Hausa novels

Harijin Sarki Page 30 Romantic Hausa Novel

Washe gari bayan tashin lamarin hatimi, masarautar Zirkan ta tashi da firgici da ban tsoro.Sarauta tayi shiru, dabbobi sun yi tsere kamar suna gudun wani abu da ba a gani, iska ta ɗauki ƙamshin ƙasa mai ƙonewa.A cikin fadar sarki, Rashid yana zaune bisa gadon mulki, jikinsa yana daure da wani farin zani me zanen hatimin tsafinsu.Likitoci sun zagaye shi, ciki har da Samha, wadda take rike da littafin rubuce-rubucen da ta samu a cikin ɗakinsa jiya bayan haɗuwarsu da duhu.Tana karanta rubutun cikin sanyi:“Jinin sarauta biyu ne na haske da na duhu.Idan suka haɗu, ko mulki zai rushe ko duniya zata sake sabo tabbas sabon shine Ƙaddarar da duhu ta tsana.”Ta ɗago idanunta ta kalle shi, cikin damuwa tace “Sultan… wannan rubutun yana nufin akwai wani jinin sarauta daban, ko?”Ya kalleta cikin gajiyawar rai, amma idanunsa suka nuna tsoro da damuwa.“Na san akwai wanda aka ɓoye.Kuma nayi tunanin ya mutu…amma na fara jin numfashinsa tun jiya da dare.”Samha ta ɗan ja baya, tana jin sanyi yana ratsa jikinta tace “Wane ne? Kuma me yasa kake jin numfashinsa?” Rashid ya lumshe ido. Yace “Ɗan uwana… Sultan Ameer.”Cikin sauri Samha ta zaro ido ta kalleshi da mamaki, zuciyarta ta dinga dukan uku-uku.“Jin numfashinsa? Rashid… wane kake nufi?” Ya miƙe a hankali, ya ɗauki takalmin sarauta ya saka, kamar wanda yake son ya tafi wani wuri amma zuciyarsa na ja da baya.“Na daɗe ina ganin mafarki, Samha.A cikin mafarkin nan, wani yaro nake gani yana kiran sunana, yana cewa ‘ka karɓe ikon da aka bari.’Daga farko nayi tunanin saƙo ne daga ruhin mahaifina… amma yanzu, ba mahaifi nake ji ba shi nake ji”Samha ta tsaya, idanunta suka kaɗa tace. “Shi wa?”Rashid ya ɗago idanunsa, cikin rauni da murya mai cike da nauyi yace: “Ɗan uwana… Ameer.”Samha ta ɗan ja baya kamar wacce aka cusa mata wuta.“Amma Rashid… Ameer dai an ce ya mutu! Gobarar da ta ƙone sashen mahaifinku ita ta kashe shi kai ma a lokacin ka faɗi, sai Allah Ya tsare ka!”Rashid ya girgiza kai, ya furta cikin murya mai sanyi:“Ba gobara bace, Samha.Wani abu ya faru a daren nan wani tsafi da mahaifinmu ya so ya kare mulki da shi.Amma tsafin ya juyo a kansa.Ameer bai mutu ba, kawai an ɗauke shi daga duniyar nan zuwa wata duniyar duhu ta hatimin da aka ɓoye.”Sai ya durƙusa, yana riƙe kansa yace.“Na dade ina jin motsinsa a cikin ruhi, amma jiya ne karo na farko da numfashinsa ya dawo kusa da ni.Ina jin shi yana kiran sunana daga waje, yana cewa ‘Lokacinmu ya cika, Rashid.’”A hankali Samha ta matsa kusa dashi, ta riƙe hannunsa.“To me kake nufi da hakan? Me yake nufi da lokacin da ya cika?”Ya kalleta cikin idanu, muryarsa ta ƙasa.“Yana nufin lokacin dawowarsa.”Kafin su ƙara magana, sai aka buga ƙofar ɗakin da ƙarfi.Wani ma’aikacin sarauta ya shigo da gaggawa yana haki ya zube a ƙasa yace.“Mai martaba! A gaban masarauta akwai tutar da ba mu taɓa gani ba!Ana cewa wanda ke riƙe da ita yana da hatimin sarauta biyu ɗaya fari ɗaya ja!”Rashid ya tsaya cak.“Tutar hatimi biyu?…”Samha ta ɗan girgiza kai cikin tashin hankali.“Rashid… wannan alamar jinin duhu ce.” cewar Samha,Ya nufi taga da gaggawa, yana kallon nesa ya ga wani rukuni na mutane cikin baƙaƙen kaya suna tsaye,a tsakiyarsu kuma wani mutum sanye da riga me kalar ruwan shuɗi me duhu,idanuwansa suna suna haske da ja, kamar wutar da ta fito daga cikin duhu.Rashid ya faɗi da sanyi cikin murya mai ɗauke da zafi da tsoro yace “Ya tabbata… Ameer ya dawo”…..****************RAYUWAR AMEER A DUNIYAR DUHU*Wanda aka ƙone, amma bai mutu ba.”A cikin zurfin wani kogo mai baƙin duhu, ƙasa tana motsi kamar tana numfashi.Wata rana, shekaru ashirin da takwas da suka wuce — lokacin da fadar masarauta ta ƙone, wani ƙaramin yaro ya faɗi cikin ramin da aka ɓoye ƙarƙashin fadar sarauta.Wurin da ya faɗa ba rami ne na duniya ba ƙofar duhu ce.Daga nan ne Sultan Ameer ya shiga wani wuri da ba rana ko wata ke haskakawa ba sai ƙamshin wuta, hayaki, da murya.“Yaron da jini ya zaɓa… ka tashi.” yaji an faɗaYa buɗe ido, yana kallon wani hali me kama da mutum amma ba mutum ba.Idanunsa kamar duwatsu masu walƙiya, muryarsa mai cike da iko.Shi ne Sarkin Duhu, wanda ake kira Al-Mazhur — wanda ya taɓa bautar tsoffin sarakuna kafin a rufe ƙofarsa.Ameer yana rawar sanyi, yana kuka yace.“Ina mahaifina?… Me yasa komai duhu ne?… Me yasa nake numfashi amma ina jin zafi?”Al-Mazhur ya kalli yaron cikin taushi da ɗan tausayi na mugun hali.“Saboda kai jinin sarauta ne kuma an ƙi karɓar rabinka.Jinin haske na Rashid ya fi, amma na duhu… shine naka.”Ameer ya ɗago kai cikin hawaye yace “To me yasa sai ni?”“Saboda jarin zuciyarka. Duhu baya samun iko sai akan wanda zuciyarsa ta yi kuka da gaskiya.”Daga wannan rana, Al-Mazhur ya fara horar da Ameer.Yaron ya koyi karanta kalmomin da zasu iya narkar da ƙarfe, ƙulle zuciyar mutum, ko canza surarsa.Shekaru suka ja, Ameer ya girma cikin wuta, yana ɗauke da zafin ƙiyayya da rashin amincewa.Lokacin da yake cikin shekaru talatin da bakwai, sai Al-Mazhur ya bashi hatimin duhu — alamar ƙarfin da ba kowa yake rayuwa da shi ba.“Hatimin nan yana da ikon rushe mulki da kafa sabo.Amma yana da sharadi guda ɗaya zai ci gaba da rayuwa ne idan zuciyarka ba ta da soyayya.”Ameer ya ɗauki hatimin ya saka a kirjinsa, sai wata rana ya farka yana jin numfashin Rashid daga sararin duhu.Ya zuba ido a cikin madubin wuta, yana ganin ɗan uwansa yana zaune a gadon sarauta cikin haske da mutane.Yana rayuwa, yana da kowa, yana da duniya…Ni kuwa, a nan cikin duhu nake, ina cin abincin ruhohi.”Sai ya kalli sama mai duhu, ya ɗaga hannunsa cikin murya mai ƙarfi.“Na rantse da jinin da muka fito daga shi Zan dawo, Rashid!Zan dawo in karɓi rabona na duniya, koda kuwa da jini ne!”A wannan lokaci, duhu ya fara juyawa kamar guguwa, Al-Mazhur ya bayyana, yana dariya.“Idan ka fita daga nan, ba zaka iya komawa da sauƙi ba.”“To ba na son dawowa.”“To sai ka bi ƙa’ida ka sha jinin wanda kake son maye gurbinsa.Sannan nan zaka iya rayuwa a sarautarsa.”Ameer ya saki murmushi me taushi da mugunta.“ Zan sha jinin ɗan uwana.”ƙofa ta buɗe da haske mai baki, iska ta tashi daga ƙasa ƙofar dawowarsa duniya. Wannan rana ce ta farko da duniya ta sake jin kamshin jinin duhu bayan shekaru Ashirin da takwas.

Back to top button