Hausa novels

Fentin Zina Page 36 Hausa Novel

FENTIN ZIN🅰️EESHERT ADAMUPAGE 36.–Jiki a sanyaye ya bude motar shi ya shiga, sai daya dauki kusan mintuna biyu kamin ya iya tada motar ya bar wajen.Karar motar shi ita ta ankarar da fateema da cewar ya wuce hakan yasanya zuciyarta cikin kunci, bata san tana zubar da hawaye ba sai da taji fateema da shigowarta kenan yanzu don ta dade a bakin kofa tana kallon addan tata ta ce lokacin da take matsowa kusa da ita tasa hannu ta share mata hawayen. Adda kina cikin matsananciyar soyayya amma kiyi hakuri fa kada kiji kamar na raina kine yasa na fadi hakan! Sai ta girgiza kai ta cigaba da cewa, gani nayi shiru na bazai haifar da komai ba face cuta a gare ki, tun lokacin muna asibiti ina lura dake kikan kasance cikin nishadi da walwala idan kika ji muryar shi koda baki ganshi ba sannan idan ya shigo ward din kina yawan satar kallonsa wanda ni kam duk ina hankalce da ke, ganin baki mun maganar bane yasa naja baki na nayi shiru, nidai abunda zance miki yanzu shine ki sassautawa zuciyarki kada kiyi saurin yanke hukunci domin nasan halinki adda zaki iya korar shi alhalin kina son shi Kuma baki san wani irin zuciya gare shiba wani yana iya barin duk abunda yake so idan an wulakanta shi musamman idan yaga kamar da raini a cikin al’amarin, kiyi tunani sosai kafin ki yanke hukunci.Gabanta ne ya fadi jin fateema tace zai iya barinta, ita kam data shiga uku to ai bata ce bata son shi ba lallai idan ya gudu bai mata adalci ba, toma idan bai sake dawowa ba ya zata yi? Ina zata kai dinbin soyayyar da take mai? Ya Allah ka agajeni kasa ya dawo!. Duk wadannan maganganun a zuciya take yin su.Fateema ce ta dafa ta. Ta daga ido ta kalleta. Fateema ta sauke numfashi tace Adda kina son shi ko? Domin tun fitan ki ina tsaye a bakin kofa har kika dawo na kuma leka nagan ku na kuma ji duk abunda kuka tattauna da naga kin juyo ne sai nayi sauri na koma na tsaya daga bakin kofa, amma adda bai kamata ki fada masa maganganun da kika fada masa ba a farkon zuwan shi kamata yayi kice masa zakiyi tunani.Kuka Ameena ta fashe dashi wanda ya sanya fateema cikin rudani da firgici, kaico na fateema ina tsananin so da kaunar ammar amma kaddara a yanzu ta riga ta zana layin da saidai in hakura dashi kuma yin hakan tamkar saida rayuwa ne a gare ni. Ta karashetana mai fashewa da sabon kukan daya fi na farko don gani take karshen rayuwarta ce ta zo idan har bata mallaki ammar ba.Lallashinta fateema ta shiga yi tana cewa kada kice haka adda insha Allah zai dawo kuma zaku fahimci juna dashi wata kila ma a hada da bikina a yi naku ma.Girgiza kai Ameena tayi fuskarta cike da hawaye tana karadana sani dayin Allah wadai da Ahmad tana kuma tsine mishi tare da mishi munanan fata tace fateema na riga da na cutar da rayuwata cutarwa mafi muni da illatar wa, na shiga uku fateema koda shi ya soni na tabbata mahaifiyar shi baza ta taba sona ba, ba kuma zata amince danta ya sure ni ba.Kallonta fateema keyi tana neman karin bayani.Ameena ta ci gaba da cewa itace likitar data fara tabbatar mun da inadauke da ciki. Itace likitar dana rika yiwa magiya da roko kan ta zubar da cikin jikina. Itace likitar data rika yimun nasiha kan naji tsoron Allah kada na sake aikata wani laifin bayan wanda na aikata din. Tayaya kike tunanin a lokacin da taji zancen danta yana neman auren irin wannan yarinyar zata amince? Na tabbata bazata amince ba.Ta karasa fada tare da yin zaman ‘yan bori a saman tabarmar dake shimfide a cikon shagon tana sauke ajiyan zuciya kamar wacce ta yini tana kuka.Zama fateema tayi kusa da ita ta kamo hannunta cikin nata tace babu komai babu abunda yafi karfin addu’ah, Allah shine masanin komai shizai bamu mafita kuma ina sa rai da cewar zai tankwara mana zuciyarta zata bada hadin kai insha Allah.Hm Allah ya yarda. Ameena ta fada cikeda rashin sanin abun yi.*****Ammar tuki yake kawai amma hankali shi da tunanin shi suna can wajen Ameena da a yanzu ya gama yarda cewar itace mahadin rayuwar shi, bai taba sanin yana da cikakkiyar lafiya a matsayinshi na da na mijiba har saida ya hadu da Ameena bai tsaya a ko ina ba sai gidan su abokin shi daya dawo gari sati daya daya wuce, horn yayi mai gadi ya bude mishi gate ya danna hancin motar cikin gidan yayi parking ya fito ya nufi cikin gidan kai tsaye part din abokin nashi ya nufa kasancewar bai samu kowa a falon ba.Samu yayi yana waya da sabuwar budurwar shi da suka hadu a can garin daya je irin wayar nan dai da samari da ‘yan mata suka lalace akan sa na soyayyar shan minti. Girgiza kai yayi cike da takaicin wannan halayya ta abokin shi daya mayar da mata tamkar rigar sakawar shi yayi ta lalata diyoyin mutane anyi nasihar anyi yaki ji karshe ya kyale shine kawai ya zuba mai ido, ya rantse banda cewar dan uwan shine da babu abunda zaisa ya cigaba da abota dashi domin ya gaji da halin sa kuma sosai sukayi sabani a hali.Jin motsi a bayan shine ya sanya shi juyo wa. Ba kowa bane face Ahmad wanda ya lalatawa Ameena rayuwa ya jefata cikin tarin kuncin da take ciki.Ah yane bros yaushe ka shigo ban sani ba? Ya fadi haka ne at same time tare da fadin pardon zan kira ki. Daga haka ya kashe wayar gami da juyowa gaba daya yana fadin hey friend naji dadin ganin ka like kasan ina tunanin zuwa gurin ka anjima.Okay! Ammar ya fada tare da zama saman cushion din dakin ya shiga bin ko ina da kallo ba tare dama ya san yayi hakan ba sakamakon tunanin daya fada.Friend meke damun ka naga duk kayi wani iri?.Hum bari kawai wallahi duk na gaji ne! Ya fadi hakane don baya son Ahmad yasan ainahin abunda ke damun shi don’t hankalin shi bai kwanta daya fadawa wani damuwar shi ba idan ba ta gagara ba.Toh shikenan amma sai fuskar ka tamun kama da wanda ya apfawa tarkon soyayya a karon farko. Ahmad ya fada ba tare da ya kalle shi ba.Haka dai kake gani but am ok kawai gajiya ce a tare dani yanzuma zan koma dama naje wani waje ne nace barin biyo mu gaisa.Naji dadin haka friend amma daka bari bayan isha ka rakani gurin wata beb dita.La la la la bada ni ba kaima kadai san bazan je ba domin wannan dabi’ar taka tana matukar kuntata rayuwata and kai baka ma da niyyar gyarawa.Waya fada maka? Kai dai ayi sha’ani kawai Allah zai shiryemu idan lokacin hiriyar mu tayi.Kana da matsala wallahi friend bai kamaci musulmi kamar kai ya dinga fadin shi bazai shiryu ba har sai Allah ya shirye shi, yazo a cikin ahalari!.Ho ustazu naji to amma dai zaka rakanin ko?.A’a kaga ma tafiyata. Ya fada tare da mikewa ya nufi bakin kofa yana dagawa Ahmad hannu.Tabe baki Ahmad yayi bayan fitan ammar yace ai sai mun more mu wataya mu shana a rayuwar nan duniya saita san da mu in banda kai dan uwa nane kuma ina kaunar ka ai da tun tuni munyi hannun riga halinmu ya saba kai ustazu ne ni kuma dan sharholiya. Ya karasa tare da sakin wani irin dariya irin na ‘yan duniyan nan.*****Ammar bai zame ko ina ba sai gida, a falo ya tarad da ammyn shi zaune eye glass manne a fuskarta hannunta rike da remote na TV tana chanja channel Karasowa ciki yayi bayan yayi sallama ta amsa ya zo kasan kafafunta ya zauna ya dora kanshi saman kafafunta. Ta ajiye remote din dake hannunta ta shiga shafa sumar kanshi cikin soyayya da kauna irin ta tsakanin uwa da da.Tun bayan daya baro gidan su Ameena sai yanzu ya samu natsuwa ya shiga jero ajiyan zuciya babu kakkautawa, lokaci daya kuma ya shiga tashin hankali sakamakon tuno maganganun Ameena da tayi game da mahaifiyar shi,.Yana so ya mata maganar amma ya rasa ta inda zai fara don yana tsoron faruwar abunda Ameenan ta hasko mai zai iya faruwa. Daga kanshi yayi ya kalli mahaifiyar tashi yaga itama shi take kallo sai ya dan yi kasa da kanshi yace Ammy ina cikin wata damuwa da rudani sannan ina cikin bukatuwa da wani abu da nike jin lallai idan na rasa shi nima zan iya rasa kaina.Shiru ammy tayi tana sauraren shi saida ya kai aya tukunna tace, subhanallahi menene shi wannan abun da yake neman shiga tsakanin dana da farin cikin sa?.. Menene shi ka gaggauta fada mun ka sani cewar banida wani abunda na tsana face ganin ka cikin damuwa don haka ka kwantar da hankali ka fada mun insha Allah zanyi iyakar kokari na wajen ganin na baka shawarar data face idan kuma inada dama in yaye maka damuwar ka………….EESHERT ADAMU

Back to top button