tana bottuning shirt ɗin da iyakarshi rabin cinyarta ya fito ɗaure da towel a kugunshi da wani irin kallo yake binta ganin ta nufi bakin gado ya isa ya kama hannunta “Kina so ki yi mura ko?”Bata tanka ba yaje ya ajiye ta gaban madubi ya zaro hand drayer ya shiga busar mata da gashin cikin kulawa.Miyau take hadiyewa tana bin ginannen jikinshi dake bayyane da kallo, ganin zai kalleta ta ɗauke kai yayi murmushi ajiye drayer ɗin yayi ya duƙa sossai yana shunshunar wuyanta da baya rabo da kamshin da yake masifar so, a yanzu har da lips ɗin shi yake goga mata zuwa sajenshi da ya sa duk numfashi na kwace musu barin ma shi da yake a kunne, hannunshi ya mayar ta gaban rigar nashi dake jikinta ya fara unbottuning saman shirt ɗin yana sauke wahalallen numfashi mai rikitarwa.”Ya Saraki ka bari, bacc…”Hannun da ya tura cikin rigar ya sa ta ɗauke numfashi ganin zaunen ba zai kai su ba ya ɗagata chadak zuwa gado yana ƙarasa unbottuning shirt ɗin, tun tana resisting har ta sallamar suka rikice a duniyar masoya sai da komai ya kamallah ta zame za ta sauƙa ya dawo da ita yana shafa lallausar Fatan bayanta “Kika cigaba da fushin nan zuciyata za ta iya shiga matsala Ya Alami” (Duniyata)Yana cigaba da shafata a natse ya cigaba “A faɗa laifina in yi gaggawar tuba kin san Sameer mai biyayya ne a fadarki”Ta ɗan yi murmushi ta isa? Sarkin gobe ya zama bawan ta?”Shine har da yiwa wata murmushi a gabana har da karɓar gift ɗinta””O’ooo am very sorry ban san dalilin fushin ba kenan, kin fa san babu macen da take da daraja ko kima a idanuna bayan ke da Ammi, Afeefah ke ce mahadina daga ke kuma Ryan ya gama kallon ‘yanmata”Wani sanyi ne ke kwarara mata yana mata son da bata san adadin shi ba, ɗagowa tayi ta mayar da kanta kan pillown da yake sai ya juyo suna kallon juna tace “Na sani ba zaka taɓa zama da mace daya ba amma na rasa Meyasa duk sadda wata macen ta kallar min kai sai in ji mutuwa ne kawai ya saura mini tsabar zafin zuciya”Yayi murmushi yana riƙo hannunta a tsakiyarsu “Wa yace miki hakan?””An ce sarakai ba sa zama da mace ɗaya””Za’a fara a kan Sameer Muhammad Modibbo don daga ke na rufe kofa a gidana”Soyayyarsu suka cigaba da sha yana bata duk kulawarshi ta so ta tafi Kd ya hana don haka ta mayar da hankali kan lectures ɗinta da kulawa da shi da kuma cikinta har Allah ya kawo ta watan haihuwa, wani ranar Alhamis da dare labour ya saka su nufar asibiti babu shiri a safiyar juma’a ta santalo katoton ɗan ta fari tas mai kama sak da mahaifinshi wanda a ranar BOƊEJO ta sha kuka ganguna da kalangu sun yini dokawa kowa ya gifta Masarautar Fombina sai ya san ana cikin alkhairi dumu-dumu.Yaro ya zo da tarin alkhairi don Mai martaba ji yake kaman ranar ne ya fara riƙe Sameer a hannunshi tuni lungu da saƙo sun samu labari hotunan kuwa har ya je Kaduna uwar jego ta sha ƙauna iri iri, ko da suka dawo masarauta sashenta take wata dattijuwa ta shiga hidimar kula da ita da bata cikakken kulawa na masu jegon gargajiya, ranar suna an yi bidiri Aisha ta zo da cikinta kuwa haka sulaimi ma ta zo da nata tamfatsatsen cikin Haihuwa yau ko gobe sai Jannah da take shirin zuwa amma labour ya hanata itama a ranar sunan ta haifi danta namiji, Abeeha ma na fama da laulayi aka yi hidimar suna na ji da gani kuwa yaro ya ci suna Muhammad Sameer Modibbo.A daren sunan Rayyan ya tafi Kaduna don da Jannah ya yini, Ammi ma da kanta ta tafi da wasu hadimai duk basu dawo ba sai da aka yi suna suka bar mata hadimar da zata kula da ita mai martaba ya aika sha tara na arziki inda yaro ya ci sunan Rayyan.Bayan sunan Muhammad da suke cewa Arham Sulaimi ta koma da sati biyu itama nakuda ya tashi mata sai dai she didnt survive bayan ta haihu Allah ya karbi ranta sun shiga tashin hankali dole Afeefah suka tafi Kadunan duk sun yi jimamin mutuwar ba kadan ba, inda Sameera ta samu Saleem ta roƙe shi ko don ‘yar da ummu sulaimi ta bari tana so ta auri Sulaiman ta shayar da yarinyar kaman na ta.Kan Sulaiman ya amince Umman shi ta amince aka daura musu aure kuwa babu wanda ya hanata shan kwayoyin da ruwan nono ya zo ta shiga kula da ummu sulaimi ƙarama don soyayyar da take yiwa Sulaiman shi ya dawo kan yarinyar kuma tana haƙuri don auren mijin matacciya wanda yake son matarshi sai a hankali. Baaba jummai da Afeefah kaman jiƙa da kaka don kusan kullum suna tare a waya kuma Daga ita har Rayyan da su Ammi su kan yi mata sha tara na arziki don kaman uwa take har a gidansu Sulaiman ɗin ba ‘yar aiki ba.Rayuwa ya cigaba da juyawa ba za’a ce ba’a saɓawa ba sai dai duk abu da fahimtar juna ba karamin lasting yake yi ba, sossai rayuwar Afeefah yake kan saiti har aka wayi gari ta gama karatu inda ranar da ta gama last paper ɗinta ta shigo masarautar ta sauƙa a sashensu kawai ta ga wata hadaddiyar tsadaddiyar Maybaach Ash Color an yi mata ado da furanni, Rayyan ta gani ya fito cikin kyakyawar shiga fuskarshi ɗauke da smile yace “Congratulations Allah ya albarkaci abinda kika karanta My baby mama”Tsallen murna tayi fuskarta dauke da fara’a ainun ta karbi keyn ta buɗe motar sai taga balloons na zubowa kaloli daban daban Juyowa tayi rungumeshi cike da farin ciki take cewa “Thank you so much My love, My best friend, My for ever, My safe space. Thank you for being you and choosing me everyday..” kan yayi wani motsi ko magana sai ta fara jin tashin trumpet ana yi mata congratulations tana juyawa ta ga abokan arziki na kusa da na nesa ta ma rasa yaushe suka zo kuma ta yaya?Ameer da Abeeha sanye cikin shiga iri daya Abeeha na rungume da ɗiyarta mai sunan Mammi ana kiranta Mamah bata wuce shekara da wata biyu ba, Jannah da Rayyan ɗinta da yake ma wurin shekara uku da wani cikin a jikinta, Saleem da Aisha da suke riƙe da wani Rayyan ɗin dan wata huɗu kacal, Sameera na tura ciki ga Ummu sulaimi da tayi wayo sossai gefen ta Sulaiman, ga Samha Amarya wacce bikin ta ne next suke ta planning don abin bai zo da wuri ba, sossai take murmushi tana kallonsu yayyenta ne, Ƙawayenta ne kuma ‘yan uwanta ne… Hawaye taji ma tana ji a daidai sadda su Suhail su uku cikin shiga iri daya na kananun kaya suka zo suka rungume ta.”Congratulations Ammah”Ta ɗaga Arham ta na dariya sossai take cewa “Thank you love, na gode sossai”Rayyan ya matso yana dauke mata hawayen farin cikin da take, nan suka isa parlor abincicikka da cakes iri daban daban an ci an sha an yi hira kaman ba gobe, Rayyan dai baya cewa komai sai murmushi dama sun riga sun san hali Afeefah ce mai shan maganarshi idan ta ciyo shi.Sai dare suka watse ta fito cikin shirin kananun ƙaya wani half gown purple da ya amshe ta ya fitar da duk wani sura na jikinta, parlorn su kaman ba shine dazu kaca kaca ba hadimai sun gyare tsaff an cika turarukan wuta, ɗakinshi ta nufa bayan ta duba yaran sun yi bacci yana yana operating Phone ɗin shi hankalinshi ya ɗan dauku a chan jikinshi ba riga, tana isa ta sa hannu ta zame wayan ya ɗago ta jefa wayan kan gado tana murmushi sai ya saki baki yana kallon rigar na jikinta da ya fito da full chest ɗinta daga sama, rabin cinyanta duk a waje gashinta a ɗaure wuri guda sai sheki yake tana ta zuba kamshi bakinta da ta sa wani lilac lip gloss sai sheki yake, hannu ya wara mata ta kuwa tafi a slow suka yi baya baya tana kwanciya nashe nashe akan jikinshi don babu inda ya taɓa katifa a nata jikin, da hannunta take wasa da kirjinshi idanunshi a lumshe ya ce “Boɗɗi””uhmm Boɗɗin Boɗɗi”Idanunshi da suke ta lumshe wa a mayen ƙaunarta ya buɗe don sunan ya mishi daaɗi ‘kyakyawan mai kyau'”I love the name””kai wani suna ne baka so?”Yayi murmushi mai sauti “Ai duk sunayen ne daga kin faɗa sai sun motsa zuciyar maza”Tayi murmushi tana tuna lokacin da yake mata masifa in ta kirashi Saraki ta ce “Shiyasa baka son na ce Ya Saraki?”Ya ja iska kadan yana furta”Aouchhh sunan ya fi taɓa ni but sincerely wani irin fusgata yake zuwa gareki in kika faɗa cikin wannan voice din naki mai daaɗi”Tayi murmushi yana zame ribbon ɗinta ya cusa hannunshi cikin gashinta ya ce “Faɗamin abu mai daaɗi””I love you”Ya tsinci kanshi da lumshe ido yana jin kalmar straight to his heart.”Faɗi wani””Ina sonka!”Tayi maganan tana wasa da sajenshi cikin susa mai daaɗi.”Sake faɗamin””wani waƙa Naji da ya dace da kai in rera maka?”Gira ya ɗaga ta gyara kwanciyar ta akan jikinshi ta shiga mishi wakan “ka sace zuciyata! Kana kai mini gatah!Mata nai musu rata..Ka ce in je in hutaaa..Ga mijina mai tsafta Mai halin girma na sarauta Zama da kai sam babu wahalta..!Cikin mazaje ka cire tutaaa Mai adalci da nagarta..!Fushinka shi ke sa ni ɗimautaaa Mai haƙuri shi ke dafa dutsseee!!”Numfashi ya sauke muryarta wane sarewa haka ya buɗe idanunshi da suka mace a so yana kallonta a hankali yace “hakane kam mai haƙuri shi ke dafa dutse, nima na cire tuta tunda na same ki”Tayi dariya mai yanayi da giggle ya juya ta yana shunshunar wuyanta ta zura hannunta gashin shi tana ɗan kame jikinta tace “Toh ai ban gama waƙar ba fa Boɗɗin Boɗɗi”Ɗagowa yayi yayi pecking lips ɗinta chan ƙasa yace “Toh ƙarasa Babylove””Kaine tsanina…maqabulina!!Kai ne rabin raina… Makasudina!!Kaine muradina.. Kai neFarin cikin raina… Kai ne Al’amari babba… Kai ne Abin da duk zan ma.. So neMurmushi in kai kyau neeee”Ya kuwa doka murmushin yana rasa wani baiti ne ma ya fi daaɗi, bakinsu ya haɗe ya shiga aika mata zazzafar Kiss cikin kiss ɗin ya ɗan zame yace “Nima ke ce farin cikin raina, ke ce muradina kuma ke ce rabin raina My Hayateee… Help me mu samu Mammin mu a daren nan”Kaman jira kuwa ta sakalo wuyanshi tana mayar da Bakinta cikin nashi.*BAYAN TSAWON LOKACI*Afeefah ce ke saukowa jirgi hannayenta rike da wasu ‘yan mata kyawawa biyu, bayanta Suhail ne da Suhaila da za su yi shekara shidda zuwa bakwai sai Arham da yake huɗu da ‘yan kai bayansu wasu hadimai ne guda biyu da suke taimakonta da yaran har zuwa wani prado baƙi wuluk a jere motocin huɗu suka fice daga airport ɗin sai fadar Fombina wanda a yanzu Laamiɗo Sameer Muhammad Modibbo ne ke kan mulki, Ƙashin bayan matasan Fombina, jagoran al’umma kuma jarumin Afeefah uba ga Ciroma Arham da ‘yan uwanshi Garkuwa Fulanin duk Nijeriya.Isarsu tamfatsatsen sashen na Fulani Afeefah ana ta baza gaisuwa da ban girma tana amsawa cikin kulawa da kaunar al’ummar nasu kaman yadda suke masifar ƙaunarta, Ɗaya daga kyawawan yaran nan mace tace “Ammah mun dawo mu je wurin Abbu? I Miss himmmm?”Girgiza kai Afeefah tayi “Abbu na cikin taro Alhan, ki bari anjima idan ya dawo sai ki ganshi ko Mammin Abbu?”Ta ɗan tura lips Ɗayar tace “Ammah to mu je wurin Jadda?””Ku fara yin wanka Ahlam sai ku je na san ta yi missing surutunku”Da gudu suka yi ɗakinsu daman yan mazan sun jima da wuce wa yanzu haka bai wuce sauri suke suyi wanka su tafi wurin Abeey ba dake ji da su.Ɗakinsu ta wuce ita da mijinta don bai wani yarda da raba sashe ba tunda har yau bai yarda ya karbi auren wata ba duk kuwa da tallar da ake mishi tun kan Abeey yayi murabus ya bashi har yau, ya ce duk abinda zai nema ya samu a wurinta to na me zai sake aure? Me kuma zata bashi banda ta nemi daga mai hankali? Afeefah na iya kokarinta wurin ganin ta bashi Kulawa, soyayya da lokacinta bata aikin komai banda gidauniyarta kuma duk ba ita ke kula da komai ba sai in ya kama don haka tana da lokacinshi full kuma bai taba neman ta ta ƙi ba a koyaushe burin ta ta faranta mishi ko da har ranta bata so.Tana zame kayanta ta ɗaura towel zata shiga wanka kawai taji an yi hugging ɗinta kamshinshi da numfashin shi ya sanar mata waye, fuskarta washe da murmushi tace “Sarakina””Matar sarki, barka da dawowa ga masoyinki”Ta waigo tana Shagwaɓe mishi “Ba wani bayan ka gudu ka baro mu Abuja””Kin san ba da son raina bane hakan da a sona na ne da kowa ya tafi ya bar mu mu biyu a duniyar nan”Dariya tayi Yace”Ya taron na ganku a Tv i hope komai ya tafi lafiya?””Alhamdulillah wannan kam ya ƙare saura na Lagos”Girgiza kai yayi “Babu inda za ki je, ki wakilta wata ko wani su je miki”Karkata wuya tayi “Har kaduna? Ka ga fa akwai sunan Ɗan Samha ga yaye ɗalibai da za’a yi a gidauniyarmu na Dutsen-wai karo na wurin bakwai akwai kuma taron buɗe wani a Anchau”Girgiza kai yayi “Ba zan juri nisa dake ba, wai har ma gidauniyar nan nawa za ki buɗe ne?”Tayi dariya yana daukar ta chak suka nufi toilet don yayi mata wanka yana tambayarta Ammi da Mamminshi fa tace sun tafi sashen Jaddansu(Ammin)Suka shige cikin bahon wanka suna cika juna da kauna, tana daga cikin matan manya da ake ji dasu saboda taimako, iya ado da shigar kamalarta, haƙuri da iya maganar ta don duk tayi magana a taro sai ya kwana biyu yana circulating platforms, karama ce mai halin girma kaman yadda mijinta yake ƙarami cikin sarakunan yankunan Arewa sai dai akwai zuciya da kwarjini, idan suna tafiya a tare za ka zaci ɗawisu ne yana baza ado gaban ‘yar budurwar ɗawisunshi, komai ya wuce a rayuwar Afeefah da har in ta tuna baya sai dai tayi murmushi su kawu na chan Dutsen-wai har yau sai dai ta kai musu ziyara ta dawo. Dafa ita har Rayyan sun yi sadakatul jariya da sunan iyayenta da Mammi har basu san adadi ba.Ta samu akallah gidauniya 10 da ake bata taimako daga masarautu zuwa gomnatin jaha har na tarayya sun san da zamanta, kasancewar gidauniyarta dake tallafawa mata da yara akan neman ilimi, sana’o’i da tsayuwa akan kafafunsu kuma dama babban burin ta kenan mutane su samu ilimi kuma suna samu daidai gwargwado Alhamdulillah.ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!! ANAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFI NA HAIHUWA DA HANJI ABINDA MUKA RUBUTA DAIDAI ALLAH UBANGIJI YA BA MU LADA WANDA MUKA KUSKURE ALLAH UBANGIJI YA YAFE MANA.HAKIKA TAFIYAR NAN NA DAGA CIKIN TAFIYAR DA YA MATUƘAR YI MIN DAAƊI BISA GOYON BAYANKU DA COMMENTS NAKU, BAKI BA ZAI FASALTA MUKU IRIN DAAƊIN DA NAJI BA DA KALAR SOYAYYAR DA KUKA NUNA MIN NA GODE NA GODE KWARAI DA GASKE.HASSANA SALLAU(MAMAN MUNIFA): DOLE NA AMBACEKI DON KINA ƊAYA DAGA CIKIN WACCE TA BA NI GOYON BAYA A WANNAN TAFIYA ƊARI BISA ƊARI BAN TAƁA YIN PAGE DA BABU COMMENT NAKI BA NA GODE KWARAI ALLAH YA RAYA ZURI’A YA BAR ƘAUNA TSAKANIN KI DA ABBAN MUNIFA.FATIMA A MUHAMMAD: SIRIKA KUMA AMINIYAR ANGO INA GODIYA DA GUDUMAWARKI KWARAI DA GASKE. ALLAH YA BAR ZUMUNCI YA NUNA MANA RANAR DA ZA MU ZO SHAGALI KADUNA.SIS NANAHALIMA KWARAI NA GODE DA GUDUMAWARKI ALLAH YA BAR ZUMUNCI.HANIFA MUHAMMAD GURIN: YAYATA KUMA AMINIYATA KAWAR CIN MUSHE NA. MY SHAYLAAA🤸‍♀️🤸‍♀️ MY RIDE OR DIE🥰🥰NA GODE DA TAKI GUDUMAWAR DA SHAWARWARI AKAN KO WANI PAGE DA ZAN RUBUTA.SAFIYA GALADANCHI: ƘAWATA MATAR HAMMANMU FATAN ALKHAIRI ALLAH YA KAWO MANA KE KASAR FOMBINA💃💃OUM AMEER: MASOYIYATA KWARAI NA GODE DA ƘARFAFA GWIWA ALLAH YA BAR ƘAUNA YA RAYA MANA SU AMEER YA KAWO WASU ‘YAN UKU SAU UKU☺️DA MA DUK WAENDA BAN KIRA SUNA BA NA GODE SOSSAI DA SOSSAI, TAKU HAR KULLUM

Back to top button