Zakuna Biyar Page 23 By Princess Teema
Juya gaban screen na wayar Lion ɗin ya yi dan ya ga me ya ɗaukewa Aryan hankali suna irin wannan zama kan mission ɗinsu mai muhimmanci, ai yana juyo da wayar sai ga call ɗin Abba ya shigo. Gabaɗaya hankalin Aryan ya gama tashi, baya son su sake yin faɗa irin ta jiya, amma kuma ba zai iya jurar Lion ya yi taking wani mad reaction a kan tsakaninsa da Seraphina ba, to Abba ya kira ya raba gardama.Miƙo mashi wayar Lion ya yi yana hararansa da wannan jade cool eyes ɗin nasa, kai ka ce Leo ne a wajen saboda tsananin kamanninsu, girman idanunsu ma ɗaya.Sai da Aryan ya sauke wani musulmin ajiyar zuciya kafin ya karɓi wayar, ganin Abba ne yasa ya kara natsuwa tare da picking up, a H-free ya sanya wayar, cikin sanyin murya ya ce. “Assalamu alaikum Abba”…….. “Waalaikumussalam”….. “Good morning Abba”. Shiru Abba ya ɗan yi kafin ya ce. “Stop everything you’re doing and come, I want to see you”……. Kallon juna Lion da Aryan suka yi kafin Aryan ya ce. “Abba lafiya dai ko?”……… Daga gefen Abba Faryan ɗan Auta ya riga Abba da cewa. “Yah Aryan wlh kada ka dawo, aure Abba zai je neman maka, wai zai kaimu gidan matan……..”. Ɗiff muryan Faryan ta ɗauke, da alama toshe mashi baki Abba ya yi, dan yasan idan Aryan ya ji wlh ba zai koma ba, sun fara wasan ɓuya kenan, haka suka yi a baya, ya taɓa ce mashi zasu je wani gida neman mashi mata, Aryan ya ki dawowa, sai da ta shari watatti takwas bai taka gidan ba, ko sun kira wayansa baya ɗauka, wayar Faryan kawai yake ɗauka ya ji ya gida suke, sai da Abba ya ce an bar maganar sannan ne komai ya gyaru, to wannan karon so yake ya damki Aryan ga shi ga shi suna kallon juna kafin ya umarcesa ta yadda ba zai iya bijirewa ba. Sai dai da alama Faryan ya ɓata komai.Kuma a tsarin Abba da zarar an je an tambayo auren a wannan lokacin ake ɗaurawa, shi baya jeka ka dawo, ana bashi aure za’a ɗaura a wajen, baya bari wai bari yaran su fahimci juna, ya ce zasu fahimta a gidan aurensu, shi yake yin komai, shi dai a bashi yarinya kawai, da zarar anbashi ko tsinken iyayenta baya karɓa, sai dai ma ya basu sadaki mai tsoka, daga nan a ɗaura su ɗauko yarinya su kawota cikin family, kayan ɗaki da kayan sakawa dik zata samesu a gidan mijin, yanzu dama suna zuwa gidansu Aunty Lisa in an basu zai ɗaura masu aure ne kawai su dawo da matansu.Jama’a kunji wani ta’addancin zuciya irin na Abba? Wannan ai ɗanyen ta’addancin zuciya ne whichs mu IRON FIST family ba zamu yarda ba ko ya kuka ce my people? Ba zamu yarda ayi wa Champion namu auren dole ba! Dole mu yi ruwa mu yi tsaki, ku zo mu je mu yi kanenen mu yi uwa mu yi makarɓiya mu taya Champion namu kwatar ƴancinsa, kada mu bari kanmu ya yi marfi, dan ma dai Abba ne sai mu ɗan raga mashi, amma ba zamu yarda ba.Ai Aryan yana jin jawabin Faryn ya katse kiran, sai ya kira number Faryan ɗin dan ya ji ainahin meke going. Yana kira bugu ɗaya aka ɗaga, a sanyayye ya ce. “Faryan what’s going on? Me Abba yake shiryawa?”……. Unexpected ya ji muryan Abba ya ce. “Abin da kake tinani shi nike shiryawa, na baka 2 hours yanzu in ganka kada raina ya ɓaci”.Ɗan ɗaure fuska ya yi, zai sake yin magana Lion ya yi saurin girgiza mashi kai alamar a’a, dan haka sai ya yi shiru, daga karshe Lion ya ce ya amsa da okey kawai, da hakan ya amsa suka yi sallama da Abba. Yana ajiye wayar Lion ya ce. “Uba wani bango ne da in babu shi babu zuri’a, ba’a ja da iyaye ayi nasara, ko nan gaba kada ka kuskura ka yi ƙoƙarin ja da maganansa, and okey zata rabaka da kowa lafiya”…… A duniya Lion yana kaunar daddynsa, yanzu haka maganar mahaifi da ya yi sai da idanunsa suka kaɗa suka yi ja, shi kaɗai yasan me yake ji a cikin ransa, ga Hoosainin daddyn nasa da ya renesa ma babu shi, wlh ba dan yana da karfin imani ba da ya jima da kauce hanya, dan dai tin da ya taso kalma ɗaya mahaifinsa yake yawan faɗa mashi shi ne dik wuya kada ya kuskura ya sauƙa daga turban koyarwa fiyayen halitta, mahaifinsa da second dad ɗinsa watau Hoosainin mahaifinsa sun jajirce wajen gina rayuwansa a kan turban musulunci, idan ya tina zai yi wani abin in ya tina tarihin Annabi Musa, Annabi Dawud, Annabi Isma’il, Annabi Isa, Annabi Nuhu, Annabi Muhammad (SAW) waɗan nan Annabawa tarihinsu daban yake, in ya tinasu sai ya fasa, dik wani gwagwarmayar da kake tinani ka sha a rayuwa to ko rabinsu ba ka kai ba. Annabi Nuhu ya fi dikkan Annabawa shan wahala a duniya, shekaru 950 ya yi yana wa’azi wa mutanensa, amma dik da haka suka ki musulunta, dik hakuri irin na Annabawa sai da Annabi Nuhu ya yi fushi ya roki ALLAH da ya halaka mutanensa, ALLAH ya ce ka kyara jirgin ruwan da zaka ɗauki ƙalilan ɗin mutanen da suka bika, saura zasu hallaka, imagine hakurin Annabi Nuhu, shekaru ɗari tara da hamsin yana masu wa’azi, amma daga karshe ma ce mashi suka yi mahaukaci ne bashi da hankali. Daga Annabi Nuhu sai Annabi Musa, ya sha wahala, ya azabtu kafin ya samu ya kwato mutanensa banu Isra’ila daga hannun mutanen Masar watau fir’auna, ya sha azaba bawan ALLAH nan, suka sha da kyar, suka tsallaka teku, amma me ya biyo baya? Yana cetansu daga azaba me suka ce mashi? Annabi Musa ya zo ya samesu suna sassaƙa gumaka, ya ce ya haka? Suka ce kai Musa mu fa ba zamu taɓa binka ba, ba zamu bautawa abin bautan naka ba, mu namu zamu sassaƙa yanzu! Imagine, mutanen da ka sai da ranka ka cecesu, ka wahala, ka juri yaki da dik wani barazana, babban mushiriki kamar Fir’auna ka kwatosu daga hannunsa, cikin kunci da azaba ya fito da su izuwa iskar ƴanci, amma me suka saka mashi da shi? Dik da haka bai yi fushi ba, ya cigaba da yi masu wa’azi, amma suka ki, sai wasunsu ne suka aminta, Annabi Isa, har ɓoye kansa yake yi a ɗaki saboda jefansa da kalmar mara uba da ake yi, bai yi wasa da yara kamar yadda kowani Annabi ya yi ba, ya rayu cikin ɗaki shiyasa ya taso baya son hayaniya kuma shiru-shiru, ya fuskanci ƙalubale da dama. Kai Annabawan ALLAH akwai hakuri jama’a, su ɗin karshe ne! Wani nan ko kyauta yai maka baka gode ba an dinga bala’i kenan, amma su ku duba, ALLAH ka bamu ikon koyi da su!.So Lion yana mugun son daddynsa, baya barin mutun ya yi wasa da mahaifinsa, shiyasa ya takawa Aryan birki.Miƙewa Aryan ya yi tare da cewa. “Ina zuwa, let me check them”….. Kai Lion ya jinjina mashi alamar to kafin ya ce. “Ka san yadda zaka yi da Abba, amma ko mutuwa zaka yi kada ka yarda da shiga cikin abin da ya shafi waɗan can halittu na mata, kasan dokar IRON FIST”. Kai ya jinjina alamar gamsuwa, sannan ya matsa kusa da Lion ɗin, rungumar Lion ya fara yi, hannu Lion yasa ya ɗan bubbuga bayansa alamar jinjina, sumbatar gefen kumatunsa Aryan ya yi, shi ma Lion sumbatarsa ya yi kafin su raba jikinsu da juna, ya matsa ya rungumi guru ma, suka sumbaci juna kafin ya fito. Kai tsaye benen su Seraphina ya nufa, dan ya duba ta tashi lafiya. A lokacin da ya shigo tana tsaye a tsakiyar ɗakin tana rike da waya, sam bata ji shigowansa ba, sai ji ta yi ya kwace wayarta. Da sauri ta ɗago da kallonta a kansa, ko da ya shigo ma sai da ya tsaya for good 5 mins yana kallonta, amma bata san ya shigo ba, sai da ya karewa surar jikinta kallo, tana sanye da shorts jeans zuwa tsakiyar santala-santalan cinyoyinta, daga sama ƴar riga da bata gama rufe cibiya ba mai dogon hannu kamar crop top haka, kun san shigarsu ai su, ba hankali aka sika ba, kafafunsa sanye da socks and bedroom crocs faro tas mai tsada.Ash hair ɗinta a gyare, ya sha gyara wajen Madam, sai sheki yake yi, ga wani irin fitinannen kamshin dake fitowa daga jikin gashin ga kuma na jikinta, sai kamshin ya bada wani kala mai ɗaukar hankali. Sai da ya tsaya ya karewa jikinta kallo kafin ya shigo. “Daddy kai ne?”. Ta faɗa tana ɗan murmushi. Harara ya dalla mata kafin ya ce. “Baby anya ba zan hanaki waya ba kuwa? Baki iya amfani da ita ba”….. Zazzaro eyes ɗinta a kansa ta yi kafin ta ce. “Daddy me na yi kuma?”….. Ganin kamar zata faɗo jikinsa ta rungumesa ne yasa ya wuce saman sofa ya zauna yana faɗin. “Me ma baki yi ba? Haka ake amfani da waya ne? 24h baki komai sai pressing phone? On Monday zaku fara zuwa school, anya zaki yi karatun kuwa?”. Da sauri ta dawo kusa da shi, a gefen bed ta zauna suna fuskantar juna. “Please daddy kada ka rabani da wayar, i promise you that zan yi karatu sosai, kaga ai sss 1 zan shiga, dole in dage ko? Kuma dole sai da waya, and daddy ni karatu ma fa kawai nike yi da wayar, idan ka rabani da ita kaga karatuna zai ka baya tin da kamar lesson a gida nike yi da ita. Na yi alkawarin kula, zan warewa waya lokacin taɓawa daban, zan ware lokacin karatu”……. “Baby ni zaki yi wa kalaman yaudara?”. Ya faɗa yana kallon idanunta a tsaitsaye, ga gashin idanun nata sun mimmiƙe, alamar kawai so take ta yaudaresa kada ya rabata da wayar, wai ita ma ta yi wayau, a haifeta a gabansu su sanya mata suna amma wai zata yi mashi wayau.”Daddy trust me, kasan ai bana karya, kuma da gaske karatu nike yi a cikin wayar, and kaga wayar yana da amfani ko?”…….. Miƙa mata wayar ya yi ba tare da ya sake cewa komai ba, dan Seraph tana goge mashi hadda yarinyar nan. Karɓa ta yi har da sauke ajiyar zuciya, a tinaninta ta mashi wayau ya yarda da ita, cike da wayau ta ce. “Daddy tin ɗazun ma karatu nike ta yi da wayar fa, kaga yana da amfani na ce maka, kamar uncle ɗina mai mun lesson yake”. Wai irin ta sake sanyawa ya yarda da ita sosai ɗin nan………… Shi dai ido kawai ya zuba mata yana mamakin yarinyar nan, bata san kome take a wayar yana ganinta ba.Shammatarsa ta yi ta sake snapping ɗinsa pic har guda biyu bai sani ba. Sai dai tana ɗauka ya miƙa hannu ya kwace wayar tare da cewa. “Me kike yi da pics ɗina? Kin ɗau na farko bai isheki ba sai kin ƙara ne?”…… Ai a zabure ta miƙe ta faɗa jikinsa da nufin ta kwace wayar, tamkar zata yi kuka ta ce. “Daddy ni ban yi snapping ɗinka ba, give me my phone”. Shi kuwa ɗaga hannunsa sama ya yi yana kallon hoto, sai ya danna delete zai goge. Wani irin zabura ta yi game da miƙewa a jikin nasa zata kwace ta hanasa gogewa. Baya ya yi da hannun nasa, binsa ta yi dole sai ta kwace, idanunta sun cika tab da kwallar yaudara tana son karya mashi zuciya irin ya kyale mata ɗin nan.Daidai kyakkyawan gefen face ɗinsa ta kwanto mashi da kirjinta tana miƙa hannu zata kwace wayar. Hannunsa ɗayar yasa ya tallabo waist ɗinta ta baya wajen mazaunanta, da ɗayan hannunsa kuma ya danna delete ya goge hoton, ya koma kan ɗayan ma ya goge. Take ta ɗauke wuta, tamkar ta yi sumar tsaye, shiru bata motsa ba. Sauke hannunsa ya yi, sai yanzu ya lura da yadda ta kwanto jikinsa. Take ya ji ya ɗan ɗauke wuta shi ma, a hankali ya ɗan yi ƙasa da ita yana jin tamkar kada ya raba jikinsa da matasan tula-tulan nata dake saitin face ɗinsa, amma ya ɗan yi ƙasa da ita.Wai irin ta yi fushin nan ne fa taki motsawa. Dawo da ita daidai suna fuskantar juna ya yi, ya ɗan kwantar da ita gefe yana tallabe da bayanta da hannunsa ɗaya. Zubawa face ɗinta idanu ya yi, ta datse idanu tana hura kumatu, ga hawayen da suka cika mata ido sun fara zubowa, ta ji zafin goge hotunan da ya yi, ta ci alwashin turawa Rimsha hotun nan yau, amma ya ɓata komai, abin da ya fi bata takaici ma shi ne yadda ya ganota, yanzu tasan zai rabata da wayarta ne ko kuma ba zai sake yarda da ita ba bare ya bata daman zama da shi har ta samu damar ɗaukarsa wani hoto.Shi kuwa slowly ya sunkuyo da kansa a kanta, a gefen wuyanta ya ɗan kwanto da kansa, a hankali ya fara shakan kamshin shampoo na gashinta mai daɗin kamshin dake kwantar da hankali, sai ya rungumeta sosai a jikinsa, kawai ingiza shi zuciyansa take yi da ya yi kissing ɗinta, gudun kada yai hakan ne yasa ya kwantar da kansa a gefen wuyanta. Jin sauyawar numfashinta ne ya sanya shi ɗago kai, sai ya ga kuka take yi sosai, nisawa ya yi tare da zuro tongue ɗinsa waje, hawayen nata ya fara lashewa wanda ya sanya ta dakatar da kukan cak. Da sauri ta waro idanunta waje, kai tsaye sai a cikin nasa idanin very close to her haka. Ɗan zabura ta yi, lokaci guda kuma ta ji tsoro ya shigeta, bata san tsoron me ba, kawai ta ji tsoro ne. Cigaba da lashe hawayen nata ya yi bai damu da tana zazzare mashi idanu ba. Ɗan lasar lips ɗinta ya yi da ya gama lashe hawayen, sannan ya dawo da kallonsa gabaɗaya a kan idanunta, suna fuskantar juna, suna shakar numfashin juna. Saura kaɗan ta saki mashi fitsari a wando, take jikinta ya soma kerma, zazzare idanu ta cigaba da yi a kansa.”Baby, watau ni ne baki yarda dani ba ko? Ban isa in hanaki abu ba ko? Bincike kike yi a kaina? Baki tinanin hakan zai iya affecting rayuwata ne? Baki san dik abin da ake ɓoyewa yana da haɗari bane? Baki yarda da daddynki ba? Ke fa yakamata ki rufe asirin daddynki, amma kece kike ƙoƙarin ɗaukana hoto dan ki turawa duniya ko?”. Ya ɗan dakata yana jinjina kai. Gagara motsawa ta yi, jikinta dik a mace, ba zata iya yin magana ba. Kara matso da face ɗinsa dab ita sosai ya yi, kara zaro mashi ido ta yi, shi kuma ya ɗaure fuska tamau tare da cewa. “Ban yi zaton zan ce ga abin da nike so ki yi gaban kanki ba, idan kina son sanin waye ni why ba zaki yi facing ɗina ki tambayeni ba? Meyasa zaki tambayi wata bare? Good!”. Ya faɗa tare da saketa, a hanzarce ya miƙe, jefa yai da wayarta a saman bed.”Ki nuna hotona a koma ina ne ki tambayi waye ni idan kin yi ra’ayi, amma ki sani ko mutuwa na yi a kan hakan kece sila”. Yana kai karshe ya nufi hanyar fita da sauri tamkar zai tashi sama…… Shiru ta yi tamkar mara lafiya, ta zuba mashi ido har ya fice. Yana fita ne ta samu damar fashewa da kuka, a ranta take jin bata kyauta ba, meyasa zata nemi dole sai ta binciko waye shi tin da ba zaluntarta yake yi ba? Meyasa idan tana son sani ma ba zata tambaye shi ba kamar yadda ya ce ba?.Da sauri ta miƙe ta ɗauko wayar tata. Jikinta har yana rawa wajen laluɓo number ɗinsa. Kira ta fara danna mashi tana ruwan hawaye. Na farko ta kira har ta katse ba’a ɗaga ba, na biyu kuma yana shiga ya katse kiran, na uku ma haka, da ta takura mashi sai ya kashe wayar gabaɗaya, ta kira ta ji switch off. Take jikinta ya kara mutuwa, ta yi nadamar ɓata mashi rai har ya yi fushi da ita. Da gudu ta fito ta nufi room na Madam tana kwala mata kira. A lokacin Madam tana cikin toilet, hakan yasa ta zauna a gefen gadonta tana jiranta.Tana zama sai ga wata mata ta shigo room ɗin bisa jagorancin Aisha, matar ma tare take da wata budurwa wacce a kallah zata kai 23 haka. Cike da mamaki Seraphina ta bisu da kallo kafin ta ce. “Aisha who are those people?”. Kallon tsab matar ta yi wa Seraphina kafin ta ce. “Wannan ita ce yarinyar kenan?”. Da alamar walaƙanci da ƙasƙanci a maganar matar. Jinjina mata kai Aisha ta yi kafin ta ce. “Ita ce mai gidan”. Taɓe baki matar ta yi tare da cewa. “Ina Aunty Rohisha ɗin ne?”. Aisha ta amsa da. “Tana toilet”…… Ganin yadda matar ta kalleta ya sa Seraphina ta ɗan sha jinin jininta, a sanyaye ta ce. “Good morning”. Matar ta amsa a takaice tare da wucewa ta haye saman bed ɗin Madam ta yi kane-kane har da miƙe kafafu tamkar wata ballagaza ta zauna a kasuwa. Matashiyar yarinyar dake tare da ita ce ta kariso wajen Seraph, sai da ta dallah mata wani irin harara kafin ta ce. “Give me a way to pass”. Cike da mamaki Seraph ta kalli filin dake gadon, dik bai isheta hanyar wucewa ta haye saman gadon ba sai in da take? To amma da yake ba bakuwar zafi bace sai an taɓota sosai sai ta miƙe ta basu waje, ta koma saman sofa ta zauna, ita ba don tana son faɗawa Madam halin da take a ciki bama da ta bar room ɗin. Aisha ma waje ta samu saman sofa kusa da Seraphina zata zauna kenan muryan matar ta katseta da cewa. “Ke wuce ki fita a nan”…….. ALLAH sarki, suna nunawa Aisha kyara ne dan marainiya ce Madam ta ɗauko take reko, abu ba abu ba sai su ce mata maganar family ake yi. Wannan mata kanwar Madam ce uwarsu ɗaya ubansu, wannan budurwar ƴar kuma ƴarta ce, basu da mutunci ga shegen son duniya, sun ji Madam ta samu matsugunni a CRYSTAL PALACE ne shiyasa suka ce suma dole su zo aci arziki da su, yanzu dai wai sun dawo gidan da zama. Miƙewa Aisha ta yi zata fita fita jiki ba kwari Seraphina ta riketa tare da cewa. “For what reason zata fita? Is it your room? Su waye ku nema da zaku zo ku samemu a ɗakin mom ɗinmu ku ce ta fita? Is it your room?”. A kule ta faɗa tana kallon matar, jinin IRON FIST basa ɗaukar rainin wayau, da farko ta ɗauka bakin arziki ne shigasa tai masu shiru, amma da ta ga basu san arziki ba shi ne ta gwada masu jinin IRON FIST take.Budurwar ce ta amsa da. “Ke baki da tarbiya ko? Babban mata zaki faɗawa haka? Bata haifeki bane? Ko a gidanku babu manya ne?”….. Wani irin mugun harara Seraphina ta dallah mata kafin ta ce. “Keda gidanku suke da manyan ai naga basu baki tarbiyar adalci ba, kuma basu koya maki yadda ake magana ba”. Ta faɗa tana zazzare mata ido, irin ta san bafa tsoronta take ji ba. Kallon juna yarinyar da mamanta suka yi, sun gano Seraphina ba wacce ake takawa ta taku bane. Daidai lokacin Madam ta fito daga toilet, ta yi wanka har ta shirya a ciki dan da kayanta ta shiga, cikin arabian dress ta shirya. Ganin suna musayar yawu yasa Madam ta yi saurin cewa. “Safiyya me haka? Daga zuwanki? Ke ba zaki canza hali bane wai?”. Wannan budurwar ce mai suna Suhana ta ce. “Mommy Ummina bata da laifi, wannan yarinyar ce ta zageta”…… “Ya isa haka Suhana, babyn daddy me yakefaruwa ne?”…… Sake hannun Aisha Seraph ta yi tare da miƙewa ta isa gaban Madam, a ɗan shagwaɓe ta ce. “Mommy daddy yana fushi dani, ya tafi cikin fushi, kuma ina ta kiransa baya ɗauka, daga karshe ma ya katse kiran”. Riko shoulders ɗinta Madam ta yi. “Jeki room ɗinki ina zuwa sai ki faɗa mun me kika yi mashi ya yi fushin dan mu san daga in da zamu fara gyara, Aisha ku je da ita”. Ta kai karshe tare da saketa. Da sauri ta juya ta nufi waje ba tare da ta sake kallon in da suke ba, Aisha ta rufa mata baya. Suna fita Madam ta kalli Safiyya tare da cewa. “Ke baki da hankali ko? Sai kin ɓata mana dik wani shirinmu a kansu kin sa asirinmu ya tonu ko? Yanzu idan kuka fara nuna mata kiyayya kuka ja aka koremu ba shikenan komai ya lalace burinmu ba zai cika ba ko! Meyasa baku da tinani ne?”. A taƙaice Aunty Safiyya ta ce. “Kai Aunty Rohisha, ni fa yarinyar ne take bani haushi, na tsaneta daga kallon farko, na kasa ɓoye tsanar ne yasa na nuna halin”…… Nufosu Madam ta yi tana faɗin. “Gara ki koyi danne abu, dan wlh a kan wannan yarinyar babu irin matakin da ba zasu ɗauka ba, zai ma koremu a gidan nan, kada ki manta saboda ita ya ɗaukomu dan ta yi farinciki, dan haka dik abin da kake son cimmawa a hankali zaka bi da shi har ka cinma, bugu da ƙari ina son ki san cewa gidan nan gabaɗaya kewaye yake da camarori, cikin bedrooms ɗinmu ne kawai babu camera, amma bedroom na Seraphina akwai ɓoyayyen Camera, ranar da na shiga unexpected ina ɗaga kai jikin bulb na wuta ta ƙasa naga karamar camera, da alama basa son Seraphina tasan da camerar ne a wajen yasa ya ɓoye, amma sauran ɗakunan gidan babu, su parlo, kitchen har balcony dik akwai Camera, dan haka ku yi taƙa tsantsan, ku kuji shiga harkar Seraphina a gaban camera”. Kai suka jinjina alamar gansuwa, sannan Suhana ta ce. “Mom gaskiya CRYSTAL PALACE duniya ne kuma karshe ne, amma kuma gaskiya suna ji da yarinyar nan sosai, dubi irin daular da aka zuba mata, sannan Camera ta ko’ina dan kula da dik wani motsinta, tsaro sai ka ce zasu iya hana mala’ikan mutuwa ɗaukar ranta in ya zo?”. Tana ɗaure fuska alamar hasada dan bata samu irin hakan ba ta faɗa.Madam zata yi magana Aunty Safiyya ta rigata da cewa. “Gaskiya Aunty Rohi kin iya ɓadda kama, ni ba dan na ji muryanki bama ba zan gane ke bace, kin iya sanya fuskar boge wlh, kuma kowa ya ɗauka fuskanki ce fa”. Ta kai karshen magana suna murmushin dake kama dana mugunta. Madam ta ce. “To ya zan yi, biyan buƙata yafi kwana masallaci, dole in yi basaja, dole in ɓadda kama in shiga jikin Seraphina dan cikar burina”. Shiru Aunty Safiyya ta yi tana tinanin makudan dalolin da ta karɓa kan ta fito masu da Seraphina daga CRYSTAL PALACE, a ranta ta fara tsara yadda zata shawo kan lamarin, ta samu ta ja Seraph wajen CP ɗin. Watau sun san a cikin CP dai kam basu isa shiga su ɗauketa ba, dole sai an fito da ita waje, lallai kuwa akwai gagarumin matsala, meyasa suke neman Seraphina? Su waye su? Madam Rohisha da ɓadda kama for what? Meyasa ta shiga rayuwar Seraph? Me manufar su Safiyya? Zasu yi nasara ko kuwa?. Uhm mu leƙa WS-HOSPITAL mu dawo. —————————🔥WS-HOSPITAL. Bayan wani lokaci, zan yi skipping na labarin ne kaɗan saboda wani dalili da a gaba zaku gane!.Gabaɗaya 3D haɗe suke a cikin section D suna duba lafiyar jariran dake cikin cikin uwar da suka kirkira da kansu, yaran sun fara wayo, dan wajen transparent ne kana iya ganin yadda suke rayuwa a ciki, suna motsawa a hankali tamkar yadda suke motsi a ciki uwa, kallonsu daga ta waje abin sha’awa da ɗaukar hankali, dikkansu kuma lafiyayyu ne sosai, dan in baku manta ba su Dr suna tace maniyin namiji su cire mara karfi sai su kara mashi alluran karfi dan ya zama daidai da wancan.Bari in baku wani haske a nan yadda zaku fi fahimta, nasan kunsan halittar mace da namiji ba ɗaya ba, mace tana da rauni, namiji ya fi karfi, to wannan maniyi mai karfi shi ne na ɗah namiji, wanda bashi da karfi sosai kuma shi ne na ƴa mace, to in baku manta ba na faɗa maku su basa kyankyashe mata ai, maza kawai suke kyankyasa, shiyasa suke karawa maniyin karfi da allurai domin ya basu ɗah namiji ba mace ba, fatan kun gane?.Idan kunga yadda jariran nan ke motsawa sai sun burgeku, a yanzu sun kai watanni bakwai, sun zama halittar mutun, a kallah zasu kai jarirai 150 a wajen, dikka kuma maza ne, babu mace ko ɗaya, sannan dikkansu farare ne tas da su, da alama sperm ɗin sai an zaɓa ake saya, ba kowanne ake saya ba.Dr James ne ya ɗan tsaya a gaban na’urar kwalba guda, hannu ya ɗaura a saman oxygen control na jikin gwalbar, kashe wajen ya yi, hakan yasa iska ta daina shiga cikin kwalbar, komai ya tsaya jim. Idanunsa a kan wata ƴar madaidaiciyar touchscreen computer dake jikin kwalbar wanda suke amfani da shi dan duba bugawar zuciyar jaririn, yanayin da yake ciki da sauransu, so ya zuba ido a wajen yana kallon yadda computer ke harbawa da karfi-karfi, zuciyar yaron tana bugawa da karfin gaske ne, saboda rashin iskar shaƙar numfashinsa. Slowly ya dawo da kallonsa a kan jaririn, nan ya ga yaron ya fara motsawa da karfi alamar yana neman iskan shaƙa, ya ware ƴan yatsunsa dake ƴan ƙanana sosai yana ƙoƙarin mikar da kafafu, jikinsa babu kwari bare ya yi wani yunkuri. Mai da kallonsa a kan computer Dr James ya yi, nan ya ga zuciyar yaron ta tsananta bugawa da karfin gaske.Dawo da kallonsa a kan kwalbar ya yi, unexpected ya ga jaririn ya waro idanu waje, azaba ta yi azaba, babu iska babu shaƙar numfashi ai kunga babu azabar da ta kai wannan. Nisawa ya yi tare da dan lna oxygen control ɗin ya kunna mashi. Haba ai har sai da computer ta yi ƴar kara alamar bugawar zuciyar yaron ta dawo, slowly jaririn ya maida ƴan yatsunsa ya dunkule su kafin ya ɗan juya tamkar yadda suke juyawa a cikin uwa. Yana juyawa cibiyarsa dake manne da uwa ne ya ɗan naɗe mashi wuya. A daidai lokacin su Dr Kamal suka iso wajen, in a low way Dr James ya ce. “Kamar wannan project ɗin ya fi dik waɗan da muka yi a baya kyau! Karfi da kuma lafiya!”.”Meyasa ka ce baman?”. Dr Mark ya tambaya. “Saboda yaran suna da karfi da lafiya, a ƙaida jariri baya iya rayuwa babu iskan oxygen na second 30, amma yaron nan ya kai 1 minute babu iska, kuma da na dawo da iskar bai shiga wani yanayi ba, yakamata nan da 30 days mu yi test na brain and heart ɗinsu dan tabbatar da ingancinsu”.Dr Kamal ne ya ce. “Gaskiya yaran suna da lafiya sosai, nima na shaida duba da yadda suke motsawa da karfi, bamu taɓa kyankyasan yara masu karfi da lafiyarsu ba”……. Dr Mark ne ya ce. “To ko dai akwai jinin FIVE LIONS a jikinsu ne?”…….. Siririn tsaki Dr James ya ja tare da wucewa gaba bai sake magana ba, Dr Kamal ne ya ce. “Ga dikkan alamu har yanzu FIVE LION suna ranka Mark”. Ya faɗa tare da bin bayan Dr James.Bayansu Mark ya bi yana faɗin. “Dole FIVE LIONS su tsaya a raina, kuma nasan suna ranku, dan ba’a taɓa shegun jami’an da suka kusantomu irinsu ba, jami’an da suka shirya mission a kanmu, jami’an da basa tsoron mutuwa, jami’an da basu ɗauki ransu a bakin komai ba”. “Hmmm”. Kawai Dr Kamal ya ce, na ciki na ciki, su kaɗai suka san me yake a cikin ransu. Kai tsaye wani ɗaki dake a cikin section D ɗin suka nufa. Ɗaki ne wanda kun sani, cike yake da glasses dayawa, sannan kamar chemical lap haka wajen yake, dik ta in da ka juya manyan chemical ne masu mugun haɗarin gaske a wajen.Sister Zinta and sister Maya suna sanye da chemical care gown, hand gloves a hannu, socks a ƙafa, eyes care a idanu, sun dukufa gaban computers sai aiki tuƙuru suke yi. 3D na shigowa suka miƙe tsaye dan girmamawa a garesu, yanzu almost 4 months kenan suna wannan aikin, tin ranar da suka sanya hannu, barci wannan rabi da rabi suke yi.Abin da zai baku mamaki kuma basu taɓa sanin aikin me suke yi ba, kawai suna tsamo wasu chemicals ɗin ne su sanya a wasu, amma kowanne sai sun tacesa sun ciri mai karfin cikinsa, idan kun fahimta su Maya ilimin chemical kawai suke da shi.Duba aikin nasu 3D suka yi, komai na tafiya yadda yakamata, jinjina masu Dr Kamal ya yi, da alama ya fi su Dr James sauƙin kai, fitowa suka yi daga cikin room ɗin izuwa side na dabbobi watau section B. Yau wajen a cike yake da kukan dabbobi kala-kala, ga waɗan nan jiga-jigan guards ɗin suna ta aikin kai komo. Sanya gabaɗaya guards ɗin suke da kayan kariya a jikinsu, da alama aiki tuƙuru suke yi. Gaban wasu manyan guards biyu 3D suka tsaya, matasan nan suna rike da zabga-zabgan macizai guda biyu, sun mace kan macizan jikin wani kwalba, sun ɗaura hakwaran macizan a bakin kwalbar, sannan sun matse tsakiya wajen cikin macizan, macizan sai fito da wani green ruwa daga bakinsu suke yi yana zuba a cikin kwalbar. Wannan green ruwa shi ake kira da neurotoxic, hemotoxin, sinadarai ne masu matuƙar haɗari da illah, dan suna hana jini gudana a jiki, and yana lalata jijiyoyin jini, a hankali ya lalata tsokoki jikin mutum, to wannan sinadaran suke matsowa daga jikin macizan. Jinjina kai 3D suka yi alamar aiki na tafiya da kyau, sai suka matsa kusa da wasu guards dake mace sinadaran corpion mai suna chlorotoxin, watau wani sinadari ne dake shafar jijiyoyi, yana haddasa raunin jijiya daga nan shanyewar jiki, shi ma sinadarin da yanayin yadda suke tatsansa a jikin dabobbin, kowacce dabba tana da sinadari mai cutarwa kuma tana da mai amfani, dan haka kowanne da yanayin yadda ake fitar da shi, kunga maciji tana da sinadarin da ake iya yin maganin ciwon zuciyaa da shi, kunga wannan ba mai cutarwa bane, amma su a nan mai cutarwa suke fitarwa.A nan ma sun tabbatar komai ma tafiya daidai sai suka wuce gaba. Nan ma wasu guards ne ke ta faman matse sinadarin dart frog mai suna batrachotoxin, sinadari ne da idan ya shiga jikin mutum yana toshe sodium channels, yana haddasa bugun zuciya ta tsaya cak, amma a hankali yake aiki na likitoci guda ba…… Nan ma duba aikin na tafiya daidai.Gaba suka ƙara wajen masu tatsan dafin pufferfish mai suna tetrodotoxin, watau sinadari ne da idan ya shiga jikin mutim yana toshe jijiyoyin jini, yana sanya numfashi ta dinga ɗaukewa tana sama-sama kamar mutum zai mutu. A nan ma komai na tafiya daidai. Wucewa gaba suka yi wajen guards dake tatso tsinadarin cone snail mai suna conotoxins, shi wannan sinadarin idan ya shiga jiki yana hana jijiyoyi aiki, yana haddasa shanyewar gaɓoɓi ya baka sassaiɓar mutuwa ba mutuwa da gaggawa ba, sai ya gana maka azaba a jiki.Oh ni Princess Teema na shiga uku, ko me suke yi da wannan sinadaran? A tinaninku me suke yi da shi?. Kai idan kana raye babu abin da ba zaka gani ba, ALLAH ka kawo mana agaji, ka dubemu da idanun rahama ka dafa mana, ALLAH ka jiƙanmu ka jiɓancin al’amurranmu.Sai da suka tabbatar komai na tafiya daidai kafin su fito daga wannan ɓangare, kai tsaye suka koma wannan ɗaki na meeting ɗin nasu da suke zama. Dr Mark ya ɗauko glass cup da wani tangamemem drink ya nufi saman sofa. Dikkansu zama suka yi a kan sofas ɗinsu, Dr Mark ya tsiyaya drink ɗinsa a cup, dan shi karatu ta fi shigansa idan yana yi yana sipping drink mai sanyi, kuma ɗan banza kullum Americano yake sha. Dr James ne ya miƙe tsaye tare da kunna light na tangamemen touchscreen computer dake gabansu sofas ɗin nasu, ya ɗauki wani sanda siriri dake wajen ya rike da hannu dan ya ji daɗin bayani. Hannu ya ɗaura kan screen na computer, pressing ɗinta ya shiga yi cikin kwarewa for like 5 mins, sannan ya ɗauke hannu.Take wani rubutu ya bayyana a kan screen ɗin, P-C shi ne sunan project ɗin, idan baku manta ba project da suke yi da su Maya kenan, sai yau zasu mana bayanin wani irin project ne.NEXAPOX-31 shi ne ainahin sunan da suka sanyawa wannan aiki, a jikin folder na aikin ma sunan dake rubuce kenan. Cikin folder ya shiga kai tsaye. Take wani dogon jawabi ya bayyana. Kara natsuwa su Dr Kamal suka yi dan sauraran wannan aiki, gagarumin aiki ne da sun jima suna yinsa, ba tin yau bane, ya haura shekaru 5 suna shiryasa, yanzu ne da aka hura masu wuta daga can WORLD SYSTEM shi ne suke son kaddamar da aikin cikin gaggawa su fito da shi, dakon jiransu ake kamar hauka, hakan zai tabbatar maku makudan biliyoyin daloli ne a kan wannan project ɗin.A natse ya ce. “Menene NEXAPOX-31?”. Ya faɗa yana mai da kallonsa a kan su Dr Mark da suka kara natsuwa, one thing, dikkansu 3D ɗin nan Dr James kamar malaminsu yake, ya fisu kwarewa a kan komai, bugu da kari shi yake yin dik wasu manyan project irin NEXAPOX-31 da sauransu, sai ya kammala shirya manyan abubuwa game da project ɗin, sannan yake zama kamar dai yanda suka zauna yanzu ya zayyana masu irin project ɗin, amma a tare suke yin komai, sai dai ba lallai su san kai tsaye ga abin da suke shiryawa ba, sai an yi tafiya mai nisa yake zama yai masu bayani, daga nan su karisa a tare! Fatan kun fahimceni?.”NEXAPOX-31 wata…….


