Uncategorized

Abin mamaki baya ƙare wa a duniya: Wata Mata Ta Auri Maza 7 A Rana guda

 Wata dattijuwa mai suna Ling ta girgiza jama’a inda ta amarce da angwaye har 7 a rana ɗaya. Dattijiwar data kasance likitar gargajiya ta bayyana cewa Ubangijinta shine ya bata wannan umarnin, ta ci gaba da cewa ko a yanzu Ubangijin nata ya sake bata umarni to zata ci gaba da auren mazajen har yanda hali yayi. 

Karanta Wasu Maƙalun

Shugabannin Afirka Wadanda Suka Fi Daukar Albashi, Shugaba Buhari Yana Cikinsu.

Dattijuwa Ling ta ci gaba da cewa Ubangijinta ya umarce ta da ta haifi ƴaƴa da yawa wanda hakan yasa nake auren mazaje kuma yanzu haka ina da ƴaƴa shida rayayyu a cewar ta.

Yan jarida sun tambayi Dattijuwar kan cewa kinsan maza da yauda, shin ya zaki ji idan ɗaya daga cikin mazajenki ya yaudare ki?

Sai ta kada baki ta ce, ai duk mazajen da take aura ba wai haka kawai take aurensu ba, sai Ubangijinta ya nuna mata wanda yake son ta aura sannan zata je kai tsaye ta sanar da shi muradinta, kuma nan take wannan mutumin zai amince ba tare da wata matsala ko jayayya ba.

Dattijuwar ta ci gaba da cewa dukkan mazajen nata 7 ta gina masu gidan da zasu zauna, kawai dai bata son mijin nata ya ci amanar ta, domin muddin ya ci amanarta to duk abinda ya faru da shi ya kuka da kansa.

Wasu daga cikin mutane suna ganin wannan auren da Ling ta yi a matsayin auren mutu’a wanda mace take auri maza biyu ko fiye a lokaci guda.  

Daga ƙarshe muna yi maku godiya da ziyartar wannan shafi namu na Aihausanovels  da fatan kuna nishaɗantuwa da shirye shiryen da muke kawo maku.

Back to top button