Halysaah Page 73 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 73…Safiyyah na bude kofa ta washe baki tana kallon Khaleesat tace “Wallahi na zata wasa kike da kika ce kina hanya, shigo ciki mana” Khaleesat ta ɗan yi murmushi ta shiga parlon, Safiyyah ta ja ta zuwa Bedroom dinta tace “Ni kadai ce a gidan, ko ina suka tafi oho, ni sai nake ga kamar fa ciki Surayyah tayi, in ko haka ne zan kama kaina in dena biyeta a gidan nan kar taje ta haifi kyakkyawa kamar ni…” Khaleesat ta cire veil din jikinta tace “Sallah zan yi” Safiyyah tace “Kin ci abinci a can kuwa?” Khaleesat tace “Abinci kuma?” Safiyyah tace “Ko da yake waye zai baki gida duk maza, bari inje in dafa maki noodles kafin ki idar da sallahn” Mikewa Khaleesat tayi ta shiga bandaki, Safiyyah kuma ta fita zuwa kitchen, bayan Khaleesat ta idar da sallah Safiyyah ta shigo dakin da indomie da kwai da ta dafa mata ta ajiye, Khaleesat ta kalleta tace “Thank you” Safiyyah tace “Naga duk kinyi wani sanyi, ko dai koran ki Ajayn yayi?” Khaleesat tayi er dariya tace “Saura kadan dai ya kore ni” Safiyyah ta kankance ido tace “Fitinanne, to sai aka yi yaya? Did u meet Housemate in the House?” Khaleesat tace “Eh na gansa” Sai kuma ta jawo handbag dinta ta bude ta ciro kudin da Mai martaba ya bata, Safiyya tace “Wa ya baki wannan kuma?” Khaleesat tace “I think their uncle, ya zo ya same mu a gidan ne, shi ne ya bani da zan tafi” Safiyyah ta ɗan bude ido tace “Ko dai babansu?” Khaleesat tace “Babansu kuma? babansu fa Sarki ne, a’a ba babansu bane” Safiyyah ta amshi kudin tana kirgawa tace “Atoh, dama sai dai ko uncle din nasu, amma ina sarki yaga lokacin tsayawa dake har ya baki kudi, da sarki ne ai kya gansa da guards dinsa kuma yaushe ma zai tsaya maki magana, dogarawansa ma baza su bari ba, amma fa ke Hajiya ce kinsan nawa kudin nan in an canza a Naira?” Khaleesat tayi murmushi ta fara cin indomie din gabanta, Safiyyah tace “Wallahi kudade ne masu yawa, har karamin gida sai ya iya siya maki a maririn ku, yanxu ya ku ka yi da Ajay din bayan kin gaya masa abinda ya faru?” Khaleesat tace “Ai bamu gama magana ba Uncle din nasu ya zo, but after i left the house ya kirani yace kar in koma apartment dina, Housemate dina ma ya kirani….” Safiyyah ta hade rai tace “Ba nace kar ki sako Housemate a ciki ba? Shi fa Abdul namiji fitananne ne kawai zai iya dealing da shi, shi kuma Housemate dinki ba mutum bane me son hayaniya” Khaleesat tace “Kilan Ajay din ne ya gaya masa….” Safiyyah ta mike jin ana danna bell tace “Kilan sun dawo daga gantalin da suka je” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba Safiyyah ta mike ta fita daga dakin, ba a dau lokaci ba ta dawo tace “Ban ga kowa a bakin kofar ba kuma, ko dai kunne na ne yaji kamar an danna bell?” Khaleesat ta ajiye fork din hannunta tace “Kuma kin bude kofar?” Safiyyah tace “Haba dai sai kace ni ce ke, ta peephole na duba mana” A hankali Khaleesat tace “Ban san me yasa gabana ke ta faduwa ba Sophie, Abdul can be cunning kar ace ya fa biyo ki yaga gidan nan baki sani ba” Safiyyah tayi wani dariya tace “Saboda yana shan codeine sai ya biyo ni gidanmu, ai yasan ni ba ke bace hauka tuburan zan masa wallahi, to ya biyo ni akan me?” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, taji abincin ma ya fita ranta, Safiyyah tace “In zaki ci abincinki ki ci, idan su Ya Musty sun dawo zan sa ya duba surveillance camera din bakin kofar mu ga wani shege ne ya danna bell” After a while Khaleesat ta tura abincin gabanta don ya isheta ga baccin da take ji, Safiyyah dai chatting kawai take da wayarta, Khaleesat ta dau kudin da Safiyyah ta ajiye mata ta cire dala dubu biyu a ciki ta ajiye mata kusa da ita, Safiyyah ta hade rai tace “Meye wannan?” Khaleesat bata kalleta ba tace “Na baki” Safiyyah tace “Inyi me da shi? A’a bana so wallahi, ki ajiye kudin ki kawai zai maki wani amfanin” Khaleesat bata tanka ta ba ta mike tayi kwanciyarta gefen gado ta lumshe ido, cikin dubara Safiyyah ta jawo handbag dinta ta mayar mata da kudin ciki sannan ta ajiye. Wajen karfe shidda da rabi Safiyyah ta tashi Khaleesat dake bacci ta dalilin wayarta dake vibrate, Safiyyah tace “Ana kiran ki a waya” Khaleesat ta mike zaune ta jawo wayar ta duba taga Housemate ne ke kiranta, daga kiran tayi ta kai kunne, daga daya bangaren yace “I am outside Halysaah” A hankali Khaleesat tace “To” Veil dinta ta dauka Safiyyah ta rakata zata bude mata kofa, Khaleesat ta riko hannunta da sauri tace “Ki fara duba waje kafin ki bude mana” Safiyyah tace “Ke dai matsoraciya ce wallahi, shi Abdul din ai ba ɗan iska bane da zai zo ido na ganin ido, baki ga kamar barawo ya shige maki gida ba ranan da daddare” Bude kofar tayi Khaleesat ta makale a bayanta gabanta na faduwa, bayan ta hango motar Jay ta ɗan sauke ajiyar zuciya, Safiyyah na washe hakora tace “Yau dai Allah yayi za mu gaisa da shi” Khaleesat ma murmushin tayi suka fita zuwa gun motarsa a tare, yana ganin Safiyyah ya sauko daga motar, ya rungume hannu yana kallonta yace “Good evening kawar Housemate” Safiyyah ta tuntsire da dariya tace “Welcome Yaya Housemate, sai yau Allah yayi za mu hadu tunda ka dawo” Yace “Amma ai ina ce ma kawarki ta gaisheki” Safiyyah tace “Wallahi bata taɓa gaya min ba” Jay ya ɗan kalli Khaleesat dake kallonsa, ta sauke idonta da sauri bayan sun hada ido, murmushi yayi yace “Gaskiya ban taɓa cewa ta gaishe ki ba, it’s not her fault…” Safiyyah tayi dariya tace “Wai don ka kareta ko, ai nafi ka sanin wacece Housemate dinka” Jay na murmushi yace “Ya mutan gidan?” Safiyyah tace “Duk lafiya lau suke, yanxu take gaya min uncle dinku gave her much money a taya mu yi masa godiya plss, ranan kuma ta nuna min diamond ring da ka siya mata, Allah ya saka da alkhairi Yaya Housemate, Allah ya bar ku tare” Khaleesat ta bude baki tana kallon Safiyyah with shock, Jay dai yayi murmushi yace “Our father… not uncle Safiyyah” Daga Safiyyah har Khaleesat kallon Jay suka yi, Safiyyah ta bude ido sosai tace “Kana nufin Mai martaba da kansa? That’s surprising, Allah ya kara masa girma…..” Jay na murmushi yace “Ameen” Ita dai Khaleesat tayi shiru tana tunanin yanda yayi ta hira da ita a parlon kamar random person babu wanda zai yi tunanin sarki ne, Safiyyah tace “To ni zan koma ciki Housemate” Jay yace “Alright Safiyyah, thank you so much” Tana murmushi ta juya ta koma cikin gida, shi dai Jay kallon Khaleesat yake, sai kuma ya bude mata front seat, ba musu ta shiga motar ba tare da ta kallesa ba, ya zaga ya shiga driver seat yana kallonta yace “Kin ci abinci ne?” Kai ta gyada masa, jin bai sake cewa komai ba ta daga idanuwanta ta kallesa, zoben hannunta taga yana kallo baya ko kiftawa, tayi saurin boye hannun a bayanta kamar ta nutse don kunya, yayi murmushi yana kallonta a hankali yace “Wai yaushe kika fara jin kunyata Housemate? I am only admiring the ring, it look soo cute in your finger” Taki daga kai ta kallesa, ita kanta ta rasa gane wannan sabon kunyan nasa da take yi, ya jinginar da kansa da kujeran motar yana kallonta babu ko kiftawa, tunda taji yayi shiru tasan kallonta yake hakan yasa ko da wasa bata yarda ta dago kanta ba balle su hada ido, murya can kasa taji yace “Me yasa ni baki gaya min Ex dinki yaje wajenki a schl ba sai Ajay?” Shiru tayi jin tambayar da yayi mata, can ta dan kallesa, still speaking slowly yace “Why?” Tace “Ae ko an kira ka baka picking call dinka…” Yayi shiru yana kallonta kafin yace “Yaushe kika kira ban yi picking ba?” Ta langwabar da kai tace “Anytime i call, you don’t pick” Jay ya sauke idonsa kasa, after some seconds yayi kasa da murya yace “I promise i won’t do that again, i will prioritize ur call from henceforth yanda nake prioritizing na Mami da me martaba” Khaleesat ta daga kai suka hada ido, tayi saurin dauke idonta daga nasa, yace “Me yace maki da ya sameki a school din?” Khaleesat tace “Safiyyah ce ta kulasa suka yi exchanging words” calmly Jay yace “Do not worry Halysaah, i will bring an end to ur fright about ur Ex Husband very soon in sha Allah, i promise you this, zaki samu kwanciyar hankali fiye da yanda kike tsammani” Khaleesat ta kallesa, cikin sanyin murya tace “But i don’t want you to confront him pls, he can be cunning” Jay ya ɗan yi murmushi yace “I am not confronting him Halysaah, kawai dai zan yi abinda zai yi cutting duk wani Intention din da yasa ya dawo yake bibiyan ki, i will put a total stop to that, kuma babu yanda ya iya haka nan zai hakura ko ba don Allah ba….” Khaleesat tayi shiru tana kallonsa, After some seconds tace “Amma yanxu i will prefer inyi ma brother din Safiyyah magana to let me stay in their home har sanda zan gama exams, don bazan iya zama a apartment dina ni kadai ba kuma, i am very afraid” Jay yace “Kar kiyi inconveniencing dinsu Housemate, and I don’t want you to be a burden to them considering the high cost of livelihood in this state…. ki zauna a apartment dinki kawai, i will be there also, i will be there to protect you….” Khaleesat tace “Zaka dinga zuwa kamar sanda muke former apartment dina?” Yayi murmushi yana kallon kwayar idanuwanta yace “Sure, anything for you Halysaah” Sosai taji hankalinta ya kwanta, cikin sanyin murya tace “To Nagode” Yace “Lokacin sallah ya kusa, can we go home now” Tace “Let me get my handbag” Gyada mata kai yayi, ta bude motar ta sauka, ya bi ta da kallo har ta shiga apartment din, after some minutes sai ga ta ta fito daga gidan da handbag dinta da waya, ta shiga motar ta rufe tana kallonsa taga kallonta yake…. Khaleesat na zaune dakinta wajen karfe takwas da rabi na dare suna WhatsApp call da Aunty Farida, gaba daya jikinta a sanyaye yake ga faduwar da gabanta yake ta yi jin abinda Aunty Farida ke gaya mata, labarin biyota da Abdul yayi har sabon Apartment dinta da kuma cikin makaranta take ba Aunty Farida, a nan ne Aunty Farida ke sanar mata ai yaje Mariri ma yafi a kirga few weeks ago kawai gaya mata ne bata yi ba don bata son daga mata hankali, Cikin sanyin murya Khaleesat tace “To Aunty ya aka yi yasan ina America ne?” Aunty Farida tace “In kin tambayeni in tambayi wa Khaleesat? Kilan ko bincike yayi a unguwan aka gaya masa, kinsan babu abinda yan unguwan nan baza su yi ba akan kudi, dama kuma ga tsegumi ya masu yawa, in kuma ba a unguwan ya bincika ba kilan shi ma yaga hotonki da wannan mutumin da ya dora ki a Instagram” Khaleesat kamar zata yi kuka tace “Toh me yake so kuma a guna Aunty da yake bibiyana ne?” Aunty Farida tace “Mutumin da yana zuwa cewa yayi ya maida auren ku, Allah ya so Nenne ta zo ranan sai abinda ta manta ne bata gaya masa ba ta kusa tara masa yan unguwa, kuma tace ai kin gama iddansa tun wani shekara in ma yau ya farka bacci tun sanda ya sake ki to yaje ya duba calendar yaga yau shekara nawa da yayi sakin, Nenne ta sille sa tas, ni ai shi yasa hankalina bai wani tashi ba, da dai baki idar da iddansa bane shine babban tashin hankalinmu gaba daya, amma da baki da hakkinsa ai kinga Allah ya kada hankalinsa sai bayan da kika gama ya waiwayo ki, yana sake zuwa inda kike ki kira masa hukuman kasar kawai su ja maki layi da shi….” Khaleesat dai ta kasa cewa komai, Aunty Farida tace “Dama in kika ga ya hakura da bibiyanki ai sai in wani auren kika yi tunda babu tsoron Allah a ransa, ban taɓa ganin mara kunya ma irin sa ba, babu kunya babu tsoron Allah fa ya zo ya marairaice ma Babanki wai ya maida ke, ya zo gidan nan yafi sau goma wallahi, to Allah na tuba ko da ace baki gama iddansa ba da ba sai dai mu makasa a kotu ba akan ki koma gidansa, shi ɗan iska, danginsa matsiyata marasu mutunci” Khaleesat taji hawaye ya cika idonta tace “Toh Aunty ni tsoro nake kar ya sake cewa zai daukeni kema kinsan halinsa fa” Aunty Farida tace “A American zai dauke ki saboda ba shi da seti?” Khaleesat dai tayi shiru gabanta na faduwa don har yanzu bata mance yanda aka dauketa aka kai masa ita ba, tunanin hakan yasa hawaye ya fara zuba idonta, Aunty Farida tace “Yanxu dai ki kwantar da hankalin ki tunda kin ce Jarabawa za ku fara, su Junaid ma baza su bari ya cutar dake ba in sha Allahu, kiyi ta addu’a kina neman tsari daga sharrinsa, in sha Allahu Allah zai kare ki” Khaleesat ta gyada mata kai cikin sanyin murya tace “To Aunty” a haka suka yi sallama da Aunty Farida tana goge hawayen da yaki tsaya mata, kiran Safiyyah ne ya shigo wayarta tayi picking ta kai kunne, Safiyyah tace “Khaleesat kin san wa yayi ring din bell daxu kuwa?” Sosai gaban Khaleesat ya fadi tun kan Safiyyah ta gaya mata, Safiyyah tayi wani dariya har da kyakyatawa tace “Wallahi shi ne in gaya maki, Abdul ne ba wani ba, gashi nan an duba Camera na gansa, to da na bude kofar uwar me zai min ne? Wato ban taɓa ganin ɗan iska mara aikin yi kamar sa ba, ki ji har yayi locating inda nake saboda rashin aikin yi, to me zai min da Allah bai min ba?” Cikin rawan murya Khaleesat tace “Kin dai ga abinda nake gudu ko, wallahi da baki kulasa ba Safiyyah, ba kowa ake musayar yawu da ba” Safiyyah tace “Wallahi ba abinda ya isa yayi min da izinin Allah, shi kuma yaya Musty idan ya gama bambamin fadan da yake yana cewa ina dauko masa magana a kasar nan sai ya daukeni mu tafi mu kai ma Cops report, sai an gano Abdul duk inda yake ya fadi abinda ya zo yi a apartment dinmu wallahi…” Tana kai wa nan ta katse wayarta, knocking din kofar dakin Khaleesat taji ana yi, ta juya ta kalli kofar har sannan zuciyarta na bugawa ta mike ta dau hijab dinta ta saka ta tafi ta bude kofar, sauke idonta tayi bayan sun hada ido, yana kallonta da damuwa ganin hawaye idonta yace “Are you crying Halysaah? Me ya faru?” Kamar jira take ta jingina da kofar dakin ta fashe masa da kuka dama ta kwana biyu bata yi ba, nan da nan ta rikitasa a wajen…..*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah**Ur evidence 07087865788*
