Mejo Najeeb Page 45 By Autar Alheri
“Ahankali isseta ta ɗago takalleshi batareda tace komai ba hawayen idonta na ƙara zubowa…mejo kuwa izuwa yanzu jiyakeyi kamar zuciyarshi ta fashe domin kamar ana ɗiga Mishi darma hakan yakejin kukan isseta acikin ranshi. “Mlm Musa kuwa hawaye yashare afakaice “Maryama kiyafemun na cutarda rayuwarki kiyafemun dan girman Allah naɗauki huɗubar mata data sheɗan na hukuntaki akan laifinda baki aikataba nashiga tashin hankali marar misaltuwa nashiga ruɗani da fargaba Maryama nakasance araye amma nida matacce bawani banbanci sanada tashin hankali danake ciki kiyafemun Maryama, yakasance yana sakin kuka me ban tausayi…itama Isseta kuka kawai takeyi amma batace komaiba. “Ikon Allah mlm Musa mufa kasakamu acikin duhu abinda muka kiraka ayi daban abinda kukeyi yanzu kaida iyalinka daban kuwaye mana kai wai mike faruwa ne? Ko raɗe raɗin da’skeyi agari akan cewa Maryama bibiyar maza takeyi har acikin gidanka take kawosu shiyasa kakoreta gaskiya ne? Megari yatambaya cikeda tuhuma. Wani mugun kallo mejo ya dokawa megari badan darajar furfurarshiba daseya ɗan ɗana mishi uƙuba akan aibata mishi mata dayayi ayanzu.. Kafin mlm Musa yayi magana mamansu ya balah tace “tabbas hakane ranka yadaɗe Maryama tagama lalacewa agari tana neman lalata sauran yaran gidanne shiyasa yakoreta. “Azabure mejo yamiƙe cikin tafasar zuciya yace “wacce kewannan maganar ? Kowacece tabayyana kanta narantse da Ismul a’azamu sekinyi danasani zuwanki duniya kika ƙara aibatamin mata, yaƙarasa zancen yana zaro bindigar dake gefen wandon general Faruk. “Innalillahi wa’innailaihi raji’un Dan girman Allah yaro kayi haƙuri duk abin bekaiga hakaba tayi kuskure bazata ƙaraba. “Cikin sauri general Aliyu yamiƙe tare da riƙo hannunshi yace “please mejo kayi haƙuri mana kazauna idan angama magana semu ɗauki mataki akai. “nayi haƙuri aina Aliyu bakajin yadda suke aibatamin mata suwayesu dazasu wulaƙanta min rayuwata? Maryama rayuwatace Aliyu ba iya mataba ita ɗin jinin jikinace yadda bazeyu a aibata ummi mufeedah agabanaba wlh ba mahalukin daze aibatamin mata ko abayana nabarshi balle agabana, sekuma yajuya yana kallon mutanen dake wurin cikin kakkausar murya me tabbarda gaskiya da gaskiyar shi yace “Maryam ba lallatacciya bace cikakkiyar mace ce mekima da daraja kuma a cikakkiyar mace nasame abata, sekuma yajuya gunda isseta take zaune tana kuka riƙota yayi yamiƙarda ita atsaye kana yariƙo hannunta tako ɗaya tayi ana biyu tasaki kuka, murmushi yayi meɗaukeda ma’anoni kana tace “ina me faɗar mummunan kallima akanta to idan keɗin cikakkiyar macece kamar ita kiduba daga yanayin tafiyarta zaki bawa kanki amsa, kuma wlh daga….Riƙo hannunshi da Abba yayine yasaka shi dakatawa daga abinda yayi niyyar faɗa, Abba bece Mishi komai ba wuri kawai yanunamai ya zauna. Ahankali ummi dake kuka itada mufeedah suka zaunarda Isseta….Kowa yayi tsit awurin, kowada abinda yake saƙawa azuciarshi, mamansu ya balah kuwa da iyya hassi tuni sukasha jinin jikinsu se rarraba ido sukeyi. gyaran murya megari yayi kana yace “dan Allah kowa yayi haƙuri akan wannan abun dayafaru Nima ina me matuƙar baka haƙuri ɗana domin nine nafara faɗar wannan zancen ayanzu sabida haka dan Allah kayafemun. Sekuma zance na gaba mlm Musa wannan abinda yafaru ya tabbatar muna dacewar akwai abinda ke faruwa acikin gidanka munason sanin minene domin awarware komai cikin sauƙi. “Nice zangayama abinda kefaruwa ranka yadaɗe, cewar mama bintu. “to muna sairarenki. Gyara zama mama bintu tayi tafara basu labarin isseta tun lokacinda Hajiya Hannah takawo mata ita har izuwa lokacinda mlm Musa yakoreta har kawo zuwansu Hajiya Hannah garin karɓar ƴarta,,,Seda takai ƙarshen zancenta tarusheda matsanancin kuka….Kowa awurin, salati kawai yakeyi yayinda isseta Takoma tamkar mutun mutumi, tunani takeyi aranta dama ba mama bintu ce tahaifetaba to wacece mahaifiyar Tata? Mutanen gari kuwa kowa yasha jinin jikinshi kasancewar sunji duk tashin hankalin da jami’an tsaro keyi a garin sabida neman isseta ne. General Faruk kuwa seyanzu yake ƙare mata kallo tabbas tayi matuƙar kamada Hajiya Hannah sedai yanayin shekarune kawai ze banbatasu, kenan dagaske mejo yaganeta awannan picture ɗin shiyasa yace matarshi ce. General Aliyu da mejo kuwa kowannensu yayi shiru bazaka iya tantance abinda suke tunaniba.”Ikon Allah kenan duk rayuwarda Maryama tayi agarinnan ashe ba ƴar mlm Musa bace? Cewar Sarkin fada. Ajiyar zuciya megari yasauke kana yace tab ɗijam lallai wannan al’amarin akwai ɗaura kai acikinshi, to yanzu yaza’ayi kenan mlm Musa? Dama su Alhaji Abubakar sunzone akan zancen da’akayi dasu nacewar idan ankai Mishi hawwa’u yasauwaƙawa Maryama kuma yanzu ga wannan al’amari daya fullo minene sharawarka, akwai? Kafin mlm Musa yayi magana Sarkin fada yace “to ai ranka yadaɗe inaga abin yazo da sauƙi domin kuwa yanzu yanada damar zama dasu duka ba doli seya saki ɗaya ba. “Doline yasaki ɗaya Sarkin fada, suka tsinkayo Muryar mlm Musa, kana yaci gaba da faɗar”domin kuwa iyayen Maryama basu aminta da wannan aurenba. Dumm gaban damm hakan gaban mejo yafaɗi hakama Isseta wanda suka ɗago atare suna kallon mlm Musa, ɗaga mata kai mama bintu tayi alamar tabbarwa kana tace “kojiya danayi waya da mamanki seda ta jaddadamin cewar megirma shugaban kasar Niger zezo dakanshi neman ki dakuma neman mijin da’aka aurawa ke domin yasawwa ƙa Miki sabida kinada mijinki tun kina cikin zanen goyonki sedai kuyi haƙuri yazaunada hawwa’u kawai…azafafe majo yace “wlh ba macenda zanzauna da ita kuma bazan daki matata ba hakama bazan zauna da mace biyu ba Ni Maryam ce kawai matata ita nasani kuma ita nakeso, wadda kuke magana akai nibanida aure tsakanina da ita domin tunranarda Abba yasarnamun zancen aurenta tun a ranar nayi mata saki ukku…”whatt?? Mikake nufi najeeb?? Cewar Abba cikin mugun. Mamakin ɗan nashi.”Please abi komai asannu Alhaji cewar Alhaji Abubakar…ajiyar zuciya kawai Abba yasauke aranshi yake faɗar wato haryanzu najeeb na nan da kafiyarshi da taurin zuciya…”ranka yadaɗe mungode sosai da wannan karanci damuka samu awurinku kuma muna neman afuwarku abisa hukuncin da yaro yayanke batareda wani tunanibaKuma in sha Allah zamu nemi shi megirma shugaban kasar Niger domin zancen yazo ƙarshe in sha Allah. Alhaji Abubakar yafaɗa cikin Dattako…ajiyar zuciya megari yasauke kana yace “bakomai Alhaji ai awurinmu daga Maryama har hawwa’u duk ɗaya ne sedai yanzu da Maryama ɗin tafi karfinmu sabida hakan wlh ba komai Allah dai yasa hakan shine mafi alkairi…Ameen y Allah. “To yanzu mlm Musa ya za’ayi muga shi mahaifin nata tunda naji me ɗakinka tace yana garinnan? “Nima bansaniba domin banmasan yana garinba itace zaku tambaya bintu ina zasuga Alhaji? “Ajiyar zuciya mama bintu tasauke kana tace yana gidan gwamna. “Shikenan Bara mujecan ɗin. Mejo najeeb kunema muna izinin zuwa gidan gwamna tunda kune manyan jami’an ƙasar. Alhaji Abubakar yafaɗa cikin barkwanci. Wani irin kuka Anty hawwa tasaka alokacinda taga tabbas dai tarasa mejo domin tunda taji kallimar saki hankalinta yatashi sedai jin bayanin Mahaifin isseta be yadda da aurenba ne yasa hankalinta ya kwanta sabida duhun jahilci domin inba jahilci ba tayaya za’ayi saki ukku kayi wani tunani akan auren. To yanzu dataji labari nason canjawane yasa Takoma birkicewa, juwaira kuwa tuni bata wurin domin duk wannan abun da’akayi batanan….hakan su Abba sukayiwa su megari sallama zasu tafi da mlm Musa da mama bintu dole za’aje. Mejo dakanshi yaje yariƙo hannun isseta suka fara takawa ahankali se share ƙwallar idonta takeyi tana kallon mijin nata, aranta tana jinjina girman soyayyar dayake mata wadda bata taɓa tunanin takai hakaba, yakasa ɓoyeta agaban kowa yake nuna tsananin son da yake mata itakuwa tayaya zata bari arabatada wannan mutun? Tanacikin wannan tunanin taji Muryar halima daƙarfi tana kiranta. Cikin sauri tajuya aiko suka rungume juna suna kuka kuma suna murmushi alokaci ɗaya, “my Beasty nayi kewarku ina inna da ammina? Ɗan harararta halima tayi kana tace sunyi fishi Beasty aida tafiya zakiyi baki nemesuba musamman Ammi kullun setayi zancenki yauma tunda sassafe tacewa inna tanaji ajikinta yau zataga ƴarta ashekema tafiya zakiyi abinki inda yaya shamsu begayamin kinzoba. “Ayya ba haka bane Beasty Kinga muna tare da mutane shiyasa amma zanzo ai. “Sune zasu hana kiganta aikuwa Sena gaya mata, sekuma ta kalli hannun mejo dake riƙeda isseta kallonshi tayi cikin murmushi tace “isseta wannan shine angon namu? Murmushi ƙarfin hali itama Isseta tayi tare da kallon mejo sekuma Takoma kallon halima tace “shine Aminiya yayi ko bemikiba? Ɗan harararta mejo yayi tare da waro blue eyes ɗinshi, dudda yana cikin damuwa amma barkwancinsu ya birgeshi. Balle ma general Aliyu da tunda halima tazo wurin yakafeta da ido ko kiftawa babu domin sosai tayi Bala’in birgeshi. Dariya halima tayi tana rufe bakinta da tafukan hannunta tace “wlh yayi 💯 aminiyata Allah yabada zama lafiya yabamu baby’s kyawawa kamarshi domin yafiki kyau. Ido isseta tawaro sekuma takwaɓe fuska, shikuwa mejo wani kayataccen murmushi yasaki yana ɗage mata gira ɗaya, general Aliyu ma murmushi yayi shida general Faruk. “Dan Allah muje Ammi taganki kaitsaye seki wuce abinki kinji isseta, halima tafaɗa cikin rarrashi….cikin sauri general Aliyu yace “okay zamuje taganta semu wuce hakan yayi miki beautiful baby. Dukkansu da kallo sukabi general Aliyu hadda shi gogan,,,shiko yi musu yayi kamar besan dasuba yajuya gurin da su Abba suke yace “Abba please zamushiga nan gidan Maryam taga amminta wai semu wuce. Damm gaban Abba yafaɗi amma seya dake yace wacce Ammi kuma? “Mamana Abba, cewar isseta. Kafin Abba yayi magana mama bintu tace “wace mama kuma Maryama?? “Mama Ammi mamatace inasonta sosai nasanta tun Batasan wake kantaba please kuzo muje duka kuganta daganan Sena gaya muku ko wacece ita, inaso ma natafi da ita idan zamu koma yah najeeb. “To amma Kinga sauri sukeyi Maryama karki tsaidasu mana..”a’a bakomai taje taganta muma zamuzo duka muje idan taganta semu tafi aibakomai Abba yafaɗa yana fitowa daga motar kuma yanajin yadda bugun ƙirjinshi ke lunkuwa.Ahakan suka nufi gidansu halima cikeda farin ciki isseta mejo dake riƙeda ita da kuma halima suka shiga gidan cikin ɗauki isseta tace “Amminaa gani nazo. Harara halima tadoka mata tareda cewa bamazaki bari nayi mata albishir ba…kafin isseta tayi magana sega Ammi tafito cikin sauri innar halima nabiyeda ita tana dariya, sedai ganin mejo riƙeda hannun isseta seda gabanta yayi mummunan faɗuwa, cikin dakiya takira Allah kafin taƙaraso da murnarta tayi ƙiba sosai haskenta yaƙara fita tayi kyau sosai abunta. Oyoyo Takwarata lale marhabin da Maryama ƴar Maryama kuma takwarar Maryama, taƙarasa tana rungume isseta, itama rungumeta tayi cikin farin ciki tace “oyoyo Ammina nasameku lafiya? “Lpy qalau Maryama. “Ohh ni suwaiba wato Maryama Kinga mamarki ba’akotatamu ko? Dariya tayi har fararen haƙoranta suka bayyana “ayya innarmu yi haƙuri ina ɗaukin ganin Ammi ne, tafaɗa tana rungumar innar halima. Bayan hakan mejo yagaidasu tare da su general Aliyu suka amsa cikin sakin fuska, kallonshi Ammi tayi sosai kana tace “amma kai ɗan Niger ne ko? “Ɗan murmushi yayi abinda kemishi wahala yace a’a ɗan Nigeria neni, domin hakan kawai yaji matar takwanta Mishi arai. “Ikon Allah amma wlh da’a Niger kakai “abinda ze hana nace kai ɗin ɗan yayana ne, kamar Maryama itama alokacinda nafara ganinta tabbas da TANTI nada ƴamace ba’abunda ze hana nace ƴarta ce seyazam batada ƴa mace kamace kawai. “Murmushi dukkansu sukayi isseta tabuɗe baki zatayi magana kenan su Abba suka shigo abisa jagorancin mlm Musa shida yasan mutanen gidan, Alhaji Abubakar ne agaba bayan mlm Musa se Abba da mama bintu…. sallama sukayi innar halima da Ammi suka amsa..wani irin faɗuwa gaban abba yayi jin wannan murya tadoki dodon kunnenshi domin koshekara ɗari za’ayi baze mantataba sedai yaɗauka gizone Muryar kemishi kamar yadda tasaba hakan yasa yaɗago kanshi danufin ganin me Muryar, cikin wani irin tashin hankali da ruɗu da fargaba yawaro duka manyan idanuwanshi tare da nunata yatsa baki narawa yace “Maryama…!




