Karfe A Wuta Chapter 18 By Ayshercool
Ganin Aminu ya ɓace masa, ya sanya ya koma gida da sauri, rahila sai kururwa take yi, tana jijjiga Abba.Ƙannensa mata su azima, suka kewaye shi suka hau kuka.Abbu ya ɗebo ruwa, ya din ga zubawa Abba, har Allah ya sa ya buɗe ido.Cikin kuka take cewa “Ka gani ko? Ba zaka taɓa yadda da ta’addancin ɗanka ba, har sai ranar da ya kashe mini ƴaƴa, me yayi masa zai yi masa wannan ɗibar karan mahaukaciyar ya watsar? Wallahi na gaji, ina ga tafiya zan yi na bar maka gidan nan kai da ɗanka, na rasa uban me yaron nan yayi masa, ko dan ba kai ka haifi abba ba, ya tsane shi daga shi har nazifi ni ban sani ba. Ni ba abun na kai shi ƙara wurin hukuma ba, ba sa yi masa komai sai dai a sako shi, ni na gaji”.Abbu ya ce “Dan Allah ki daina wannan maganganun, bari na samo mota, mu kai shi asibiti”Abba kuwa ko magana ya kasa, Nazifi ne ya taimaka aka fita da Abba zuwa mota.Al’amin kuwa da ya tabattar da ya tserewa Abbu, ya samu wani lungu, ya jefar da wuƙar hannunsa, ya samu wuri ya zauna, yana ƙoƙarin haɗiye wani abu mai tsananin ɗaci da zafi a maƙogwaronsa, ji yake kamar numfashin sa zai ɗauke, babu abun da zuciyar sa ke raya masa, banda ya kashe matar Abbu wato rahila ya huta.***Gidan babu kowa, duk yaran sun tafi makaranta, mama tayi sallama a falon zakiyya.Ta amsa tare da fitowa daga bedroom ɗin, tayi miƙa ta ce “Lafiya kuwa?””Au bacci ma ki ke yi? Lallai kam, to magana na zo mu yi”Zakiyya ta ce “Ok, bisimillah zauna mana”Ta nemi wuri ta zauna, ita ma ta zauna.Mama ta kalleta ta ce “Kin san waye yake son Jauhar kuwa?””A’a sai kin faɗa”.”Ɗan familyn mai atamfa ne”Waro ido Zakiyya ta yi, har tana neman faɗowa daga kan kujera, ta ce “Wani mai atamfar?””Waɗanda dai ki ka sani,ba ma wannan ba shi zai tsaya takarar majalissar tarayya a yankinsu, jiya na tutsuye shi, yake gaya mini, ga kasuwancin atamfofi da lesuna da yake sayarwa, daga ƙasashe daban-daban yake order kaya, na din ga bugun cikinsa yana gaya mini, wai zata yi karatu idan tana so, idan business take so zai ba ta jari, idan ma zaman gida take so, ayi din ga yi mata komai, duk zai iya kuma nan kusa yake son ayi auren”.”Bantan uba, namu ƴaƴan suna zaune za ayi hakan, muna me?”Mama ta ce “Hmm, ni fa na daɗe ina hana faruwar wasu abubuwan, rannan daga aikenta gidan Hajiyar lamin, wai ɗan wan maigidan ya ganta, ya ce ayi masa hanyar aurenta, uban yaron fa sanata ne a Adamawa, hauka nake? Na toshe na hana, na din ga aika su surayya, da walida amma ko kare a familyn babu wanda ya sinsuna su.Lokacin da suka yi sauka ma, babu kunya wai chairman yana son ta, tun ba ta kai haka ba ma, na ce ba za a lalata mata tunani ba, karatu take yarinya ce, na rasa wannan masifar”.”Mun shiga uku, meyasa kowa sai ita? Kuma duk masu kuɗi, namu yaran fa?”.Mama ta ce “Wannan shegiyar farar fatar suke yi wa ai””Wace farar fatar? Su ma duk ba suna shafa mai ba, manyan zaratan ƴan mata, sun sha mai da kwalliya amma ace su duk shiru sai ita?””Shiyasa tun jiya ban yi bacci ba wallahi, na saƙa wannan na kwance wancan, dole fa a rusa wannan maganar ma”Zakiyya ta ce “To yanzu menene shawara? Wallahi na rasa abun cewa, ko malamai zamu shiga ne?”.”Babu lallai yayi tasiri, na fuskanci ƙashin masu arziki ne da ita, amma mu cigaba da shawara kafin faruwar abun”.Zakiyya ta ce “In sha Allah “Mama ta miƙe ta ce “Sai na ji ki”.***Cikin ikon Allah Abba ya warware, babu abun da ya same shi, sai dai ya bugu, ya yi ta fama da jiri, sai da ya kwana uku a asibiti, aka sallame shi.Rahila ta cigaba da ɗagawa Abbu hankali a kan Al’amin, a kan lallai ya kai shi wurin hukuma, a san yadda za ayi da shi, kafin ya yi mata kisan gilla ita da yaranta.Gaba ɗaya maganganun Al’amin sun yi tasiri a zuciyarsa, amma kuma wani ɓangaren, Rahila tana da gaskiya, al’amin barazana ne a gare su, saboda yadda sunan mai dogon zamani, yayi ƙaurin suna a bakin mutanen unguwa, ba iya unguwar ba, har gidajen radiyo, duk wani faɗan daba da zai tashi a arear rukunin unguwannin to sai an ambaci mai dogon zamani wato Al’amin.Ƴan sanda har sun gaji da kama shi, idan an kama shi ma, ƴan siyasa sai sun saka an sako shi, daɗinta ɗaya ba ruwansa da taɓa kowa ko kayan kowa, sai ƴan daba da jami’an tsaro da su yake faɗansa.Bayan Jauhar ta dawo daga makaranta, mama da Anty suka sakata a gaba, suna sake yi mata tambayoyi a kan Alhaji mu’azzam, Jauhar ta rasa me za ta ce musu, dan ita ba komai ta sani a kansa ba, dan tun da ya zo sau ɗaya, bai sake zuwa ba, dan haka ta din ga ce musu ba ta sani ba.Aikuwa suka din ga zaginta, tare da kiranta munafuka.Suka gama zaginta, ta cigaba da sabgoginta.Yaya tijjani ya shigo, wanda shi ne babba a gidan, ya shiga wurin mama, jauhar ba ta san hawa ba, ba ta san sauka ba, ya kamata ya zane a yammacin nan, wai an ce masa kule-kulen maza take yi.Ihun jauhar ne ya sanya yaya saifu shigowa, ya tarar TJ yana mata bala’i, wai tana kula maza.”Haba yaya TJ, idan ba ta kula maza ba, kai za ta kula? Ko za a jiƙata a ruwa a sha ne? Da iznin baba fa ya zo wurinta idan ma a kan wannan mutumin nan”Mama ta ce “Rufe mini baki, kai da ba ka san me duniyar take ciki ba, yadda maza ke lalata yaran mutane yanzu, idan aka sake lalata ta kawai zai yi ya gudu, kuma fuska ya gani shiyasa ya biyota har gida, da ba ta bashi fuska ba ba zai zo ba. Idan da gaske yake auren zai yi, duk ga mata nan da suka fita komai sai ita.Saifu kawai ya girgiza kai ya fice, ransa ba ya yi masa daɗi, da irin riƙon da ake yi wa ƙanwarsa a gidan nan, shikenan maraici sai ha zama makamin cutar da bawa?.Har jauhar ta gama girkin dare, kuka take yi, dan ta daku sosai da sosai, fatarta duk tayi ja.Baba da ya dawo, bai san me aka yi ba, na dukan Jauhar.Ɗan autansu ne wato amir, ya shigo ya ce “Jauhar ana kiranki a waje, in ji wannan mai motar, kin ga har ya bani kuɗi dubu biyu”.Anty ta ce “Ba zata je ba, je ka ce ba ta nan, ki mayar da kai ki gama sauran aikace-aikacen ki, idan kuma baki da abun yi, ki zo ina da shi ki yi mini”.Baba ya fito da kansa ya ce “Amir, je ka ka ce tana zuwa, Waliyiyya, ajiye duk abun da ki ke yi, ki je ki sallami baƙonki”.”Amma Alhaji…..”Amma me? A kan me zaku hana yarinya zance, maganar aurensu fa za a fara kwanan nan, da yaya za su fahimci juna?”.Jauhar kamar ta ce wa Baba ba zata je ba, dan tana tsoron a sake saka yaya TJ ya dake ta.Amma ta kasa magana, ta zura hijjabinta, ta fita.Tun kan ta fita ta fara jiyo ƙamshin turaren sa, kamar wancan karon ta durƙusa tana gaishe shi.Sai dai bai amsa ba, ya ce “Na yi missing ɗinki Jauhar, sai dai na baki lokaci ne, dan kar na dame ki. Yaya ake ciki kin yi mana addu’ar? Kin fara so na?”Maimakon ta bashi amsa, sai ƙifta ido take yi, tana waiwaye kar TJ ya zo ya ce zai sake dukanta, tun da ta tsaya da wani ne ba sa so.Ya ɗora da cewa “Dama baba ne ya ce na ɗan baki lokaci, to kuma ga tafiya ta kamani babu cikkaken shiri, na ce a kawo mini kuɗin aure, kafin na tafi, amma na ga bari na ji ta bakinki, kar na yi miki shigar sauri”Tayi shiru kamar ba da ita yake ba.”Baby yangar nan tana yawa fa, dan Allah ki yi mini magana na ji nutsuwa mana” yayi maganar yana dawowa kusa da ita ya tsaya.”Jauhar ki yi magana mana””Allah ya zaɓa mana abun da ya fi alkhairi” ta faɗa a hankali.Ya ce “Kin amince zaki aureni?”Ta ɗaga masa kai alamar eh.”Wow, anya ba zan ce a ɗaura mu tafi chinan tare ba?”Ta ce “A’a, dan Allah a bari na gama makaranta, mun kusa yin WAEC”.Alhaji mu’azzam ya ce “Na so ace zan iya yi miki hakan, amma ba zan iya jurewa ba, kar wani ya rigani, ko da na tafi ina can, iyayena zasu zo ayi maganar, da na dawo sai maganar bikinmu, i will be with my little baby amarya very soon in sha Allah”Tayi murmushi cikin jin kunya, tana murmushi.”Jibi in Allah ya kaimu fa zan tafi, babu tsammani tafiyar ta zo, me zaki gaya mini kafin na tafi, da zan din ga tunawa da ke, kin ƙi yarda na baki waya, balle mu din ga waya ina jin daɗi. Yanzu me zaki ce mini?”.Ta ce “Duk lokacin da ka tuna ni, ka yi mini addu’a””In sha Allah amaryar mu’azzam, zan din ga yi mana, daɗin auren mace mai addini kenan”Ya din yi mata hira, har ta ɗan sake tana yi masa murmushi.Ita dai ba ta sani ba tana son sa ko ba ta son sa, duk da ya girme mata, ya iya magana, ya sauke shekarunsa dai-dai da nata, ga ƙamshin turaren sa daɗi yake yi mata, dan a hakan yadda take fama, idan ta samu ƴan kuɗi, baka rabata da turare.Daga kan Surayya zuwa walida da hafsa, babu wadda ba ta fito ba, da niyyar za su fita yin wani uzurin, kuma babu wadda ba ta gaishe shi ba, sai dai gaba ɗaya hankalinsa da nutsuwarsa yana kan ƴar bainun gabansa wato Jauhar.Da zai tafi, sai da ya haɗe rai sosai, sannan ta yarda ta karɓi kuɗin da ya bata.Sai da ya tabattar ta shiga gida, sannan ya tafi.Ɗaki ta je ta bawa baba duk abunda ya bata, kuɗi masu yawa, mama ta din ga masifa, kamar ta ari baki, da sunan kula da tarbiyyar Jauhar.***Al’amin yana kashingiɗe yana busa wiwi, yana kaɗa ƙafarsa ɗaya, yana jin sa a sama, dai-dai da kowa, sai dai busa hayaƙin yana bashi nishaɗi, yana jin daɗin hakan.Wuƙar gefensa ya ɗauka ya zauna sosai, ya karta ta a ƙasa, ya gyaɗa kai sannan ya ɗago ya ce “zan shiga ƙofa, zan tayar da tarzoma, zan je ɗaukar fansa””Wurin madakin dai?” Walid yayi maganar yana kallon sa.”Koma wurin waye, ka manta abun da suka yi mana kafin na je prison?”Walid ya girgiza kai ya ce “Ban manta ba””Zamu ɗauki fansa, madaki kuma ban ce kowa ya taya ni ba, faɗana ne nikaɗai wannan”.”Shikenan yaushe zamu shiga?””Shammatar su zamu yi, zan yi muku magana”Ya koma ya kashingiɗa, ya cigaba da zuƙar wiwi.*****Tun da Allah ya sa Alhaji mu’azzam ya tafi, Jauhar ta manta da babinsa, sai dai in mutanen gidan sun ɗaukko hirarsa, ita da yake zuwa wurinta ma ba ta zancensa kamar yadda suke yi.Babbar murnarta ita yanzu, ganin yadda kantunta yake ƙarewa da wuri, duk da ana yi mata mugunta a gidan, yaya saifu ya ƙara mata jari, ya bata dubu ɗaya.Ɗan kuɗin da take juyawa, da na riɗin, da na shirin dutsen, bai fi dubu biyu da ɗari biyar ba, amma murna take yi da hakan, jin kuɗin take da yawa, dan ƴar hamsin ɗarin da take bi na riba, ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba, dan nan da nan ta tara kuɗin pad, har ta fara tarin kuɗin makarantar islamiyyarta, kan lokaci yayi ta zo tana nema.Yau an tashi daga islamiyya, ta sayar da riɗinta tsaf, dama da ɗaurin shirin dustenta, ta fito daga aji, tana lissafin tayi maza ta kai musu, ta karɓo wani.Ko da ta fito wajen gate ɗin makarantar, matasa suka gani suna guje-guje, wai faɗan daba ake yi, mai dogon zamani ya shigo ɗaukar fansa.Jauhar ko a jikinta tayi gaba, tun da daga in da ake gudun bayansu ne, dan haka tayi gaba abun ta, ta nufi hanyar gidan da take karɓar shirin.In da take bin shiru babu mutane ma, tana shiga layin gidan shirin, ta ɗaukko robar riɗinta, ta ciro kuɗin cinikinta, ta hau ƙirgawa murmushi ta saki, tana jin daɗi, ta fara tunanin tambayar kuɗin aya gwangwani biyu, ita ma ta din ga soyawa da gishir tana sayarwa.Hankalinta ne yayi mummunan tashi, bayan da tayi baƙin ganin da ba ta farga da shi ba sai yanzu.Hannunsa riƙe da wani mutum, da ba ta da tabbacin yana da rai ko babu, da wuƙa a gefen cikin mutumin, hannunsa duk jini, kuma shi ma da yake riƙe da mutumin da take kyautata zaton kashe shi ya yi ƙafarsa sai zubar da jinin take yi.Tun da ta shigo layin ta fara lissafa kuɗi, ya ɗaga kai ya ganta, amma ita sam ba ta ganshi ba, hankalinta yana kan lissafin kuɗin da yake hannunta, sai da ta je tsakiyar layin, ta kusa zuwa daf da shi sannan ta farga.Zuciyarta ce ta fara wani iri razanannen bugu, gashi ta kasa ko da motsa ƙafarta, balle ta cirata ta gudu, ba ta taɓa ganin mummunan tashin hankali ba tun da take a rayuwarta ba sai yanzu, ita ko film ne ta ga ana kashe-kashe, ko harbe-harbe bata kalla, kodayeke ita kallo ma bai dameta ba, amma sai yau gata ga gawa da jini.Ba tare da ta yi tsammani ba, wani irin ƙarfi ya zo mata, ta taƙarƙare iya ƙarfinta, ta kurma wani irin uban ihu, ta yinƙura da niyyar ta gudu, sai dai tsananin bugun da zuciyar ta take yi, ya sanya numfashinta kasa daidaituwa a ƙirjinta, kuma ta gaza ɗaukar nauyin jikinta, dan haka ta faɗi a wurin a sume, robar da cinikin, da jakar islamiyyar duk suka watse a wurin, gefen kwata.Duk da wannan uban ihun da tayi, babu wanda yayi ƙoƙarin buɗe ƙofarsa ya ga mai yake faruwa.Duk da dama, gidaje biyu ne kacal a layin, sauran duk bayan wasu gidajen ne a cikin layin.Tsaki ya ja, ya mayar da idonsa kan liti, da yake numfashi sama-sama.Ya kalli ƙafarsa da take ta zubar da jini shi ma, saboda saran da aka yi masa.Ya kwantar da liti, ya tashi ya tafi kan jauhar, ya kai hannun sa kan hancinta, ya ji tana numfashi.Ya kamo hannunta, ya riƙe tsintsiyar hannunta, ya ji zuciyarta na wani irin bugu, da saurin gaske.Kamar ya ɗauki tabarma, haka ya ɗauketa daga kan hanya, ya kwantar da ita a tsallaken kwatar, ya tattaro kayanta ya haɗe mata wuri guda, sai dai uniform ɗin ta, duk sun ɓaci da jinin da yake zubarwa.Wald ne ya ƙaraso layin da sauri, shi ma hannunsa riƙe da wata sharɓeɓiyar wuƙa tana zubar da jini, ya ƙarasa in da Al’amin yake harya fara ganin jiri, saboda jinin da ya zubar.”Subhanallah, waye yayi gangancin yankarka?””Ƙyaleni, ka kira su baffan?””Eh, suna bakin titi da ɗan sahun”Ya miƙe ya saɓa liti da yake zubar da jini a kafaɗarsa.Walid ya ce “Kawo shi, na ga kamar jiri ka ke yi mu ƙarasa”.Ya ce “A’a bar ni da shi, zan yi wa honorable waya, ya aika mana ƴan sanda asibiti, waccan yarinyar, ka buga ɗaya daga gidajen layin nan, su fito su kaita Asibiti, ta tsorata ne, idan kuma ba haka ba za ta yi musu mushe a wurin, saboda zuciyarta na bugawa da sauri sosai”Walid ya ce “Wai wa yake ta wata yarinya, kai kaɗai zaku tafi asibitin, kalleku fa jina-jina””Mai rai ce fa, idan ba su buɗe ba, ka haura gidan kawai, ka saka su buɗe, yanzu idan muka tafi da ita zai zama wani abun daban” daga haka yayi gaba, ya nufi barin layin.Walid ya yamutsa fuska, ya samu ɗaya daga gidajen, ya din ga wani irin bugu, kamar yaƙi.***Cikin tsananin hanzari ta yinƙura, za ta diro daga kan gadon da take, tana faɗin”Innalillahi wa Innalillahi raji’un, dan Allah ku taimake ni, zai kashe ni”Cikin azama baba ya riƙe ta, ƙoƙarin ture shi take yi, ta saukko daga kan gadon. Baba ya ce “Jauhar, buɗe idonki, ki kalleni ni ne ki nutsu” sannu a hankali ta buɗe idonta, ta kalli baba, ta juya ta kalli su mama da Yaya saifu da suke wurin, sai malam jamilu da malam hamza.Jikinta ya hau wata irin tsuma, ta dinga fizge-fizge tana ƙoƙarin fizge robar ruwan hammunta.”Ke ki nutsu mana, meye haka ne ana yi miki magana” mama tayi maganar tana haɗe rai.Ta girgiza kai ta ce “Mama tsoro nake ji, wani ya kashe fa, dan Allah ku ɓoye ni zai kashe ni nima, ganinsa nake yi a idona, dan Allah baba ku tafi da ni tsoro nake ji” tayi maganar tana ƙoƙarin tashi tsaye.Baba ya ce “Wai shi wa?”Cikin kuka ta ce “Ban san shi ba, kawai gani nayi dai ya kashe wani yana kallona, nima na san zai biyoni ya kashe ni”.Baba ya ce “To ai babu wani wanda aka gani an kashe, ke kaɗai aka gani a layin a sume”.Anty ta ce “Uban me ma ya kai ki can, in da ba hanyar gida ba?”.”Shiri na je karɓowa””To ubanwa ya aike ki?”Baba ya ce “Dan Allah duk a daina wannan maganar, yanzu a bari ta samu nutsuwa”.Ƙoƙarin kwantar da ita Baba yake yi, ta kalli jikin uniform ɗin ta, ta ga jini, ihu ta sake yi, tana faɗin “Meya same ni, baba kalli jini a jikina, na gaya maka nima kasheni zai yi, kalli jini fa wataƙila ma na mutu ne”.A take wani abu ya ɗarsu a zuciyar mama, tayi wani shu’umin murmushi, yaya saifu kuwa likitoci ya kira, aka sake yi wa jauhar allurar bacci, dan gaba ɗaya nema take ta zare.Malaman islamiyyar suka yi wa su baba sallama, malam Jamil dama a kusa da layin da take zuwa karɓar shirin yake, yana yawan ganinta, wataran shi yake korata makaranta ko gida, tun da ya fuskanci halin da take ciki, yake ƙyaleta, dan watarn har gidansu take shiga, ƙannensa ƙawenta ne.Shi ya din ga bawa baba baki, da bashi tabbacin jauhar ba yawo take tafiya ba, kamar yadda mama ke ta iƙrari.Baba ya ce “Ni ma na san jauhar ba ta yawo, wannan abun da ya faru ma tsautsayi ne, Ubangiji Allah ya kiyaye gaba” suka yi sallama su malam jamil suka tafi.Kusan awanni biyu, jauhar ta sake farfaɗowa, sai dai wannan karon da sauƙi, ba cikin razani ta farka ba kamar da farko.Likita ya zo yana sake dubata, Mama ta ce “Likita kun dubata da kyau kuwa, wannan jinin na jikinta ba fyaɗe ƴan daban suka yi mata ba?”Dummm! Ƙirjin Jauhar ya buga, ba ita ba hatta baba sai da gabansa ya faɗi, suka kalli mama a tare.Likitan ya girgiza kai ya ce “No, bana tunanin hakan, razani ne kawai”.”To amma meya kawo jini jikinta?”.Likitan ya yi shiru yana kallon jauhar.Baba ya ce “Likita ka yi magana mana”Jikin jauhar ya cigaba da rawa, tana nanata fyaɗe a zuciyarta, amma kuma da gaskiyar mama, meyakawo jini jikinta?.Likitan ya ce “Zaki iya tuna abun da ya faru?”.Ta ɗan yi shiru sannan ta ce “Na shiga layin kawai na ga ya kashe wani, da wuƙa a cikin sa, shi ma ƙafarsa tana zubar da jini””Kin san shi ne? Kin taɓa ganinsa?” Ta girgiza kai alamar a’aYa ce “Zaki iya tafiya?”Ta jinjina masa kai alamar eh.Ya cire mata ruwan sannan ya ce “Saukko ki biyo ni” ta yinƙura ta sauka daga kan gadon, ta bi bayan likitan, zuwa wani ɗakin daban, ya kira wata nurse ya ce ta duba masa jauhar, amma jauhar fafur ta ce ba zata buɗe jikinta ba, sai ma ta hau kuka.Nurse ɗin ta din ga lallaɓata tana yi mata tambayoyi, ta saka ta ciro mata phant ɗin ta, ta duba ta ce wa likitan ba abun da aka yi wa jauhar ɗin mai kama da fyaɗe.Wataƙila da ta suma ya taɓa ta, tun da ta ce shi ma da rauni a jikinsa, amma ba dai fyaɗe ba.Likita ya koma ya yi wa baba bayani, baba ya din ga hamdala, mama ta ce likitan ƙarya kawai yake yi, babu yadda za ayi, ta samu jini a jikinta, idan ba fyaɗe aka yi mata ba.Likitan ya ce “Amma dai ba ƴar ki ba ce hajiya, da taki ce ba zaki yi mata wannan mummunan fatan ba, bani da wata riba da zan ci, idan na yi muku ƙarya, kuma babu yadda za ayi ayi mata fyaɗe ku kawota a haka, ba wani rauni ko alamu na fin ƙarfi, dan babu ɗan iskan da zai yi wa yarinya fyaɗe ya tsaya mayar mata da kayanta a tsakiyar layi, kamar yadda muka karɓi report”Baba ya ce “Doctor, a bar zancen ma gaba ɗaya, ni dai na gode sosai da sosai, na gode Allah da babu abun da ya sameta, za a iya sallamar mu yanzu?”.Ya ce “Eh, yanzu zan sallame ta”. Aka rubuta musu sallama suka tafi gida.Maƙwabta suka din ga shigowa yin jaje, saboda labari ya cika tsukin, faɗan daba ya rutsa da jauhar, an tsintota can a sume.Sai dai duk wanda ya zo, sai su mama sun bashi labarin, cewar cikin jini aka tsintota kuma jikinta babu rauni, ana kyautata zaton ko sun yi mata fyaɗe.Jauhar hankalinta ya kasa kwanciya, ta din ga tunani daban-daban, ko da ƙarancin shekarunta, a science class take ss2, kuma tana zuwa islamiyya ta san duk wadda aka yi wa fyaɗe sai ta ji wani sauyi a tare da ita, amma ita ba ta ji komai ba, babu wani abu da take ji na sauyi a tare da ita.Tun tana damun kanta, har ta watsar, sai dai ƙasan zuciyarta tana jin zafin abun da su mama suke faɗa, dan idan ta fita har tambayarta ake yi, wai da gaske an yi mata fyaɗe?.Har fita ta so ta fara gagararta. Sati biyu da faruwar lamarin, Baba ya zo ya sanar musu da cewa, iyayen Alhaji mu’azzam za su kawo kuɗin auren jauhar.Hankalinsu yayi mummunan tashi, daga su har ƴaƴan su. Suka ƙara tsananta tsangwama da kyarar jauhar.Duk da tana da matuƙar juriya, da kawar da kai, har abun ya fara effecting ɗin ta.Bai sanar da su lokaci ba, sai ranar da za a kawo ya sanar da su, hankalinsu ya ƙara tashi, sai dai ba su tsinke da lamarin ba, sai da aka kawo kuɗi masu yawan gaske.Anty ta kira Rahila, cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali take gaya mata, tare da tambayarta ko akwai wani zazzafan malamin ta haɗa su, a samu a watsa lamarin.Rahila ta ce “Wallahi ni kaina a cikin matsala nake Zakiyya, yaron nan ya zame mini bala’i fiye da koyaushe, idan ya ga dama fa cikin gidan yake zuwa ya kwana a tsakar gida, gaya miki ne ban ba, sai da muka kwanta a asibi, ya ɗaga Abba ya buga da ƙasa saboda babansa ya hana shi zuwa gidan, gashi kamar ya fara jin tausayinsa, wallahi kamar na bawa tsinanne guba ya ci ya mutu””Innalillahi, rahila menene abun yi? Ni fa sonake maganar ta watse, a dawo mutumin ya auri hafsa”.Rahila ta ce “Aikuwa kin yi dabara, ina da wani malami, wurinsa nake son komawa, ina jin daɗin aikinsa sosai da sosai, duk da su ma malamn yanzu duk sun zama ɓarayi, su ci maka kuɗi babu biyan buƙata, amma nasa babu laifi”.”Wallahi kuwa, saka mana rana, ko da tsiya da masifa, lamarin ya dawo kan hafsa”.”Idan a shirye ki ke, kawai ki zo mu je, ba a bori da sanyin jiki”Suka yi sallama a kan haka, ɓangaren mama ma, tuni ta zari mayafi ta tafi nata wurin malamin, a kan lallai al’amarin nan kar ya yiwu.Haka ita ma anty ta shirya, ta tafi gidan rahila.Ita kuwa jauhar, addu’a take ta yi, Allah ya sa mutanen unguwar su manta da sharrin su mama da suka yi mata, na cewar fyaɗe aka yi mata.Maganar kawo kuɗin auren duk bai wani dameta ba, ita gaba ɗaya ba ta jin dadin rayuwar ma gaba ɗaya, gashi har a lokacin tana yawan tsorata, idan ta tuna abun da ta gani, haka take ganin abun a mafarki, sai dai tayi ta addu’a tana fatan Allah ya yi mata tsari da wannan mutumin mara imani.Malamin ya gama surƙullensa, ya kalli su zakiyya ya ce “Za a iya watsa lamarin amma fa kafin dawowarsa, muddin ya dawo, babu yadda za ayi”.Zakiyya ta ce “Malam tayaya kenan?””Ko dai a aura mata wani, ko kuma a kasheta”Tayi jimmm ta ce “Kisa kuma malam, a’a gaskiya ban da kisa, muguntar tawa ba ta kai nan ba, ni fa burina kawai ya auri ƴa ta”.”Ta yaya zai aureta, alhalin yana ganinta?”Rahila ta ce “Sai a juya masa tunani mana malam”.”Za a iya juya masa tunani, amma ba zai juyu yadda ake so ba, abun zai sake shi da wuri, dan su ma masu kuɗin ba da ka suke zaune ba, kuma maganin ba zai yi aiki a kansa ba, dole sai ya dawo ƙasar nan, zan haɗa laƙanin, ya manta da wannan ya auri wadda ku ke so, amma muddin ya dawo yayi tozali da wadda yake son ɗin, ƙasa ta nuna mini ba zai yiwu ba”Zakiyya ta ce “Tirƙashi! Ana wata ga wata, ga ƙoshi ga kwanan yunwa”Rahila ta ce “Malam mun gode, idan mun yanke shawara zaka ji mu, tashi mu je ki ji ina da shawara”Suka sallami malamin, suka tashi suka fito, ta kalli rahila cikin damuwa ta ce “Wace irin shawara ce da ke?””Shawara ce mai kyau, amma ina ga mafita ce, tun da damuwar mu kusan ɗaya ce, me zai hana a haɗa ta aure da wannan fitinannen yaron na gidana, kin ga kun huta na huta, su je su ƙarata, ya bar ni da mijina da ƴaƴana”.Zakiyya ta buɗe baki ta ce “Ta yaya? Babanta kuwa zai yarda?””Ke dalla can, shiga zaki yi ki fita, idan ba haka ba wallahi daular da ki ke kallo ta gagareki, kin ga mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya”.”Wallahi maganarki gaskiya ce rahila, zan yi magana da matar gidan, ta fi ni iya sarrafa shi yadda take so a kan yarinyar, zan je mata da zancen, ayi a ƙarƙare kan wancan ɗin ya dawo”.”Yauwwa, amma fa kar ki gaya mata wurin malami ki ka je”Zakiyya ta ce “Hauka nake zan gaya mata haka? Ke dai ki saurare ni kawai””To shikenan, sai na jiki, yadda ku ka yi ki sanar da ni da wuri, nima zan wa babansa magana” suka yi sallama zakiyya ta tafi da ƙarfin gwiwar ta.
Ayshercool 08081012143
