Hausa novels

Halysaah Page 122 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 122…Khaleesat na isa gidansu Safiyyah ta danna bell ta koma gefe ta tsaya, with the hope that ba Surayyah bace zata bude kofar don ko kadan bata son tashin hankali ita dai, after almost a minute aka bude kofar suka yi ido hudu da Surayyah, Khaleesat ta ɗan yi murmushin karfin hali tace “Ina kwana Maman Aslam” Surayyah ta juya ta bar bakin kofar tace “Sannu da zuwa, shigo mana” Khaleesat ta shiga parlon still not comfortable ta cire takalmanta a bakin kofar, tana tafiya a hankali ta karasa cikin parlon ta zauna edge din kujera, Surayyah ma ta zauna tace “Ya gida, fatan an dawo lafiya?” Khaleesat da mamaki ya cikata tace “Lafiya lau, ina Aslam?” Surayyah tace “Aslam yana bacci, naji kinyi aure, to Allah Ubangiji ya bada zaman lafiya, congratulations” Khaleesat ta sauke idonta tace “Ameen, Nagode” Surayyah tace “Kawar taki tana daki” Khaleesat tace “Ohk to, nagode” Mikewa tayi ta bar parlon ta nufi dakin Safiyyah har sannan mamaki ya kasa barin ta, wai Surayyah ce ke mata magana faram faram har da mata fatan alkhairi tayi aure, nan taga Safiyyah na lekosu ta kofar dakin nata baki sake kamar taga wawan zama, Khaleesat ta karasa ta shiga cikin dakin tana mata murmushi tace “Yanxu kika tashi ko” Safiyyah ta kulle kofar har sannan bata rufe baki ba alamar shock, can tace “Tun da uwata ta haifeni ban taɓa ganin makira irin matar Ya Musty ba, wato yanxu kinyi aure kin fita daga kasuwa tasan ko kallon ki Ya Musty bazai sake yi ba da wata manufa shine har da zaunawa parlor ku gaisa cikin mutunci da mutuntawa, kiji mata, daxu fa da ace na kulata da mun yi batattciya a gidan nan, duk wani abu da tasan ina ci sai ta dauke a kitchen ta boye a dakinta, gashi tayi ta saka min wakokin habaici tun da sassafe, dama yaronta ta dena barin ya zo kusa da ni yanxu” Khaleesat dai murmushi kawai tayi tace “Kema ai kina da naki” Nan da nan Safiyyah ta hade rai tana kallonta, Khaleesat ta kauda zancen tace “Yaushe aka saka date din Quiz dinmu?” Safiyyah tace “Sai ranan Alhamis, we still have time, yau sunday fa, ina mijin naki? Did you sneak out ko kuma shi ya bar ki kika zo?” Khaleesat ta hade rai tace “Ni ki dena ce masa mijina bana so, mijina kamar yaya?” Safiyyah tace “Au to, ina Guard man din ki?” Hararanta Khaleesat tayi taki cewa komai ta tafi ta zauna gefen gadonta, Safiyyah tace “Bani labarin Convocation da kuka je kawata” A hankali Khaleesat tace “Ba wani labari fa” Safiyyah tace “Uhum, kun yi hotuna a can?” Khaleesat tace “A’a ba hoton da muka yi” Safiyyah tace “Masu convocation din dai sun sha hoto kam su” Khaleesat dai bata ce komai ba, Safiyyah ta ɗan yi murmushi hade da taɓe baki, can ta mike tace “Ni ko breakfast fa ban yi ba, ban dade da tashi ba, ke kin yi?” Khaleesat tace “Na yi” Safiyyah tace “To bara in je in dafa ko Indomie” Daga haka ta fita daga dakin, Khaleesat ta jawo handbag dinta a hankali ta ciro wayarta ta bude data ta hau WhatsApp tana jiran messages dinta, message din Jay ta dinga kallo wanda ya shigo a karshe, tun ranan da za su bar England da tayi masa message sai yau yayi reply kuma ko minti goma bai yi da replying message din ba and he is even online, a hankali ta kai hannu ta danna masa WhatsApp call, amma har ya gama ringing bai ɗaga ba kuma yana online, ta sake kiransa nan ma bai yi picking ba, wani message din taga yayi mata yace “Hm” ta tura masa Sad emoji, yace “Later….” Daga haka taga ya sauka online, dai dai nan Safiyyah ta shigo dakin rike da plate din abinci tace “Ina shiga na tarar ashe tayi girki, ko babu ration dina ni dai na debo ba ruwana” Ita dai Khaleesat bata ce mata komai ba, Safiyyah ta zauna tana kallonta ganin yanda mood dinta ya canza tace “Me ya faru Coursemate?” Khaleesat dai taki ce mata komai, Safiyyah ta kalli wayar hannunta, hannu ta kai zata amsa wayar Khaleesat taki bata, ta mayar da wayar gefenta, Safiyyah bata sake kulata ba ta fara cin abincinta, Khaleesat ta kwanta gefen gadon Safiyyah a hankali, Safiyyah dai sai kallonta take da gefen ido tana cin abincinta. Sai kusan karfe biyu da rabi Khaleesat ta tashi daga baccin da ya dauketa a kan gadon Safiyyah, bayan tayi sallan azahar tana zaune kan darduma Safiyyah tace “Me zan dafa mana, ko za ki ci Indomie? Or should I make us Couscous?” Khaleesat dai tayi shiru don gaba daya taji bata da appetite har sannan she was moody, Safiyyah ta mike ta fita daga dakin ganin ba tanka mata zata yi ba, a hankali Khaleesat ta jawo wayarta wanda tun da ta ajiye daxu bata sake dauka ba sai yanzu, message din Ajay ta gani, ta wani hade rai ta bude message din taga yace “Start coming back home now” Few minutes ago ya tura mata text din, ta wani hade rai zata mayar da wayar ta ajiye sai kuma ta bude data ta hau WhatsApp dinta, zaro ido tayi ganin miss call din Jay ya mata WhatsApp call, she couldn’t believe her eyes ta dinga kallon call din babu ko kiftawa, duk da he is not online haka nan tayi returning masa call din, har sai da ya katse sannan ta ajiye wayar, ko da Safiyyah ta dawo dakin bayan minti talatin tayi mamakin ganin Khaleesat ta sauko kamar ba ita ba daxu har da hiranta, Safiyyah ta ajiye masu Indomie din suka ci, duk tana kula da yanda Khaleesat ta sake kamar ba ita ba, Safiyyah tace “Kin ki bani labarin Convocation din da kika je ko” Khaleesat ta ɗan bude ido tace “Da gaske fa ba wani labari, I met Jay’s Cousin sisters a wajen kuma gaba dayansu basu yi welcoming dina ba, even his Aunties ni ban san me nayi masu ba” Safiyyah dake ta kallonta tace “Ohk ba cousin sisters din Ajay bane kenan sai dai Jay?” Khaleesat tace “Oho, duk daya ne ai” Safiyyah tace “To baki hadu da matar Jay ba” Shiru Khaleesat tayi taki ce mata komai tana cin Indomien gabanta, Safiyyah tace “Na zata ita ke convocation din ai” Khaleesat tace “Ni ban sani ba kam” Daga haka Khaleesat ta canza labarin zuwa na Practical din da za su yi gobe a schl, bayan sun gama cin abincin Safiyyah ta kai plate din kitchen ta dawo, Khaleesat ta dauko laptop din Safiyyah tace “Let’s study a little about the practical before tomorrow” Duk da collective reading da suke yi lokaci lokaci Khaleesat ke jawo wayarta ta duba, Safiyyah duk tunaninta agogo take dubawa, can dai tace “Ya baki lokacin da zaki koma gida ne halan?” Sai a sannan Khaleesat ta tuna text din da Ajay yayi mata daxu, ta turo baki tace “Toh ba karatu muke ba, ban gaya maki ba ina apartment dina fa” Safiyyah tace “Ban gane ba” Khaleesat tayi murmushi don har cikin ranta dadi take ji apartment dinta da ya maida ta, tace “Jiya ya kai ni Apartment din, I think his stepmom and Aunty sun zo Maryland ne, kuma kinsan basa so na….” Safiyyah tace “Ashe gata yayi maki, to ke kadai ce a apartment din?” Khaleesat ta gyada mata kai tace “Eh, kawai ya bar motarsa a Garage ne, amma ni kadai na kwana gidan” Safiyyah tace “Ikon Allah, duk abun sa kuma yana da kirki da hangen nesa fa, gashi baya son a tsangwame ki ya maida ke apartment dinki kilan har zuwa lokacin da za su tafi” Khaleesat bata ce komai ba ta ci gaba da karatun da take, daga karshe ta tashi zata shiga bandaki tayi alwala tayi sallah ta tafi gida kafin ya turo mata wani text din, Safiyyah ta bi ta da kallo har ta shiga bandakin sannan ta jawo wayarta da sauri ta bude don ta san password dinta, WhatsApp ta bude bayan ta kunna data, DM din Jay ta shiga ta fara cin karo da WhatsApp calls din da suka ma juna, can ta fara scrolling chat din nasu tun daga farko making sure she is fast kafin Khaleesat ta fito, ita dariya da mamaki ma abun ya bata ta dinga kallon ikon Allah tana karanta chat, jin alamar Khaleesat zata fito ta maza ta fita daga WhatsApp din ta kashe data tayi saurin mayar mata da wayar ta ajiye ta ci gaba da danne danne a laptop dinta, bayan Khaleesat ta fito ta tada sallah Safiyyah ta mike ta shiga bandakin tayi alwala ita ma. Karfe hudu da rabi Khaleesat ta gama shirinta zata tafi, Safiyyah tace “Bari in shirya in raka ki apartment din naki tunda ke kadai ce” Khaleesat ta daga kai ta kalleta tace “Da gaske?” Safiyyah tace “Eh mana, in na raka ki ba sai in dawo gida ba” Khaleesat ta ji dadi har cikin ranta, tace “To kiyi sauri ki shirya, tun karfe biyu da wani abu fa ya turo min text in koma gida” Safiyyah ta bude baki tace “Tun karfe biyu shi ne kika yi ignoring text din??” Khaleesat ta hade rai tace “To ba karatu muke yi ba? Ai ba wasa muke ba” Safiyyah tayi er dariya bata ce mata komai ba ta mike ta fara shiri, bayan ta gama tace “Ina zuwa” Fita tayi daga dakin, Khaleesat na ta zaune bayan tayi order din masu Lyft da zai kai su gida, har minti goma ya shude Safiyyah bata dawo dakin ba, zuwa yanxu kam hankalinta yayi gida don karfe biyar ya gota, ganin Lyft din ya iso ta mike ta dau handbag dinta bayan ta saka wayarta a ciki ta nufi kofa ta fita daga dakin, Safiyyah ta fito kitchen rike da leda ganin Khaleesat ta fito tace “Yauwa fito mu tafi” Za su fita daga parlon Safiyyah tayi kasa da murya tace “Tana kitchen leka kiyi mata godiya ki ce kin tafi, har da tsaraba ta baki” Khaleesat ta ɗan bude ido da mamaki, can ta leka kitchen din tayi ma Surayyah sallama, Surayyah tace “Yauwa sai anjima ki gaida gida” Da haka suka fita daga parlon, sai kusan karfe shidda suka isa gida, bayan sun sauka Lyft Safiyyah ta kalli Garage tace “Ke ya dawo” Khaleesat tace “Ai bai tafi da motar jiya ba dama” Safiyyah tace “Au to, don da na juya na yi komawata bana son jaraba” Suka karasa bakin apartment din Khaleesat ta bude kofa ta shiga Safiyyah na biye da ita a baya, kamshin turarensa taji a parlon, can ta juya da sauri ta kalli bakin kofa bata ga takalminsa ba, tayi ma Safiyyah alamar da tayi shiru ta tsaya, tana tafiya a hankali ta haura sama ta bude duk dakunan bata gansa ba, ta sake dawowa kasa ta shiga kitchen nan ma baya nan, turo baki tayi tace “Kilan ya zo ne yaga ban dawo ba shi ne ya tafi” Whereas bata san yana nan neighborhood din ba kuma yaga sanda suka shiga apartment din, Safiyyah ta rike haɓa tace “Naga wani sabon raini kike ma Ajay din nan, ko da yake shi ne bai yi maganin ki ba har yanxu” Khaleesat ta wani kalleta tace “Ni dai mu je sama” Sama suka tafi zuwa dakinta, Safiyyah tace “Ni ba ma dadewa zan yi ba kinga yamma yayi” Zaunawa gefen gadon tayi ta fara bude ledan dake hannunta, Khaleesat dai sai kallonta take, Safiyyah ta tsuke fuska ta ciro magungunan mata dake cikin ledan tace “Ga su nan saboda Allah ta baki kuma wai kin yi aure bata baki komai ba, wallahi ba kowa ma take ba ma ba wannan kayan ba, baki ga jikinta luwai luwai ba da kika zo, duk kayan gyaran jiki ne, ance in mutum na da kyau ya kara da wanka, fatar ki zai kara fresh fiye da yanda kike yanxu, kinga wannan da madara ake sha ko zuma, nasan ba lallai ki samu zuman ba so kiyi using madara, wannan kuma saboda raman nan da naga kinyi ne zai sa ki murmure nima shi nake sha nake cikowa idan naga na rame, shi ma da madara zaki sha, wannan kuma riga-kafin infection ne kinsan mu mata, to shi ne ta baki ki dinga using nima kwanaki ta tsam min…..” Khaleesat ta dinga kallon Safiyyah da ta dinga zayyano mata amfanin magunguna kusan shidda dake cikin ledan da kuma yanda zata sha su, har sai da ta gama tace “Kin gane ko in dawo farko? Naji kinyi shiru” Khaleesat ta mata wani shegen kallo daga sama har kasa tace “Sai dai ki raina ma kanki hankali, ke kije ki gyara jikin ki da su mana, zaki wani kawo min maganin mata ki ce min na gyaran jiki, nace maki I have anything to do with them ne??” Safiyyah tayi dariya don ita mance cewar Khaleesat ta taɓa aure ma take, ashe fa tasan duk magungunan nan, can dai Safiyyah ta mayar da magungunan gefe ta hade rai on a serious note tace “Bari ki ji Malama idan zaki kama mijinki ki rike hannu bibbiyu ki dena hauka kan Housemate din ki to ina baki shawaran kiyi hakan tun wuri, don Housemate dai na can yana shagalinsa da matarsa sai abinda suka manta, da koro koro eyes dina naga zafafan hotunan da yayi updating a status dinsa na shi da matarsa kamar zasu hade su zama daya ga wani kallon soyayya da yake mata, ke kina ganinsu kinsan ba karamin amarci aka ci ba, see the way they were looking at each other a pics din ai duk nayi screenshot, tsabar shock sai da na farka cikin dare na sake kallon hotunan na koma na kwanta, sabili da haka yasa na sa Surayyah ta debar maki kayan gyaran nan kema ki ji da mijinki ki samu lada, ke idan ma kina da isasshen hankali har sai wani ya baki shawaran abinda ya kamata bayan dawowarku daga England? Na zata you will be motivated ai ki dawo senses din ki, wai ko ba gabanki suka dinga hotunan bane?” A takaice Khaleesat tace “Ban san maki ba, ba cewa kika yi ba dadewa zaki yi ba idan mun zo, beside it’s almost dusk ya kamata ki zo ki tafi” Safiyyah tayi shiru tana kallonta, can tayi kasa da murya tace “Naji amma kina da kayan shayi a gidan nan ki dibar min, Surayya dai ta boye nasu” Har sannan fuskar Khaleesat a daure yake ta nufi kofa zata je ta dibar mata kayan shayin da Ajay ya kawo mata jiya, tana fitowa daga dakin ta gansa tsaye a corridor ya rungume hannu, she was very shock taji kamar ta juya ta koma cikin dakin tace ma Safiyyah ya zo, can kuma ta turo baki ta ki yarda ta kara kallonsa, kamar munafuka ta fara sauka downstairs, ya bi ta da wani kallo, Safiyyah na ganin Khaleesat ta fita ta mike da sauri ta dauko handbag dinta ta bude ta ciro wayarta tayi unlocking sannan ta shiga WhatsApp, blocking number Jay tayi bayan tayi deleting duk chat dinsu, ta tafi call logs dinta na WhatsApp da phone call ma duk ta goge numbersa, ta shiga text message shi ma kafin tayi deleting sai da tayi blocking number ta yanda phone call ma bazai shigo ba sannan ta mayar mata wayar cikin jaka ta ajiye da sauri, waige waige ta fara yi jin kamar kamshin turare alamar dai wani ya shigo, ta mike kamar munafuka tana rike da handbag dinta ta nufi kofar dakin da Khaleesat ta bari slightly open, ido hudu suka yi da Ajay that is looking at the room, Safiyyah ta ɗan yi yake tana sosa keya tace “Good evening” Bata jira sai ya amsa ba ta sauka downstairs da sauri, Kitchen ta samu Khaleesat ta tula mata Milo da Madara a ziplock bag, Safiyyah ta zaro ido tace “Ke kika siya?? Ji min mata” Khaleesat tayi kasa da murya tace “Ya dawo fa” Safiyyah ta rike haɓa tace “Baki ga na lallaba na sauko downstairs ba babu shiri” Khaleesat tace “Is he still upstairs?” Safiyyah tace “Eh mana, kawai kamshin turare naji na leko na gansa, ai ko sum sum na sakko kar ya koreni” Khaleesat tace “To me yake a wajen har yanzu?” Safiyyah tace “Oho” Ni dai nayi ordering Uber, sai mun hadu school gobe, tare suka fito daga kitchen din bayan ta ba Safiyyah ledan kayan shayin da ta dibar mata, a nan kan kujera a parlor Safiyyah ta ajiye mata ledan cikin dubara don ita ba abinda zata yi da kayan shayi, ko damunta bai yi ba ma kawai tana son using privilege din ne tayi abinda zata yi a wayar Khaleesat, Khaleesat ta rakata har wajen apartment din sannan ta koma ciki, amma fa duk ta tsargu kar ace Ajay yaji conversation dinsu da Safiyyah.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788*

Back to top button