Halysaah Page 74 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 74…
Juyawa Jay yayi ya sauka downstairs don bai son yayi abinda zuciyarsa ke tunzura sa yayi a wannan moment din, yasan in ya ci gaba da tsayuwa yana sauraron kukanta a wajen the case will be totally different, sai da Khaleesat taga ya sauka kasa sannan ta dena kukan da take har lokacin tana jingine da kofar tana goge idonta a hankali, juyawa tayi ta koma dakinta ta dau laptop dinta ta zauna kan gado zata yi karatun wani course dinsu amma ta kasa karatun, sai kuma tayi tagumi tana kallon screen din laptop din babu ko kiftawa, after a while ta maida Laptop din gefe ta sauka daga kan gadon ta nufi kofa ta fita daga dakin, walking slowly ta fara sauka downstairs tana kallonsa, zaune yake kan kujera idonsa a wayar hannunsa, ya juya yana kallonta jin foot step dinta, har ta karaso karshen staircase din, ta sunkuyar da kai ganin kallon da yake mata, mikewa yayi ya nufeta yayi kasa da murya yace “Halysaah… ” Ta daga idanuwanta ta kallesa amma bata ce komai ba, yace “Why are you crying?” Kamar bazata ce komai ba sai kuma ta jingina da bango ta rungume hannunta tace “Ba sai kace min inyi hakuri ba amma ka wani tafi….” Murmushi yayi yace “To ai ban san ta yanda zan fara cewa kiyi hakurin bane ta yanda zaki gane da gaske nake baki hakurin, shi yasa na tafi” Ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, can ta juya zata bar wajen, ya dakatar da ita yace “Halysaah” After some seconds ta juyo fuska a daure, ya ɗan yi murmushi yace “Mu je parlor in baki hakurin to” Ta wani turo baki ta kara rungume hannunta, yana murmushi ya juya ya koma parlon, sai kuma ta bi bayansa, ya jira har ta karaso ta zauna kan kujera, sannan ya zauna same kujeran leaving some space between them yana facing dinta yayi kasa da murya yace “Now tell me, why were you crying Halysaah?” Ta sauke idonta a hankali tace “I just can’t understand why Abdul is still after me…” Jay yayi shiru yana kallonta babu ko kiftawa, can yayi kasa da muryarsa yace “But mun gama maganan nan just few hours ago ai Housemate, i told u i will put a stop to that soon, i promise you this, kina gama jarabawa idan mun koma Nigeria komai zai zo karshe in sha Allah” Muryarta na rawa tace “Why not now? Ai bazai daina bi na ba, and i want to concentrate fully on my exams….” Jay yayi shiru yana kallonta, ya sauke idonsa with calmness in his voice yace “Are you sure you will want that now?” Ta gyada masa kai looking so confuse tace “Ya fa je har gidanmu a can kano so many times, sannan daxu muna gidansu Safiyyah sai da yaje gidan fa ya danna bell and left immediately….” jay ya daga idanuwansa yana kallonta da mamaki yace “Really?” Ta marairaice masa tace “Aunty Farida ta gaya min yana ta zuwa gidanmu, pls kawai we should report him to authorities don ya fita hanyata, ni wallahi tsoronsa nake ji, he can be so cunning….” Jay was quiet for almost a minute, sai kuma ya daga kai suka hada ido don kallonsa take, ita ta fara dauke idonta, har zai kamo hannunta sai kuma bai yi hakan ba ya fara kokarin kara barin enough distance tsakanin, yayi kasa da murya yace “Do you want to get married Khaleesat?” Shiru Khaleesat tayi tana kallonsa babu ko kiftawa don tambayar tasa ya zo mata a bazata, shi dai kallonta kawai yake yana jiran amsarta, a hankali tace “Aure kuma?” Jay yace “Yeah” Tana son tambayarsa aure da wa amma ta kasa, nan da nan jikinta yayi sanyi don babu inda tunaninta ya tafi sai ko yana da wani da zai hadata aure da, speaking slowly yace “Aure ne kawai zai sa ya hakura ya dena bibiyanki Halysaah, in kuwa ba haka ba bazai hakura ba ko da an hadasa da hukuma he will only change his tactics…” Hawaye taji ya fara taruwa idonta, sai tayi da ta sanin sauko ta samesa a parlon, kilan da bai gaya mata wannan magana ba, ganin hawaye a idonta cikin sanyi yace “Baki shirya auren ba ko Housemate?” Ƙin ce masa komai Khaleesat tayi tana kokarin ganin bata fashe da kuka ba a wajen, ta rasa me yasa ta zama heartbroken all of a sudden da jin furucinsa, was it because that wasn’t what she was expecting or wanting, she still can’t tell, Jay ya sauke idonsa daga kallonta, after some seconds yace “To kiyi hakuri, i shouldn’t have brought this suggestion up, may be you have other plans than marriage ko” Ita dai bata ce komai ba tana goge hawayen dake sintiri a fuskarta, ya jinginar da kansa da kujera bai sake cewa komai ba, tayi karfin halin cewa “Ai baka ce min da wanda zan yi auren ba” Ya girgiza mata kai still not looking at her yace “A’a, naga ba aure bane plan dinki na gaba, i am sorry i came up with the idea, kawai ina ganin kamar hakan kadai ne mafita… I am sorry” Tana girgiza masa kai still trying not to cry out loud tace “Ni bani da wani plan wallahi, kawai burina Abdul ya fita rayuwata ya kyaleni, duk wani abu da zai tabbatar da hakan i will welcome it wholeheartedly, as far as he will stay far away from me” Jay ya kalleta a hankali yace “To nace aure kin fara kuka ai Housemate” Ta girgiza masa kai tace “In hakan ne best solution i will welcome it, kawai dai ban san da wanda zaka hadani bane” Jay dai kallonta kawai yake amma ya kasa cewa komai, ita kuwa sai goge hawayenta take without looking at him, yayi kasa da murya yace “I don’t know ko za kiyi turning down din wanda zan hada ku Halysaah, bazan so in maki dole ba, ko kuma nauyina yasa ki amince bayan ke ba hakan kika so ba a ranki” Khaleesat ta girgiza masa kai cikin karfin hali tace “I won’t… as far as it’s ur choice i will never turn it down, i trust ur choice, and i know it will be the best for me, nasan baza ka min zabin da bazai yi favouring dina ba, i know this…” Magana take amma Allah yasani karfin hali kawai take, she was very very heartbroken deep inside her and she can’t even say why, Jay dai bai fasa kallonta ba yana tunanin what he is about to voice out and how she will react to it, jin shirun nasa yayi yawa ta daga idanuwanta da har sun fara ja suka hada ido, kamar me rada yace “Za ki iya aurena Halysaah?” His question almost took away her breathe cause it hit her unexpectedly, she was stunned into silence at the same time paralyzed with surprise, she couldn’t stop staring at him with wide eyes, shi ma kallonta yake babu ko kiftawa kamar yanda take kallonsa, and she realize they’ve been staring at each other for almost 30 seconds, da sauri ta dauke gaze dinta daga idonsa zuciyarta na bugawa, cikin dubara ta fara kokarin mikewa zata bar masa parlon, yana gano abinda zata yi yayi saurin rike hijab dinta yana kallonta murya can kasa yace “Ba inda za ki je without giving me my answer Halysaah” Boye fuskarta tayi jikin kujera da sauri taki yarda su sake hada ido tana jin kamar ta nutse cikin kujeran, ta dade bata ji irin wannan kunyan da take ji a yanxu ba, yana kallonta yace “Halysaah” Taki dago kanta tana kara shigewa cikin kujeran tace “Uhm” Yayi kasa da murya yace “Look at me plss” kamar zata yi kuka tace “Uhm ni bazan iya ba” Gaba daya ta gama narkar da shi a wajen, ya duka gabanta yana kallonta as if he is whispering yace “Pls say something Halysaah, i want to hear you say something” Khaleesat dai taki yarda ta dago kai su hada ido da shi, she can’t even explain what she is feeling at the moment, slowly yace “To tashi ki je ki kwanta, sweet dreams Dear, I love you so much….” Sake gigitata yayi da kalamansa, ta fara kokarin mikewa daga kan kujeran tana rufe fuskarta da Hijab din jikinta, saboda saurin da take ta bar wajen ta take dogon hijab din jikinta kiris ya rage ta fadi har zai rikota kawai ya hana kansa yin hakan, tayi regaining balance dinta within a twinkle of an eye har ta isa staircase ta wuce sama da sauri ta shiga dakinta ta kulle kofa ta jingina jikin kofar tana sauke ajiyar zuciya kamar warce tayi tseren gudu…
Daren ranan Khaleesat bata yi baccin kirki ba, she can’t even explain her emotions, da gari ya waye har karfe sha daya na safe ta kasa sauka downstairs gashi karfe takwas suke da class ranan, har ta gaji da kiran da Safiyyah ke ta doka mata tun daxu, da sauri ta juya jin ana knocking kofar dakinta, ta kasa tashi ta bude kofar, ita kanta bata san kunyanta ya kai haka ba sae yanxu, da kyar ta mike jin an sake knocking kofar, ta dau veil dinta ta yafa kamar sabuwar amarya ta karasa bakin kofar, nan ma sai da ta tsaya for almost 30 seconds kafin tayi karfin halin bude kofar kanta a sunkuye, yana tsaye bakin kofar calmly yace “Good morning Housemate” Still not looking at him cikin sanyin murya tace “Ina kwana” Yace “Lafiya lau, baki da lectures ne?” Kanta a kasa tace “Ina da” Shi dai kallonta kawai yake ganin wani sabon kunyansa da ta tsira kuma, ya ɗan yi murmushi ya mika mata karamin tray din hannunsa yace “Here…. Idan kin gama sai inyi dropping dinki a school din” Iya abinda yake mika mata kawai ta ɗan kalla sannan ta amsa, shi dai kallonta kawai yake ta juya ta koma cikin dakin sannan ta kulle kofar, Hot chocolate da cookies ta gani a saman tray din, ta zauna saman carpet din dakin da breakfast din a gabanta, bayan Khaleesat ta gama sai da ya kira wayarta sannan dai ta karasa shirinta ta dau handbag dinta da tray din breakfast dinta ta sauka downstairs, yana zaune parlon ta samesa, kanta a kasa ta wuce kitchen ya bi ta da kallo, bayan ta wanke utensils din ta fito daga kitchen din ta tsaya bayan kujera tana wasa da fingers dinta a hankali tace “Na gama” Mikewa yayi ya dau makullin motarsa yace “Ohk mu je” Kofa ta nufa yana biye da ita a baya zata bude kofar taji a bude yake ta fita sannan shi ma ya fita, ta tafi garage ta jirasa ya kulle apartment din, as usual shi ya bude mata door din motar bayan ta shiga ya kulle, sannan ya zaga ya shiga driver seat ya tada motar ya fara Reverse, sai da suka dau hanya yace “We saw our dad off to the airport in the morning, na san kilan bacci kike lokacin da na fita” A hankali Khaleesat tace “Ya koma Nigeria kenan?” Jay yace “Yeah in sha Allah” Khaleesat tace “Toh Allah ya kai su lafiya” Jay yace “Ameen” duk wannan maganar da take taki yarda ta kallesa balle har su hada ido, ya ɗan yi murmushi kamar bazai ce komai ba sai kuma yayi kasa da murya yace “Ko sai mun yi auren zan cire maki wannan kunyan naki?” Wani sabon kunyan ne ya kara lullebeta a motar, ta kauda kanta kamar zata yi kuka tace “Ni dai bana so” Yana murmushi ya gyada kai yace “Za ki yi bayani” Gaba daya Khaleesat ta zama so uncomfortable a motar, Allah Allah take su isa makaranta ta sauka, shi dai lokaci lokaci yake kallonta yana kara admiring din irin kunyarta, can dai yayi murmushi yana gyada kai, suna isa makarantar bayan yayi parking Khaleesat ta bude motar, a hankali yace “Halysaah” Bata fita ba amma kuma bata kallesa ba tana dai jiran jin abinda zai ce, taji yace “To kalleni mana” Ta girgiza masa kai still looking outside, yayi kasa da murya yace “Please” Ta marairaice tace “Bazan iya ba” Yace “Please” Shiru tayi tana jin kamar ya hadata da wani gagarumin aiki kallonsa da yace tayi, da gasken gaske kunyarsa take ji yanxu, a hankali tace “Don Allah nayi latti fa” Yace “To me yasa baza ki kalleni ba” Cikin sanyin murya tace “Zan kalle ka anjima” Yace “A’a ni yanxu nake so” Shiru tayi tana ɗan murmushi tana kallon wajen motar, shi dai kallonta kawai yake, sai da tayi gathering buhun courage sannan ta dake ta ɗan juya a hankali ta kallesa suka hada ido, she could see nothing but her love in his eyes, sai yanxu ta kara fahimtar irin kallon da yake mata tun bayan dawowarsa daga Nigeria, kallon so ne tsantsarta yake mata, ya kashe mata ido daya yana murmushi yace “I love you” Ta rufe fuskarta da mayafinta da sauri, sai kuma ta bude motar cikin hanzari ta sauka ta kulle without turning back ta bar wajen ya bi ta da kallo, Jay was sitted in the car for almost 15 mins ya kasa tafiya, nan kuma duk tunanin inda Khaleesat zata zauna har ta gama Exams dinta yake don shi dai yasan a yanxu dai bazai iya zama under the same apartment with her ba, he just can’t, a sanda suka zauna gida daya he had no feeling toward her, ganinta yake just as his normal Housemate and nothing more, babu komai game da ita a ransa har ma sanda suka samu encounter din farko da Abdul a apartment din, he is just being kind and nice to her as a Housemate sannan kuma matsayinta na er uwarsa musulma from Nigeria, ko a sanda ya biya mata kudin jirgi taje duba Ummanta yayi hakan ne kawai saboda shi yasan girman mahaifiya don baya wasa da tasa, but outside of their apartment bayan abubuwa sun faru tsakaninta da Abdul ya maidata gidansu he gradually started developing feelings for her from nowhere, shi kansa bai san ta yaya ba amma yafi tunanin tausayinta da ya saka a rai ne ya ja hakan, he can’t even say how everything happened all of a sudden and he fell deeply for her tun period din da suke Exams dinsu, yanxu kuma bazai ce zai kai ta gidansu ta zauna ba don baya fatan wani family member dinsa su sake ganinta a gidan, Ya jinginar da kansa jikin kujeran motarsa ya lumshe idanuwansa cause he is so confuse, yasan yanxu kam ba ɗa bane and he won’t risk staying in the same apartment with just the both of them inside, yeah she need him to protect her from her Ex amma zuciyarsa bazai jure zama gida daya da ita ba don yasan lallai na ukun su Shaidan zai zama, and getting another apartment for her is not even an option, bude ido yayi jin wayarsa na vibrate yana dubawa yaga Ajay ne ke kiransa, picking call din yayi ya kai kunne kafin Ajay yace komai yace “Are you at home?” Ajay yace “Did you come across my debit card?” Jay yace “Tare muke amfani da card din… Are you home now cause i need to speak to you Ajay” Ajay dake sauraronsa yace “Bout what?” Jay ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace “I will be home now, kar ka fita ka jira ni” Yana fadin haka ya katse wayar ya tada motarsa ya kama hanyar gidansu……
Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa bello jidda
Ur evidence 07087865788
