Sirrin Rike Miji

Amfanin ‘ya’yan kankana 7 a jikin Dan Adam:


Kankana tana da matukar mahimmacin kuma sananniya ce a cikin ‘ya’yan itatuwa, wadda ‘ya’yanta ke dauke da sinadarai masu gina jikin dan adam, kamar su vitamin B, niacin, folate da kuma irinsu magnesium, potassium, manganese, iron, zinc, phosphorus da copper.

‘yayan kankana wadan da ake kira da ‘tarbooj ke beeja’ yaren hindi, ana amfani dasu kamar a kasar Asia, a matsayi kayan abinci, inda a Najeriya kuma ake amfani da ita a cikin miya, inda man ‘ya’yan kuma ana amfani dashi a don gyara fatar jiki.

Karanta>>> Sakonnin Soyayya Na Mata Na Barka Da Shan Ruwa Ga Samarinsu 2023

 

Ga wasu daga cikin amfanonin ‘ya’yan kankana a jikin dan adam:

1. ‘Ya’yan kankana suna water da jikin dan adam da sinadaran magnesium wanda ke taimakawa zuciya wurin harba jinni da kuma magance ciwon diabetis.

Karanta>>> Maganin Toilet Infection Da Kuma Rashin Sha’awa Ga Mata

2. ‘Ya’yan kankana suna da sinadarin lycopene wanda keda kyau ga fuskar dan adam da kuma kara lafiyar namiji.

 

3. ‘Ya’yan kankana suna samar da sinadarin multivitamin B, wanda yana karawa jiki lafiyar jinin dan adam.

Karanta>>> Ga Masu Neman Karin Kiba Ga Hanyar Da Zaku Bi

4. ‘Ya’yan kankana ana amfani dasu wurin magance ciwon diabetes, idan aka tafasa ruwa ‘ya’yan kankana 1litre na tsawon mintina 45, sai a ringa shan ruwan kamar shayi.

Karanta>>> Fassarar Mafarkin Ruwan Sama 

5. ‘Ya’yan kankana suna taimakawa wurin samun karfin jiki bayan rashin lafiya sannan kuma suna kara kaifin tinani.

Karanta>>> Amfanin  Zobo Ga Lafiyar Jiki Da Kuma Illolinsa

6. Kusan fiye da rabin ‘ya’yan kankana na dauke da mai a cikinsu wanda kusan 20% sina darin Fat ne a cikin ‘ya’yan kankana wanda ke sanya girman jiki.

Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata

7. Jikin dan adam na bukatar amino acids wanda jikin dan adam baya iya bayar da irin wadannnan sinadarai sai dai daga abinci idan mutun yaci.

‘ya’yan kankana suna da irin wadannan sinadarai masu karawa dan adam lafiyar jiki da karfi.

Karanta>>> Amfanin Dabino Da Kuma Magungunan Da Yake Yi Guda 50

Allah Ya karbi ibadunmu, Amin

Back to top button