Fentin Zina Page 29 Hausa Novel
*****–Maryam ce ta soma zuwa tana kokarin rungumo Abdul saidai ya goce ya nufi inda Ameena take tana masa murmushi yana mayar mata da alamu ya manta da maryam a falon ya rungumeta ya mikar da ita tsaye yana sunsunar wuyarta kana ya koma yana mata sumbata a saman lebbanta har na tsawon dakiku kafin ya saketa yana fuskantar ta yace ina fatan kin yafe laifukana a zuciyar ki? Ya fadi hakan da murmushi mai salo.Lankwasa wuya tayi tana kara dagula sauran natsuwarshi tace comon ruhul-jasad kaima kasan kaiba mai laifi bane a gareni amma idan ma kayi din gimbiyar ta jima da yafe maka. Kara kankame hannayenta dake cikin nashi yayi yace nagode rayuwata, dan Allah kada ki barni komin rintsi gareni kece hasken fitila ta kece mai sama mun natsuwa kiyi hakuri da dabi’una zanyi kokarin gyarawa ko domin farin cikin ki na miki alkawari.Da yake ya bada baya wa kofa ne shiyasa ya manta da batun Maryam tana falon don inda ya wuceta nanta daskare tana hawaye.Ameena ganin maryam na zubarda kwalla saita dan bata tausayi nan take taji bata kyauta mata ba, kallon cikin ido tama Abdul mai cike da ma’anoni tace kada ka damu ai Ameena takace! Idan kaga nabar rayuwarka to dayan biyu ko a fitar da gawata ko kuma ka sakeni kamar yadda kayi. Da sauri ya girgiza kai yana fadin wancan ma sai yanzu na kara tabbatar da girman kuskuren da naso aikatawa kaina kuma hakan bazata sake faruwa ba nayi alkawari.Dats my man……Kukan maryam shiya dawo dashi hayyacin shi, da gudu ta shige daki ta kife a gado tana kuka mai ban tausayi, kukan da daga ji kasan tun daga karkashin zuciyarta yake fitowa.Kallon kofar dakin maryam din yake yana son zuwa saidai yana tsoron dan shirin daya fara samu ka guje masa don haka ya gwammace yayi hakuri zuwa anjima zai rarrasheta da kalamai yasan zata hakura. Kallon shi ya dawoda kan Ameena sai tayi murmushi ta nuna mishi kofar dakin tana jinjina kai alamar ya tashi yaje, girgiza kai yayi itama ta kara jinjina kai tana mikewa tace zan dan shiga cikine idan kana bukatar wani abu sai ka kirani ga abincin ku a kan dinning ni na ci nawa. Tana kaiwa nan a zancenta ta shige da takunta mai daukar hankali. Bayan ta yabi da kallo yana hadiyar miyau daga bisani yaja kafafunshi zuwa dakin maryam ya shiga bata hakuri cikin kalmomin soyayya masu tsayawa a zuciya ai kuwa baiyi wuyan shawo kanta ba nan suka komo palo zuwa dinning suka ci abincinsu cikin yin hira jefi jefi har suka kammala.*****–Bangaren Ameena tana shiga daki dama bata ci abincin ba kamar yadda ta fadawa Abdul sai ta rufe da makulli don bata bukatar hayaniya, ta jawo kularta ta bude fridge ta dauki multina guda daya don bata rabo da drinks duk da ba baki take yi ba domin kanta take ajiyan su.Ta zauna ta hau cin abincinta cikin nishadi.*****Yau kwana ya zagayo kan Ameena, maryam tunda ta tashi take yada habaici ta fadi wannan ta fadi wancan saidai bata samu ko kallon arziki bane daga Ameena.Ita kuwa Ameena tana sane tayi banza da ita don bahaushe yace sai an kula kashi yake doyi. Ta ba banza ajiyarta ta cigaba da tsabgar dake gaban ta, babu ta inda maryam bata takali Ameena don neman fitina ba amma Ameena taki kulata hakan ya kona ranta sosai kuma ya tsaya a zuciyarta kwarai.Kafin ayi kiran magriba Ameena ta kammala komai ta jera a kan dinning ta koma ta feshe ko ina da air freshner mai kamshin dadi ta wuce ta shiga daki saida ta bari aka idar da sallah kamin tayi wanka a gaggauce ta fito don ta tabbata war haka ya kamata yana gida saidai idan ya biya wani waje ne don haka light make up tayi ta zabo wata doguwar riga ta atamfa mai dinkin bubu an zuba stones a gabansa sunyi matukar jeruwa sun zauna daram ta sanya a jikinta tayi daurin ture kaga tsiya ta karkata shi gefe kana ta dau glass dinta mai kusan launin kayan ta sanya takalmanta lokacin ne kuma taji karar tsayuwar motarsa, ta gaggauta fesa turare a jikinta ta dau mayafi ta yafa ta fice waje.Samu tayi yana gyara parking sai ta dan dakata saida ya gama ya bude kofar ya fito gaba dayansa ba tare da jakarsa ba. Ta karaso da sassarfa ta rungume shi tana sauke ajiyan zuciya ya dago habanta suka kalli juna cikin ido na tsayin wasu dakiku kamin ta katse shirun da cewa da fatan ka dawo lafiya cikin aminci abun kaunata.Ina lafiya da fatan na same ku lafiya kuma. Tace insha Allahu.Daga haka suka jera hannunsu sarkafe dana juna suka shiga falon, sannan maryam ta fito ganinsu tare ba karamin dukan zuciyarta yayi ba haka dai ta daure ta hadiyi abunda takeji ta kakalo murmushin dole wanda akewa lakabi da yake ta sanyawa fuskarta tace baby sannu da dawowa.Kallonta yayi sai ya sakar mata murmushi tare da cewa yawwa sannu baby ya kike ya gidan, hope komai lafiya? Ya fada still idanunsa a kanta.Gyada kai tayi tace sai kuma kewar ka ba. Ta fada tana mai fari da idonta da suke kanana.Ameena tayi saurin cewa muje kayi wanka an kusa kiran isha.Ok. Yace tare da bin bayanta don bata bashi kofar musawa ba.Koda suka shiga daki da gangan Ameena ta shiga suka yi wankan tare suka fito suna dariya da hira, taimaka masa tayi ya shirya itama ta koma nata dakin ta sauya kayanta i zuwa kanana ta kara komawa dakinshi suka fito falo ya tafi masallaci ita kuma ta koma daki tayi sallah.Da akazo kwanciya ta dauka yanzu zai danyi nisa sakamakon taga amarya har yanzu bata fara complain ba so tayi zaton yayi magani ne saidai ashe zatonta ba gaskiya bane domin yadda dai aka saba haka dince ta kasance saidai abunda yafi damunta kullum matsalarsa kara girma takeyi sannan shi ya kasa fahimtar cewa ita tana cutuwa har ya iya wani hobbasa na neman magani ina, kullum shi tunanin shi wai bazai sha magani ya nakasa kan shi ba, tun tana masa maganar magani harta daina ta fawwalawa Allah ta sanya wa kanta dangana da hakuri.Yaudai kam ranta ba karamin sosuwa yayi ba don koda ya samu natsuwa daga gareta ya sauka lokacin ita kuma taji bukatuwa na musamman ta dinga masa magiya a kan ya taimaketa ya dan sama mata natsuwa itama ko kadan ne karshe ma yakiceta yayi daga jikin shi ya juya mata baya, kallon shi kawai take hawaye na tsiyaya daga idanunta domin ita kadai tasan halinda take ciki sai kuma wanda ya taba riskar kanshi a cikin irin yanayin da take ciki.A fusace ta mike taja towel ta daura ta nufi ban daki tayi wankan tsarki ta fito sai tsaki take ja a cikin ranta fiye da misali, ta rasa wani irin son kai ne dashi, takan rasa me yake daukar rayuwar aure, abubuwa biyun nan su suka fi damunta dashi, rashin kyakkyawar mu’amala ta aure a matsayin ta na mace lafiyayya sai kuma saurin fusata da rashin uzuri. Haka ta kwanta tana jin haushin shi sai data kunna wayarta ta shiga app din Qur’ani na karatu ta fara karanta suratul baqara, ta karanta shafi biyar kafin ta kashe tayi addu’ahr bacci ta rufe ido.Can cikin dare maryam ta fito ta hau bubbuga musu kofa, kamar a mafarki sukaji bugun kofar tashi sukayi dukkansu adan tsorace sai shi Abdul dinne yayi karfin halin budewa ganin maryam ce sai ya sauke ajiyan zuciya tare da fadin lafiya kike buga mana kofa da wannan tsohon daren?Kyabe baki tayi tace ji nayi kamar zan mutu tsoro nike ji dan Allah ko zaka zo mu kwana idan kuma baza ka iya ba ni zan kwana tare daku anan amma bazan iya kwana ni kadai ba.Shiru yayi kamar yana tunani can ya nisa yace ina zuwa, sai ya koma ya samu Ameena ya mata bayanin abunda ke faruwa harda langwabe murya irin ya tausaya mata dinnan, ya karashe da cewa yanzu ya kike gani tazo mu kwana anan din tare me Ko kuwa ni in bita muje in taya ta kwana?Kallon kama rainawa kanka wayo take mai yace bakice komai ba! Ai kuwa dai bazan yadda da wannan shashancin a cikin gidannan ba taya zata ce ta kasa bacci bata daiyi addu’ah bane kawai taje idan tayi addu’ah ta kwanta baccin zai zo.Yace haba Ameena tace albarkacina mana kinga fa sabuwace a gidan nan sai a hankali zata saba.Eh nima ai da aka kawoni da hakan na saba lokacin ma ni kadai a cikin gida.Haba ki daina haka mana wannan halin ai bashi da kyau ko kadan.Ta juya kwayar idonta ta kalle shi tace ban amince ba kuma ban bada kwanana ba. Daga haka ta juya baya ta kwanta tana jin zuciyarta na mata zafi………. *EESHERT ADAMU* *MATAR MAJEEDADI* ✍️




