Karfe A Wuta Chapter 60 By Ayshercool
Ya cigaba da zazzare ido, yana kallon ɗakin, ya ɗauki wayar da ya watsar, ya sake haɗata, ya kuma kiran lambar, amma a sai ace masa lambar dose not exist.Ya fita waje, ya zagaye gidan yana dube-dube amma bai ga kowa ba, ya koma cikin gidan ya ɗauki wayar da rigar da ya yayyaga, ya shiga banɗaki, ya watsa su a masai ya fito.***Nabila kuwa bayan tafiyar sumayya, ofishin Barrister Habib ta koma, suka sake gaisawa da matan nan, ya ce “Ina sumayyan?””Ta tafi gida ne, na ce gani me yake tafe da su ne?”Ya kalle su sannan ya kalli Nabila ya ce, maganarki da ki ka yi, su sumayya T ladan suka saka a radio, a kan Barrister Naja’atu Bunkure, shi ne ya sanya suka zo, su sanar miki da wasu abubuwa da zai taimaka miki”.Nabila ta ce “Masha Allah, bari na aika baba masinja, ya sayo musu ruwa da lemo, naga azahar ta wuce, kafin nan nima nayi salla”Ya ce “To babu laifi”Tayi salla ta dawo, suka zauna da matan, ɗayat ta fara bata labarin abun da ya faru “Ni ‘ya ce da ni, mun rabu da mahaifinta, tana wurin babanta, yayi mata auren dole, take ta guje-guje saboda ba ta san mijin. Ake ta fama har tayi yinƙurin kashe kanta, magana har gidajen rediyo, ta turo wakilanta, suka tafi da mu can office ɗin ta, ta ce aure ba dole bane ba, dan haka dole a kashe auren nan. Da fari na so ayi sulhu yarinya ta koma ɗakinta, tun da bama tare da ubanta.Na din ga yi mata nasiha, a kan tayi haƙuri, tun da babanta yana ta tsine-tsine a kan ta bujire masa, ta haƙura ta yarda, amma matar nan ta ce sai an kashe auren, zata kai ni ƙara hukumar kare hakkin ɗan Adam, ta ɗauke mini ‘ya, ta tafi da ita, sai da aka yi sati biyu sannan ta dawo mini da ita ga babanta da mijinta suka ƙara matsa mini lamba, bayan ta dawo da ita, yarinya ta ƙara tuburewa ba ta san zancen aure ba.Tamkar an canza mini ita, idonta ya buɗe, har mijin ‘yar tawa ta saka aka kama aka rufe, aka kashe auren nan. Yanzu maganar da nake yi miki, shekru uku kenan, yarinyar nan ta ce aure wani abu ne al’ada da muke takurawa kanmu a kai, addini bai wajabta mana ba, haka take rayuwarta, sai ta shafe kwanaki ba ta gida, tana yawonta. Babanta ya sallama mini ita, bayan ya gama tsine mana daga ni har ita. Har a cikin unguwa ta cigaba da yi wa sauran ƙasayenta mummunar huɗubar adawa da aure, wai ana tauye musu hakki, kuma wallahi Naja bunkure ce ta mayar mini da ‘ya haka,tana fakewa ne kawai da taimako, tana zaluntar mutane”.Ɗayar ta ce “Nima kusan hakan ne, wani yaro ɗan masu kuɗi, ya lalata mini yarinya daga aikenta gidan, jami’an tsaro suka ƙi kama yaron, uban ɗan ya ce in dai arziki yana rana, zai kare ɗan sa, ba wanda ya isa ya kama shi ya hukunta. ni kuma jin shirye-shirye da ake yi a kanta, na taimakon marasa galihu, ya sanya nima na je neman ta taimaka mini. Da farko abu kamar gaske zata taimaka mini, ƙarshe abun ya juye, aka nemi a mayar da case ɗin wai sharri muka yi wa yaron.Wallahi ƙarshe yarinyata fiya-fiya ta sha ban sani ba, yar shekara goma sha huɗu ta mutu. Wallahi matar nan azzaluma ce, bamu da wurin da zamu je, mu nemi hakkinmu sai wurin Allah, haryanzu idan zance yayi zance a kan tayar da maganar abun da ya faru da yarinyata, wanda hakan ba ƙaramin tsaye mini yake yi ba” tayi maganar tana kuka mai ban tausayi.Nabila ta tashi ta rungume matar, tana rarrashinta ta ce “Ki yi haƙuri dan Allah, ki kwantar da hankalinki, Allah ya jiƙanta, kuma in sha Allah da ikon Allah sai mun kai matar nan ƙasa, zan yi iya yi na, in bankaɗo duk wani mugun abu da ta aikata muku, kuma sai ta girbi abun da ta shuka, ku yi haƙuri. Yanzu duk zaku bani adress ɗin ku, zan bi cases ɗin ɗaya bayan ɗaya, na tabattar da abun da ya faru kafin na san abun yi”Jikin Nabila yayi sanyi sosai da sosai, da jin abubuwan da Bunkure take aikatawa, tamkar ba ‘ya mace musulma ba, da matan ke iƙrarin ciwon ƴa mace, na ‘ya mace ne.Har kuɗin mota ta basu, bayan tafiyarsu ta kalli barrister Habib ta ce “Yaya habib, ka ji wani yahudanci? Ina laifin ta tsaya a kan iya kashe auren an yi wa ‘yar auren dole?””Ke ce baki san wacece ita ba sai yanzu, wannan wata ɓoyayyiyar aƙidarta ce, na bawa mata damar ƙin zaman aure da lasisin karuwanci. Tana saye yaran da kuɗi, da abun duniya wurin cusa musu wannan mummunan ra’ayin, da koyar da su daidaiton jinsi tsakanin su da maza”.”Innalillahi wa Innalillahi raji’un, amma duk da haka Alhamdilillah, na samu hints a kan yadda zan bankaɗo asirin matar nan, and one more thing kuma” ya kalleta ya na jiran me zata ce.”Maganar da muka yi da kai kwanakin baya, a kan case ɗin Aminu Viper” “Ina jinki””Naja’atu Bunkure tana cikin tawagar lauyoyin da suka tsaya kai da fata a kan shari’ar da aka yi masa. Kuma ka san ita ungulu ce ba ta jewar banza, dan haka akwai manufa a cikin shiga shari’ar da tayi. Viper ba ɗan siyasa bane ba, kuma ba shahararren mai kuɗi bane ba, balle ace tsaya masa tayi a shari’ar. Dan haka akwai ayar tambaya a kan charges ɗin da aka yi masa na kisan kai.Take a look at it barrister, an tsare mutum shekara biyar, an yi masa shari’a sau biyar kawai, an kai shi prison an ajiye babu conclusion na shari’ar, is je guilty or innocent? Kwatsam an ce ba a ganshi a prison ba, kuma an cigaba da nemansa, ruwa a jallo, anya akwai gaskiya a lamarin nan kuwa?”Ya tsura mata har ta gama, yayi murmushi ya ce “Haka kwanyar nan take cike da basira, amma aka ƙarar da ita a wurin iyayi da kwalliya?.Maganarki gaskiya ce Nabila, amma ina rabaki da case ɗin Vipern nan, akwai badaƙala sosai a kan case ɗin”.Nabila ta ce “Me da me ka sani a kai?””Nothing much, kawai na san dai akwai bita da ƙulli ne a ciki sosai”Ta jinjina kai ta ce “Haka ne, bari na tafi gida, yau a matuƙar gajiye nake” tayi masa sallama, ta tafi office ta ƙarasa shirinta, ta tafi gida. Ta sake karo da file a office ɗin.Cikin mamaki ta ɗauka, ta fara buɗewa.Aka rubuta continuation a ciki.Cigaban tarihin Naja bunkure ne, bayan rape da aka yi mata, cousin brother ɗin ta, aka rufe case aka ce abu ne na dangi, bayan ta ƙara girma tayi aure, ta sha wahala sosai a hannun mijinta na farko, ya azabtar da ita tamkar baiwarsa, ko haihuwa ba ta yi ba auren ya mutu.Yayanta ne ya taimaka mata, ya mayar da ita makaranta, tayi candy, ta shiga jami’a, sai dai bayan rasuwar yayanta, aka rasa mai sponsiring ɗin ta, ta cigaba. Mahaifiyata na can wani garin tana aure, babanta kuma ya ce ba ruwansa da ita, tun da taƙi zaman aure.A lokacin har wurin ɗan majalisar su, ta je neman kuɗin makaranta, lokacin yana tare da Indabo, indabo ya ce zai bata, amma sai dai ayi bani gishiri na baka manda. Ta amince tun daga nan, ta zama tamkar matarsa su watse ya biya mata kuɗin makaranta, babu wani sirri nasa da bata sani ba.Ta nemi ya aureta, bayan tayi graduation, amma yaƙi, ganin haka ya sanya, ta samu wani suka daidaita ya aureta, sai dai Indabo ya cigaba da bibiyarta.Ta fara aiki a matsayin lawyer mai zaman kanta, Naja tana da burin yin luxry life sosai, sai dai mijinta yana da rufin asiri amma ba irin wanda take hange ba, Indabo yayi mata alƙawarin haɗa ta da manyan mutane, lokacin ya zama ɗan majalisa, wanda zata din ga samun alkhairi da damarmaki.Kwaɗayi da buri, ya sanya suka koma ruwa da aurenta, ya din ga kashe mata kuɗi, yana kuma haɗata da manya. A wurinsa ta koyi shaye-shaye. Tsakanin ta da mijinta babu ragayya ko kyautatawa, duk son da yake nuna mata da kulawar da yake bata sam baya gabanta.Ta fara tashe sosai tana shahara, ana programs da ita a kafafen watsa labarai, ta buɗe ƙungiyar ta ta kanta, bayan joining ɗin ƙungiyoyin yahudawa, masu da’awar daidata jinsi, reshen Nigeria, ta cigaba da yi musu aiki ta ƙarƙashin ƙungiyar ta.Sai dai a haka take miyagun harƙallarta, na yi wa manyan mutane safarar mata a birnin tarayya, musamman ƙananan yara, da akan yi amfani da su saboda asiri.Red handed mijinta ya kamata, chats ɗin ta da wani minista, na ƙazanta, yayi kuka, amma ko a jikinta, ta ce idan ba zai iya ba ya rabu da ita. Haka ya saketa, ta samu cikakken gashin kanta.Ba ta taɓuwa, ko da kuwa tayi laifi, yanzun nan ƙungiyoyin kare hakkin ɗan Adam zasu shiga lamarinta. Ta din ga binne mutane ta hanyar bayyana musu kyawawan ayyukanta, da ɓoye na laifin.Bayan mutuwar aurenta labari ya bazu, mutane suka din ga tsinewa mijinta, wai ya saki macen kirki, aka yi hira da ita, ta din ga kuka tana yi tsohon mijinta sharri kala-kala.End the story…. Aka rubuta a ƙarshen page ɗin.Wani irin gumi, ya din ga tsatstsafowa Nabila, ta ma rasa abun yi, da tunanin da yakamata tayi, ba ta bari ta takura ƙwaƙwalwarta wurin hasaso waye ya kawo mata file ɗin a karo na biyu ba, kawai ta ɗauki jakarta ta fita.***Sumayya ce a tsaye tana kuka wiwi, shi kuma ya zuba mata ido, ko ƙiftawa baya yi, sai da tayi mai isarta sannan ya ce “Kukan ya isa haka, meyafaru?”Ta share hawayenta ta ce “A gaskiya sir, ni na gaji da aikin nan, na samu matsala da ni da Nabila, ni Nabila ba ƙawata ce kawai ba, ƴar uwata ce, ta riga ta yi fushi, ba zata saurare ni ba, ni ban san wanda ya gaya mata ina bibiyarta ba, ga wancan honorable ɗin ya addaba mini, duk motsina sun sani, sai kuma sun tambaye ni, me tayi me take ciki, banda barazana da suke yi mini ba yau ba gobe, ni dai dan girman Allah ka yi wani abu a kai, kar ni ko ita ayi wa wani illa, indabon nan fa ba imani ne da shi ba” ta ƙarasa maganar tana sake fashewa da kuka.Yayi murmushi ya ce “Haba ƴar jarida, ya da kuka wiwi haka da karaya nan da nan? Da kin sanni, kin san zan taimake ki? Baki san ya aka yi na gane Indabo yana yi miki barazana ba. Har na shigo lamarin ba, dan haka ba zan bari a cutar da ku ba, dukkaninku a kan gaskiya ku ke, sai dai ita naga buyaginta yayi yawa.Ki yi haƙuri ku daidaita, da haka zan cigaba da yi mata supplying abubuwan da take buƙata a harkar shari’ar nan””Sir yanzu fa ka gama cewa buyaginta yayi yawa, sai ce mini munafuka take yi, babu yadda tsakanunmu yanzu”Ya ce “No, tayi fushi ne kawai, and ki ƙara kiyayewa sosai da sosai, ki daina bari tana gane kina bibiyarta”.Sumayya ta ce “Yanzun ma, wallahi ina kiyayewa, ban san yadda aka yi ba”Ya din ga rarrashinta, sannan ya saka aka ɗauke ta a mota, aka mayar da ita gida.***Nabila da ƙyar ta isa gida, ta watsar da kayan a kan gadonta, ta fara kiran wayar Viper, amma a kashe, ta kira ta Walid amma baya ɗagawa, haka ta haƙura ta shiga banɗaki tayi wanka ta yi alwala ta fito.Har washegari da safe, Nabila tana neman layin Walid, hankalinta ya ƙara tashi, tayi tunanin ko wani abun ne ya same shi.Tana saka kayan abinci a motarta, Nasir ya fito.Ta ce “Yaya ina kwana?”Ya amsa da “Lafiya ƙalau, wai ina ki ke zuwa da kwanukan abinci kwana biyun nan ne?”Ta ɗago ta kalleshi ta ce “Ci nake yi mana, wataran ai wuni nake yi bana gida”Ya ɗage kafaɗa ya ce “Ban sanki da dakon flask ba, saboda haka kin gwammace ki ci biscuit da sauran kayan ciye-ciye””Haba yaya, yanzu ba mota ce da ni ba? Kuma zan je in ta cin abinci nikaɗai duk ga mutane ne a wuri?”Ya girgiza kai ya ce “A’a, amma yanzu ƙarfe bakwai saura kwata, har shida da rabi kin fita, saɓanin da har goma saura sai ki kai a gida”Ta tsaya sosai ta dube shi ta ce “Yaya me kake nufi ne? Ka daina ɓoye-ɓoye ka fito fili ka sanar mini cewar, tuhumata kake yi, da aikata rashin gaskiya mana”Yayi murmushi ya ce “Ai ba a tuhuma sai an tabattar da zargi my dear””Da ka daina zargin, dan wahalar da kanka kawai zaka yi, ko kuma irin abun naku zaka yi mini na masu kaki” tayi maganar tana murmushi.Shi ma murmushin ya yi, ya ce “A sauka lafiya”Ta amsa da Amin ta tafi.Tana tafe a hanya sai ga kiran wayar Walid, ta ɗaga wayar ta ce “Oga Walid, sai kiranka nake yi a waya, shi wayarsa ba ta shiga, wayarka kuma baka ɗagawa”Walid ya ce “Bari kawai, kin san halin mutumin naki sai a hankali ai, jiya bayan tafiyarki, ya kafa mitar sai an sallame shi daga Asibiti, da mu da likita muka din ga rarrashin sa, yayi mana banza, mun fita salla ya gudu, baki ga yadda hankalinmu ya tashi ba, na ce musu kawai mu koma gida, dama ya saba irin haka, ko lokacin da ƙanwata take raye, haka take fama da shi, idan aka kwantar da shi, da ɗanyen ciwo haka zai bar asibiti sai dai ta ƙarasa masa dressing a gida ya warke”.Nabila ta ce “Allah sarki, Allah ya yi mata rahama, shi kuma ya bashi juriya. Kana ji na, zan shigo dan ga abinci ma nayi, yayana ya fara saka mini ido ne, dole na canza takuna, zuwa azahar zan bar motata a chamber, zan zo in sha Allah”Ya ce “To Allah ya kawo ki, dan zuwan naki yana da amfani, yaƙi cin abinci ya ƙi shan magani, yana kwance kawai tun jiya””In sha Allah zan zo, ayi masa sannu” ta ajiye wayar tana murmushi, rigimar Viper tana da yawa, idan ba ka da haƙuri ba zaka iya da shi ba.Har ta fara neman lambar sumayya, sai kuma ta fasa kiranta, dan har ta manta sun yi faɗa. Kawai ta din ga jin ta wani iri, akwai abubuwa da dama da take son gaya wa sumayya, saboda kusancinsu da shaƙuwarsu, ta musamman ce. Sai dai haryanzu tana mamakin dalilin da zai sanya a din ga bibiyarta ta hanyar sumayya, kuma waye yake bibiyar ta ta.Sai dai ta fara zuwa courts ɗin da take da trials, ta gabatar da shari’oi, sannan ta koma asibitin da aka kai ramma, lokacin da aka yi mata fyaɗe.Ta nemi a bata copyn report ɗin da aka yi confirming rape case ɗin, aka ce an bawa ƴan sanda. Ta nemi ganin likitan da ya kula da ita, aka ce ya tafi ƙaro karatu, a bata lambarsa nan ma aka cigaba da yi mata yawo da hankali.Sai da ta gama zagayenta, sannan ta ajiye motar a wani wurin parking, ta karɓi pass, ta tafi wurin su Viper.Yau a tsakar gida ta tarar da shi, sun shimfiɗa masa tabarma, yana zaune yana ya danna wayarsa, sai dai idanunsa sun ɗan yi wuri wuri ya faɗa, gabansa kuma kwalin sigari ne da lighter.Tayi sallama duk suka amsa, ya ɗaga kai ya kalleta ya mayar ya sunkuya.”Ohhh masha Allah, the most handsome man ever saw, kaga yadda ka yi kyau sosai da sosai” ta nemi wuri ta zauna a gabansa ta ce “Manya gatan wasa, fisabilillahi mutum sai ya gudu daga Asibiti ba a sallame shi ba? Idan kuma bai warke ba fa, ni gaskiya ban ji daɗi ba” Ba ta saka ran zai kulata ba, ta ce “Ina wuninku, ya mai jiki kuma?”Suka amsa da sauƙi.Walid ya ce “Ba yadda bamu yi da shi ba, amma sai nemansa muka yi muka rasa”Tayi dariya ta ce “My, ya kake haka ne, duk muna ta taka, amma kai ko a jikinka. Wannan sigarin ina fatan ba sha aka yi ba, kaga an ce jininka ya hau, kuma kana smoking ba zai sauka da wuri ba, an ce mini baka cin abinci, duk ka rame ai ba zan ji daɗi ba” ta janyo ledar abinci ta ce “Ka yi haƙuri ban kawo abinci da wuri ba, Yaya Nasir ya fara saka mini ido” ta ƙarasa maganar tana miƙa masa plate, da cup ɗin da ta zuba masa kunun alkama.Ya saka hannu ya karɓa, ya fara ci.Liti ya ce “Wato mai zamani mune dai ba ma yi maka gwaninta ko?”Nabila ta yi murmushi ta ce “Ka san wani abu?” Ya girgiza mata kai alamar a’a.”Ni fa na gaya wa Sumayya, na san tana bibiyata, duk da jiya ta kawo mini wasu mata, da suka yi mini complain a kan Bunkure, amma mun yi faɗa da sumayya.Sannan an sake ajiye mini file a office ɗina, na ƙarashen labarin Naja’atu Bunkure.”Ku ka yi faɗa ba ƙawarki ba ce ba?””Eh, amma meyasa zata ci amanata?”Ya kalleta ya ce “Ya aka yi ki ka tabattar da cin amana ne ya sanya take bibiyarki?””Saboda kai ka gaya mini””Ban ce tana bibiyarki dan ta ci amanarki ba, kuma baki da tabbacin da gaske nake ko akasin haka”Ta gyara zamanta ta ce “A labarinka da na ji, baka ƙarya dan ka ci amana, kuma bana tunanin zaka fara a kaina”Ya jinjina kai ya ce “Bani wayarki” ta ɗaukko wayarta ta bashi, ya nutsu sosai yana ta daddanawa.”Yayanki ma na ƙoƙarin yi wa layinki kutse, sai dai na rufe damar hakan. Yana zarginki a kan da shi kansa bai san menene ba. Yayanki ya ga Indabo yana yi masa aiki a kaina, yana kuma gargaɗin sa a kan abun da ki ke yi a kan bunkure, na san zuwa yanzu ya matsa miki lamba a kan ki rabu da ita”Ta waro ido ta ce “Ya aka yi ka sani? Anya yayan kuwa?”Ina bibiyar kiran wayarsa ta hanyar amfani da wayarki, hakazalika duk wasu maganganu da yake yi, recording ɗin suna kan computer ki. Wayarsa da Indabo kawai nake bibiya, ba ruwana da sauran harkokin sa.Ta ce “Subhanallah, amma yaya ya bani kunya, shiyasa yake ta uzzura mini? Amma nima ka yi hacking ɗin wayata kenan? Kana jin duk wayar da nake yi da samarina?”Tsaki yayi, ya jefa mata wayarta. Ya ce “Ina magana serious kina yi mini shirme?”Ta ce “To ai kar ka ji ina kalamai ne, ka zo kana kishi, nifa duk ba son su nake yi ba, kai kawai nake so” tayi maganar da niyyar sake kunna shi.Ƙoƙarin tashi yayi, tana dariya ta ce “Yi haƙuri, dan Allah ka duba mini ƙarashen labarin nan, na Najar bunkure ka gaya mini menene opinion ɗinka”.”Mu yi aiki kawai, ki daina yi mini wannan shirmen””Ba shirme bane ba fa, ni da gaske nake” ya karɓi file ɗin, ya cigaba da duddubawa.Ya ɗaga kai ya kalli walid ya ce “Mai laya””Mai zamani”.”Yakamata ku je ku daba mini mahaifiyar Nura, tun da na fito yakamata ace na je na ganta, amma ba zan iya ba, ban san wace irin karɓa zata yi mini ba, maybe ita ma irin kallon da ake yi mini, take min”Liti ya ce “Haba maza, babu lallai gaskiya”Nabila ta ce “Ina kakarka to? Wadda oga walid ya bani labarinta?””Ta mutu ina prison”Walid ya ce “Har tare da ita mun je prison, sau biyu ba a bari mu ganshi. Baiwar Allah nan tashin hankali da damuwa ne, suka haɗu suka kasheta”Jiki a sanyaye ta ce “Allah sarki, Allah ya yi mata rahama, ya sanya sun huta baki ɗaya, da yar madara, da Hajiya, da mamana da sauran al’ummar musulmi baki ɗaya” suka amsa da Amin.Walid ya ce “Mamanki ta rasu?”Ta jinjina masa kai ta ce “Eh, ban ma santa ba, sai dai hotunanta na gani a wurin Abba””Allah sarki, Allah ya jiƙanta”Liti ya ce “Shiyasa ba kya ji, ina tausayawa mariƙanki, sun sha wahala da ma ba kowane maraya ne yake ji ba””Oganku shi ne na farko a marasa jin, in dai maraya baya ji” ta yi maganar tana satar kallon Viper.”Amma Viper, ka sake komawa wurin Abbanka kuwa? Na san zuwa yanzu ya huce, zai kuma fuskance ka, ka yi masa bayani, shi fa tsakanin ɗa da iyaye sai Allah” yayi mata shiru.”Ni ka bani dama naje na same shi, na san zai fahimce ni”Ya ajiye file ɗin ya ce”Kar ki kuskura ki fara wannan gangancin, kar ki kusanci unguwarmu, ko ki ce zaki je unguwar da gidana yake, idan ki ka yi ɗaya daga ciki, zan yanke aikin da zan yi da ke, kuma hakan zai iya sanya wa na kashe ki””Au ba zaka daina zancen kisan kan nan ba ko? To maza nima ka kashe ni, na ga wanda zai din ga rarrashinka.Ta tashi ta ɗauki jakarta, ta tattara kwanukanta, ta ce “Bari na tafi, kar nayi yamma da yawa, zamu yi magana” tashi ya yi ya ce “Muje””Rakani zaka yi? To muje” suka fita kamar gaske. “Ina sake gargaɗinki, kar ki sake ki ce zaki nemi gidanmu ki je, ko gidan su ‘yar madara, zaki ɓata mini aiki, duk da na samu labarin sun bar unguwar, idan kuma ki ka ɓata mini aiki, ba na jin zan iya yafe miki”Ta ce “Subhanallah, in sha Allah ba zan je ba, amma yakamata ku daidaita da mahaifinka.”Ba wannan ne a gabana ba” “To menene a gabanka? Iyaye fa ba a fushi da su””Ki rabu da ni”Ta ce “To, Allah ya baka haƙuri””Ki cigaba da kula sosai da sosai a kan zuwanki wurin nan, za a iya biyoki har nan, bana tunanin iya wayarki ake bibiya”Ta kalleshi ta ce “Akwai wata mota da na lura da tana bina kwanakin baya, amma ba wannan ba. Na faa tunanin anya a cikin yaranka babu wanda suke sanar da wasu abubuwan da muke yi? Ko kuma wani yana binka ko kuma ni da ake bi, an san ina zuwa wurinka ba? Suwaye suka ɗaukeka kwana biyu? Sannan ya aka yi aka san kana asibitin nan, har aka biya maka kuɗin asibiti”Ya sauke numfashi ya ce “Kar ki shagala da tunani da yawa, ki manta da abubuwa masu muhimmanci, ki je zamu yi magana”Ta kalleshi ta ce “To, amma dan Allah ka ɗaga wayata da daddare in ji muryarka, ka ji Oga” wani irin mugun kallo yayi mata, ya nausa ya bi wata hanyar, ita kuma tayi gaba tana murmushi.***Ramma na zaune a kusa da Abdul, yana kallon ball, ita kuma ta kunna radio a wayarta, tana ji.Ya kalleta ya ce “Dan Allah ki rage radion nan””Ina ruwanka da ni ne, ka yi kallonka mana””Kin cika mini kunne da radio ne””To ita ball ɗin magana ake yi? Ba ihu bane ba kawai?”Abdul ya ƙure volume, ita ma ta ƙure volume, ta kara masa radion a kunnensa.Yayi mata shiru ya ce “Kya yi kya gama”Sumayya ce tare da murtala a studio, suka gabatar da program, kasancewar an samu akasi masu gabatar da program a dai-dai lokacin ba su samu zuwa ba.Program suke yi akan abubuwan da suka shafi rayuwa, suna yi suna karanto saƙonnin masu sauraro.Murtala ya ce “T ladan, ga wata tambaya daga masu sauraro, wai an ce a tambayeki, wace irin alaƙa ce tsakanin ki da Nabila Yusuf maitama, da kullum ba kya taɓa aiki ki tashi, baki ambace ta ba, baki tsokane ta, ko saka waƙoƙi domin jin daɗinta ba?”Sumayya ta yi murmushi ta ce “Barrister Nabila, voice of voiceless a lady of her words, a hardworking, strong minded young barrister, she’s exceptional, lovely and simple sister of me” tayi maganar tana jin zafin saɓanin da suka samu a tsakanin su.Murtala ya ce “Tirƙashi, duk wannan kirarin itakaɗai?””Sosai, Nabila mutum ce ta mussaman a rayuwata, ina yi mata son fisabilillahi””To yanzu da saurayinki, da Nabila wa ki ka fi so?” Ta kwashe da dariya ta ce “Uncle murtala wannan ai haɗa faɗa ne””To yanzu kafin muyi sallama da masu sauraro, gaya mana kalma ɗaya tak a kan Barrister Nabila””Mai gaskiya ce, ina yi mata fatan nasara, ya ɗaukaka mini ita, ya kuma kare mini ita a duk in da take, ya dauwwamar da ita a kan gaskiya”Murtala ya ce “Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum, Allah ya bar wannan ƙauna, kafin mu ƙarƙare shirin, mun karɓi takardar wata baiwar Allah da za a yi wa ɗanta aikin ƙaba, amma ba ta da hali, tana neman taimakon bayin Allah. Akwai kuma wadda take neman kuɗin sayawa mahaifiyarsu magani mai fama da hawan jini, muna fatan zaku taimaka”Nabila kuwa tana driving, ba ma’abociyar jin radiyo bace ba, amma saboda sumayya take sauraren radio. Hawaye ta din ga sharewa, tare da tuna abun da ta yi wa sumayyan.Ramma kuwa cewa ta yi “Allah ya ƙarfafi wannan baiwar Allah, ya tabattar da ita a gaskiya, kar ya kauce hanya, kamar waccan munafukar mara imani” Abdul yana jin ta, yayi mata shiru. Ganin bai kulata ba ya sa ta ce “Ba zaka ce amin ba””Ni fa ball nake kallo””Allah ya sa a cinye club ɗin da kake yi””Ba amin ba” ya ɗauki wayarsa, ya kira admin ɗin asibitin sa, ya ce a je gidan radion su sumayya, a kai yaron nan ayi masa aiki kyauta, mai hawan jinin ma a kai ta a bata magani.Ramma ta ce “Kalle shi kamar na Allah” duk yaƙi kulata, ta tashi ta nufi ɗaki, ta saka hannu ta kashe tv ta riga ɗaki da gudu, kawai yayi dariya.***Kwanaki biyu, Nabila ta daina samun Viper a waya, sai dai da ta kira walid, ya tabattar mata da lafiyarsa ƙalau.Nabila ta fara gazgata zancen Viper, duba da yadda Nasir yake kashe-kashen kuɗi, ya canza mota ya cigaba da gininsa, kuma salarynsa gaba ɗaya ba wani shahararre bane ba.Nabila tana kwance tana waya da Alhaji Wada M karofi, yadda yake lallaɓata yake yi mata magana, har kunya yake bata. Fuskar viper kawai take hangowa, yanzu da shi take yi wa kalaman nan, da tuni ya haɗe rai yana hararta. Bayan sun yi sallama ta ajiye wayar, Walid ta shigo ɗakin ta ce “Arfa, isa ne ya shigo yanzu, wai ana sallama da ke a waje””Kai, wane ɗan baƙin cikin ne zai hana mini jin daɗi a magaribar nan? Ni fa ban yi da kowa za a zo wurina ba”Walida ta ce “Ace ya tafi kenan?””A’a gani nan zuwa”Ta yafa mayafin abayarta, ta fita, a ƙa’idar Abba a cikin gida suke zance, ganin bai shigo ba, ya sanya ta gane lallai wanda ya zo ɗin baƙo ne.Ta zira kai ta leƙa ƙofar gida, dan duba waye.A opposite ɗin gidan ta ga Viper a tsaye yana kallon ta.
Ayshercool 08081012143

