Halysaah Page 172 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 172…….jay da ajay na isa wajen ,jay ya fido wayar shi yayi dialing number Walid kusan five missed calls amma ba a dauka yayi tsaki ya juya ya kali ajay ya juya ya kali wani direction yayi kamar baisan ma yana kallon shi ba sbd yasan daga gani wannan abun wani shari walid ya hada after some minutes jay yace ma ajay ya kake ganin zamu yi inata kira amma ba adauka ajay kawai kallon shi yayi yayi wani murmushi jay yace look ajay bana son haka ya ina tambaya ka kana wani kallo na haka ajay dai bai kale shi ba wani direction din yake kallo Chan da ban,jay ya bude baki zaiyi magana kenan a fusace sbd ya gaji da abinda ajay yake na halin koh in kula da yake nunawa akan walid ai koh bakomai walid jinin süne kafin yayi magana kawai suka ji halbin bindiga ajay ya juyo a firgice yana kallon jay yace na gaya maka walid ba abun yarda bane setup ne ya shirya manaassuming ya ma ga Walid din ne da sai kawai su tafi Ajay ya biyo su Calabar din washegari, wannan yasa Jay yayi rescheduling tickets dinsu zuwa gobe da safe kawai, Ajay yayi lodging same hotel da su Jay suka yi lodge, har kiran da yake ma Khaleesat ya katse bata daga ba, and he suspect she might be sleeping, wannan yasa bai sake kiranta ba, zai kira number Yakumbo aka yi knocking kofar dakin hotel din ya daga kai don dama bai kulle kofar ba, Jay ne ya shigo dakin, tun zuwan Ajay hotel din kawai ta waya suke communicating sai yanxu suka hadu, Ajay yana kallonsa har ya karaso cikin dakin, Sounding so pissed off Jay yace “Ni dama tun da Mai martaba yace ayi tafiyar nan da Walid nasan kawai da abinda zai wahal da mu za muyi tafiyar, we just can’t say no to Mai martaba banda haka duk abinda zai hadani harka da Walid bana so sam, wannan wani irin nonsense ne?” Ajay dake ta kallonsa yace “So what happened?” A fusace Jay yace “Yanxu aka kirani wai yayi hatsari a hanyar Lokoja” Ajay yace “Ban gane ba, me ya hada Abuja da Lokoja?” Jay yace “How will I know? Tun a jirgi yake ce min kafin ka iso da akwai abinda zai je yayi a lokoja, wai wasu agent sun nuna masa fili zai je ya gani ko location din yana da kyau ya sa Mai martaba ya siya masa yayi set up din new business a can” Ajay yayi wani murmushi yace “So tun safe ya tafi Lokoja din kenan?” Jay yace “Oho, tun dai da muka yi lodging hotel din nan ban gansa ba, ya dai kirani twice, na farko wai in tura masa miliyan uku da rabi” Ajay bai san sanda yayi dariya ba yace “Kudin plot din ya biya kenan” Jay yace “Ta yaya zan sani, lastly ya kira ni around 4:30pm, yana tambayar karfe nawa ne flight din mu to Calabar, sai kuma yanxu da aka kirani wai yayi hatsari” Ajay ya gyara zama yace “To Allah ya kiyaye gaba, call his father” Jay yace “I don’t understand I should call his father” Ajay yace “What is it that you don’t understand Jay, an kira ance yayi hatsari shi ne nace ka kira Abbansa ka sanar masa ga shi can yayi hatsari a hanyar Lokoja” Jay yace “So mu meye amfaninmu da har sai na kira Mai martaba da magrib din nan na ɗaga masa hankali?” Ajay yace “Kai ma baka ji kace Magrib ba, ina za mu je da Magrib? Yayi shawara da kai before leaving for another state or did he inform you? So we just have to call the father a san abun yi, cause ni dai da ka gan ni nan babu babu abinda zai bi da ni wannan hanyar da magriban nan, su mutanen da suka kiraka ai kamata yayi su kai sa asibiti sai ayi communicating da ma’aikatan asibitin da aka kai sa before tomorrow” Jay zai yi magana wayarsa ya fara ring yana dubawa yaga number Walid ke kiransa, dagawa yayi ya saka handsfree yaji muryar wani mutumi dake hada Hausa da kyar yana cewa “Idan ma baku a Lokoja kawai kuyi waya da wani ɗan uwanku dake Lokoja ya taho ya daukesa ya kai sa asibiti cikin sauri don yana ta loosing blood, he is unconscious already” Duk da hayaniyar dake wajen alamar an taru a gun Jay duk yaji abinda mutumin ke cewa, da turanci yake ce ma mutumin why not su taimaka su kai sa asibitin kafin ya karaso, Da sauri mutumin yace “Lai Lai oo… Babu ruwanmu da police case, bamu san waye shi ba, mu dai mun yi abinda za mu iya….” Jay yace “Yanxu haka muna Abuja, how many hours kafin mu karasa wajen? So do the favour of taking him to the nearest hospital kafin mu iso” Mutumin yace “Rara oo, ga wani mutumi me chemist a nan ya daure masa jinin da yake fita a jikinsa, till u go arrive nothing will happen to him, just start coming” Daga haka mutumin ya katse wayar, Ajay dai yana ta kallon Jay, calmly Jay yace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, baza ka taɓa tafiya da Walid baka yi ɓacin rai ba” Ajay yace “To wai numberka ne kadai a wayar Walid? Me yasa sai kai ake kira, idan haka ne last call dinsa is suppose to be from the people he went to meet to see the plot not you, su ya kamata ace an kira ai, just reason this critically Jay, and how were they able to access his phone, don nasan definitely bazai bar wayarsa babu password ba tunda ba gaskiya garesa ba, baya ma barin waya babu password” Jay yace “Whatever Junaid, this is not the right time for all this ur questions, Kai baka jin hayaniyar dake background din call da nayi yanxu da mutumin nan alamar a titi ne, ga dai hayaniyar jama’a kana ji, kuma ai ya kirani wajen karfe hudu da rabi, so definitely numberna zai iya zama shine last call dinsa, i am suspecting immediately we arrived Abuja ya kama hanyar lokoja tunda nace masa sai da yamma zaka iso…. Nayi waya za a kawo min mota yanxu, i am leaving for Lokoja” Yana fadin haka ya nufi kofa, Ajay ya mike yana kallonsa yace “Jawwad, baza ka je garin nan ba, zan kira Mai martaba, shi zai yi making calls ko yaya ne baza a rasa masu kai sa asibiti ba a garin, idan ya so gobe da safe sai mu je ido na ganin ido” Jay ya juya ya kallesa yace “Kar ka kira Mai martaba ka daga masa hankali, even this morning before leaving yace min baya jin dadi, he even called his doctor for check up, ko fada bai fita ba ai sai ko bayan da muka taho” Ajay yayi shiru don duk bai san wannan ba kuma wajen karfe uku sai da ya shiga wajen Mai martaban ya samesa a part dinsa amma bai gaya masa baya jin dadi ba, Jay yace “He even went ahead and told me to keep an eye on Walid…. So now ta yaya zan fara ce masa Walid ya tafi Lokoja ba tare da na sani ba har yayi hatsari?” Ajay ya koma ya zauna yace “Naga ai ba yawo zaka dinga yi da shi kamar jaka ba since he is not a Baby, Walid is an Adult ba yaro bane balle ace a kula da shi….” Jay bai sake tankasa ba ya fice daga dakin Ajay ya bi sa da kallo. After a while Ajay ya mike ya nufi kofa ya fita ya kulle dakin hotel din, a reception ya tarar da Jay dake zaune yana jiran isowar motar da za a kawo masa, Mikewa yayi bayan kiran drivern dake tahowa da motar ya shigo wayarsa, ya fita daga reception din Ajay ya bi bayansa, bayan Jay ya amshi car key din hannun Driver ya sallamesa Ajay dake kallonsa yace “Wait Jay, let me ask you, anya kuwa kasan awa nawa daga nan zuwa inda zaka je?” Jay yace “I will reach there before 3 hours in sha Allah” Ajay yace “Driving din awa uku fa da daddare, gashi hanyar nan ba Guarantee garesa ba?” Jay ya kallesa yace “So what are you insinuating Junaid? In bar sa ya mutu sai mu ce ma Mai martaba me?” Ajay yace “Sai kace ma Me maraba me dai, tunda ba dani aka hadosa ba ai” Jay yace “Good, don haka stop the discouragement, no matter what, Walid is still ur blood saboda kana da grudges da shi doesn’t mean abu ya samesa sai nima kayi discouraging dina kar inyi abinda ya kamata, tunda kasan ba da kai aka hadosa ba pls back off” Bai jira cewar Ajay ba ya zaga ya bude driver seat ya shiga, Ajay dai ya dinga kallonsa, can kasan zuciyarsa yana jin bazai iya barin sa ya tafi shi kadai ba, kasa daurewa yayi kawai ya bude front seat ya shiga motar, Jay dai bai ce masa komai ba ya ja motar suka bar hotel din, babu wanda yace komai cikinsu har bayan kusan minti arba’in da fara tafiya, Ajay ne yayi breaking silence din cikin motar yace “Amma mun yi magana da kai ne nace maka i still have Walid grudges in mind? Na zata kafi kowa sanin i don’t hold grudges for long, saboda ba mu good term da Walid doesn’t mean I have anything bad in mind about him” Jay yace “Baka da grudges a kansa shi ne ka kamasa kwanaki kayi masa dukan kawo wuka?” Shiru Ajay yayi kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya karyar da kansa yace “Kai ma kasan ba mahaukaci bane ni, infact duk wanda ka ga zuciya ya sa na kai masa hannu to definitely da dalili me karfi sannan ni bana son dogon magana da bayani, kawai nafi gane duka, either ka dokeni ko in doke ka kawai a wuce wajen no long talk” Jay ya taɓe baki yace “Just little issue da ku ka samu a masallaci wajen karatu da shi shine har yayi deserving irin wannan dukan kamar ka kama barawo?” Ajay ya ɗan yi murmushi, and he went mute immediately, Jay ma bai sake ce masa komai ba, bayan kusan minti goma Ajay ya sauke ajiyar zuciya yace “I was heartbroken because Ina tunanin idan kowa bai min uxuri ba ko kuma bai yi considering dina ba kai bazaka yi haka ba, sai naga kafi kowa ma rashin considering dina a lokacin, ina ganin ka fi kowa sanin halina da abinda zan aikata da wanda bazan aikata ba amma kayi ignoring haka….” Jay yace “Look, ni ban ce Walid bai maka laifi ba, nasan abu ya hadaku ya ja kayi masa wannan dukan, amma ko ma wani irin laifi yayi maka bai cancanci irin wannan dukan da kayi masa ba gaskiya….” Ajay ya juya yana kallon Jay dake driving baya ko kiftawa, shi dai Jay Idonsa na kan titi, Ajay ya jinginar da kansa da kujeran motar yayi shiru, after some seconds yace “To Jeeddah ya bi har cikin dakinta da asuba….” Jay bai san sanda ya juya da sauri yana kallon Ajay ba ya ma mance gaba daya akan titi yake, har sai da ya kusa buge wani me machine banda Ajay yayi saurin swerving steering din motar, sai a sannan Jay yayi saurin concentrating kan driving din har suka wuce wajen, daga yanda ya rage gudun da yake zaka san he is very shock at what Ajay just said, bai iya yace ma Ajay komai ba har bayan minti biyar, a hankali Ajay yace “So bai yi deserving dukan da nayi masa ba ko?” Jay ya sauke ajiyar zuciya yace “But why did you decide not to say anything to anyone about this? Meye na boye wannan magana?” Ajay yace “For her reputation, nasan definitely za a canza al’amarin a basa different meaning a masarauta, and she will be painted black, shi yasa kawai naga babu amfanin fadin maganar….” Jay ya gyada kai yace “Haka ne” Ajay yayi murmushi yace “To yanxu ba gashi ya wuce ba?” Da mamaki Jay yace “But walid is very very stupid, ko dai ba shi da hankali ne? Shaye shayen da yake yi ne yake gaya masa karya or what?” Ajay dai bai sake cewa komai ba, Jay yace “But why didn’t you tell me about this, ni da sai nayi ma Mai martaba magana, da ko zaman meeting baza ayi ba lokacin….” Ajay ya ɗan yi murmushi yana kallon titi, can ya kallesa, a hankali yace “Da attitude din da kake nuna min ko kuma da Malice din da kake keeping da ni zan samu courage din tunkarar ka da wannan maganar? Tell me where to start from a lkcin?” Jay yayi shiru, sai kuma ya girgiza kai gently yace “Let’s face the present and say nothing about the past forever Ajay….” Ajay dai kallonsa kawai yake, Jay yace “Yeah, if possible we should erase the memories of 12 months ago, let’s assume those 12 months never happened, let’s assume those months never exist in our history” Ajay bai ce komai ba, ya dauke Idonsa a hankali daga kan Jay, sai a sannan Jay ya ɗan kallesa yana ci gaba da driving dinsa, after almost 20 minutes of silence Jay yayi breaking silence din yace “So now, you left her under whose care before leaving the Emirate?” Ajay yace “But you didn’t consider that before fixing the trip today” Jay ya girgiza kai yace “Ba haka bane ina son mu gama da Calabar da wuri ne in tafi Nijar in huta, i will spend months before coming back to Nigeria, staying in the Emirate is pissing me off saboda bana son ana min maganar Hadiyah” Ajay yace “Ohk, i left her with Yakumbo” Jay bai sake cewa komai ba, Ajay ya ɗan kallesa kamar yayi magana kamar kar yayi, sai kuma dai a hankali yace “She is pregnant….” Jay ya kallesa suka hada ido, shi ya fara dauke idonsa ya mayar kan titi calmly yace “Probably i observed that before you…. So what is the gestational age?” Ajay yace “6 weeks and some days, and… She is carrying twins” Jay ya juya ya kallesa yace “Really?” Ajay ya gyada masa kai, Jay ya lumshe ido ya bude, ya ɗan yi murmushi yace “Maa sha Allah, that’s a good news, Allah Ubangiji ya raya su cikin koshin lafiya, congratulations, but da ka bar ta a Kano na wani lokaci har taji sauki” Ajay yace “Hajja refused, ita ta sa aka je aka daukota” Jay yace “To me zata mata da baza ayi mata a gidansu ba…..” Ajay dai yayi shiru bai ce komai ba, Jay ya duba wayarsa dake ringing yaga number Walid, dagawa yayi ya kai kunne, after some seconds yace “Confluence Bridge? Ina ne haka? Ohh Murtala Mohammed Bridge kenan? Ok we are almost there” Ajay dai kallonsa kawai yake, ya jira har Jay ya katse wayar yana concentrating gaba daya a tukin da yake yi sannan yace “Me za ayi a Confluence Bridge?”


