Karfe A Wuta Chapter 74 By Ayshercool
*BRIGHT PENS SECOND BATCH*KU KASANCE DA LITATTAFAN BRIGHT PENS A SECOND BATCH, NA ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL).MUTALLAB (NIMCYLUV)ZAYTOON (ZEE KUMURYA) DA HADARIN GABAS (NAZEEFA SABO NASHE)Idanunta yake kallo, jikinsa a sanyaye amma yayi shiru bai yi magana ba.”Kayi magana, ka gaya mini wacece wannan? Bani ba ce a jiki, amma meyasa take kama da ni? A ina take?”Still bai yi magana ba, ƙara tsananta riƙon da tayi masa ta ƙara yi, cikin matsanancin kuka tashin hankali da ƙaraji, take jijjiga shi ta ce “Ka yi magana, ka gaya mini wacece meyasa take kama da ni? Kuma a ina take?”Viper ya ce “Ban santa ba, tsintar su nayi, naga ya dace kema ki gani, ban taɓa jin kin ce kina da yar uwa da ku ke ciki ɗaya ba, amma kamarku ta ɓaci da ita, shiyasa na ga ya dace na baki ki gani””Ka san wacece, ka saba yi mini wasa da hankali wasu lokutan, Please na roƙe ka, don’t play with my emotions, ka gaya mini dan Allah” tayi maganar tana kallon ƙwayar idonsa.Ya ɗan jima yana kallonta, kan ya saka hannu ya cire hannunta daga riƙon da tayi masa, yana riƙe da hannunta ya ce “‘yan gidanku yakamata ki tambaya bani ba””Tayaya zan tambaya? Alhalin a duniya babu abun da Abba ya tsana sama da nayi masa zancen mahaifina, ban san dalilin wannan mummunar ƙiyayyar ba, sun yi abun su ya riga ya wuce, amma ya nesan ta duniyata da mahaifina, duk wata hanya da zata saka na san in da yake, Abba ya tosheta wai ba wani abu da zai tsinana mini. Wani abu ne mai ciwon gaske da yake addabar zuciyata, ka fama mini ciwon da yake zuciyata, kuma ka bar ni a duhu, ka taimaki rayuwata wallahi ko Wacece wannan tana da alaƙa ta kusa da ni”Viper ya ce “How, an ce kowane mutum akwai irinsa guda uku a duniya…”Ba wani guda uku, wannan kamar nice a jikin hoton, kamannin nan sun yi yawa, ka wayar mini da kai dan Allah””Me ki ke so na ce, duk abun da zan faɗa miki ƙarya zan yi miki, ki je gidan abun da suka ce miki shikenan”Ta fizge hannunta, ta yinƙura zata tashi, jiri ya kwasota ta hau tangaɗi, ya riƙe ta, ta ɗan yi shiru ta samu nutsuwa, ta juya ta bar wurin.***Ramma kuwa kwana suka yi, Abdul yana juye-juye, ciwon cikinsa ya tashi, ko baccin kirki ba su yi ba, sai bayan sallar asuba ya ɗan lafa masa, ya din ga tofa fatiha da bisimillah tana bashi yana sha.Yana kwance a kan cinyarsa, tana ta shafa masa ruwan tofin a kan cikin, tana shafa masa, ya riƙe hannunta yana mayar numfashi.”Sannu Abdul” ya jinjina mata kai alamar yauwwa.”Wai wannan ciwon cikin, ka dudduba kanka sosai mana, kana likita amma ka din ga wasa da lafiyarka, kalli yadda ka ke shan wahala dan Allah””Tausaya mini ki ke yi?”Ramma ta ce “Duk rashin imanina, idan ban tausaya maka wannan wahalar ba, ya zan yi, idonka har ja yayi saboda wahala”.”Rahama ina ga ciwon cikin nan ne zai yi ajalina, har ƙasashen waje na je, an kasa gano menene”Dummm ta ji ƙirjinta ya buga, jin abin da ya ce, amma ta ce “Dan Allah ka daina wannan maganar, ka din ga addu’a ka cigaba da shan magani””Rahama baki san me nake ji ba ne, ina shan wahala fa” yayi maganar yana miƙa, tare da lanƙwashe yatsun ƙafarsa, hawaye na bin gefen idonsa, saboda azabar ciwo””Dan Allah ni ka daina wannan maganar” ya juya yayi ruf da ciki.”Idan na mutu zaki yafe mini?”Ta ce “Wataƙila, ai ni dama bana fatan na je gaban Allah ina neman hakkina a wurin wani, ko wani yana nema a wurina, a duniya nake fatan Allah ya saka mini abun da ka yi mini, da kai da wannan jakar matar”ya yi murmushi ya ce “Hakan ma na gode, alfarma ɗaya da zan nema, dan Allah rahama kar ki zubar mini da cikin nan, ina matuƙar son abun da yake cikinki””Wallahi sai na zubar tas, sai ya bi rariya, ni ka daina yi mini magana kamar wasiyya wasiyya, dan na tausaya maka”Sai da yayi dariya ya ce “Abubuwa ne suke ta hargistewa Rahama, komai ya cukurkuɗe, ban san ya abubuwan za su kaya ba, ina ta ƙoƙarin baki kariya ne iya yi na, duk da ni mai laifi ne” yayi hamma ya ce “Idan ya lafa sai na ji daɗi, gashi bacci nake ji, ke ma na hana ki bacci”Yayi maganar yana shafo fuskarta, ta saka hannu ta sauke hannunsa, ta shafa kansa ta ce “Kayi baccin, ko ka samu relief” ya juyo yana fuskantar cikinta, da yake shafe a jikinta ya ce “Bari na yi magana da yarona” maganar ta sa tayi daidai da jin motsi a ƙasan mararta.A haka bacci ya kwashe shi, ta zuba masa ido, tana jin tausayin sa, gaba ɗaya ya rikice saboda ita, ta ƙara lura da shaye-shaye da rashin tarbiyya ne kawai yake ingiza shi yake rashin mutunci.”Kayi haƙuri Abdul, amma komai ya kusa zuwa ƙarshe da yardar Allah”*****Walid ne ya magantu, dan tun shigowar Viper ya lura kamar yana cikin damuwa, ya ce “Mai zamani, ya ake ciki ne? Jikin ne ko wani abun ne ya faru?”Ya numfasa ya ce “Na yi abun da ka ce, Nabila”Walid ya ce “Masha Allah, ya ake ciki?””Ba ta da masaniya a kan hakan, things are complicated, ta shiga matsala daban daban, ta samu matsala da gidansu, an ce lallai ta bawa ɗan uwanta dama ya kama ni, she’s almost alone, kamar ban kyauta ba, na ɗora mata abun da ya fi ƙarfinta”Walid ya girgiza kai ya ce “Ƙaddara ce ta haɗa ku, kuma she’s not alone, tana tare da kai, muna cigaba da addu’a in sha Allah, komai zai dai-dai ta, ba ta gaya maka komai game da labarinta ba?” Viper ya girgiza masa kai.”Bata bani ba, amma na bata hoton, na ce taje ta tambayi yan gidansu””Ina jin alamun nasara, in sha Allah ka kwantar da hankalinka”Viper ya amsa da Allah ya sa.****Nabila kamar mara laka, ta fito daga wanka, jikinta ɗaure da towel, ta jiƙo kanta da ruwa, idanunta sun yi jawur, saboda ta yi kuka sosai da sosai.Kawai ta ɗaga kai ta ga Nasir a tsaye a ƙofar ɗakin, ta ƙara haɗe rai, ta ƙarasa tsane jikinta.”Nabila, lokaci yana cigaba da ja, kuma ke nake jira, haryanzu baki ce mini komai ba, ki gaya mini in da zan samu mutumin nan, ina ɗaga miki ƙafa ne saboda Abba, kuma nima ina jin nauyin aikata miki hakan”Buɗe wardrobe tayi, ta ɗaukko phant da breziar ta jefo kan gado.”Magana fa nake yi miki”Tayi masa banza, ta ɗaga breziar tana ƙoƙarin fara sakawa.”Nabila wai baki da hankali ne? A gaban nawa zaki saka kaya?””Ni na kawo ka? Ko ka manta bin maza nake yi? Ba abun da zai hanani saka kayana, ai yanzu ba kunyar wani nake ji ba”Galala ya bi ta da kallo, jakar da ta fita da ita, ta janyo, ta ciro ƙaramar wayarta da take vibrating ta ciro ta ɗaga ta ce “Hello V””Are you safe?””Yes Alhamdilillah””It seems you are bit disturbed””No at all”Yayi ajiyar zuciya ya ce “Kin tambaya ɗin?””A’a, ai bai dawo ba, yayi tafiya ne, ni yanzu ina jiran abun da zai kasance a kotu ne gobe in Allah ya kaimu, and su oga Walid su shirya, zasu kasance cikin shaidun da zamu gabatar a kotu fa””Shikenan, zan gaya musu””Yauwwa, gobe in Allah ya kaimu daga kotu zan wuce wurin ‘yan sanda, a kan case ɗin ka, Allah ya sa……”Nabila, wai me ki ka zama ne?” Nasir yayi maganar yana tunkararta zai fizge mata waya, ta ja da baya ta ce “Wallahi ka zo in da nake sai na saki towel ɗin nan, na saki ihu ai kai ka zo in da nake, get out from sight, wallahi Nasir ko me zaka yi ina kan bakana, ni, ko wani kaga zai yi mini ƙazafin da ka yi mini, yakamata ka tare mini, amma ka ɓata ni a wurin mutumin da bani da tamkarsa, wallahi ka cigaba da matsa mini kai ma sai na ɓata maka suna a gidan nan, ka fita daga rayuwata ba ɗan daba ba, ko uban wa zan kare ni naga zan iya. Ka je ka yi aikinka nima na yi nawa, kai ma ai amfani ake yi da kai, ake son kama shi ba dan taimkon al’umma ka ke son kama shin ba, get out please” yadda jikinta yake rawa take nema ta saki towel ɗin, muddin ta saki ba shi da kalaman da zai kare kansa da su.****Indabo ya kalli Abdul da yake zane yana wasa da mukullin motarsa ya ce “Wai meye ne, na ganka kamar wani mara lafiya?” Ya ce “Bakomai, ka yi haƙuri na san maganar yarinyar…..”A’a, ai ba maganar yarinyar nan zan yi maka ba Abdul, ka yi abun da ka ga dama, yau saura sati biyu ɗaurin aure ko wurin yarinyar da zaka aura duk ka kyauta. Magana ce zan yi maka a kan kuɗaɗen da nake sanya wa a account ɗin ka, balli na nema ya tashi, an naɗa kwamiti bincike a kan kuɗaɗen nan, shi ne nake son ka dawo mini da shi, na mayar kan balli ya tashi asiri ya tonu”Abdul ya yi sororo yana kallon Indabo .”Kake kallona kamar shashasha, ka dawo mini da kuɗi na ce, na mayar musu dama na ɗan jinkirta ne, idan komai ya tafi daidai ayi yaƙin neman zaɓenka da su, amma zan tanade su a kusa, da na ji ƙishin-ƙishin na mayar da su”Abdul ya ce “To, zan dawo da su” ya tashi ya fita.Bayan fitar Indabo P.A ya shigo, ya samu wuri ya zauna, suka gaisa da Indabo.Indabo ya ce “Yaya me ka gano?””Eh, ana bibiyarsa gidan sa na lay out, ba kowa a ciki, duk gidajen shaƙatawarsa, baya nan abokansa duk na neme su, na bibiye su, amma babu alamar sun san zancen yarinyar ma, amma na in da yake kwana ne, haryanzu ba a gano ba, ka san wayo ne da shi, wasu lokutan a asibiti yake kwana, amma sannu a hankali ana cigaba da bibiyarsa””Abdul ban san ya aka yi ya zama haka ba, yanzu idan na matsa tsaf zai yi wani rashin hankalin, yanzu ka duba ka gani, saura sati biyu fa auren sa, amma gaba ɗaya hankalinsa baya jikinsa, idan na matsa masa a kan yarinyar nan hauka zai yi mini, shiyasa nake bin sa a sannu, zai zo hannuna sai ya ci ubansa”P.A ya ce “Distinguish akwai matsala fa””Wace irin matsa kuma? Kullum cikin kiran matsala ka ke kwanakin nan”Ya gyara zamansa ya ce “Distinguish, yarinyar nan sumayya T ladan, sai buɗa maka aiki take yi, kuma duk yan siyasar nan a kanka ta fi cin kashinka, yanzu wasu matasa daga yankinmu, sun kafa wata ƙungiya suna wayar da kan jama’a, wai za su rubuta takarda kiranye za su yi maka, ka dawo gida babu abun da kake tsinana musu sai kwashe musu kuɗi”Indabo ya kalleshi ya ce “Kai ka taɓa ganin wanda aka yi wa kiranye a Nigeria? Rabu da su, ƙaryar banza ce, yanzu muna da abubuwan da suka fi wannan muhimmanci”.P.A ya ce “A’a honorable, kar a fara a kanmu, matasan nan fa da gaske suke yi, ka san yanzu muna zamanin social media ne, har cikin ƙauyuka suke bi, da gaske kiranye zasu yi mana””Ka je ka haɗa sojojin bakan da muke da su, a basu kuɗi, su je su karemu, da daƙile abun, sannan a saya musu fili a kafafen watsa labarai, su shiga su karemu”P.A ya jinjina kai ya ce “Shikenan, babu laifi za ayi hakan”****Nabila kusan raba dare ta yi, tana kallon hotunan matashiyar da yake hannunta, ta takura ƙwaƙwalwarta, wurin yin tunani, ko ita ce a jikin hoton, amma ita dai ba ta san lokacin da aka ɗauki hotunan ba, tabbas ta san ta nuna hotunan nan, akwai sabon rikici, sai dai ta shirya karɓar duk abun da zai faru, amma sai ta san wacece a jikin hoton.Gaba ɗaya ta ɗauki gaba da yan gidan, ba wanda take kulawa, ko abincinsu ba ta ci.Ta shirya tsaf cikin uniform ɗin ta, ta shirya ta fice.Nabila ce a tsaye a gaban kotu ta nemi kotu ta bata damar gabatar da shaidun da take da su, wanda ba ta gabatar ba a kotun baya.Kotu ta bawa Nabila dama, Nabila ta taso wata mata, matar ta zo ta tsaya a gaban kotu Nabila ta ce “Hajiya ko zamu iya sanin sunanki?””Sunana hajara wali””Wacece ke a wurin rahama?””Ni mahaifiyarta ce, ‘ya ta ce””Ko zaki iya yi wa kotu bayanin meyafaru”Mahaifiyar ramma, tayi bayani tiryan-tiryan.”Kin san wannan?” Tayi maganar tana nuna mata dattijon.”Eh, tare da shi muka yi ta ɗawainiyar zuwa kai rahama Asibiti””Shi ne ya dawo ya ɗauke ta?”Ta girgiza kai ta ce “Ba shi bane ba, wancan matashi ne”Nabila ta ce “Yanzu ina rahama take?”Cikin kuka ta ce “Ban sani ba, tun da ya ɗauke ta ban sake ganinta ba”.”Kafin ya zo ya ɗauketa meyafaru?”Ta goge hawayenta ta ce “Wata mata ce ta zo ta ce mu karɓi kuɗi, a rufe maganar, na ce ban yadda ba, hakkin ‘ya ta nake nema, shi ne bayan ta tafi ya zo ya ɗauke ta, bayan kwana biyu ya dawo ya ce mini na bashi kayanta, ta zama mallakinsa””Ko zaki iya gaya mana sunan matar?”lauyan gwamnati, ya nemi kotu ta dakatar da Nabila, tambayoyinta na ƙoƙarin ƙetare iyaka.Ya taso zuwa gaban majaifiyar ramma ya ce “Hajiya wanda ya zo ya tafi da itan, bayan ya tafi da ita, meyasa baki sanar da jami’an tsaro ba?””Na sanar da su, amma suka ce na je gida za su neme ni””Da basu nemeki ba kin koma?””Na koma har na gaji, amma babu wani cigaba””Sai aka neme ki aka rasa, ko sama ko ƙasa””Bibiyar abi mini hakkin ‘ya ta da nake yi, ya sanya aka fara yi mini barazana, shiyasa na bar gidan” ya yi wa kotu godiya ya koma ya zauna.Nabila ta sake komawa gaban kotu ta kalli dattijon nan ta ce “Baba a kotun baya, ka amsa kai ne ka yi wa rahama fyaɗe, shin da gaske kai ne ka yi mata fyaɗe?”Ya girgiza kai ya ce “Cewa aka yi idan na ce bani bane ba, abun da ya samu rahama zai samu ‘ya’yana”.”Meyafaru ranar da abun ya faru?””A ranar aka ɗaukko ramma daga ƙauye, akwai ƙanin matar gidan ya zo a buge, ya tambayeni matar gidan sun dawo, na ce masa a’a, amma ya shiga, bayan wani lokaci ya fito ya ɗauki motarsa ya tafi. Sai bayan zulai ta dawo daga sayayya, ta fito tana ihu, ta ce na zo na gani, muka tarar da ramma a kwance a ɗakin girki, cikin jini”Nabila ta ce ta gama tambayoyin da zata yi, mai shari’a ya ɗaga shari’ar zuwa sati biyu domin yanke hukunci.Suka fito tare da barrister Habib da mahaifiyar ramma, da yaran dattijon, ta ce “In sha Allah, mune ke da nasara, hukuncin da kotu zata yanke zata yi mana adalci”Barrister Habib ya ce “In sha Allah, komai ya kusa zuwa ƙarshe”Nabila ta ce “Zai dai zo, burina kawai a wanke baba, daga nan mu ɗora da cigaban shari’a” iyalan dattijon suka din ga yi mata godiya.FEW DAYS BACKCikin tsananin mamaki, kankarofi yake kallon Nabila. Ya ce “Barrister, ke ce da kanki a office ɗina? Ya aka yi ki ka san wurin nan?”Tayi murmushi ta ce “Ba abun mamaki bane ba, matambayi ai baya ɓata, yau gani a ofishin masu ƙasa”Ya ce “Allah ya sa ba laifi nayi ba aka zo kama ni?”Ita ma murmushin ta yi masa ta ce “Yan sanda ai su ne suke kama mutum” ya bata izinin zama.Ta samu wuri ta zauna ta ce “Na yi sa’a, kana kano baka tafi Abuja ba kenan?””Eh, ina hutu ne, amma haryanzu mamaki nake yi, yadda aka yi ki ka tako da kanki, ki ka zo har in da nake”Ta numfasa ta ce “Ka san komai dalili ne yake kawo shi””Haka ne, bari na saka a kawo miki abu mai sanyi”Ta ce “A’a, Alhamdilillah tambayoyi ne nake da su a gareka Yallaɓai””To gimbiyata ina jinki””Case ɗin da nake yi, na yarinya da aka yi raping, ashe a gidanka aka yi. Na sake komawa na lura da sunan street ɗin sunanka ne, kuma na tambaya aka nuna mini gidan aka ce naka ne. Abun ya ɗaure mini kai, sai dai na jajje amma ban samu abun da nake so ba, matar gidan ta koreni, kusan sau biyu ma, yaya aka yi haka yallaɓai?”Yayi murmushi ya ce “Waye ya ce miki gidana ne?””Sir gidanka ne mana, Mu’azzam wada kankarofi street, kuma aka nuna mini gidan aka ce gidanka ne, sir ban yi tsammanin haka daga gareka ba, ɓoye mai laifi a ɗorawa wanda bai ji ba bai gani ba mai gadinka?””Nabila, ina iyakar ƙoƙarina, am even supporting you, baban yaron nan abokin adawata ne, matata kuma akwai yara a tsakanin mu, bai kamata na tona mata asiri haka anyhow ba””Amma yarinyar mutane da aka zalunta fa? Maigadinka da aka rufe ba da laifinsa ba fa? Wannan ba hujja ba ce ba, what if ɗanka aka yi wa haka? Haba yallaɓai””Nabila, lamarin ƙasar nan ya wuce duk in da ki ke zato? Dole sai mutum yana lissafi, amma in tambaye ki mana? Waye ya ajiye miki tarihin Bunkure a Office ɗin ki? Waye ya tura miki message ɗin babar ramma? Duk kina tunanin wannan, ko kuwa kawai sabgarki ki ke yi?” Waro ido ta yi tana kallonsa.”Mayar da idanun madam”Cikin mamaki ta ce “But how?””Through barrister Habib my dear. Ba zan tona wa yaron asiri kai tsaye ba, saboda ubansa ne tushen lalata shi, ba kuma nayi haka ne dan na ɓoye laifinsa ba, ina jan ƙafa a lamarin ne, saboda ki gano komai a sannu, yadda babu mai zargina, duk da akwai jiƙaƙƙiya tsakanina da ubansa.Mahaifiyar ramma na tare da ni, ni na saka aka ɗauketa, tun kan a illata ta saboda case ɗin nan. Zan haɗa ki da ita, zata yi miki bayanin komai, amma ki daina zargina a kan ɓoye mai laifi, am supporting you, program ɗin ma da ki ke yi am supponsoring the program sweetheart, ki daina zargina please, tabbas a gidana aka aikata laifin, kuma ina iya ƙoƙarina a kai madam. Ki je ki cigaba da aikinki, zan cigaba da ƙoƙarina in taimaka miki”Saroro tayi tana kallon kankarofi kamar sokuwa.”Akwai alamar gajiya a tare da ke, ki je zan saka Habib ya kai ki in da take””Amma duk tsawon wannan lokacin, kuka rufe ni ka ke yi mini yawo da hankali?””Akwai dalili ne, amma ki yi haƙuri dan Allah, a dalilin haka aka saka miki wuta a office, aka kusa taka ki da mota, duk dan ina tsayawa ina tsawatar wa ne, akwai hatsari a abun da ki ke yi nesa ba kusa ba, shiyasa nake taimaka miki ta ƙarƙashin ƙasa, amma kiyi haƙuri” ba ta ce masa uffan ba, ta ɗauki jakarta za ta fita.”Ina baƙonki kuwa? Idan kun sake haɗuwa ki ce ina gaishe shi” ta tsaya ta waiwayo ta ce “Wane baƙon kuma?””Viper” ya amsa mata kai tsaye.”Ka san Viper?”Kankarofi ya ce “Na san shi, akwai labari mai sarƙaƙiya ne, amma kar ki matsa, ki bi a hankali, zai kawo ƙarshen labarin, kamar yadda ya faɗa, a sauka lafiya abar ƙaunata” ba ta iya magana ba, ta murɗa ƙofar ta fice.Tun a hanya ta kira barrister Habib, take yi masa masifa, a kan abun da ya yi mata, ya din ga yi mata yawo da hankali da nuna bai san komai ba.Sai da suka haɗu, yayi ta bata haƙuri, yana ƙara yi mata bayani, kankarofi yayi mata kwarjinin da bata tsigale masa ba, amma ta yi wa Habib ta tas.****Nabila tana tafe tana kallon hotunan hannunta, ta kira Viper ya ɗaga ta ce “V ina wuni?””Lafiya ƙalau, ya ake ciki?””Ina hanya zuwa zan yi””To, Allah ya kawo ki lafiya”****Ramma ta tsurawa Abdul ido, ya ce kunun gyaɗa yake so, yana sha yana waya, ya ajiye kofin kunun ya ce “Daddy ni dai dan Allah ka yi haƙuri, wallahi ba zan iya fito maka da rahama ba”Ashariya Indabo ya din ga zabga masa, ya ce “Wallahi zan saka jami’an tsaro su kama ka, su ci ubanka, uwar yarinyar nan ta bayyana a kotu, an ambaci sunanka, duk da ba a faɗi cikakke waye kai ba, ga maganar kuɗi na yi maka, duk ka yi kunnen uwar shegu da ni, Abdul kana son ka gama da duniya lafiya kuwa? Dole sai ka tozarta ni?””Daddy ba tozartaka zan yi ba, makomar rahama nake dubawa ita ma….Wata ashar ɗin indabo ya lailayo, kamar ba babba ba, ya gama masifar, Abdul ya ajiye wayar ya dafe kai.”Kai ma da naci kamar me, ka fitar da ni mana, ko ma me za ayi mini ayi mini, sai ɓoye ni ka ke yi kamar ciwo, ni kaina tun ina masifa har na gaji, haba dan Allah” tsaki ya ja, ya tashi ya bar mata dining ɗin.***”Abba ya yi tafiya, yau nake saka ran dawowarsa, zan nuna masa hoton nan, na ji mai zai ce, tun da kai kaƙi gaya mini wacece?””Yaya shari’ar ta kasance?””Alhamdilillah, babar ramma ta je kotu ta bayar da shaida, ina jin alamar nasara in sha Allah””Mhmm, a ina aka ganta?””Ta gudu ne wani wuri ta ɓuya, daga baya da taimakon barrister Habib, muka ganota”Viper ya jinjina kai ya ce “ya nawa, ni ya ake ciki?””Shiyasa na zo ai””Ok””Kamar yadda na fara gaya maka jiya, dole ina buƙatar su oga walid, da wannan bugaggen a kotu su bayar da shaida””Wane bugaggen?””Oho ni na san sunansa ma? Amm sannan sai ka yi haƙuri, duk wasu rashin ji da ka yi, sai mun yi exposing ɗin su a kotu””Rashin ji kamar yaya?”Ta kalleshi ta ce “Kamar yadda ka yi mana, sara suka, ƙulla wiwi black market duk da ka yi”Haɗe rai yayi ya ce “Amma ba prison zan koma ba ko?””Idan ta kama ai dole ka koma”Ya ce “What? Gaskiya ki yi yadda zaki yi, ba zan koma prison ba, wanda nayi 5yrs fa?”Ta zumɓura baki ta ce “Ni na ɗaureka, sai abun da ya kama kawai, bari na je gidan, na ji wadda zamu yi da su, sai anjima”*****Nabila ta tafi ɗakin Abba, domin amsa kiran da yayi mata, ta tafi bakinta ɗauke da addu’a, ta shiga ɗakin da sallama, suka amsa ban da Abba da yayi shiru ransa a ɓace.Ta je ta durƙusa ta ce “Abba gani””Nabila ban isa na gaya miki magana ki ji ba ko?” Tayi shiru ta sunkuyar da kai.”Dole sai kin nuna wa duniya cewa ban haife ki ba ko Nabila? Kin nuna mini iyakata, ban isa na nemi alfarmarki ba kenan ko Nabila? Sai kin tozarta ahalin nan gaba ɗaya ko Nabila?”Ta girgiza kai ta ce “Abba bani da wannan burin, kuma wallahi ba zan taɓa aikata wani abu da zan janyo maka zagi ba. Amma dan Allah Abba a yanzu, ka yi mini wani taimako, saboda zatin Allah kar abun da zan nema ya ɓata maka rai”Ta miƙa wa Abba hotunan, da Viper ya bata, ta ce “Dan Allah Abba wacece wannan? Ni dai na san ba ni ba ce ba, dan Allah Abba ko kana da masaniya a kan ta jikin hoton nan.Abba ya saka hannu, ya karɓi hotunan yana dubawa.Ya gama ƙarewa hotunan kallo, ya ce “A ina ki ka samu hotunan nan?”
Ayshercool 08081012143




