Gargadar So Chapter 58 By M Shakur
Ayanda yau taga idanun Khaleel saida Hawwa ta tsorata wlh, bata taba ganinshi haka ba, yanda ranshi yakai ga baci yasa kawai ya turata yajuya yabude kofa yafito Baba da Ammi na tsakar gidan sunyi charko charko a tsaye, yama kasa kallonsu sabida baison suga kwayan idanunshi yawuce zaure da sauri Ammi tabiyoshi daidai ya shiga zaure tace “Ibrahim!” Chak Khaleel ya tsaya batare daya juyoba, dasauri Ammi ta taho tazagayo ta gabanshi sai kawai Ammi tasa hannu takamashi ta zaunar dashi kan bench dake zauren ahankali yazauna sai kawai yakai hannayensa biyu yarufe fuskansa yafuzar da iska masu zafi kaman zai kama da wuta sakonnin nan nacimai rai, ahankali Ammi tace “it’s okay ya isa Khaleel ya isa” sauke hannunshi yayi ya gyadamata kai ahankali yace “thank you Mom” anatse Ammi cikin hikima tace “can you show me sakonnin da aka turamaka game da Hawwa”? Araunane ya girgiza kai yace “Mom banso kowa yagani, sirrin matana ne I can’t show you banso kumata wani kallo” kirji Ammi tanuna tace “nine mahaifiyar Hawwa, show me Ibrahim idan akwai abinda yakamata namaka bayani zan maka, banso ku fara aure da zargi ko kokonto aranka, ayanda abin ke tafiya nan gaba hala za’a iya maka sakonnin dayafi wayan nan daci ma da tada hankali ma, so show me” Allah yasani sabida nauyin Ammi dayakeji ne yasa gently yamikama Ammi wayanshi daya bude mata message yace “5 numbers suka turo sakkonni, nasa anmin tracking akace lambobin wasu beggars ne, jiya danai magana da ita suna tare a office dinta, I believe somehow she took my number from wayan Matana batare datasan anyi ba” duka sakon nin Ammi tabi takaranta ran Ammi yama Ammi badadi sai kuma takaraji ta natsu da Khaleel tama aminta dashi gabaki daya, dawani ne da yasaketa yace yafasa aure but shi yazo kawai yayi warning nata kan zama da Ni’ima ne, ahankali tace “Khaleel wlh karyane kazafi akeso ama Hawwa! Babu wani abu na Hawwa daban sani ba, Ni’ima so take takashe auren ku, wlh Hawwa bata taba soyayya da Oganta ba, Hawwa maza tsofaffi ma basa burgeta, sheri ne diyata ba haka takeba, sai kuma abokin aikinta Abraham tabbas ta sanar dani yaron na bibiyanta shima bawai ya iya yafurta da bakinsa yana sonta ba, ai bata bashi fuska, yana mugun shakkanta, Hawwa bazata taba iya soyayya da wanda ta girma ba Khaleel kuma wanda yake ba addininta ba, saikuma na karshe sauran samarinta“ anatse Ammi tace “Ibrahim Hawwa na can be everything, stubborn, mafadaciya da sauransu amman Hawwa na ba mazinaciya bace! Dudda ta dade batai aure ba bata taba kallon zina as solution na matsalolinta ba, duk ina maka bayanin nan sabida ni uwa ce bazanga ana so akashe auren y’ata naja baki nai shiru ba, duka sakon nin nan karya ne Khaleel koda bakai trusting Hawwa ba trust me ni mahaifiyarta, I will never lie to you kaji”.Sosai Khaleel yake kallon Ammi natsuwan da tun jiya yakasa samu bayan yaga sakonnin nan sai Ammi tabashi natsuwan in just few minutes ya yarda and he believed her, gyadama Ammi kai yayi ahankali yace “I know! Deep down I know my wife is not like this, kawai bansan mesa zuciyana keta zafi yana radadi ba bayan na karance messages din” yasan inda Hawwa yar iska ce da bazata taba tsanan halinshi ba, sabida batayi saisa she despise his way of life, dan murmushi kadan Ammi tayi tace “sabida kana sonta ne saisa kakejin haka!” Tsare Ammi Khaleel yayi da ido jin tace yanason Hawwa bayan shi yasan baya sonta he just wants to show her he can have her idan yanaso, ahankali Ammi tace “Khaleel aure dole agina foundation da trust, you have to trust matarka, itama matarka have to trust you, ta hakan ne zaku iya strengthening bond naku ta yanda babu any makiyi dazai iya zuwa ya jijjigaku kaji” gyadama Ammi kai yayi ahankali Ammi tace “tashi kaje gida kai wanka Ni’ima zanje har gidansu naga mahaifiyarta” gyadama Ammi kai yayi baiso yagayama Ammi what he’s planning dan zata iya hanashi but Ni’ima zatasan she messed with the wrong person this time, tashi yayi yawuce haryakai kofa saikuma yajuyo hada ido sukayi da Ammi kai yadan sosa yana sauke idanunshi kasa ahankali yace “thank you Mom for guiding me” yana maganan yawuce yafita Ammi tai shiru tana kallon inda yabari saiga hawaye ya sauko daga idanunta daidai Malam na zuwa zauren ahankali Ammi tace “Malam ina alfahari da wannan miji dakama Hawwa hakika Hawwa tai sa’a! Hawwa tai dace” ahankali Baba cikeda damuwa yace “nagode Zainabu da babu ke da bansan yanda zanyi handling issue din nan ba, me Ni’ima ta turo a sakon”? Karantama Baba sakon tayi tass sannan suka tashi suka wuce dakin Hawwa tana zaune ganinsu yasa ta tashi ta taho wajen Ammi tace “Ammi wlh ita tazo wajena an off…….” Tassss! Ammi ta yanka mata mari mai kyau da lafiya Baba yace “nagode Zainabu!” Hawwa ta dafe kuncinta dasauri, wani irin feeling Ammi keji aranta, irin after much struggles da wahala da kata katan rayuwa da gori, habaici maganganun banza, gulman makota da mutanen gari, kasamu ka aurar da diyarka wata yar iskan kawa na kokarin kashema yarka aure, cikin murya mai rauni Ammi tace “Hawwa magani Ni’ima tabaki a abinci kikaci da bazaki iya rabuwa da ita ba ko me? What did I tell you about that girl ranan nan? Ni da mahaifinki nan mun gayamiki Ni’ima bata kaunarki kona miskala zarratin, ta tsaneki, kukanta kukan mazuru ne, kukan karyane da yaudara, so tabiyoki jiya office kika bari tazo, kinsan cewa Ni’ima ta dauki wayanki a sace ta kwashi number mijinki?” Hawwa dake dafe da kuncinta tana kallon Ammi da mamaki tabude baki in disbelief, tace “Ammi karya yamiki kawai ya tsani Ni’ima ne” “kinci mai garinku Hawwa kaniyanki” Baba yamata dakuwa yatsunshi kaman zasu shiga kwayan idanun Hawwa yace “mijinki kike kirada makaryaci”? Sauka kanta tayi kasa ahankali, Ammi tace “ta aikama Ibrahim sako cewa DIG oganki, Abraham da duk duka samarinki dasuka gudu jikinki kike basu suna amfani dake” dawani irin sauri Hawwa takalli Ammi, Ammi tace “tayi amfani da wayan masu bara jiya at exactly 2:15 ta tura” shiru Hawwa tayi basu wani dade da rabuwa ba aka tura sakon, Ammi tace “he tracked the number masu bara sukai kwatancen ta da motarta you are lucky bai sakeki ba Allah yaga zuciyanki yabaki miji mai sonki da tsaya miki haka” Ammi ta nuna kanta tace “idan har ni Ammin ki Zainabu na kai mahaifiyarki na isa dake, dagayau namiki iyaka da Ni’ima baki ba ita! Ko wayanta kika kara dauka ban yafemiki ba Hawwa!” Sosai Hawwa ke kallon Ammi, Baba yace “nima idan na isa nakuma kai matsayin mahaifi agareki namiki iyaka da Ni’ima har abada! Ni’ima bata kaunarki! Ta tsaneki, bakin ciki take dake, idan Ni’ima tasami hanyar kasheki zata kasheki Hawwa, dan haka bassss! Bassss! Enough! Bake ba ita, da raina bazan bude idanu inga kawa na neman kashema y’ata auren da ba’a riga an kai daki ba, tundadai an baki hutu awajen aiki dagayau na ijiye dokan kada ki kara fita daga gidan nan unless shi mijin naki ne yazo yanaso yafita dake, sa hijabi muje gidansu Ni’ima Zainabu”.


