Karfe A Wuta Chapter 49 By Ayshercool
Cikin matsanancin tashin hankali Nabila ta nufe su, Walid ya rikice, ya rasa me ma yakamata ya yi ya taimakawa Viper.Cikin azama Nabila, ta ɗaga kan Viper yana kallon sama, ta ciro hular kanta, ta toshe hancinsa da yake zubar da jini, ya zamana ta gefen bakinsa yake numfashi.Cikin kuka ta kalli walid ta ce “A kai shi asibiti mana, ya bugu da yawa, tun da abun ya kai ga zubar da jini ta hancinsa”Walid ya ce “Ba za a kai shin ba, uban waye ya ce ki kuma zuwa ai duk ke ki ka ja?”Cikin rashin fahimta ta ce “Ni kuma? Ni me na yi? Zuwa na yi na bashi haƙuri a kan abun da na yi bisa kuskure, wallahi ban yi masa komai ba, tarar da shi na yi yana yi wa kansa allura jikinsa yana rawa, na karɓa amma wallahi ban yi masa komai ba. Ko duk haushin abun da na yi wa ɗan uwanku ne? Na je station ɗin ai, kuma na yi magana da shi, dan Allah ku yi haƙuri rashin sani ne ya sanya na aikata abun da na yi masa, abun da ake faɗa a gari a kansa daban, ni kuma ban san gaibu ba, amma dan Allah ku yi haƙuri” tayi maganar hawaye wani na bin wani a fuskarta.Walid ya ce “ya isa haka, tashi ki tafi””A haka za a bar shi, ba zaka kai shi asibiti ba?””Ta yaya zamu kaishi asibiti ana nemansa a kama shi?”Fizge-fizge Viper ya fara yi, yana ƙoƙarin tashi, Walid ya daddane shi, cikin ɗaga murya ya ce “Walid”Ya ce “Na’am Al’amin””Liti” walid ya ce “Ya shiga banɗaki”.Viper ya sake cewa “Mai laya””Na kiyayi mai zamani, Allah ya ƙara maka lafiya””Gobe zamu je asibiti da ƙanwarka ‘yar madara, sun ce inducing za su yi mata ‘yar madara za ta haihu, ragonta yana ƙauye wurin Hajiya”Walid ya ce “Masha Allah, Allah raba su lafiya””Walid””Na’am mai zamani””Cikin nan yana ba ta wahala, nima na ƙagu ta haihu, na ga yarona, sunan ƙanina nura zan mayar, idan ta kuma haihuwa na saka sunan Sadik”.Walid ya ce “To Allah ya kawo mana su lafiya da albarka”Wani irin ihu ya hau yi, yana ƙoƙarin ture Walid, cikin ƙaraji ya ce “Walid matata ɗa na, ba zan iya komai ba, ka riƙe madaki, kar ya illata mini mata, ka riƙe shi walid wai me ka ke yi ne?”Sosai suke kokowa da Walid, ga hancinsa na cigaba da zubar da jini, ga damuwa da fita hayyaci a dalilin allurar nan.Walid ya ce “Sai na ci uban ɗan mama idan ya dawo, bai ji me na gaya masa a kan kawo maka kayan maye ba, sai ya saka mun yi babu ka rasa ƙwaƙwalwarka tukuna”.Nabila kuwa iya ƙarfinta take kuka, tsananin tausayinsa ya mamaye zuciyarta, da ƙyar walid ya danne shi, a hankali jikinsa ya saki, ya daina motsi, amma yana motsa idanunsa, a buge yake ya fita hayyacinsa amma ba bacci yake yi ba, abubuwan da suka wuce ne suke dawo masa cikin mayen.Nabila ta ce “Dan girman Allah ka gaya mini ƙarashen labarin nan, ina jauhar ina abun da yake cikinta?”.Walid ya ce “Kin ga ni ba wannan ne a gabana ba, lafiyar ɗan uwana da taya shi ɗaukar fansa ita na saka a gaba, dan haka ki tashi ki tafi kawai”Nabila ba ta sake magana ba, ta tashi jiki a sanyaye, ta ɗauki jakarta, har ta kai bakin ƙofa, ta waiwayo ta sake kallonsa, hakan yayi dai-dai da buɗe idanunsa, sun yi jawur gwanin ban tsoro, ya tsura mata ido, a hankali ta juya ta fice.Cikin maye ya ce “Mai laya””Allah ya taimaki mai zamani””Ba na son ganin yarinyar nan, zan iya fara kisan kai a kanta”.Walid ya girgiza kai ya ce “Ba ka taɓa yi ba, kuma ba zaka fara a kanta ba” surutan da Viper ya cigaba da yi ne, ya tabattar wa da Walid ba ya cikin hayyacinsa.***Ramma ta na zaune, ta na cin farcenta, tana zancen zuci, ta ji Abdul ya kama hannunta.Sai da ta firgita, kasancewar tayi zurfi a zancen zuci.Hannunsa riƙe da nail cutter, ya fara cire mata faratan ya ce “Ƙazama kawai, da baki ki ke cin farce” janye hannunta ta yi ta ce “Ni kar ka shafa mini cuta” tayi maganar tana haɗe rai.”To cuta ta nawa kuma, in dai ina da ita da tuni kin ɗauka ta can wurin. Duk rashin ji na, ina using protection, a kanki ne kawai nake gaba gaɗi, shi ma dan na san am safe na killace ki” tsaki ta yi ta kawar da kanta gefe.Ya kama hannunta, ya cigaba da yanke mata farcen ta ce “A banza, wallhi ko haɗiyeni zaka yi, ka fito da ni, ba zan yafe maka zaluncin da ka yi mini ba”Bai kalleta ba ya ce “Dama ban ce ki yafe mini ba ai” ya na cikin yanke mata, ta ga yana ɗan yamutsa fuska, ya gama ya tashi ya koma ɗaki, ta kalli falon komai tsaf solomon yake gyarawa, a ranta ta ce “Dama aure ne da ni, ace nan gidana ne ba wannan ƙazantar ba. Tunanin hakan kawai ya saka idanunta cika da hawaye.Ta ɗaukko magazines ɗin da ke falon, tana ta kalla, har ta manta da shi a gidan, ta shiga bedroom ɗin, ta tarar shi a kan gado yana murƙususu.Ta kalleshi ta ce “Menene?”A wahale ya ce “Kira mini solomon” ta juya ta fita, ta kiro shi.Ya ɗaga kai ya ce masa ya kawo masa biro da takarda.Ya kawo masa, yayi rubutu a jiki, ya ce yaje ya sayo masa.Solomon ya fita cikin sauri, ta kalleshi ta ce “Wai menene?”Ya ce “Epigastric pain ne””Me kenan” ya nuna mata cikin sa.Ramma ta ce “Sannu Allah ya sa mutuwa zaka yi na huta”Yayi mata shiru, ya cigaba da juyi, ya dunƙule hannunsa yana dukan gadon a hankali, yana yi yana miƙa alamar yana jin jiki sosai.Ta tsaya tana kallonsa, gumin da yake yi, ya sake tabattar mata ya fara galabaita.Yayi mata nuni da hannunsa ta je, ta ce “In zo in yi maka me?”Girgiza kai ya hau yi, yana kiran “Mummy, rahama cikina am in pain””To sannu”Ta samo jarka da ruwa, ta tofa masa bisimillah ƙafa 19, da suratul fatiha ƙafa 7, ta hau kan gadon ta ce “To tashi ka sha ruwa” ya tashi da ƙyar ya karɓa, ya shanye, yayi jifa da jarkar, ya kwanta a kan cinyarta ya ce “Rahama cikina””Allah ne yayi maganinka, a cikin sakans idan ya ga dama, zai rabaka da rayuwarka, ka ga idan mutuwa zaka yi, ga saɓo kana yi, ga zaluncin da ka yi mini, Allah ya sa ka mutu”.Abdul ya ce “Da na mutu shahidi, ciwon ciki ne ya kashe ni, kuma ƙarshe ace ke ki ka kashe ni”.”Ko shahidi ka mutu kan ka shiga aljanna, sai ka shiga …. Sai kuma ta yi shiru. “Allah dai sai ya ƙwatar mini hakkina a wurinka na zalunta ta da ka yi”Solomon yayi knocking, Abdul ya ce ya shigo, ya shigo da leda a hannunsa, Abdul ya karɓa, ya sakawa kansa butterfly needle, ya saka ramma ta haɗa allurar da aka kawo, ya ce tai masa.”Ni ba zan iya ba, tsoro nake ji””Tsoron me malama, ciwo zai kashe ni””To ni taɓa yi na yi?”Cikin tsawa ya ce sai ta yi, hannunta na rawa, ta zuba allurar a cikin butterfly needle ɗin.A haka ya nuna mata yadda za ta saƙala masa ruwa, yana yi suna faɗa, ta saka masa ya sa hannu ɗaya ya janyota, ya sake kwanciya a kan cinyarta.Yadda yake wash wash da kiran sunanta, sai ya ƙular da ita kamar ba namiji ba.”Ni ka daina kiran sunana tun da ba ni na ɗora maka ba””Wash rahama cikina” tsaki ta yi ta ce “Wai shekarunka nawa?””36yrs” yayi maganar yana kallonta.”Amma an yi asarar ƙuruciya, idan ba ka yi wasa ba kana cikin wanda annabi ya ce kun yi asara, ka tafiyar da ƙuruciyarka a shirme da shashanci, a mintuna ashirin ɗin nan da Allah ya ga dama, da yanzu babu kai, me zaka ce wa Allah, ka sha giya ka kwana kana zina da ‘yar da ka raba da uwatta, ka canza tunani da halaye, ko Allah ya yi maka rahama”.Ya lumshe idanunsa ya yi shiru, bai ce mata komai ba.***Nabila kanta tamkar zai tarwatse ita ma haka take ji, so take ta kamo bakin zaren tallafawa Viper. Babban abun da yake buƙata yanzu rehabilitation ne, a fara nesanta shi da shaye-shaye, sannan a kwantar masa da hankali da ƙoƙarin tirsasa masa karɓar ƙaddararsa ta hanyar da ya dace. Sannan a fuskanci kamo zaren tsaya masa, ya ɗauki fansar abun da aka yi masa ta hanyar doka, ba ta hanyar da yake tunanin ɗauka ba, sai dai alamu sun nuna mata ba zai sarrafu cikin sauƙi ba, balle a samu fahimtar juna da shi, sai dai ta ƙudurce a ranta, duk tsanani da wahalar lamarin, za ta tsaya a kan sa, ko da kuwa sanya rayuwarta cikin hatsari ne, za ta yi domin taimakon Viper.Sai dai hakan ba zata yiwu ba, sai ta ji ƙarshen labarinsa, amma ta yaya?. Da ta tuna yadda yake kururwa yana kiran matarsa, ɗansa sai ta ji ta karaya, tausayinsa ya ƙara kamata.Ringing ɗin wayarta ne ya katseta daga tunanin da take yi, ta ga lambar sumayya, ta ɗauki wayar ta kara a kunnenta.Sumayya ta ce “Na yi wa Uncle murtala kwatancen gidanku, zai zo ya same ki, sai ku yi magana”.Nabila ta ce “Kai sumy, ban da ni ki bari na je na same shi, ni da nake nema?”Sumayya ta ce “Ya zo ya same ki is more safe, ba wanda zai kawo wani abu, kin san yanzu rayuwa babu tabbas mussman irin aikinmu”.Nabila ta yi murmushi ta ce “Hakane masoyiyya, na gode sosai, saura ɗaya aikin””Wanne kenan?””Waye indabo?””Kin ga ki raba kanki da indabon nan, wai me ki ke nema a kansa ne? Ba dai kin yi masa wulaƙanci kin ƙi gaishe shi ba, menene na bibiyarsa”Nabila ta yi murmushi ta ce “Ba zaki gane ba, ki taimaka kawai””Nabila kamar kina ɓoye mini wani abu fa”.”Ba abun da nake ɓoye miki, mamakinki kawai nake yi, duk kin canza kina abu kamar mara gaskiya kwanan nan sumayya”Dummm gaban Sumayya ya faɗi ta ce “Ban gane ba”Nabila ta yi dariya ta ce “Kar ki manta fa ni lawyer ce, idan na so zan gane idan ma baki da gaskiya, don’t mind me kawai dai na ga kina ƙoƙarin kawar da maganar indabon nan ne, shiyasa nake tsokanarki, am about to do something big, zan gaya miki menene daga baya””Nabila Please, kar ki je ki yi abun da ba shikenan ba, ki raba kanki da duk wani abu da zai sake haɗa ki da Aminu Vipern nan, kar ma a cetare ku ke. Ki bar DSP yayi aikinsa dan Allah””Ni ba maganar Viper nake yi miki ba, case ɗin dattijon nan nake magana a kai, amma ki binciko mini maganar indabon nan, ko na binciko da kaina”.Sumayya ta ce “To shikenan na ji zan yi, amma ki san in da zaki din ga zuwa da abun da zaki din ga yi kin ji arfan Abba”Nabila ta yi murmushi ta ce “Ji sai ka ce wata uwata, to na ji sai anjima” ta kashe wayar tana murmushi, a duniya bayan Abba ba ta tunanin akwai wanda ya kai Sumayya damuwa da ita, da tsoron ta aikata wani abu, da zai janyo mata matsala.Bayan sallar magariba, Murtala ya kirata a waya, ya sanar mata da ya zo, yana ƙofar gidan su.Ta saka hijjabi ta fita, suka gaisa ya ce “Sumayya ta ce “Ki na nemana””Au ba ta yi maka bayani ba?”Murtala ya ce “Tayi mini, daga bakinki nake son ji”.”Haka ne, ka ga wani case na samu, na wani dattijo, an yi framing ɗin sa, wai yayi wa wata yarinya ‘yar aikin da yake gadi fyaɗe, na je na yi magana da shi, yayi mini bayani, ya ce ba shi bane ba, ɗan yayan matar gidan ne, so abubuwa da yawa are similar to rahoton da ka bayar kwanakin baya, shiyasa na ce bari na neme ka, ka ƙara yi mini bayanin yadda abun yake”.Murtala ya numfasa ya ce “Kin san duk abun da aka ce, harka ta manya ce, sai dai a lallaɓa a yi komai a ɓoye ko ba haka ba, an ce yaron nan ɗan manya ne, kar mu je ki yi wani abun da zaki sakamu a matsala fa”Nabila ta ce “Uncle murtala, ba zan saka kowa a matsala ba, dattijon nan nake son na taimakawa, kunna mini recording ɗin matar, na sake ji”.Ya kunna mata recording, ta saurara tiryan-tiryan, Nabila ta ce “Uncle murtala, case ɗin dai ai wannan, ba shi ne aka ce Naja’atu Bunkure ta shiga case ɗin ba, ai da na ce zan shiga case ɗin yarinyar”.Ya ce “Shikenan, faɗuwa ta zo dai-dai da zama, amma dan zatin Allah don’t mention my name”.Ta jinjina kai ta ce “Kar ka damu in sha Allah ba zan yi mentioning ɗin ka ba. Naja’atu Bunkure ko da me take yawo a kanta, sai ta gaya mini in da case ɗin ya tsaya, ka san ina station ɗin da aka fara case ɗin, aka ƙwace file ɗin daga hannuna, wai ba zan duba ba”.Haske su aka yi da fitilar mota, Nabila ta tura baki, tana kare fuskarta, Nasir ya gyara parking ɗin sa, ya fito ya nufo su.Ta ce “Yaya sannu da zuwa” bai amsa mata ba, ya kalli murtala ya ce “Malam ya dai, ya aka yi?””Yaya idan saurayina ne, haka zaka yarfa ni dan Allah? Abokin aikin sumayya ne, muna tattaunawa ne a kan wani case”.Nasir ya sake tsuke fuska ya ce “Kuma da daddaren nan?””Eh, saboda shi ɓoyayyiyar shaida ne, da ba zan bayyana shi ba, ba na kuma son a samu trace, na wani ya ganshi, shikenan uncle murtala ka gaida gida”Yayi wa Nabila sallama ya tafi.Ta cigaba da yi wa Nasir mita, “Gaskiya yaya na fuskanci saboda kai wasu samarin namu suke tafiya, da haka za a aure mu, kana zare musu ido, kamar wasu ‘yan ta’adda”.”Eh, gara a zare musu idon, su san nan ba wurin da za su zo su kawo wargi bane ba” kawar da zancen ta yi, ta hanyar bashi labarin case ɗin dattijon nan, da yadda aka ƙwace file ɗin.Sosai ya din ga mita, har yayi alwashin rakata sake komawa station ɗin, a bashi tun da tana lawyer, dole a bata dukkan haɗin kan da take buƙata.Bayan ta koma ɗakinta, ta din ga murmushi itakaɗai, abu zai case zai haɗa ta da Naja’atu Bunkure, “Sai na ga abun da ya ture wa buzu naɗi kuwa” sai dai walwalarta ta ɗauke, bayan tuno wa da Viper, kar ta shagala da ramuwar gayya a kan Bunkure ta sakankance ta gaza samo mafita a kan nasa case ɗin.Tana buƙatar wanda zata tattauna case ɗin da shi matuƙa, amma ba ta ga wanda ya dace tayi maganar da shi ba. Dan ko da wasa ba zata tunkari DSP ba, balle sumayya tsfa zata ce za ta gaya wa Abba, dama ban da su biyun nan, ba ta wanda ya dace, ta sanarwa wannan gangancin da take shirin yi ba.Sai dai kwana ta yi, tana tunanin ko yaya Viper, ya farfaɗo gaba ɗaya ya warware ko kuma yaya?Washegari da safe, da DSP suka tafi station ɗin nan, a hanya yake sanar mata da an yi belin Liti, ta tambaye shi waye ya yi belin Litin, ya ce mata bai sani ba, waya kawai aka yi masa aka ba shi umarnin ya sake shi.Nabila ta ce “Nigeria ƙasata”Suka isa police station, Nasir ya nuna musu id card ɗin sa, sannan ya nemi su bashi file ɗin da Nabila ta nema, amma suka tabattar masa da an zo an karɓi file ɗin an mayar da shi babbar headquarter.Nabila ta ce “No wonder, hakan ya sake tabattar mini da lallai wanda ya aikata laifin, ɗan manya ne, kuma ba dattijon nan ne yayi ba” ta cewa Nasir kawai su tafi dama ta san a zaman farko sai an aike da baba prison, kafin ta gama tattara hujjojinta.Sai dai duk da haka, Nasir ya nemi a ba su in details, statement ɗin, da Asibitin da aka kai yarinyar, amma suka ce ba a ba su wannan umarnin ba, komai da komai yana babbar headquarter.Suna tafe take ce masa “Kar ka damu yaya, zan baka mamaki ƙoƙarin da zan yi a kan lamarin nan, zan tattara hujjojina na shiga kotu” yayi murmushi tare da ccigaba da ba ta ƙwarin gwiwa, ya biya ya ajiyeta a wurin aiki sannan ya tafi.Cak ta tsaya a harabar wurin, tana ƙarewa motocin kallo, ta tsayar da idonta a kan baƙin motocin da ta gani guda uku, sai dai ɗayar ita ce motar da ta din ga bin ta, har ta tsaya tayi knocking ɗin glass. Ta ƙarasa ta zagaye motar, ta sake tabattar da ita ce, ta jinjina kai ta shiga.Ta je office ɗin ta, ta ajiye jakarta, ta fita ta tafi office ɗin Barrister Habib, a hanya ta ci karo da MD barrister Kabir da wani babban mutum, da ta taɓa haɗuwa da shi a office ɗin sa.Cikin girmamawa ta risuna, ta gaishe su, suka amsa, Barrister kabir ya ce “‘yar ƙwalisa in ji habib, an shigo kenan?””Eh sir, na biya neman wata shaida ne, ban samu ba ma, na taho”Ya ce “Sai haƙuri, haka lamarin aikin dama yake, wataran nasara wataran sai haƙuri, na ji daɗi da na ga kina mayar da hankali yanzu kin rage kwalliya”.Mutumin ya zuba mata ido, yana ta murmushi kamar an yi masa kyautar kujerar makka, dan sai da ta faki idon Barrister kabir, ta galla masa harara, sannan ta yi gaba.”Yaya Habib”Ya ce “Yau kuma?”Ta ce “Eh mana, yau baƙi muka yi ne?Ya gyaɗa kai ya ce “Dama wurin nan ai kullum cikin baƙi yake””Wasu motoci na gani, wata farar mota ta waye?”Ya ƙura mata ido sannan ya ce “Hala na samu demotion ne zuwa mai gadi?” Tayi dariya ta ce “Am very sorry, ka san wani abu?””Sai kin faɗa””Ka san shi Allah, mai son bawansa ne, da kuma jin ƙan sa”Barrister Habib ya ce “Wannan haka yake”.”A wannan karon, ba tare da na yi tsammani ba, akwai yiwuwar case ya haɗani da Najar bunkure, to kuma ka san ni yanzu kai ne mentor ɗina, na zo mu yi magana “Yayi dariya yana mayar da wasu files, drower gabansa ya ce “Nabila ‘yar ƙwalisa, haryanzu ba ki san wacece Bunkure ba ko?””And ba na buƙatar na sani, kawai i need your support, i want expose her hidden face to the world “”How?”Nan ta bashi labarin duk abun da yake faruwa, da case ɗin da yake hannunta.Ya ce “Nabila””Na’am barrister yaya Habib”Yayi murmushi ya ce “Zaki ga yaya, aradu ki ke shirin tara da ka fa””Na shirya mata”.”Tana da wanda suka tsaya mata matar nan “”Ni ma Allah ya tsaya mini”Ya jinjina kai ya ce “Kin gama magana”Nabila ta ce “Yauwwa barrister, and i want you to support me, dan Allah ka taimaka mini””Ba ƙi nayi ba Nabila, matar nan manyan mutane da manyan ma’aikata sun kasa ja da ita, ke kin san ba haka nan take ba”Nabila ta sake gyara zamanta ta ce “Support me, you will be proud of me”Ya sauke numfashi ya ce “Duk abun da ki ke buƙata na taimako, ki yi mini magana kamar yadda na taimaka miki ki ga file ɗin Viper, zan cigaba da taimaka ki, amma ya zama sirri tsakanina da ke” tayi shiru tana kallonsa, ji tayi kamar ta yi masa zancen Vipern, sai dai a zuciyarta ta ji, ba ta gama amincewa da shi ba, kuma ba kowa za ta yi wa magana a kan case ɗin sa ba, dan haka ta yi murmushi ta ce “Na gode Allah ya saka da alkhairi ya raya maka zuriya. Amma yanzu ya kake ganin za ayi? Office ɗin ta zan je, a kan ina son bayanai daga gare ta, da bakin yarinyar?””Eh mana, go as a barrister, ke ma lawyer ce, go with your full confidence”Tayi murmushi ta ce “Na gode sosai ranka ya daɗe” ta juya ta fita cikin farinciki.Sai dai kuma tunanin Viper ya cika mata zuciya, ko yaya jikinsa? Ya warware gaba ɗaya ko kuwa?Ba tare da dogon tunani ba, ta ɗau jaka ta fita, ta samu mai sayar da fruit, ta sai uban kayan marmari ta tari abun hawa ta tafi.Sai dai ta sha wahala, tana ta bulayi, ga uban kaya a hannunta, ta kunna Google map, yau sai ya fara yi mata hauka ta ce “Wai shi wannan ma anya ba aljani bane ba?”Har ta fitar da rai, kawai ta hango roofing gidan, haka ta cigaba da tafiya, har ta isa ƙofar gidan.Duk da tsoro da fargabar waccan shaƙar da ta sha, na neman kashe mata gwiwa, ta tsananta addu’a tare da neman kariyar Ubangiji.Jin sallamar mace ya sanya gaba ɗaya suka ɗago suna kallonta, liti ya zabga ashar ya ce “Ke uban me ya kawo ki nan, munafuka macuciya?”Ta ce “Ashe kuma ka fito””Ban sani ba, uban me ya kawo ki?””Wurin Viper na zo” ta bashi amsa kai tsaye. Ya tashi tsaye zai zare wuƙa, Walid ya hana shi, ya ce mata “Me zaki yi masa, kin manta abun da yayi miki ne? Ki bar taƙama da baya kisan kai, zai iya farawa a kanki, dan yanzu ƙwaƙwalwarsa sai a hankali “Nabila ta ce “Shi ne dalilin sake zuwana, in ji ya jikinsa kuma na ji ƙarshen labarin nan”Walid ya ce “Jiki yayi sauƙi mun gode, amma ki tafi kar ki sake zuwar mana, saboda zuwan da ki ke yi zamu canza wuri”Liti ya fusata ya ce “Ke dalla fita””Ka daina hantarata, ba wurinka na zo ba. Ni dai ku taimaka ku haɗani da shi, yakamata na ji da bakinsa ya yafe mink””Ke! Ni ki ke gaya wa haka?”Walid ya ƙara dakatar da Liti ya ce “Ya riga ya yafe mikin ai”Ta girgiza kai ta ce “Ban ga alama ba, akwai buƙatar sama masa nutsuwar ƙwaƙwalwa kafin tunkarar duk wani abu, a ɗan zuwan da na yi, na fuskanci kuna amfani da ƙarfi wurin tursasa masa karɓar abun da ya zo masa a yadda yake. Baku da raunin, da zaku tausasa masa yadda yake buƙata”Walid ya ce “Kamar yaya?””Kamar yadda nake faɗa yanzu, a fara samo ƙwaƙwalwarsa, ta hanyar daidaita gangar jikinsa, da hana shi ta’amalli da miyagun ƙwayoyi, a saita tunaninsa da tunatar da shi shi wanene, ko ba duka ba, ayi ƙoƙarin samar masa da wani abu na farinciki ko yaya, a gwada canza masa tunani ba ta ƙarfin tsiya ba, kuma a sama masa likitan da zai din ga duba ƙwaƙwalwarsa”Walid ya ce “Taɓ, ke zaki iya duk wannan ɗin?”Cikin ƙwarin gwiwa Nabila ta ce “Ku bani dama, na san kuma a ba a karon farko ya karɓe ku ya saba da ku ba”.Kafin wani ya kuma magana, ya turo ƙofa ya shigo.Walid ya ƙure shi da ido, dan kar yayi wa Nabila wani abu, ko nuna ya ga mutum a wurin bai yi ba, balle ya yi wani abu, ya shige ɗakinsa ya nemi wuri ya zauna a kan katifa.Babu fargabar komai, ta bi bayansa, tare da yin sallama a ɗakin, bai amsa ba kuma bai ɗago ba.Ta je gabansa, ta durƙusa da gwiwoyinta a ƙasa, ta ce “Ranka ya daɗe, wurinka na zo fa” ya cigaba da ‘yan dube-dube.”Duk da na san, ba zaka amsa mini ba, amma na san kana ji na, wannan zuwan da na cigaba da yi, ina yi ne don neman afuwar kuskuren da na tafka bisa duhun kai, da rashin sani, amma dan Allah ka yafe mini ka yi haƙuri dan Allah” tayi maganar muryarta na rawa.”Dan Allah ka yi magana, wallahi na kasa sukuni, a dalilin jahiltal abun da ya sameka, ban san haka abun yake ba, ka yi magana ka ce ka yafe mini please”Still bai yi magana ba, sai dai ya ɗago ya kalleta, hakan ya sanya ta saurin cire idonta daga nasa.Ya miƙa mata hannunsa ya ce “Bani”Jakarta ta ɗaukko ta buɗe, ta ɗaukko wayarsa, ta miƙa masa, ya saka hannu ya karɓa, sannan ya ce “Sai da nayi kaffara a dalilin rantsuwa da na yi zan kashe ki, ban kashe ki ba, ki ka sake na sake rantsewa sai na aiwatar””Da kuwa ka ci amanar ‘yar madara”
Ayshercool 08081012143
