Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 29 Book 2 Complete Hausa Novel

Tsayawa Mummy tayi tana kallonsa, yace “ki dauka kiduba mana, kika tsaya kina kallona, ganin da yayi Mummy bata da niyyar taba jaridar yasashi yasa hannu ya bude ya ajiye mata a gabanta, 

Hoton Kabir ne da Jeje da wasu mutane da bindigogi agabansu, tittle din ta karanta, da hanzari jikinta na rawa ta dau jaridar tafara dubawa, an yankewa Kabir zaman gidan yari na shekaru goma sha biyar sakamakon saida makamai da fataucin miyagun kwayoyi, sannan an yanke masa shekaru Ashirin a prison saboda Yunkurin kisan kai, da kuma shekaru goma sha hudu sakamakon lalata da kanan yara mata. 

Sekuma su Jeje da’aka yankewa hukuncin shekaru ashirin2 a gidan prison. 

Daddy ne yasa hannu ya karbi Jaridar shima ya duba, Jalal yace

“Mummy Allah yakawo karshen mutumin da dasa hannunsa a lalacewata, shiyabada kwangilar koyamin shaye2 saboda ya huce takaicin abunda kikayi masa akaina, kalli keda laifi nida karbar hukunci” 

Daddy yace 

“Jalal kai waya gayamaka shiya bada kwangilar hakan?” 

“ba gayamin akai ba, Jeje abokina yaronsa ne, idan nagaya muku wanda yayi sanadiyar kama Jeje da uban gidansa har nasan wannan lamarin kila karyatani zakuyi, sanin hakan bashida Amfani, Mummy yakamata ki zubar da makamanki kikoma ga Allah tun kafin kema ya dankeki, Kabir makiyinane na boye bansan dashiba sedaga baya, nasan makiyana na fili, suma ina nan nasasu a Addu’a very soon Allah ze yimin maganinsu”

Yasa hannu ya dauke Jaridar ya fice. 

Daddy yaja ajiyar zuciya yace “Khadija lokuta da dama bana ganin laifin yaron nan, ba wai ina goya nasa bayane ba, amma kinmasa laifuka masu tarin yawa, ba kya duba haka se wanda yakemiki, anyway Ansamosa aikinyi na gwamnati wanda muke saka ran ze dauke masa hankali daga kan shaye2” 

Kallon Daddy tayi tace “bangane ansamosa aiki ba, wani irin Aiki? Me Jalal yanema yarasa da zeyi wani aiki, ina kamfaninsa na sarrafa robobi meyasa bazaka bashi abunsa ya rike ba?” 

“ba an samomasa aiki ne dan wani abuba, ansamo masa ne dan hakan zesa yayi kokarin dena shaye2, kuma bazan iya cewa wanda yasamo masa din A’a ba, kuma nima naga dacewar hakan” 

“wai waye ya samo masa?” ta tambaya cikin kosawa

“General Abdurasheed ne” 

Dan zare ido tayi tace “Ina yasanshi daze bashi aiki, sannan wani irin aikine haka? Dan dana baze aikin soja ba” 

“Eh ya gayamin Jalila ce tace tanason yasama masa aiki a NDLEA, hakan ze temaka masa wajen dena shaye2” 

Hade rai tayi sosai tace

“Baze yuwu ba, baza’a mayar minda ďa bawa ba, 

Akan mene? Meye hadinta dashi dazata sa a samo masa aiki, banda cin mutunci tasan yana shaye2 shine zatace yayi aiki a hukumar yaki da shaye2 salon tasaka akama shi, kokuma taji dadin juya shi yadda takeso ko? Dama yanzu na fuskanci maganarta yakeji akanta ba irin wulakancin daba yawa Ilham, to bata isaba da raina babu yarinyar dazata juyamin ďa, baze yuwu in haifi ďa wata ta juyamin shiba”

Mikewa daddy yayi tareda yin murmushi yace “Eyya kin makara khadija, duk abunda kayi se an maka, ki gode Allah da yarinyar ba cutar dashi take ba, dan ta damu da halin dayake cikine hartasa a sama masa aiki, nayi farinciki da hakan, kuma batun kice baza’a juya miki ďa ba daga baya kenan aikin gama ya gama” be jira yaji martanin da zatayi ba ya shige bedroom ya kulle kofarsa. 

Jawwad ko sallama basuyi da Jalal ba suka tafi bauchi shida Abba. 

Maama kam a sukwane take tambayar Jalila “me Abba ke nufi, me kika gaya masa haka? Sannan wa zeje nemawa Aure? 

“niba abunda nagaya masa, yaushe rabon da in zauna dashi balle ince masa wani abu, nibansan waze nemawa aure ba be gayamin ba” 

A fusace Maama takoma dakinta tana tunanin yazata bullowa lamuran. 

Jalila takoma daki suka dinga murna itada Nana, Jalila tace “Nana ban taba zaton Abba ze yadda da abunda nagaya masa ba” 

Dan bata rai Nana tayi tace “Jalila nayi mamakin abunda ya fusata Abba haka, har yayi fushi yake ikrarin abar masa gida, nayi mamaki sosai be taba hakaba fa”

“to yanayi na rayuwane Nana, tunda kikaga haka akwai abunda ya bata masa raine, sannan akwai dalilin dayasa yayi haka”

Nana ta dan numfasa tace “Jalila nifa damuwata naji Abba yana batun akawo kudin Aurena, Allah yasa ba dana Yaya Jawwad za’a hadamin ba, nan da wata hudu da ‘yan kaifa kenan”

Nana takarasa maganar kaman zatayi kuka

Jalila tace “to meye aciki? Keda rabin rankine fa Mahmud zaku kasance inuwa daya”

“To Jalila karatun fa? Kinsan Mahmud a kasar waje yake nasa karatun tayaya abun ze yuwu?”

“ze yuwu mana, kicigaba da naki karatun a can riba biyu, Allah sarki Rayuwa hajiya Nana za’a zama matan Aure, bari in lissafa yaushe zaki haihu”

Hade rai Nana tayi “Ke Jalila komai sekin sako wasa a cikine? Inamiki maganar serious kinamin wasa, ke yanzu akace za’ayi aurenki nan da watanni hudu kin shiryane? Ni yanzu ma meyasa Abba bece a hada dake ba”

Dariya Jalila tayi tace “gidan Ahmad yana bauchi, shi yana aiki a maiduguri, ni ina karatu a kano tayaya kike zaton inyi Aure yanzu, se nagama tukuna”

Wayar Jalila tafara ringing, ta kalli Nana tace “Excuse me, let me pick the call”

Nana ta daga mata kai, Jalila ta amsa wayar tareda yin sallama

Amsamata yayi sannan ya dora da “Babyna kwana biyu kin gujeni you are not picking my calls, ina fatan ba laifi nayi miki ba?”

Cikin siriyar muryarta na shagwaba tace

“Ohh no ni bakamin laifi ba, bana dan jin dadine kawai, amma yanzu Alhamdilillah naji sauki”

“Ya salam amma baki gayamin ba, yau zan shigo kano dama shiyasa na kiraki, in kin amince zanzo in ganki”

“Babu damuwa my one, ina fatan in ganka nima am missing you”

“Like serious, karkisa inyi Ihu attention din mutane ya dawo kaina”

Murmushi tayi tace “ba sekayi ihuba, aini yakamata inyi, kwana nawa zakayi a kano?”

“zanyi sati daya Insha Allah, zanyi wani assignment ne”

“Shikenan Allah yakawo ka lafiya”

“Ameen my queen, bazaki tambayi Antynki ba?”

Dan yamutsa fuska Jalila tayi tace “Ainasan tana lafiya tunda najika haka”

Murmushi yayi yace “Queen da alama kinada kishi sosai, anyway sena shigo, idan nazo da wuri zaki ganni yau, in ban shigo da wuri ba se Allah ya kaimu gobe”

“to shikenan Allah ya kaimu, take a good care of your self”

“Ok Baby i will Insha Allah” ta katse wayar, Nana ta zuba mata ido tana kallonta, Jalila tace “Madam lafiya kuwa?”

“Lafiya mana, nina kasa gane inda kika dosane, gane lamarinki se Allah mutum baya taba ganeki, gaba daya rayuwarki zigza ce”

Sosai Nana tabawa Jalila dariya tace “rayuwartawa ce zigza, lallai ma Nana bakida dama, Rayuwata normal ce kaman ta kowa”

“A’a ban yadda ba, Allah yasa ayi miki aure kafin ayiwa Yaya Jawwad”

“Ba Ameen ba, back to sender muguwa kawai”

“eh amma ni kikayimin fata saboda son kai”

Wayar Jalila ce takuma daukar ruri, ta kai hannu ta dauka tana dubawa taga Hanan ce dan haka ta kashe wayarta. 

Tunda suka fara tafiya Abba beyiwa Jawwad wani gamshashen bayani akan wannan tafiyar ta bazata ba, yanason yayiwa Abba magana amma yakasa duk sunyi shiri Jawwad na driving, 

“Dama Aliyu akwai wadda kakeso kaki ka gayamin kabari ake kokarin auramaka wannan yarinyar?” 

Tambayar tazowa Jawwad a bazata, kuma idan yaji Abba ya ambaci sunansa na gaskiya kai tsaye haka, alama ce ta  he is so much serious. 

Jawwad ya dan sosa keya yayi shiru 

“yaka sosa kai kayi shiru? Kamin bayani mana” 

Cikin kame2 Jawwad yace”Amm.. Dama Abba, ai…” 

Abba yacce ” Jawwad da farko sister dinka Jalila tagayamin inyi bincike akan yarinyar nan Naja, tacigaba da gayamin hakan, sannan taki gayamin komai game da Naja, sedai cewa inyi bincike, tacigaba da nunamin cewa kunyarka da kawaicinka baze bari ka nuna abunda ke ranka ba, na dauki maganarta serious nafara kokarin bincike, ina kan binciken ne, Mahaifin Hanan ya kirani yamin magana akan in dai dagaske kana son ‘yarsa yabaka dama ka fito, wanda ni bansan da zancen ba, nayi kokarin in zauna da kai muyi maganar kafin ta kai ga haka Jalal yazo ya sameni har gurin aiki yamin bayani akan alakarka da’ yar gidan general Abdurrasheed, sannan ya daukeni ya kaini inda aka gayamin komai akan Naja, bantaba tunanin Mamanka zata zaba maka mace irin wannan mara kamun kai a matsayin mata ba, Jawwad meyasa baka gayamin abunda ke ranka ba, kabari nakusa gangancin saka rayuwar ka a hatsari? “

“Abba nasam bazaka zabamin abunda ze cutar dani bane, banason bijirewa umarninka dana Maama, shiyasa na amince”

“Nasan da wannan Jawwad, amma dukda haka a matsayin mu na iyaye yanada kyau mudinga baku zabi, ba wai bin son zuciyarmu da tirsasamuku akan abunda bakwa ra’ayiba, yana da kyau kadinga faďan ra’ayinka ba laifi bane naji dadin kokarin yimana biyayya dakayi, Allah yayi maka Albarka yakara haďamin kanku, Allah ya shirya mana ABDUL JALAL dukda kasancewar halinsa amma yadamu da lamuranka sosai, yadda yazo ya sameni kaman zeyi kuka, Alhamdilillah nayi mamaki naga abubuwan sa sun fara raguwa, yafara dawowa hanya, ya rage rashin ji”

“hakane ya rage sosai makuwa, abokiyar fadansa keta kokarin sashi a hanya ai” 

“Wa kenan?” Abba ya tambaya

“Jalila mana, tanata kokari akansa, kuma naga inga masa nasiha koba duka ba yana ďan dauka” 

Abba yace “masha Allah, at least kaga an samu improvement, itama General Abdurrashed yamin magana, yace akwai abokin ďansa dayake sonta, wai Ahmad sunansa kowaye?, yabiyo ta hannunsa a nema masa Aurenta, amma nace na bashi wuka da nama shima babanta ne, duk abunda yaga dace yayi” 

Jawwad yai murmushi yace “hakane Abba, lokacin da mukaje kaduna yamin zancen nima, yace shima mutumin sojane yana da kirki sosai” 

“Hakane, Allah ya tabbatar mana da alkhairi yamuku zabi da abokan zama nagari” Jawwad a zuciyarsa yace Ameen. 

Hanan taita kiran wayar Jalila amma Jalila taki dagawa, saboda bataji dadin abunda Hanan tayi mata ba, sako Hanan ta turimata kamar haka

    “Assalamu Alaikum, Am very sorry my twiny, nasan na miki laifi kiyi hakuri dan Allah, Yaya Jawwad yazo kano shida Jalal, yamin bayanin komai abunda ke faruwa, kiyi hakuri so dakuma kishinsane yasa namiki haka, sannan naji Yaya Abdallah yana maganar Ansamawa Jalal aiki za’a gama interview ranar laraba amma har yanzu bejeba, you have to take action”

Jalila nagama karantawa ta kira Hanan, seda Jalila ta kira sau biyu sannan Hanan ta dauka tace

“‘yar rainin hankali inata kiranki kinki ďagawa, amma da kikaji batun ABDUL JALAL harkin kirani” 

Jalila ta hade rai kaman Hanan na ganinta tace “ke banason wulakanci, ai banji dadin abunda kikayimim ba sam wallahi” 

“Nasani amma ai nace kiyi hakuri, you won’t understand how far my loves go on your brother, inasonshi ina kishinsa shiyasa na shiga damuwa, inata addu’a dai amma ina cikin damuwa Queen” 

Tausayin Hanan yakama Jalila tace “ki kwantar da hankalinki kinji my twiny, komai ze wuce kece zaki zama matar Yaya, ina nan ina tayaku da Addu’a” 

“Masha Allah, Allah yabiya ki da mafificin Alkhairi Jalila, bazan iya biyan kaunar da kike nunamin ba” 

“bakomai Sister na, nace are you serious Jalal beje interview din nan ba?” 

“Wallahi dagaske nake miki, hala aikinma kekisa aka samo masa?” 

“to meye naki aciki nason kisani, nice nagayawa Daddy ya samo masa, kuma be isa ya watsamin kasa a ido ba zan sameshi, seyaje interview din nan” 

Dariya Hanan tayi tace “wai zaki sameshi irin Mum din nan tasa, kai lamarinku din nan yana birgeni wallahi, kowa da guntun taurin kansa dan Allah duk yadda kukayi ki gayamin dan wallahi…. 

Katse wayarta Jalila tayi jin Hanan zata fara mata bare2. 

Ilham shiryawa tayi takanas ta tafi gidansu, domin taji abunda yakamata suyi, dan ita ta riga ta karaya da lamarin nan bata tunanin akwai nasara dan kullum Jalal kara bauďewa yake, babu alamar ze sakko. 

Tayi sa’a ummannata tana gida, suka kule a daki kaman yadda suka saba in Ilham ďin tazo. 

“Umma nifa najiki shiru ya’ake cikine? Na ďora mata sata amma Jalal bakiga rashin mutuncin dayayi min ba, wallahi son yarinyar nan yake, kincemin zakije Nijar gurin wani malamin amma shiru kullum abubuwan kara tabarbarewa sukeyi” 

Umma tace “ke nayi maganar zuwa nijar, munyi waya da mutumin na masa bayanin komai, amma budar bakinsa wai yayi bincike akan yarinyar indai inason a yimin aiki akanta zan bashi dubu ďari biyar, nikuma ina naganta? Banida ita bani da wata kadara da zan sayar in bashi wannan uban kuďin, dan haka nakoma gurin wanda muke zuwa tun farko, shikuma yacemin baze iya aiki akanta ba sedai a kara watsa rayuwar Jalal”

“to Umma batun Auren namu fa?” 

“shima za’ayi ne amma yace muďan kara hakuri” 

“umma kenan, mu kara hakuri fa kikace? By mistake idan Asirin ya karye gaba ďaya kuma yaya zamuyi?” 

“bazeyiba, malamin yabani wannan tabbacin ki kwantar da hankalinki burinmu seya cika, sena wulakanta shi shida uwarsa hada uban nasa, bana yafiya ga wanda yamin laifi” 

“to shikenan Umma, Allah yasa, ni bari in tafi, zan ďan tsaya inyi siyayya”. 

Dogon wandone a jikin Jalila da riga, dan haka ta ďakko katon hijjabinta me hannu tasaka ta fito part ďin Jawwad taje tana tsammanin ganin Jalal a can amma baya nan, rabonta da shiga gidansu Jalal kuwa harta manta, direct ta nufi gidansu Jalal, amma tarasa ina zatayi tasan dai be dace ta tafi part dinsa nemansa ba, fasawa tayi ta juyo tanufo gate zata fita itakuma Ilham ta shigo. 

Tsayawa sukayi suna kallon kallo itada Ilham, haďe rai sosai Ilham tayi tareda yin tsaki tazo zata gifta gefen Jalila ta wuce, caraf Jalila tasa hannu ta riketa ta janyota gabanta suna fuskantar juna, a fusace Ilham tace “ke dalla malama meye haka? Meyasa bakida tunani ne?” 

Jalila taja wasu seconds tana karewa kwayar idon Ilham kallo sannan tace 

“banida tunani kam, dole ki fadi haka, kinsan ba’a tabani a zauna lafiya, dan haka sekinyi hakuri da duk abunda zaki gani har se kin biya abunda kikayimin” 

Hararta Ilham tayi takuma kokarin rabawa ta wuce ta barta, amma Jalila takuma shan gabanta tace 

“Ilham nasani tsawon shekaru ina bata miki rai, kinyi alwashi daban2 akan ganin bayana, baki taba nasara ba se wannan karon da kika ďora min sata, to bari kiji in gayamiki wani abu dabaki saniba, babu abunda zakiyi a rayuwa ki rama abunda nayi miki, na riga nagama dake Ilham, kuma Wallahi Jalal baze taba aurenki ba, nagaya miki dama muddin kudirina yayi karo da naki sena watsa naki, kudirinki akansa yaci karo da nawa na watsa shirinki watsawa ta har gaban abada zanso ingaya miki wani abu daya kamata ki sani amma ban saniba ko kinason ji”

Kallonta kawai Ilham take batareda tayi magana ba, Jalila ta ďora tace

“Ranar da Jalal ya kwanta a Asibiti, kukazo duba shi keda Mahaifiyarki kisani idonsa biyu yaji duk abunda kuke faďa, dan haka ki cirewa ranki cewar burinki ze cika, Na riga naganoki Ilham tuntuni shiyasa nayi miki illa inda ba wanda ze gani, na illata shirinki bakida wata dama data miki saura, damarki ďaya shine ki jajirce kicigaba da jarraba sa’arki kozaku daidaita” 

Jalila takarasa maganar tana mata wani mugun kallo sannan ta juya tayi ficewarta, gaban Ilham ne ya shiga dukan hamsin2, kaddai Jalila dagaske take, amma to in hakane da yaji aida yaďauki mataki, “kai karyane bejiba, koma yaji wallahi seya Aureni, se burin mahaifiyata yacika” 

Ta shige cikin gida da sauri hada tuntube. 

Maama takasa zaune takasa tsaye, Naja batasan budurin da’akeba dan lokacin da Abba yayi wannan maganar bata nan tafita yawonta, harta dawo Maama tarasa ta inda zata fara mata bayani. 

Jalila na fitowa taga Jalal ya dawo a mota, yana kokarin shiga gida, ganin da yayi ta tsaya ta ki tafiya ta kura masa ido yasan akwai magana a bakinta, tsayawa yayi agaban ta yayi parking, yana tsayawa ta zagaya inda yake, ďan ďage mata gira yayi alamar meke faruwa? 

Ďan kallonsa tayi tace

“daga ina?” 

“kin aikenine?” ya tambayeta

“Ohh No Allah yabaka hakuri” 

Yace “Ina Jawwad ne? Na duba baya nan ban san inda ya tafiba?” hade rai tayi itama tace

“ka duba shi mana, kokabani ajiyarsa ne?” 

Kallonta yayi, wato ta rama kenan

Yace “A’a ban baki ajiyarsa ba” 

“dama..” sekuma tayi shiru 

“Dama me?” 

“inada magana ne” 

“fadi ina jinki” 

“toka fito daga motar mana” 

“In fito kuma? Gaskiya ni yunwa nakeji, zuwa zanyi in kwanta, naje neman Abinci narasa me zanci, dama in kin bawa Jawwad nake ci nima amma yanzu baya nan nasan bazan samuba” 

“Hmm to kace Ilham tabaka mana” 

Hade rai yayi sosai yana Kallonta, sunkuyar da kai tayi tana dariya kasa2

“Yi hakuri, ai yanzu mundena faďa ka jirani a part din Yaya Jawwad zan kankaro maka kanzo in za kaci” tayi maganar tana dariya, tana matukar kyau idan tayi dariya, gyaďa kai yayi ta juya ta tafi, yabi bayanta da kallo harta shige gida, sannan yaja motar ya shiga da ita gida. 

Gida takoma taje ta ďakko masa breakfast ďin Jawwad da yatafi beci ba, dayake da zafinsa a cikin flask, tana zuwa ta tarar dashi a zaune a palourn Jawwad yana jiranta, ta shiga tayi sallama amma be amsaba, seda tazo kansa ta tsaya takuma yimasa sallama ya ďago ya kalleta ya amsa a hankali, ta ajiye tray din tace

“Yana daga hakkin musulmi akan musulmi in yayi sallama ka amsa masa, kadinga amsa sallama please” 

Shiru yayi yaki kulata, Jalila tarasa wane irin miskilin mutum ne Jalal, koma tace ďan rainin hankali kana masa magana yana jinka amma yayi maka banza dan tsabar wulakanci, 

ta aje masa Abincin ta zauna a kujerar dake kallonsa. Ta danne fushinta 

Ya hada Abincinsa yafara ci, can yace “Me ya kai Alqur’ani dana baki hannun Ilham?” yai tambayar kamar bashi yayi ba

“ďauka tayi” tabashi amsa a takaice

“Ya’akayi ta ďauka baki hanata ba?” 

“Ina bauchi aka aikota taganshi shine ta ďauka” 

Bekuma cewa komai ba yacigaba ds auna loma, can Jalila tace

“Ya akai kasan yana gurin ta?” 

Kallonta yayi ya danyi murmushi 

“in kinaso in dawo miki dashi, yana gurina, amma bakiga abunda na ajiye a cikiba ko?” ďan yatsina fuska tayi sannan tace

“Nifa tsawon lokacin da yayi a gurina banga komai a ciki ba” 

“zan dawo miki dashi kikuma dubawa” 

“to naji zan duba” 

Ya cigaba da cin Abincin sa, can ta ďan nisa tace

“An baka aiki ance kaje interview kaki why?” 

Ďagowa yayi ya kalleta, “dama nayi tunanin kece kikasa aka nemamin wannan aikin, tayaya ina shaye2 zakice asamomin aiki a hukumar dake yaki da shaye2, amfanin me zanyi ko nima so kike a kamani?” 

“calm down let me explain, mezesa in so akamaka? da hakane naso akamaka da nasa an ka maka kaida abokinnaka jeje ai” 

ďagowa yayi ya haďe rai kaman be taba dariya ba

“Am sorry banyi hakan da wata manufa ba, sedai inkana aikin na farko ze rage maka yawan damuwa, sannan ze sa ka kara kokarin kadena shaye2 kaima, at least in kana da gurin zuwa ze kara dauke hankalin ka daga kan Shaye2” 

Zuba mata ido yayi yana tunani daban2 akanta, ta damu dashi dayawa, she’s so simple and calm, matsalarta kawai taurin kai da rashin kunya, Amma tanada zuciya me kyau. 

Tsarguwa tafara yi da kallon dayake mata tace

“Ya dai?” 

“meyasa kika damu dani haka?” 

Shiru tayi dan bata san mezatace masa ba, basarwa tayi tace

“dan Allah kaje interview din nan karka watsamin kasa a ido” 

“Senayi shawara” yabata amsa

“shawara kuma, dan Allah mene kuma na wani shawara dan Allah Yaya Jalal kaje please karkasa inji kunya” da shagwaba takarasa maganar 

Bude baki yayi tareda yin murmushi kaman karta dena magana

“Nine Yaya kuma yau, yarinyar bakida kunya fa” 

“Aida ďinma dan muna fada ne amma yanzu mundena faďa, dan Allah kaje ba dan halina ba, kaji Yayana ďan gidan daddy abokin Yaya Jawwad, badan halina ba” murmushi yayi ya ďan girgiza kai yace 

“Aikuwa kinsan  indan halinkine bazaniba, innayi tunani zan gaya miki” 

“to Allah yasa inji alkhairi” 

Be amsaba ya kai hannu ya dauki cup ya kai bakinsa amma jikinsa yafara rawa yakasa kaiwa

“lafiya menene kuma?” 

Ajiye cup din yayi, yai shiru yana rintse ido”

Da sauri ta mike ta nufi inda yake tana faďin “Subhanallah meyafaru?” 

Dagowa yayi idonsa yayi jawur yace 

“Gi.. Giy….. Giya,…. Giya zansha, ita nakeson sha” 

“giya kuma? Meyasa zaka sha giya?” 

Numfashi yake ja ya mike tsaye ya nufi hanyar fita, idonsa yayi jawur jikinsa se rawa yakeyi da sauri ta sha gabansa

“dan Allah Jalal karka sha giya, meyasa idan kuma kasha ka bugu daga nan ka mutu mezaka cewa Allah? Dan Allah karka sha kayi hakuri zaka ji bakason sha” 

Tureta yayi ze fita, takuma tare kofa tana masa magiya, yasa hannu ya hankadata jikin kofa ta bige kafaďa ta faďi a gurin shikuma ya fice kaman wani horrorn dayake bukatar jini. 

Jalila ta bugu sosai, ta rike hannunta tana rintse ido saboda azabar zafi, shikam yasa kai ya fice yabar dakin. 

Ta dade a gurin a zaune, sannan ta mike ta koma cikin gida tana yamutsa fuska. 

Su Jawwad kam har la’asar sannan suka isa Bauchi, Abba yakira daddyn Hanan a waya yagaya masa sun karaso, aka turo wasu sojoji sukazo suka tafi dasu har estate din, Ba Jawwad ba har Abba seda yayi mamaki irin tsaruwar da estate din yayi sekace barrack duk inda ka juya sojoji ke shawagi a ciki, akai musu Jagora zuwa gidan daya kasance nan ne center. 

A dankareren dakin Daddy akayi musu iso, da murna daddyn Hanan ya tarbi su Abba, suka gaisa yai musu barka da zuwa, seda suka fara gabatar da salla sannan daddy yai umarnin akawo musu Abinci. 

Wasu matasan ‘yan matane dabasu wuce sa’ anin su Hanan ba su uku suka kawo Abincin suka ajiye, tareda gaida Abba da Jawwad, ďaya daga cikinsu wadda da gani kasan hutu da jin dadi ya ratsata tace 

“daddy wannan yana matukar kama da Yaya Yusuf, ko shine sirikin naka?” Jawwad ya sunkuyar da kai saboda kunya 

Daddy yace 

“kaniyarki yusra, sarkin surutu, tunda kunkawo Abincin kukoma, ki gayawa Inna bakin sun iso zasu shigo anjima su gaisheta” 

Murmushi Yusra tayi tace

“Yadda kace haka za’ayi daddy” 

Abba yace “General wannan ma ‘yar wajenka ce?, tana kama da Hanan” 

“‘ yar wana ce, gaba dayansu yaran ‘yan uwanane, Aini Hanan da Abdallah kadai Allah yabani, sekuma diyata Autar mata Jalila, Zuma kenan ga zaki ga harbi” 

Gaba daya sukayi dariya, daddy yace su ci Abinci, Amma gaba daya Jawwad yakasa sakewa yaci Abincin nan saboda kunya “Sekace wani mace🙄, (ya kuke gani in goga Jalal ne? 😂 yaseen cin abunsa zeyi) 

” 

Daddy yace “Jawwad baka cin Abincin nan fa, nifa banason fulatanci, ka saki jiki kaci Abinci” 

Jawwad murmushi kawai yayi yakuma sunkuyar da kai. 

Bayan sun kammala, Abba ya gyara zama sannan yace

“to Captain ni dai da farko Jawwad be gayamin yana soyayya da Hanan ba, har nayi masa zabin matar Aure nida mahaifiyarsa, Amma yanzu nagane akwai matsala a dangane da zabin da mukayi masa, kuma Kanwarsa Jalila da Dan uwansa suka sanar dani halin da’ake ciki har kaima ka kirani a waya kazomin da wannan zance na Jawwad ya fito in dagaske yake”

Daddy yace “Hakane, nima mahaifiyar Hanan dince ta sanar dani halin da’ake ciki, kuma gaskiya yarinyar tanada manema dayawa kuma ta nuna shi Jawwad din takeso, shiyasa nima nayi maka magana” 

Abba yace “Hakane, Amma zangaya maka wani abu, inkaga zaka bawa Jawwad ‘yarka a haka to shikenan, inkuma kaga baze yuwu ba semu hakura” 

Daddy yace “ina jinka fadi muji” 

Abba yace “kaga maganar gaskiya a yanzu a bangaren mahaifi Jawwad bashida kowa se Allah sekumani, sedai bangaren mahaifiyarsa, banida wa bani da kani, kani na ďaya shine mahaifin Jalila kuma Allah yayi masa rasuwa tun Jalila nada shekaru biyar, kuma daga ni har mahaifinta babu wanda yasan suwaye dangin iyayenmu sakamakon suma gudun hijira sukayi daga garinsu, in kana ganin zaka iya bashi ‘yarka a haka shikenan “

” Haba Alhaji Usman, Ai Jawwad ko ďan tsintuwa ne babu abunda ze hana in bashi’ yata indai yana sonta, yanada hankali ga nutsuwa da tarbiyya wannan ba abun damuwa bane ba, bari muje ku gaisa da Mahaifiyata semu karasa gidan Yayana, shi ze karbi kudin Auren”

Abba yace “Nagode kwarai da wannan karamcin naka general, Allah yasaka da alkhairi” 

Daddy yace “tsakanina da kai babu batun godiya, bari muje”. 

Jalila takoma gida ta fara baccin dole saboda azabar zugin da hannunta yakeyi, se kusan la’asar ta tashi, shima hayaniyar Naja ce ta tasheta dayake ita Naja wani lokacin kaman banza haka take bata magana a hankali, ga hauma hauma kamar rainon gabuwa, wannan hargowar ce ta tashi Jalila. 

Sannan da alamu har yanzu Maama bata gaya mata sakon Abba na tabar masa gida ba, dan har yanzu tana giginta da rawar kai, Jalila ta tashi tayi sallar la’asar tanemi abun zubawa a cikinta. 

Shikuwa Jalal tunda yaje ya sha giyarsa yayi tatul wani nannauyan bacci ne ya kwashe shi be farkaba se magariba, ya shiga yai wanka yai sallolinsa, bayan ya idar ne ya dau wayarsa yakuma kiran Jawwad, wannan karon Jawwad ya dauka Jalal yace “wai dan Allah ina ka shiga ne haka? Tun safe ban ganka ba, na tambayi kanwarka tace bata san inda kake ba” 

“Aiba bata nayi ba, kuma ba saceni akayi ba kaganni tareda Abba muna Bauchi” 

“Bauchi kuma? Me ka keyi a Bauchi?” 

“bazaka gane ba, sena dawo kawai akwai Labari” 

Murmushi Jalal yayi, yadda yaji muryar Jawwad yasan yana cikin farinciki, Jalal yace 

“To seka dawo din, amma tafiya ba sallama haka?” 

“Nima ban san da tafiyar ba, babu shiri Abba yace inzo mutafi” 

“to shikenan Allah yadawo daku lafiya” 

“Ameen ya Allah” sukayi sallama 

Bayan sunyi sallamane Yusuf ya shigo palourn daddy, Sallama yayi suka amsa gaba daya, Yusuf ya kalli Abba ya durkusa ya gaisheshi ya amsa masa cikin sakin fuska, ya juya ya kalli Jawwad ya mika masa hannu suka gaisa. 

Daddy yace “Yusuf ga Abban Jalila fa” 

Murmushi Yusuf yayi yace “Ai ina shigowa jikina yabani, ina kallonsa naga akwai alakar Jini, wannanne yayanta kenan sirikinmu” 

Daddy yace “ya akayi kasani?” Yusuf yace

“Kai daddy yadda yarinyar nan ke fadarsa, ko kunya ba taji ranar inajinta itada Nawwara (matarsa) tanata yabonsa hada yi masa waka, kaf estate din nan ba wanda besan haidar ba ko ince Jawwad” 

Gaba daya sukayi dariya, Yusuf yace

“ďan uwa Allah yabaka wuyan ďauka, dan wallahi Autar daddy fitinanniya ce, ga yarinta a cikinta” haka sukaita taba hira Yusuf yajanye Jawwad suka fice zuwa bangaren Inna. 

Suka shiga da sallama, kamar kullum tana kan darduma tana lazimi, suka zauna a gefe suna taba hira harta idar, sannan ta juyo ta kallesu dan kura musu ido tayi, Jawwad yace “Sannu Inna” 

“Yawwa ďan nan, Yusuf wannan kuma ina ka samoshi, kar in fadi wani abu ace nayi rikici” 

Yusuf yace “Inna Yayan Jalila ne” 

Murmushin fuskarta ya faďaďa sannan tace “Masha Allah, Nayi farincikin ganinka yarona, Kanwarka me kama da mairota da na dauka itace, ashe ba ita bace ba ina kabaromin me sunan larabawan?” 

“Tana lafiya Inna, tace a gaisheki” 

“Allah sarki yarinyar kirki me hankali, idan ina basu labarin kanwata se suyita lallabani wai kar in rikice musu da kuka, itakuwa kanwarka zama take muyita hira naita bata labarin wannan kanwartawa” 

Yusuf yace 

“zaki farako inna, dan Allah kiyi hakuri, kekowa sekin bashi labarin kanwarki, ko labarin tsofaffinki ba kyayi kamar ita, kimsan bakida cikakkiyar lafiya” 

Jawwad yace

“A’a kabarta ta fada maybe hakan ze rage mata damuwa, tunda kaji haka akwai kyakyawar alaka a tsakanin su” 

Yusuf yace “Ai intana wannan labarin nata daga nana zata fara kuka, kuma in tafada bata iya cin Abinci jininta ya hau sosai” 

Sallamar Su daddy ce ta katse musu hirar suka amsa musu Sallamar amma banda inna da ko juyowa takasa yi. 

Daddy yakaraso gabanta ya durkusa yace

“Inna ga baban Jalila, kuma sirikinki yazo ya gaisheki ne” 

jinjina kai tayi ba tace komai ba, Abba ya zagayo gabanta ya durkusa gaba daya ta zuba masa ido ko kyaftawa batayi, tace 

“Imamu ne? Imamu ina Mairona” cikin sanyin jiki Abba yasa hannu yakamo Hannunta ya rike a nashi a hankali ya furta “Innarmu…. Inna Hafsatu, Allah yasa kece, kece wadda Inna take bamu Labari Yayarta” 

Fashewa da kuka tayi ta rungume Abba tana fadin 

“Alhamdilillah nagaya musu, Amma sunki yarda suna ganin kaman rikici nane kawai, tunda naga yarinyar gurinka nasan tsatson Mairamunace, nasan zuwa yanzu ba lallai tana raye ba, amma ina son inga ahalinta” 

Hawaye sharkaf a idon Abba yace

“Na dade ina bulayin neman ki Inna, Allah ya karbesu gaba daya, dasu da tilon ďan uwana, ya mutu yabarmin ‘yarsa Jalila se yarana biyu, ban taba tunanin Allah ze karbi Addu’a ta ba, yau naga dangin iyayenmu” 

Gaba daya jikinsu yayi sanyi, kowa seda yayi hawayen tausayi, Abba yasha wuyar bulayi da yawo garuruwa ko Allah zesa yasamu wani nasa ashe suna kusa da juna, alakar yara ta haďa amma basu saniba, Ashe shiyasa kamannin Jalila da Hanan sukayi yawa, hatta yanayin halayensu iri daya. 

Abba yasa hannu yana gogewa Inna hawaye cikin zolaya yace “Kamanki daya da Innarmu, sedai duk babanmu yafi ku kyau” 

Murmushi tayi tace “Ai shima ďan uwana ne, kuma mairo tafishi kyau, Allah yayi musu rahama gaba ďaya. 

Nan hirar asali da tushe ya barke, nan da nan Labari ya karaďe estate din nan cewar ansamo dangin mairo kanwar Inna, nan da nan gidan yafara cika da dangi da ‘yan uwa don ganewa idanunsu hakikatul Amri. 

Daddy yace tunda hakane kadasu Abba sukoma yau, su ďanyi musu ko kwana ďayane Inna taji ďaďi kuma sannan suga’ yan uwa. 

Haka kuwa akayi, Abba yakira Maama yace bazasu dawo a yauba saboda wasu dalilai, ba wanda suka gayawa abunda yafaru, hatta Daddy be gayawa su Hanan ba. 

Jalila takira Ahmad ya sanar da ita cewar baze shigo yauba, saboda yayi dare a hanya sedai zuwa gobe Insha Allah, seda suka sha soyayya sannan sukayi sallama gefe daya kuma hannunta se ciwo yakeyi, da wanine yai mata abunda Jalal ya mata yau da seya gane bashida wayo, shima ďin dan yanzu bata son yawan fitina da shine saboda gaba ďaya yanzu tausayi yake bata, da dane da seta rama. Amma to meyake damunsa haka? Lokaci ďaya mutum ya rikice kaman wani me tabin hankali, yana zaune lafiyar Allah amma ya birkice lokaci daya wai seyasha giya. 

Jawwad kasa boye farincikinsa yayi, seda ya kira Jalal a waya, yana ďagawa Jawwad yace “My man kana inane?” 

“Ina gida mana, ina zanje tunda baka nan? Wai yaushe zaku dawo? Tun dazu nake zuba ido amma baku dawo ba” 

“Ai mu ba yau zamu dawo ba” 

“Se yaushe?” 

“Ai bazaka gane ba Jalal bansan yadda zan fasalta maka farincikin danake cikiba” 

“Abba yaje nema maka Auren Hanan a Bauchi” Jalal yafada kai tsaye

Da mamaki Jawwad yace “ya akayi kasani?” 

“Zuciya tace tagayamin” 

“ban yadda ba dama can kasani kai shiru kaki gayamin, amma akwai saura ai” 

“to gayamin inaji” 

“Abba ya gano danginsu daya daďe yana nema” 

Murmushi Jalal yayi yace “Alhamdilillah, na dade ina fatan hakan ya tabatta, kakarsu Abdallah ce Inna Hafsatu da Inna mairo take fada take bamu Labari ko?” 

Cikin mamaki Jawwad yace “wai dan Allah ya akayi kasani?” 

“Allah ne yasanar dani, dan Allah kadawo da wuri, ni bana jin dadi in baka nan” 

“wai kana in dawo da wuri, kamanta in Allah ya kaimu next week zan tafi inda aka turani aiki”? 

“kumafa hakane se yanzu nakejin babu daďi, amma Insha Allah hakanne mafi Alkhairi agaremu baki daya” 

“Amma ni ina mamaki yadda akayi duk kasan wannan zancen ni ban saniba” dariya Jalal yayi yace

“Ba abun mamaki bane, kai dai seka dawo kawai

Seda suka gama hira da Jalal ya katse wayar, Jawwad yaji kaman ya kira Jalila amma ya fasa, dan yasan idan ya kirata farinciki seyasa yagaya mata abunda ke faruwa kuma Abba ya gargade shi akan kar kowa yasan wannan zancen a yanzu harse sun koma gida. 

Maama tarasa ta inada zatayiwa Naja bayanin Abba yana bukatar ta bar masa gida, saboda tana matukar Jin tsoron Masifar Yaya Mairo, tarasa abunda yake mata dadi, yanzuma da Abba yayo waya seda ya jadadda mata baya son ya dawo ya tarar da Naja cikin Iyalinsa, tarasa ta inda zata fara harga Allah bazata iyaba sedai inya dawo shiya koreta da kansa, can wani bangaren na zuciyarta yake cemata banda ma ya raina miki hankali, ita Jalila dake zaune a gidan meyasa bece ta bar gidan ba, shekarar Jalila nawa a  gidan, se yanzu zece Naja tabar gida, indai Naja zata bar gidan nan to dole Jalila ma ta kama gabanta, Maama tayi kwafa tace 

“Zaka dawo ka sameni, dai2 nake da kai” 

Naja se iyayi take tana wasu irin abubuwa na ban haushi wai ita zatayi Aure, A gaban su Nana take waya da kawarta sunata shirye shiryen abunda zasuyi da biki, ba kunya Naja take cewa a mata booking na kayan mata na tashin hankali, masu tsada, se wasu irin lissafi takeyi, kala2 party da zatayi, da irin expensive clothes da zasu saka itada kawayenta. 

Tagama wayarta su Jalila suna jinta, tana gamawa Nana ta tinstire da dariya,

cikeda tsarguwa Naja tace “ke Nana meye abun dariya haka?” 

“A’a ni ba dake nake ba, mahmud ne yabani dariya a waya” 

Itakam Jalila bata samu zarafin dariya ba tana fama da ciwon hannu, ko uffan ba tace ba. 

Nana tagayawa Jalila Abba yace bazasu dawo yauba, Akwai abu me mahimmanci daya rikesu, Jalila a ranta taketa addu’ar Allah yasa abunda take tsamanni ne ya tabatta. 

Washegari da safe Monday ce Jalila tace bazata makaranta ba, Dan haka Nana ita kadai ta tafi, tai kwanciyar ta tana bacci, Zahra takirata a waya tagaya mata zasuyi test karfe goma shadaya da rabi na safe, Jalila sam bata da niyyar zuwa makaranta haka ta tashi tana tsaki tayi wanka tasaka kaya, doguwar riga pitch da mayafinta se wata ‘yar karamar Jakarta ta dauka, iyakacin Jakar nan ta dauki waya da kudi da ďan abunda baza’ a rasa ba sekace jakar roko, 

Jalila Ta fito fuskar nan babu walwala,  ta tarar Maama na palour tana karyawa itada Naja, yanzun ma hirar bikin suke, Jalila ta durkusa tace

“Maama zan tafi school, yanzu aka kirani zamuyi test anjima” 

Banza Maaman tayi mata taki kulata, dama batayi tsamannin Maama ta amsa ba, tayine dan hakan shime tarbiyar da Ummi ta dorata, ta mike jiki a sanyaye Zata fita Naja tace

“Aikin banza wai za’a school za’a tafi yawon gantali dai irin wanda uwale ta saba yi” 

Maama tace “dan Allah kidena shiga harkar yarinyar nan shiyasa take kara rainaki” 

ai kafin Maama ta gama magana Jalila ta waigo tace “ta Uwale tayi kyau, kekuma ki saurar kiga naki sakamakon, anzo an bararaje ana cin duniya babu a house, gara ki zage ki ciki kafin ki kara gaba, Akuya kawai” 

Ashar Naja ta mulmulo zatayi Maama ta dakatar da ita, Jalila kuwa tayi ficewarta ranta bakikkirin babu dadi. 

Maama tace

“kyaleni da ita, ki zuba ido zakiga matakin da zan dauka akanta” 

Jalila na fita ta hango Mummyn Jalal  tareda Ilham da alamu wani gurin zasuje, da kaman ta basar tayi tafiyarta sekuma taga hakan be dace ba, dan rabonta da taga Mummy harta manta dan ko gidan bazuwa takeba yanzu, dan haka ta nufi inda motarsu take, Mummy tana kokarin shiga, Jalila da fara’arta ta karasa ta durkusa ta gaida Mummy, amma ga mamakin ta taga Mummyn tayi mata wani irin mugun kallo kamar bazata amsa ba sekuma ta amsa da kyar, Jalila taji ba dadin abunda Mummy tayi mata, amma ta dake ta mike tace “Mummy Adawo lafiya sekun dawo” 

Mummy ta yamutsa fuska tace “Yawwa dama ina son ganinki kuwa, akwai magana me mahimmanci da nakeson mu tattauna dake, dan bazan saka ido abunda ke faruwa yacigaba ba” 

Seda gaban Jalila yai mummunar faduwa, wannaan wane irin abune ita kowa ma laifi take masa, kowa ya tsanenta a fili tace “to Mummy Allah yasa ba laifi nayi miki ba? Zanzo Insha Allah, Adawo lafiya” 

“Munafukar banza barauniya, me bin ďan mutane, Akuya kawai” 

Taji sautin maganar Ilham ta sauka a kirjinta saitin zuciyarta, dukda yadda maganar tayi tsauri tareda dukan zuciyar Jalila, amma ta danne taki juyowa ta kuma kallon inda suke, ta mike tacigaba da tafiya. 

Jefa kafarta take ba tare da tasan ina take saka kafar tata ba, Hawayene yake bin idonta, Allah ya temaketa unguwar tasu se kayi minti goma babu wanda yazo ya wuce, kuma wajen karfe tara ne duk wasu sun riga sun fita, hakan yakara bata damar zirarar da hawayen ta son ranta, tana cikin tafiya ne taji ana mata horn kaman za’a kashe mata kunne, ita dai iya saninta ba a tsakiyar titi take tafiya ba gefen hanya ne, Amma an cika mata kunne da horn, banza tayi tacigaba da tafiyar ta. 

motar aka sa aka sha gabanta, sannan yafito daga motar yace

“Bakya jin ina miki horn ne ? Sekace wata kurma, Kuma Se yanzu zaki tafi school karfe tara? Allah ya shirye ki, zo muje in ajeki ta nan zan wuce” ya dinga jero maganar daya bayan daya

Juyowa tayi ta kalleshi, ya saka farin yadine dukda kansa babu hula yayi kyau sosai, dan zata iya kirga sau nawa taga Jalal da dogayen kaya, kallonta yayi sosai yaganta kaman a birkice, hawayene a fuskar ta, idonta har yafara Ja, cikin tsiwa tana hararsa tace 

“bazan hauba ai da can ba kai kake kaini ba, salon in hau motar ka, ka karasa karyani bazan hauba” 

“hmm bazaki hauba ko? Bazaki hau motar mahaukaci ba, Dama interview din nan zani, Amma tunda bazaki hauba se inkoma kuma bazan kuma zuwa ba” 

Cikin sauri tace “A’a yi hakuri zan hau, Amma dan Allah karkayi gudu dani” tafada hawaye na zubowa daga idonta 

Gaba daya tausayinta ya kamashi, kome yasata kuka haka a titi, itada take da dakakkiyar zuciya? Abunda ze satana tafiya tana kuka ba karami bane ba

“bazan ba, a hankali zan tafi” ya faďa a takaice

Ta bude motar ta shiga, shima yazaga ya bude ya shiga, ya kunna motar yai mata key, suka fara tafiya, ya kalleta yace “Kukan me kike?” 

“bakomai” 

“bana son karya fa” 

Shiru tayi masa, ta maida kanta titi kyaleta yayi tunda yaga batasan faďa masa, maybe is her personal issue. Suna cikin tafiya Jalal yayi parking ya kalleta yace “Zoki rakani zanci Abinci, banyi breakfast ba” 

“Ni bazaniba, kaje ka dawo, nibana son ana ganinmu tare” ta fada tareda dauke kanta daga kallonsa

Ba tareda ya kalleta ba yace

“ohh yeah, be kamata adinga ganinki tareda ďan iska mara tarbiyya ba, kar azata irinmu daya, bari yanzu zan  dawo” 

Ta fuskanci haushi yaji, amma ta basar dan itama ranta a bace yake Befi 5 mintues ba ya dawo da leda a hannunsa, ya kunna motar suka cigaba da tafiya, yana tuki tana goge hawaye, sekace kurame, baya son ya kalleta yaga tana kukan nan, kukanta yanasa shi tuna lokacin da Umminta ka gudn abunda ze sashi kuka shida Jawwad, gani Jalila tayi ya canza hanya dan haka da sauri tace “A’a yanaga ka canza hanya?” 

Be kalleta ba yace “Wani guri zaki rakani” 

Zare ido tayi “saboda me makaranta fa zani, zanyi test” 

“Nasan makaranta zaki, amma tunda kika shigo motata sekinje, don’t mind club zamuje kawai, zan danyi caji” 

(🙄🙄 tab ba ruwana, yan ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP, kunji Jalal dinku da rigima,) 

Abba sunga “yan uwa sunga dangi, Abba be taba tunanin suna da wannan dangin ba, a hakanma sunada ‘yan uwa a wasu garuruwan, A yau Abba yace lallai zasu koma kano saboda yanada ayyuka dayawa, se sun dawo ziyara ta musamman dan kara sanin juna, ba karamin farinciki akayi ba ganin Inna ta samu zuri’ar Kanwar ta, Ashe ba a banza ba Jalila da Hanan suke wannan kamannin. 

A ranar su Abba suka dawo gida, tun Asuba suka taho, basu baro bauchi ba seda aka yanke watanni hudu, a matsayin lokacin Auren Jawwad da Hanan, sedasu Abba sukayi maganar Ahmad, Abba yace duk abunda daddy ya yanke dai2 ne, daddy yace “se Jalila ta kammala Makaranta ze bawa Ahmad, saboda yanayin karatunta dakuma aikin Ahmad 

Su Abba se  karfe shadaya suka sauka a kano, Suka sauka da matukar farinciki. 

Abba na shiga cikin gida yaci karo da Naja, a palour tana waya, bece mata komaiba ya wuce part dinsa, 

Maama haushinsa takeji akan yace Naja tabar masa gida dan haka tana jin sun dawo taki zuwa inda yake, ya shiga part dinsa yai wanka ya canza kaya,  da kansa yaje ya sami Maama a daki Yace

“kina jin mun dawo amma kikasa fitowa kiga yamuka dawo? Shikenan ina miki Albishir Anbawa Jawwad Auren ‘yar wajen Captain Abdurrasheed wato Hanan nan da wata hudu Insha Allah” 

Wani mugun kallo tayiwa Abba tace “kamar yaya? Yaza’ ayi akaiwa Naja kudin Aure dan munafunci kuma aje akaiwa wata, mata biyu ze Aura kenan, Jawwad din kwaya nawa yake daze auri mata biyu?” 

“mace ďaya ze Aura wato Hanan, maganar Naja na soketa an barmusu kudin Auren, zanje da kaina in samu iyayenta, Sannan kije ki sallami yarinyar nan tabarmin gida, tun kafin raina ya baci, bana kaunarta a cikin iyalina, kema yakamata kuje ku kara binkice akanta” 

“Impossible” Maama ta fada da karfi 

Cikide fusata Maama ke fadin “ni zakayiwa haka? Ka watsamin kasa a ido, a kai kudin Auren yarinyar mugama gayawa duniya za’ayi biki sannan kazo min da wata maganar banza, wallahi baze yuwu ba Jawwad bashida matar data wuce Naja

Abba yace

“Shikenan tunda ke zaki daura masa auren ai seki aura masa Najar in gani” 

Ya juya ze fice tace

“Kuma wallahi bazata bar gidan nan ba, in dai Naja zata bar gidan nan to Jalila ma seta bar gidan nan” 

Cak Abba ya tsaya ya juyo yace

“gida nawane, duk wanda yake ciki a karkashin ikona yake, idan yarinyar nan ta kai magariba a gidan nan to Wallahi zaku tafi tarene, ta tattara tabarmin gida nagaya miki, Jalila nan gidansune, nine mahaifin Jalila, Jalila bata da uwa ba uba seni, ita kuma wannan tanada iyaye dan haka ta koma gidansu, kowa ya zauna a gidansu” yana gama fadin haka ya juya ya fice. 

Jawwad yana zuwa ya canza kaya, ya nufi gidansu Jalal amma yatarar baya nan, dan haka ya koma gida ya samu guri ya kwanta dan ya huta

A fusace Jalila tace

“Wallahi bazani club ba, ka tsaya in sauka in yaso kaje inda yafi club be dameni ba” 

Shiru yamata ya cigaba da tukinsa, yana satar kallon yadda ta rintse ido tana masifa, ganin yaki kulata yasa a fusace tace

“Magana fa nake maka, wai meye haka?” 

Fitooo yafara yi mata yana murmushi, Jalila ta kai karshe a kuluwa, ya dan kalleta yace

“meye kuma na tashin hankali bafa cewa nayi zamuje Kisha giya  ba rakiya kawai zakiyi insha mutafi” 

Ta fuskanci so yake ya raina mata hankali, dan haka tayi shiru taga gudun ruwansa, ta dauke kanta zuwa ga kallon window tana share kwalla lokaci zuwa lokaci gani tayi tafiyar taki karewa dan haka takara fashewa da kuka me sauti Da sauri Jalal yace “Ke meye haka kuma? Nifa ba Jawwad bane da zakimin shagwaba” 

Ido duk hawaye tace “Eh aida Yaya Jawwad ne yasan inada test bazemin haka ba, kuma Allah ya kiyaye in maka shagwaba in maka shagwaba ince nayiwa wa?” tai maganar tana harararsa da kumburarrun idanunta

Dan hade rai yayi yacigaba da tukin ba tareda yace komai ba itakuma tana hawaye. 

Wata unguwa suka shiga, wadda kome za’ayiwa Jalila bata san inane ba, wani katon dogon gini ya nufa, kana ganin yanayin ginin da girmansa kasan kamfani ne, yana zuwa aka bude masa wani katon nannauyan gate ya shiga da motar, tundaga bakin gate din ma’aikatan ke durkusawa suna gaisheshi, dagani gurin kamfanine, yaje yasamu guri yayi parking, da sauri akazo aka bude masa motar ya fito,  ya zagaya yace mata

“fito” 

“ni bazan fito ba, kawai ka maidani inda ka dakkoni” 

“Wallahi in baki fito ba zakiyi biyu babu, kirasa test dinki kuma inki zuwa interview” 

Kara hade rai tayi sosai ta bude motar ta fito tana zumbura baki, fuskarta tayi jawur, yayi gaba ta bishi abaya. 

Babban abunda ya daurewa Jalila kai be wuce yadda taga duk inda Jalal ya ratsa ma’aikata manya da kanana suna girmama shiba, dan wasu har kasa suke zubewa suna gaida shi, Akayi sa’a in suka gaisheshi yana daga musu Hannu, Haka Jalal ya dinga ratsawa da ita tsakanin ginin katafaren gurin daya kayatu yadda yakamata, ko ina tsaf dashi, suna zuwa wata kofa sukaga wani mutum, ya girmi Jalal sosai ya mika masa hannu sukayi musabiha, mutumin yace “Yallabai yau akwai ruwa da kankara kaine a kamfani yau, rabonka da nan shekara nawa?” 

Murmushi Jalal yayi yace “Ya aikin?” 

“Lafiya kalau anata fama” 

Jalal yace “Masha Allah hakan yayi kyau” 

Daga nan yai gaba Jalila tacigaba da binsa, wata katafariyar kofa sukazo Jalal yasa hannu a aljihunsa ya dakko key yabude kofar ya kalli Jalila yace “Bismillah” tareda yi mata nuni da cikin gurin, jiki a sanyaye kuma a matukar tsorace ta shiga ta tsaya a bakin kofar tana rarraba ido, Office ne dankarere, sekace na hamshakin sarki ko gwamna, babu abunda babu a ciki, idonta ne ya sauka akan hotunan dake cikin Office din, akwai hoton shugaban kasa, gwamna da na sarki, sekuma hoton Daddyn Jalal, ta juya daya bangaren tangamemen hoton Jalal ne da Jawwad sanye da kaya iri daya sunyi murmushi an rubuta J&J global concept, sekuma hoton Jalal shikadai, ba karamin kyau yayi a hoton ba Ganin da Jalal yayi a tsorace take ta takure a tsaye, ya maida kofar ya rufe yasa mata key, kallonsa Jalila ta tsaya ta nayi a matukar tsorace hankali yace “muje ko?” 

“ni ba inda zani, ka maidani makaranta zan tafi fa”

Baya kaunar wannan gaddamar ta Jalila dan haka be tsaya bata lokaci ba ya danko hannunta da karfi, hakan yasa ta saki wani uban ihu saboda zafi, hannun dayake mata ciwo ya rike, a tsorace ya cikata yana kallon yada tuni ta rike hannu tana Hawaye

“Meye haka? Sekace wadda nayiwa wani abu” ya fada adan gigice

“eh dole kace haka mana, jiya ba kai ka hankadeni na fadi akan hannun ba, yana min ciwo shine ka famamin” Jalila gaba dayanta shagwababbiya ce

Dan shiru yayi yana kokarin tuna abunda ya faru shi gaba daya ya dauka a mafarki abun ya faru ba gaske ba yace “Ok naji amma yanzu zauna” 

Guri ta samu akan kujera daya ta zauna, yace “zan iya ganin hannun?” 

“Bazaka gani ba” ta fada tareda janye hannunta

“Shikenan tunda kimce bazan ganiba, am sorry, ban san nayi miki ba, a tunanina mafarki ne, idan kinga na shiga wannnan yanayin kidena zuwa inda nake, kome zanyi karkiyi kokarin hanani, in bahakaba wataran zan iyayi miki illa” 

Dan kallonsa tayi tace 

“to meyasa kake hakan?” 

“Nima ban saniba, haka kurum nake tsintar kaina a wannan yanayin, Jawwad ne kawai ya damu da halin da nake shiga, Mummy da ba damuwa tayi daniba, tana ganin kawai shaye2 danake ne ya janyo min hakan, dayawa idan nayi kokarin dena shaye2, kokuma raina ya baci, se in shiga wannan yanayin ” 

yayi maganar cike da damuwa, cikin tausayawa tace

” Ka dinga yawaita Azkar, kuma ka kulada ibada zaka dena jin abun insha Allah”

“bazan iya ba” ya fada kai tsaye

“Meyasa bazaka iyaba?” 

“Har yanzu baki gama sanin waye ABDUL JALAL ba dukda yanzu kinsan abubuwa da yawa akaina fiye da iyayena, just keep praying for ABDUL JALAL, and I really appreciate your efforts on me, Thank you, Allah ya jikan Abee” 

Jinjina kai tayi amma takasa magana, 

Can tace “dan Allah me nayiwa Mummy? Na gaisheta dazu da kyar ta amsamim tace inje tana son ganina, Allah yasa ba laifi nayi mata ba?” 

“meyasa kike tunanin laifi kikayi mata?” 

Hawayene ya zubo daga idonta, shi Jalal har mamaki take bashi, kaman shan ruwa haka take kwararar da Hawaye, basa mata wuya sam tace 

“Yanzu duk lokacin dana motsa ko nayi wani abu se ansamu wanda zasuce na musu laifi, kowa ya tsaneni komai nayi laifine, mutane kalilan ne suke sona A duniyar nan, daga masu kirana munafuka, se makira, barauniya, karuwa, Arniya se masu cewa uwata ta gudu ta banni, ba ataba barina inyi awa24 cikin farinciki se an samu me batamin rai”

Takarasa maganar cikin kuka muryarta na sarkewa, tasa hannunta biyu ta rufe fuskarta tana kuka me tsuma zuciya, Jalal jin kukan nata yake a kahon zuciyarsa, yaji gaba daya komai ya kwance masa, yace

” Kidena kuka mana, kin manta ke kikemin nasiha amma yanzu kike kuka, Allah baya mantawa da bawansa, Allah yasan halinda kike ciki, ni da nake gabanki a yanzu na isheki misali na isheki darasi, ba’a nasara ba tareda an sha wahala ba, kisawa ranki matakin nasarar kine kike takawa, duk wanda yayi miki gori a rayuwa ko ya cutar dake kisa a ranki kinfi shine, Allah yana son bayinsa masu hakuri, semene dan duniya batayi dake in har ubangijin da yayiki yanayi dake shikenan, kiran da Mummy tayi miki karki sake kije, bashida wani amfani na gaya miki”

Ya mike ya nufi wata katuwar drower ya bude, ya duba ya debo wasu takaddu yazo gabanta ya zube su yace “dauki wannan takaddun, ki dubamin abunda za’a iya nema a gurin, zanyi breakfast yanzu” 

Yakoma kan kujera daya yazauna ya fara cin Abincin sa daya siya dazu, Jalila tasa Hannu tana duba takaddun, duk na makarantun da Jalal yayine, abun mamaki results dinsa sunnuna shi din kwarone, kuma duk an masa kyakykyawan yabo a jikin results din, daga ido tayi tana kallonsa yana cin Abincin sa hankali kwance, ba ita yake kalloba amma taji yace 

“Ya dai kike kallona? Ko zakici ne?” girgiza masa kai tayi alamar A’a, tareda maida hankalinta kan Takaddun gabanta

Yace “Au Ashefa bazaki iya cin Abincin hannun dan iska ba, karkije na zuba kwaya a ciki ko?” 

Shiru tayi masa yagama ciye ciyensa, ya mike yana kuma duba wasu takaddun, yaji muryar Jalila tace

“wai Inane nan?” 

“Kamfanina ne?” ya bata amsa

Zare ido tayi, ya kalleta yace 

“kina mamakine? Nawane mallakina, akan wannan dukiyar ne aka halakar da rayuwata, dukiya mugun abu me halakar da mutane, me haddasa gaba da kiyayya, me tafiya da Imanin ma’abota kwadayinta, Akan dukiya Mummy tayi cin amana tayi yaudara ta auri daddy, 

Akan dukiya Mummy ta ajiyeni tayi tafiyarta lokacin da nake bukatar taimakon ta,

Akan dukiyar akabada kwangilar ruguza rayuwata,  Akan dukiya Mummy ta rabu da mutane dayawa, Akan dukiya da daukar fansa aka halakar da rayuwata,

Ilham da mahifiyarta suna son su dauki fansa akaina ne su gaje dukiyar dana mallaka, itakuma Mummy takasa fahimta, tunda suka kyalla ido sukaga Daddy yasayi kamfanin nan yabani, suka kasa nutsuwa, ke sheda ce, Kinsha kama Ilham na kokarin samin magani a Abinci, kuma ta dade tanayi min hakan saboda dukiya, Akan dukiya…….

Sekuma yayi shiru ya dafe teburin gabansa yayi shiru, gaba daya Jalila ta zuba masa ido, jin yadda yake sarrafa magana daki daki ta sigar rarrashi da wa’azi, ko a mafarki in wani ya gaya mata Jalal ze haka karyatawa zatayi. 

Yacigaba da cewa “Ban taba kukan babu a rayuwata ba, babu innemi abu in rasa ban taba ba, bansan talauci ba, Amma nidai wannan dukiyar da taza memin bala’i, gara ace talaka futik Mummy ta aura in tsira da mutuncina, A rayuwa bazan manta da mutanen dasuka soni dan Allah ba, family dinku mutane ne masu mahimmanci a rayuwata, kinga Jawwad na yadda in rasa duk abunda na mallaka saboda shi, Yana sona badan dukiya ta ba, duk abunda zamuyi baya sako lissafin dukiya ta, bayan Umminki da Jawwad ban taba zaton zan samu wanda ze tsaya akan lamarina ya damu dani kamar ki ba, bana manta Alkhairi, kinmin abunda banida abun biyanki, dukda bakida kunya, ga taurin kai da tsaurin ido, ga rashin kunya da iyayi, bazan manta yadda kike putting rayuwarki a risk saboda dan iska mara tarbiyya me kama da ‘yan daba, dan daba yana godiya” ya karashe maganar yana kashe mata ido, 

Murguda masa baki tayi ta dauke kai, ya danyi murmushi yace “Ai bazaki taba canza hali ba” 

Ya kwashi takaddunsa ya mayar da sauran yace mata “Tashi mu tafi” ta mike tayi gaba yazo ya bude kofar suka tafi, sosai Jalal ya dingayiwa ma’aikatan nan barin kudi kaman besan ciwonsu ba. 

Suna cikin tafiya Jalila tace “Amma meyasa baka zama a kamfanin, at least you will keep yourself busy zaka manta da wasu abubuwan” dan shiru yayi sannan yace 

“Ta yaya ina cikin wannan halin zanzo inyi aiki, Akwai manager kamfanin nan dan abokin daddy ne shike kulada komai, duk lokacin danazo na zauna da sunan zanyi Aiki se wannan abun yasa meni, idan na birkice senayi barna sosai kafin in bar gurin, wani lokacin har illa nake wa wasu, shiyasa wasu ke kallon ko inada tabun hankali, kokuma illar shaye2 ne, rabona da gurin nan nafi shekaru goma, yanzun ma saboda takaddun nan nazo, kuma abun mamaki naga nashiga na fita lafiya yau saboda muna tare da ke”

“To Allah ya baka lafiya, Amma yakamata kanemi magani sannan ka dinga Addu’a” 

Tasa hannu ta cire farin carbin counter dake hannunta ta ajiye masa tace “ka dinga Amfani dashi, ze temaka maka” Be iya cewa komai ba se kallon ta da yakeyi, har Jalila manta data bashi sekuma taji yace 

“Thank you” itama banza tayi dashi taki kulashi. 

Haka suka cigaba da dan taba hira har sukazo makarantar, zata bude tafita yace “tsaya, wai ke wannan ce jakar makarantar?” 

“Eh mana” ta bashi amsa

“wannan ba jaka bace sekace Jakar tara kudin bara, ina litattafan karatun?” 

“Jakar tara kudin maulace bata bara ba” Ji yayi kaman ya tuntsire da dariya amma ya fasa, yasa hannu ya dau Jakar ya bude jotter ce se biro da kudinta dari biyar se waya, yasa hannu a Aljihunsa ya dakko kudi yasamata ya mika mata, ta kalleshi “Ni inada kudi cire abunka” 

“Fitarmin daga Mota ko insa lock inyi gaba dake wallahi” Hannu tasa tana kokarin cire kudin ta ajiye masa yace

“Bana kyauta amayarmin, karki bari raina ya baci fita ki barmin mota, mara kunya” 

Ikon Allah yanzu suka taho girma girma cikin mutunci amma se wani korarta yake kaman rokarsa tayi, ta hade rai ta bude motar sannan tace masa “Allah yabada sa’a” 

“Ameen” ta rufe masa motarsa tayi gaba. 

Maama fa hankalin ta ya kai makurar tashi, idan tace zata tsananta maganar nan zata iya rasa Aurenta, dan haka ta nufi part din Abba dan ganin ta inda Zata bullowa Al’amarin, Amma ta tarar yayi ficewarsa, takoma daki tanata nazari, daga baya ta yanke shawarar gayawa Naja halin da’ake ciki, takira Naja dakinta ta sanarda ita abunda ake ciki, Amma bata gaya mata batun Abba yace tabar masa gidansa ba Aikuwa take Naja tafara ruwan bala’i “Harni za’a ciwa mutunci dan tsabar wulakanci da cin fuska, Akaimin kudin Aure in fara shiri sannan ace anfasa saboda tsabar rashin ilimi, wannan ai halin banzane da Jahilci” Maama na kokarin yiwa Naja bayani amma taki saurararta tayi ficewarta, taje ta kira Yaya mairo a waya tana kuka gaya mata, ai tun daga wayar Yaya mairo tafara surfa zagi ta inda ta shiga bata nan take fita ba ta cewa Naja gata nan zuwa gidan. 

Jalila test kawai tayi ta dawo gida, dan har yanzu bata jin karfin jikinta sosai tanata nazari akan Jalal, mutumin daya mallaki wannan dukiyar mezeyi da wannan Aikin? Amma akwai ayar tambaya game da Al’amuran nasa, wani lokacin har mamaki yake bata in yana abun Arziki kaman bashi ba, kuma babban abun mamakin dukda yadda Jalal yake wasa da ibasa, yake shaye2 hakan besa dukiyarsa rashin habaka ba, haka taketa tunani harta koma gida, 

Amma abun takaicin tana zuwa gida ta tarar da wannan rigimar da akeyi, Hakan ya tabattar mata dasu Jawwad sun dawo, muryar Yaya mairo data jiyone yasa gabanta faduwa, dan sam bata kaunar matar nan, Jalila tana ta Addu’a ta shiga palourn, ta tarar Naja tanata kuka, yayarta sa’ada tana rarrashin ta, Maama tayi zugum Yaya mairo tana sirfa mata bala’i, Jalila tayi sallama ta maze zata wuce, Gaba daya suka dawo kanta da zagi da cin mutunci da tsinuwa, ai kawai tayi kamar kujeru ne kawai a palourn ba mutane ba, ta shige daki ta canza kaya abunta, tayi tunani a ranta muddin tacigaba da zama a yanzu, zasu cigaba da zaginta ne itakuma bazata hakura ba, dan ba shiru zatayi musu ba mussaman in aka hada da cin mutuncin iyayenta, dan data san abunda zatazo ta tarar kenan da bata dawo gidan yanzu ba, ta mike tasa hijjabinta, takuma zuwa ta ratsasu a palour tayi ficewarta tana jinsu suna ita ta haddasa komai ita tayi munafunci batabi takansu ba takara gaba. Tana fita motar Abba ta shigo layin dan haka tayi murmushi aranta tace “yau gidanmu akwai drama” ta tsaya tana jiran karasowar Abba, ya karaso kofar gidan yayi parking cikin fara’a tace

“Abba saukar yaushe?” 

Shima cikin fara’a yace “Ai tun karfe goma muka dawo, na dan fitane nayi wani uzuri” 

“Masha Allah, sannunku da Hanya, amma tunda na dawo ko Yaya Jawwad ban ganiba” 

“Ina zaki ganshi dama? Yana can farinciki ne ya hanashi fitowa Jeki aiken da’akayi miki ki dawo Akwai albishir masu yawa, babyn Ummi” 

Cikin murmushi tace “to shikenan bari inyi sauri in dawo” tafada cike da zakuwa, Abba ya shiga gida, se yanzu tafara tunanin ina zata? Kawai ta yanke shawarar zuwa gurin Mummy taji laifin da tayi mata, dukda Jalal ya gargadeta akan yin hakan. 

Tana shiga gidansu Jalal ta tarar da motarsa, abun ba karamin mamaki yabata ba, Anya kuwa yaje interview din? Ta tambayi kanta, taga moyar Mummy dasuka fita dazu alamar sun dawo, haka tayita wasi2 harta shiga cikin gidan, palourn ba kowa tayi sallama amma shiru tasamu guri ta zauna akan kujera, wata yarinya da take musu aiki tacewa dan Allah tayiwa Mummy magana, seda Jalila tayi kusan mintuna goma shabiyar sannan taga Mummy ta fito, da fara’a Jalila tace

“Mummy ina wuni?” Mummy tace

“rike ina wuninki, na baya da kikayi ma sun isa, Allah ya amfana” nan take Jalila ta sha jinin jikinta, Mummy tasamu guri ta zauna ta dubi Jalila a wulakance tace 

“Dama na kiraki naki dan inyi miki kashedi akan ďana, sannan in soke haramtacciyar alakar da take tsakanin ku” cikin rashin fahimta Jalila tace “Mummy haramtacciyar Alaka kuma?” 

“Eh haramtacciya mana, ko ta halatta ne? Tunda yake jin maganar ki fiye da tawa ai dole akwai abunda ke tsakanin ku, da kike masa Ilham ma sheda ce” 

Nan Mummy ta ware ta kwalawa Ilham kira, Ilham ta fito tana ganin Jalila ta ya mutsa fuska kaman me shirin yin amai dan taga kashi, Ilham tazo ta zauna tace “Mummy gani” 

Mummy ta nuna Jalila tace “gata nan nace Akwai haramtacciyar alaka tsakanin ta da Jalal amma ta karyatani” 

“Mummy ai kinsan ba mutunci ne da ita ba tunda bata san darajar manya ba, tarbiyya ta mata karanci” 

Mummy ta gyara zama tace “Ina bukatar duk wata alaka dake tsakanin ki Da Jalal tazo karshe a yau, kiyi nisa da dana, ba ruwanki dashi kome ze aikata, ai ba fina sonshi kikayi ba, a palourn nan agabana kinsha kiransa mara tarbiyya, lattace, kuma dan rashin kunya seki lallaba kina kokarin kara lalata min shi bayan abaya duk fitinarsa ba Ruwansa da mata, Amma kina kokarin kizama se abunda kikeso shi zeyi ni uwarsa ban isa dashi ba seke?” Jalila shiru tayi ta sunkuyar da kai ko tari kasa yi tayi 

Ilham tace 

” Wallahi Mummy na sha ganinsu suna rungume juna, kuma har part dinsa take zuwa dakin sa, in karya nayi ki karyatani mana munafuka, Kuma…… Setayi shiru takasa karasawa, sakamakon saka idonta da tayi a na Jalal dayake tsaye ya harde hannunsa a kirjinsa, ba Ilham ba hatta Mummy seda ta tsorata,  cikin is da Izza yace “Kuma me? Karasa mana” 

Zazzaro ido Ilham tafara yi, jin muryar sa yasa Jalila daga idonta sukayi ido hudu takuma sunkuyar da kai. 

Yakara so cikin palourn ya kalli Mummy sannan ya maida idonsa kan Ilham yace 

“ki karasa maganar ki ina jinki, ke dan baki da kunya har kin manta ke abunda kika dinga yimin abaya ko danni bana zuwa ina fada, wato kin manta lokacin da kike kawomin kanki har part dina in dare yayi ko?” zare ido Ilham tayi tafara kokawa da numfashi, bata taba tsammanin ze iya fadar hakan ya tona mata asiri ba

Ya kakkafe Ilham da, ido yace 

“koba ayi bane?” kasa magana tayi se wani gumi data dinga jinsa yana ratsa cinyoyinta, ya maida idonsa ga Mummy yace

“Kinji kunya, ‘yar cikinki cefa, yarinyar data dingayi miki biyayyar dani da kika haifa ban miki ba, ita kikewa wannan bakaken maganganun, meye da ďannaki da za’ a dinga, binsa, niba hankali ba niba tarbiyya ba, sedai abini ko asoni dan dukiya ta amma bani da abunda mace kamar Jalila zata bini sedai irinsu Ilham dabasu san ciwon kansu ba” gaba daya suka zubo masa ido, da sauri Jalila ta mike tayi hanyar fita, jin yana kokarin janyo mata bakin jini tana fita ya rufa mata baya, 

Ilham tace “Wallahi Mummy Jalal karya yakemin, ni ban taba kai masa kaina ba, Mummy dan Allah kisa baki ya Aureni, wallahi Asiri tayi masa” 

“ke dalla rabu dani niba wannan ne ya dameni ba, kina gani yake gaya min magana akanta, ashe har an samu uwar data haifi wadda zata mallakemin da, ya gayamin magana akanta? Baze yuwu ba wallahi, se na dau mataki akansa da ita kanta” 

Ilham ma mikewa tayi tabi bayan Su Jalal dan ganewa idonta meze faru, ayita ta kare a yau. 

Har suka fito harabar gidan yana kiranta taki tsayawa, seda yasa hannu ya fizgota sannan ta tsaya

“Jalila meye haka? Ina miki magana kina jina kinki tsayawa, uban me yakawo ki bance karki zoba dama?” 

Cikin kuka tace “Dan Allah malam kadena min shouting, meye Amfanin abunda kayi? Zaka sa mahaifiyarka da kanwarka su kara tsanata, Mahaifiyarka tace batason ganina tareda kai, ko a hanya karka kara nuna ka sanni, bani ba kai, kayiwa mahaifiyarka biyayya kanemi Aljannarka, dama ba wani abune tsakaninmu ba mutunci ne da girmamawa tunda bata so shikenan “

Gaba daya idon Jalal yayi Ja, a hankali yace

“kince kowa yaje yayi rayuwarsa ko? Kinfison in kara komawa cikin harkar shaye2 kenan kaman yadda nake abaya? Ke Garkuwa ce a taredani me kike tunani idan kika barni, sanadiyar kasancewar ki tare dani yasa ina kara kokarin yaki da shaye2 da nake abaya, kina tunanin inkika min haka kin min adalci? “

” Kayi Rayuwarka inyi tawa, yafi adinga min kallon mazinaciya, zancigaba dayi maka Addu’a a duk inda kake, Amma bani ba kai ko a hanya balle a cigaba da zargina”

Tofa!

Masoya kaunar da nake kumu tasa nai muku dogon page gashi nan, senaji Comments dinku love you all

😍😍😍🌹❤️❤️❤️🌹🌹🌹🌹

Share please 

I want comments not stickers or just thanks 

Daga alkalamin Aysher cool 

Back to top button