Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 52 Complete Novel

*ASM Bk2052*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

…………. Lokacin da suka iso Katsina wannan dalilin ne yasa lokacin da Fatuu ta tambayi Abbas da gaske an fasa auranta yace mata eh amman an d’aura da shi haka da zata bi su Mino lokacin da Abbas yazo kai su suga gari ta saka fitted gown Yadikko tay magana kan rashin dacewar ta fita da rigar da d’an k’aramin gyale har gwaggo ta saka baki k’arshe dai saidae ta canza kaya haka lokacin da Haisam ya kirata vedio call da tace fushi take dashi har bacci ya kwashe ta ya kai hannu yana zagaye lips d’in ta saman screen lokacin duk matar shi ce ita, bayan an samu natsuwa su Yadikko sun koma aka fara shirin cigaba da karatun Fatuu lokacin gwaggo ta nemi Abbas yazo suka zauna a parlor bayan sun gaisa ne ta fad’i mashi dalilin kiran nashi dama kan Maganar sakin Fatuu ne don suna shirin cigaba da karatun ta kuma ga aure akan ta shiyasa take so ya tuntu6i Haisam da Maganar dama sadakin shi na nan a wurin Baffan ta za’a maido mashi amman sai yace shi yana ganin ba sai an yi mashi magana ba tunda ai yasan da auren shi a Kanta kuma dole zata cigaba da karatu don haka a k’yale shi taci gaba kawae cike da damuwa gwaggo tace “amman baka ganin akwae had’ari ace ta tafi wani gari karatu da auren da bata san dashi ba a kanta ni ina ganin d’ana Abbas gara ai mashi Magana ya saki kaman yadda aka tsaran” Abbas d’in ya nuna mata shi fatan da yake dama auren ya d’ore ba wai su rabu ba gwaggo ta hau girgiza kai tace “gaskiya ni bana son hakan duk da zan yi matuk’ar farin ciki in ta samu miji kamar shi to amman ana barin halak ai ko don kunya yanzu in matar shi tasan da Maganar auren da wane ido zan kalleta ita kanta zata ga an ci Amanar ta ba kamar yadda ta d’auke ni tamkar itama ni kakarta ce” cikin kwantar da murya Abbas yace “gwaggon mu wannan duk ba abun damuwa bane in dae Allah ya kaddaro dama zasu kasance miji da mata ai mu bamu isa mu hana ba kuma duk abunda zamu yi yanzu wllh bamu isa mu raba ba don haka mu bar ma Allah komae shi zai shige mana gaba kiga komae yazo da sauk’i” ba don taso ba tace mashi shikenan amman dae gaskiya bai kamata ta tafi wani gari karatu da aure a kanta ba shine ya kawo mata shawarar Fatuu ta fara yin School of Nursing tunda an kusa fara yin Medicine anan ko bayan ta gama ne sai tayi k’arshe gwaggon ta amince ta kuma rok’e shi kan ya taimaka mata wurin kula da Fatun yace in sha Allahu, tun daga wannan lokacin duk abu in ya shafi Fatuu sai gwaggo ta tuntu6i Abbas ko lokacin da zasu bikin Haulat Nijar sai da tay mashi magana shi kuma ya kira Haisam don neman izini lokacin yace mashi duk inda zasu suje ba sai an rink’a tambayar shi ba ya bada izini haka lokacin da taso zama a Hostel farko gwaggo tak’i amincewa tace saidae in ya kama ko zasu yi wani abun kaman yadda ta fad’a mata daga baya ta tuntu6i Abbas da Maganar yay ma Haisam Maganar shi da kan shi yace abarta in dae tana so ta zauna shiyasa gwaggon ta k’yaleta take zama saidae duk da haka tana saka ido sosae a kanta kaman wurin sa kaya da kuma tabbatar da tana a Makarantar duk da ta yarda da ita sosae.

 

 

***** ****** *****

 

Suna isa Abincin Haisam ya hango Dr Habeeb a bakin main Entrance gefen shi nurses ne guda biyu suna ruk’e da gadon d’aukar mara lafiya ya nufi inda suke ya parker a gefe ko kashe Motar bai yi ba ya fito lokacin itama Hajiya ta bud’e kopar bayan ta fara K’ok’arin fitowa, d’ayan side d’in Haisam ya nufa yaima nurses d’in alamar su zo suka turo gadon zuwa inda yake bayan ya bud’e kopar ya duk’a ciki ya cicci6o Fatuu da take a kwance ba numfashi ya juya ya d’aurata akan gadon Dr Habeeb ne ya basu umarnin su nufi Amenity da ita ya juyo kan Haisam da Fuskar shi ta bayyana tashin hankali hakan yasa ko gaisawa basu yi ba ya tambaye shi abunda ke faruwa nan yay mashi bayanin cikin da ke gareta da kuma yadda ta fara zubda jini sakamakon razana da tayi saidae ya nuna mashi akwae yuwuwar tayi wani abu dama don ta zubar da cikin da sauri yace mashi su je suka nufi ciki gwaggo da Hajiya ma suka rufa masu baya, lokacin da suka isa har an shigar da ita d’aki an kwantar da ita Dr yaba d’aya daga cikin Nurses d’in umarnin abubuwan da zata kawo mashi da sauri ta amsa ta juya da d’an gudu gudu ya kalli Haisam yace su jira ya shige d’akin dama d’ayar Nurse din na ciki bada jimawa ba wadda ya aika ta dawo ta shige had’i da maida kopar ta rufe, tsaye duk sukae kowa ya jingina da bango ga seats nan na zaman jira amman duk sun kasa zaunawa Saboda fargaba da ta cika kowannan su Hajiya sai k’wafa take tana kai hannu tana ruk’e ha6arta da bakin ta gwaggo dae tayi jugum sai ido kawae ita kadae tasan halin da take ciki sai Addu’oi take a zuciyarta Haisam kuma ya d’age face d’in shi sama yana kallon ceiling yayin da hannuwan shi ke zube a cikin Aljihunan jeans d’in shi, sai bayan kusan 15 minutes Dr ya bud’e kopar ya fito da sauri Hajiya tace “Dr ya ya?” d’an murmushi yay yace mata lafiya lou in sha Allah ya juya kan Haisam da ya sauke face d’in shi yana kallon shi yace mashi bari ya gan shi a Office aikuwa a harzuk’e Hajiya tace “Dr kamar ya ka gan shi a Office baka ga yadda duk muka damu bane har ma mun fi shi shiga damuwa duk abunda zaka fad’a mashi ai mu ya cancanta ka fad’a mawa ba shi da yayi silar jefata a halin da take ciki ba saboda son zuciya har da ma wannan” ta kai Maganar tana nuna gwaggo da sandar hannunta sadda kai k’asa gwaggo tay ita kanta ta k’osa taji halin da Fatun ke ciki ganin yayi shiru yasa Hajiya cewa suna jin shi a wane hali take ciki ne gyara tsayuwar shi yay yace “ta razana sosae ne shiyasa tay doguwar suma hakan kuma ya haddasa mata bleeding d’in da take don cikin dake jikinta ya fita amman akwae yuwuwar dama anyi kokarin zubar dashi don bleeding d’in yayi yawa ace iya razanar tasata zubar da jini haka sosae amman mun samu jinin ya rage ita kuma har yanzu bata farfado ba amman dae ba wani abu zata farfado in sha Allah yanzu tana buk’atar Oxygen don level d’in nata yayi k’asa sosae sannan already an samata drip yanzu tana buk’atar jini kusan leda biyu….” Tun kan ya rufe baki Hajiya ta shiga nuna mashi Haisam da sandar hannunta tace “gashi nan ja shi ku tafi a de6i nashi in ma fiye da leda biyu ake so duk shi zai bada su” Dr dake d’an murmushi yace “ai Hajiya sai in yayi daidai….” Katse shi tay da fad’in “ko ma bai yi daidai ba ku d’iba sai kuyi ma canza ku bata wanda yay daidai da nata, amman in fad’a maka gaskiya bai dad’e daya tashi daga jinya ba don haka ku binciki jinin in ba wata cuta kar aje a d’irka mata wani abun ya faru a lik’a man sharri nima a saka ni cikin wad’anda suka cuceta” d’an ta6e baki Haisam yay yayi ma Dr alamar suje da hannu yana murmushi suka tafi nurse dake ruk’e da jinin Fatuu da aka d’iba tabi bayansu suka nufi Lab, bayan sun je aka d’ibi jinin Haisam d’in duk aka gwada aka ga zai iya bata kuma cikin sa’a bai da ko malaria har Dr Habeeb na cewa da yake ba anan yake zaune ba shiyasa bai da yar Malariar zamani shidae d’an murmushi kawae yay sai kuma yace mashi a ka’ida leda guda yakamata ya bata Haisam d’in yace in dae za’a iya samun leda biyun a d’iba kawae Dr yace shikenan aka fara shirin d’ibar jinin baida yadda zai yi duk irin kyankyamin shi haka ya kwanta akan gadon, ana gama d’ibar leda guda wata irin juwa ta taso mashi har ya kasa jurewa saida ya kai hannu ya dafe forehead d’in shi Dr Habeeb na ganin hakan ya tambaye shi halan bai ci Abinci ba sai lokacin ya tuna da baici Abincin rana ba an dae siyo mashi bai kaiga ci ba Fatuu taje mashi da zancen cikin da ke gare ta, kai ya d’aga mashi alamar eh Dr d’in yace yana zuwa ya fita bai d’au lokaci ba ya dawo ya kawo mashi Maltina da cake yace bari aje a fara saka mata wanda aka d’iba ya d’aga mashi kai, Bayan an tafi a d’ibi jinin Haisam d’in Hajiya da gwaggo suka shiga cikin d’akin gwaggo ta tsaya daga gefen gadon idonta akan Fatuu dake kwance ido a rufe kanta ba kallabi gashinta ya tarwatse, a gefen gadon Hajiya ta zauna fuskarta cike da tausayi ta kai hannu ta shafa fuskar Fatun tana Fad’in “Baiwar Allah Fateema hakanan an d’auki alhakin ki ana neman asa ki rasa rayuwarki gashi ansa kin aikata babban laifi in ke kika zubar da cikin koda yake su Allah zai kama da laifi ba ke ba….” Haka tay ta surutai gwaggo dae tay shiru, Dr na fitowa ya nufi Amenity anan suka had’e da Abbas daya shigo ya nufe shi bayan sun gaisa fuskar shi d’auke da damuwa ya tambayi Dr d’in abunda ke faruwa don yaga Motar Haisam a waje alamar suna Asibitin nan ya kwashe komae ya fad’i mashi da tsananin mamaki Abbas ya maimaita Zarah ta samu ciki, jin yadda cikin ya zube ne yasa bai nuna farinciki ba tare da Dr suka nufi Amenity d’in, bayan sun shiga d’akin wata uwar harara Hajiya tabi shi da ita nan take yasha jinin jikin shi ya gaishe da gwaggo da ke zaune kan yar doguwar kujerar da take cikin d’akin da d’an murmushi ta amsa yace ya mai jiki kafin ta bashi amsa Hajiya ta amshe da fad’in “Mai jiki da kuka jefe halin da take ciki? to ai gata kana gani don haka sai ka ba kan ka amsa ba sai ka tambayi wani ba” hannu ya kai ya d’an sosa k’eyar shi ya gaishe da ita tay banza da shi ta kya6e baki Dr Habeeb ya wuce ya fara kokarin sama Fatuu jinin bayan ya gama zai fita Abbas na niyyar bin bayan shi Hajiya tace ya tsaya zatai magana dashi yace to, bayan fitar Dr tana mashi wani mugun kallo tace “Yanzu Abbas abunda ku kai kun kyauta, domin Allah kun kyauta ma Fateema dubi halin da kuka jefa yar mutane kiri kiri kusa yarinya tay ta yawo da aure a kanta ba tare data sani ba taya zaku aikata wannan d’anyen aiki haka??” d’an rankwafar da kai yay yace “Wllh hajjaju gaba d’aya hakan ya faru ne Saboda samun mafita gudun jefa rayuwar ta a matsala……” Nan ya kwashe yadda komai ya faru ya sanar da ita cikin fushi tace “to ai gashi nan matsalar da kuke gudan mata ku kun jefata a wata shi kuma in bada niyyar rabuwa da ita ya aure taba ai sai ya fito ya bayyana ma Mutane duk abunda zai faru ya faru yafi da ya kama baki yay shiru shi ga miskili sannan kuma yay kwance kwance ya d’irka ma yar mutane ciki ba kunya ba tsoron Allah banda fyaden da yay mata, iya cuta dae wllh an cuci Fateema kuma harda ku a cutar da ita don haka ku zauna da shirin in dae wani abu ya sameta ba fata nike ba sai an bi mata hakkinta, a ina aka ce don yarinya matar ka ce ka afka mata hakan ai bashi da maraba da fyad’e” kan Abbas na sadde k’asa haka ma gwaggo jin tayi shiru yasa ya d’an d’ago don duk kunya ta rufe shi ya shiga bata hak’uri yana fadin sun yi kuskure ta ta6e baki tace su dae suka sani ita dae ai yanzu jiran Fateema take sumi sumi ya juya ya nufi hanyar fita bayan ya fito ya nufi Lab duk ran shi ba dad’i, sosae baiji dad’in yadda Al’amarin ya kasance ba kamar cikin da ya zube, lokacin da ya isa d’akin da Haisam yake a lab yana shiga suka had’a ido dashi ya jingina da bango hannun shi ruk’e da abubuwan da Dr ya kawo mashi yana ci a hankali Abbas ya shiga da yar sallama can k’asan mak’oshi ya amsa mashi ya nufi inda yake ya zauna daga bakin gadon yana kallon shi da yar damuwa yace mashi sannu kai kawai Haisam d’in ya d’aga mashi suka d’an yi shiru idon Abbas akan shi shi kuma ya maida nashi k’asa can Abbas yace “ashe haka abu ya faru ba dad’i yanzu Hajiya ta tutsiye ni tana ta fad’a” ido kawae Haisam ya bi shi dashi Abbas dake kallon shi yace “to wai ya akai hakan ta faru ba tare da ka warware mata komae ba, nasan da kayi mata bayani duk hakan bazata faru ba” still idon ya bishi dashi ba alamar zai tanka mashi wata yar dariya Abbas yay yace “look dude ba fa wata fuska da zaka man bayan ka aikata 6arna ka cuci yar mutane kaja har muma ta shafe mu” shigar da lip d’in shi na k’asa yay ya d’an ciza suka bi juna da ido Abbas nata sakin murmushin iskanci can ido a d’an lumshe slowly yace “What do u want me to say Abbas? It was intentionally or what?” Abbas dake murmushi yace “kusan hakan mana in ba da niyya ba mi zai sa ka aikata?” Still idon shi na akan shi ya d’an ta6e baki kafin yace “isn’t as u think, it was mistake” Abbas yace “to ya akai har kai irin wannan kuskuren, ni mamaki na a ina hakan ya faru ko a part d’in naka” ya k’arasa yana yar dariyar iskanci d’an langa6ar da kai Haisam yay kaman bazai tanka shi ba ganin haka yasa Abbas gumtse Dariyar yace ya bari don Allah ya fad’a mashi don kan shi ya daure sai da yay d’an Jim kafin a nutse ya soma bashi labari tun daga barin su wurin dinner d’in Prince da dalilin kaita G.r.a d’in har zuwa yadda Al’amarin ya fara cike da damuwa bayan yazo nan a bayanin yace “I don’t know what came over me and how everything happen dat way, i completely lost control as if my life depends on it dat moment….” dakatawa yay ran shi a 6ace Abbas nata girgiza kai had’i da d’an murmushi Haisam d’in ya cigaba “She said she was pleading me then I dont even heard her” yar Dariya Abbas yay mai d’an sauti Haisam d’in ya jefa mashi wani kallo mai kaman Harara cikin dariyar yace “Da alama akwae bambanci kenan?” Ya d’age ma Haisam d’in gira d’an guntun tsoki yay sai kuma yay d’an murmushin gefe had’i da juyar da kan shi, hannu Abbas ya kai ya dafa k’afar shi guda da ya mik’ar a saman gadon yace “Wllh H,Zakee ba wani abu bane face rabo Allah ya k’addara a wannan ranar a kuma daidai wannan lokaci Mom Zarah sai ta samu cikin ka shine kawae kuma Allah ya kaddaro dama can ita matar ka ce shiyasa wata kil hakan ya faru don asiri ya tonu” shiru bai ce komae ba dae Abbas ya dasa “amman miyasa daga baya ba kai mata bayani ba har abun ta kasance haka” sigh yay yace “ranar da hakan ya faru naso in mata hakan but tana cikin mawuyacin hali gashi ta matsa sai ta tafi gida don ni bamma san lokacin da ta je gate ba saida security yazo ya sanar dani bayan na fita naso mu koma ciki a lokacin I intend to explain myself but sai tak’i and banso muyi jayayya don dare yayi sosae ga security zai iya tunani na daban shiyasa nai mata yadda take so sai ma dana fara kaita hospital don tay shedding blood sosae” d’an bud’a ido Abbas yay fuskar shi tay yanayin tausayi ya hau girgiza kai can yace “to amman daga baya fa, da kai mata bayani ko kuma ni kayi man magana nayi mata na tabbatar da bata yi tunanin yin abortion ba in shi d’in tayi” hannu yasa ya d’an shafo forehead d’in shi kafin yace “a ranar nima kwana nay ban lafiya dama tun da abun ya faru naji ni abnormal daga baya fever mai tsanani ya rufe ni wurin Asuba sai ga kira daga Mom ta sanar dani halin da Dad ke ciki so I have no option dole in tafi muna zuwa can nima ciwo ya rufe ni kuma harda abunda nay ma yarinyar ke damuna duk da nasan mata ta ce amman nasan ban kyauta mata ba hakan ya k’ara worsen condition d’ina bayan na d’an samu sauk’i na Kirata amman tak’i picking dama ko ranar da abun ya faru na kira bata yi picking ba, a lokacin da ina can da ta d’auki wayan zan mata bayani ne in ma bata yarda ba zance taje ta tambayi grandma d’inta so ganin bata d’auka ba I just decided in rabu da ita in na dawo sai in mata bayanin komae” Abbas dake ta kallon shi jin ya dakata yasa shi cewa “to amman data gane tana da cikin bata sanar da kai bane?” Yanayin face d’in shi ne ya k’ara canzawa yace “Yau d’in nan nasan da Maganan Abbas, ta same ni can G.r.a lately anan take sanar man tana ta ciwo a School har an fara rumours d’in ciki ne da ita shine ya ja hankalinta……” Nan ya kwashe yadda sukai da ita d’azun ya sanar mashi Abbas sai girgiza kai yake har ya gama sannan cike da damuwa yace “Wllh harda rashin rabo Allah ya k’addaro dama ba za’a haife shi ba saidae Al’amarin ya bayyana kawae” shima Haisam d’in ran shi a d’an 6ace yace “with her stubbornness also, if she had listened to me this wouldn’t hv happened……” Shiru yay bai k’arasa ba ya juyar da fuskar shi ganin yanayin shi yasa Abbas cewa “Kayi hak’uri nasan dole kaji ba dad’i kaga tak’i jin Maganar ka amman na tabbatar in ma zubar da shi d’in tay tayi hakan ne don Saboda ku duka bazata so sunan ku ya 6aci ba tunda kallon da take ma cikin bana halal bane” shiru bai ce mashi komae ba kafin Abbas ya k’ara cewa wani abu Dr Habeeb ya shigo ya nufo su da d’an murmushi kallon Haisam yay da shima ya kalle shi yace ya gama ya d’ibi d’ayan kai ya d’aga mashi Abbas yay saurin tambayar wani jinin za’a d’iba yace mashi eh cewa yay a d’ibi nashi in zai yi Dr yay yar dariya yace “Malam bari dae a diba nashi d’in tunda akwae don na tabbatar ko naka yayi sai an samu Malaria a ciki” dariya sukae gaba d’aya shidae Haisam d’an guntun murmushi kawae yay, bayan an fara d’ibar jinin Dr ke tambayar Abbas wai mara lafiyan matar H,Zakee ce yace mashi eh ya sake cewa amman yaga kaman ba itace suka je bikinta ba Abuja yace mashi eh wannan Amaryar shi ce da d’an murmushi yace “ai da yake su manya ne shiyasa har ya k’ara, itama wanccan din ai Amaryar ce tunda duka yaushe akai bikin” Murmushi kawae Abbas yayi bayan an gama d’iba saida ya zauna ya huta sosae lokacin Dr ya tafi daga baya suma suka mik’e Abbas nata mashi sannu saidae ya d’aga kai kawae bayan ya tashi tsaye Abbas ke ce mashi yakamata yaje yay wanka ya canza kaya don jini ya 6ata mashi gefen hannun shi da gefen rigar shi saima lokacin shi Haisam d’in ya lura yace suje Office d’in Dr ya wanke hannun zuwa anjima yaje yayi wankan Abbas yace to yasan in ba don ta kama dole ba ba yadda za’ai Haisam ya zauna da rigar nan, bayan sunje ya wanke suka nufi d’akin da Fatuu take lokacin da suka shiga jinin da aka saka mata nata shiga jikinta tunda Hajiya ta kalle su sau d’aya ta kauda kai Gwaggo ce tai mashi sannu ta mik’e tace suzo su zauna har yace tay zamanta tace zata shiga toilet ne lokacin Magrib ya yi ta nufi toilet d’in su kuma suka zauna yana ta kallon Fatun can suka had’a ido da Hajiya tana hararar shi ya sunkuyar da kan shi k’asa Abbas dae sai d’an murmushi yake, fitowa gwaggo tay tana gyara hijab d’in jikinta bayan ta daidaita ta kalli Abbas tace suje suyi salla kar lokaci ya shige ya amsa mata da to hannun shi ruk’e dana Haisam suka mik’e suka tafi gwaggo ta kalli Hajiya tana son yi mata magana amman tana jin shakka can dae ta tay k’arfin halin ce mata an fara kiran salla a fad’ace tace tana ji ai d’an murmushi gwaggo tay ta k’ara ce mata ga Hijab nan a jikin kujera ta d’aukko mata tace bata so ai batasa ta ta d’aukko mata ba yadda take Maganar ta d’aure fuska irin tayi fushin nan kwantar da Murya gwaggo tay ta shiga bata hak’uri har saida taga ta d’an saki Fuska ta fara k’ok’arin mik’ewa sannan gwaggon ta nufi gefe ta kwanto kallabinta ta shimfid’a ta kabbara salla, suna fita yace ma Abbas ya tsaya nan yay salla shi bari yaje yayi wanka sai ya dawo Abbas d’in yace to suje tare mana yace No ya tsaya koda za’a buk’aci wani abu sannan yace Ok sukae sallama ya tafi, ana gama sallar Abbas ya koma d’akin nan gwaggo tasa shi ya kira mata Amadu don ta baro wayarta a gida har Hajiya ma bata zo da waya ba a gida ta baro ta tun lokacin da Haisam ya sanar mata zancen cikin Fatuu, bayan ya kira ta fara ringing ya mik’a mata yana d’auka yaji muryar gwaggo ya hau tambayar ta ya Fatuu ko gaida ita bay ba dama tunda suka tafi hankalin shi ba kwance yake ba k’arshe ma kulle shagon yay ya koma gida bayan ya shiga kuma hankalin shi ya k’ara tashi haik’am ganin d’igo d’igon jini a tsakar gidan har zuwa cikin Parlor, saida ya gyara duk inda ya 6aci sannan ya shige d’akin shi ya kwanta cike da zullumi gashi duk yaga wayoyin su a Parlor balle ya kira yaji halin da ake ciki, jin yanayin muryar tashi tace mashi ya kwantar da hankalin shi da Sauk’i sosae ana mata k’arin jini ne cike da damuwa yace mata zasu iya yin Magana tace ai bata kaiga farkawa ba tukun, nan tace mashi ya zubo Abinci a Warmer da plates ya kawo da ruwa sannan ya d’aukko abun salla da buta da kayanta kala d’aya sai bargo ya tambayi Asibitin da suke sai lokacin ta tuna da bai sani ba ta fad’a mashi yace to, Haisam na barin Asibitin G.r.a ya nufa bayan ya shiga Bedroom d’in shi dole wanka ya fara ya zura jallabiya kafin yay sallar Magrib anan cikin dakin don lokacin ta ya shige, bayan ya sallame zaune yay jigum duk ya rasa mike mashi dad’i daka kalle shi zaka fahimci yana cikin damuwa don fuskar shi ta nuna, ya d’an d’auki lokaci a haka kafin yay Addu’a ya mik’e ya nufi cikin Corridor, sanye cikin wasu k’ananan kayan ya fito fess da shi ya d’auki Car key da wayarshi ya fita, saida ya tsaya yay sayayya mai yawa su lemu da ruwan roba katan katan da uban fruit harda gasassun kaji da balango mai yawa sannan ya wuce Asibitin, bayan ya isa ya parker Motar ya fara d’aukar lemu da ruwan ya shiga dasu lokacin Amadu har ya k’araso yana zaune cikin d’akin yay zugudum sai kallon Fatuu yake Haisam na shigowa ya mik’e da sauri yaje zai amshi abunda ya shigo dashi yana gaishe shi amsawa yay yace ya bashshi yaje Mota akwae wasu ya d’aukko ya amsa da to da sauri ya juya ya fita shima ya k’arasa ciki gwaggo na mashi sannu da zuwa cikin cool voice d’in shi ya amsa ya gaishe da ita kafin ya gaishe da Hajiya dake zaune akan Carpet d’in da Amadu ya kawo gwaggo ta mik’e ta koma gefen gado tace ya zauna, bayan ya zauna d’akin yay tsit Amadu ya dawo ruk’e da manyan ledoji ya aje a gefen inda sauran kayan suke ganin yay tsaye Haisam yace yazo ya zauna mana ya nufi gefen shi ya zauna shiru ta sake biyo baya har aka fara kiran sallar isha lokacin Haisam yace ma gwaggo ga kaya nan nasu ne tay mashi godiya ya mik’e ya fita Amadu ma ya bi bayan shi, bayan sun gama sallar isha ta bud’e ledojin ta d’aukko plate ta fara zuba ma Hajiya koda ta mik’a mata cewa tay bata ci da alama dae ran ta ya 6aci sosae hak’uri ta shiga bata suna haka suka dawo daga Masallaci harda Abbas nan fa ya sa baki aka cigaba da ba Hajiyar hak’uri sannan tace taji zata ci, k’ara zuba wani tay taba Amadu ya kai ma su Abbas harda Fruit d’in shima Amadun ta zuba ma shi kowa ya fara ci banda Haisam da tunda aka kai masu Abbas ya aje a tsakiyar su yay mashi magana sai yace ya fara ci yay zaune shiru idon shi na kallon floor gwaggo ta lura da bai ci hakan yasa tay mashi magana tana lallashin shi kan yaci kar yunwa tay mashi illa dama gashi bai warware sosae ba ga kuma jinin shi an d’iba da yawa jin haka yasa Hajiya ta ta6e baki tace “ai itama wadda ya kwantar bata ci ba waya san ma ko duk yau bata ci komae ba don haka ki rabu dashi” shiru gwaggo tayi shi kuma ya d’aga ido ya kalleta suka had’a ido tana ta tura baki yanayin fuskar shi ne ya d’an canza kamar zai yi murmushi amman bai bayyana ba sai daga baya ya fara ci a hankali don yana jin yunwa sosae kuma d’akin fess yake tamkar ba Asibiti ba ko d’azun gab da Magrib saida aka shigo akai Mopping tiles d’in kasan da bazai ma ci ba, wurin k’arfe tara Dr Habeeb ya shigo ya duba ta ya sanar masu da ta farfad’o don numfashin ta ya dawo bacci take yi yanzu ko wane lokaci zata iya farkawa shi lokacin tashin shi yayi amman akwae Doctor da yazo in da wani abu sai ai mashi Magana ga Nurse nan zata cigaba da kula da ita sukae mashi godiya Abbas da Haisam suka raka shi ita kuma Nurse d’in ta gaishe dasu tay masu ya mai jiki duk suka amsa tace zata tafi amman zata rink’a lek’owa in kuma da wani abu sai ai mata magana tana a Nurses station gwaggo ta amsa da to ta juya ta tafi, bayan wasu mintuna Haisam ya dawo shi kadae ya tsaya a gefe cikin girmamawa yace ma gwaggo su je Abbas na waje zai maida su gida tana jin haka tace mashi a’a Don Allah suje su ita zata tsaya ta kwana tun kan ta rufe baki a harzuk’e Hajiya tace “Yau naga ikon Allah ni Hauwa, shin wai shi d’in ba mijinta bane kuma shine sanadin kwanciyar ta to waya kamata yay jinyar ta dama bashi ba ko kuwa ya ja ma yar Mutane wahala sai kuma yaje yay share share akan gado yana bacci to kuwa bai isa ba shi zai zauna yay jinyar ta duk da kema bai kamata kiyi baccin ba shima Abbas d’in muje ya kaimun dole ya dawo nan ai jinyar ta dashi” tana gama Magana ta fara k’ok’arin mik’ewa duk gwaggo bata ji dad’i ba wllh don Haisam d’in na buk’atar isasshen bacci saidae ba yadda ta iya dole tabi Maganar Hajiyan itama ta mik’e ta d’auki kayan da Amadu ya kawo mata na sawa amman banda su bargon dama Amadu a tsaye yake sukai mashi sallama yana tsaye ya d’aga masu kai sai da ya raka su bakin k’opa yay tsaye har suka bar wurin sannan ya koma ciki, bakin gadon ya nufa ya tsaya hannuwan shi zube cikin Aljihun jeans d’in shi yanata kallonta bazaka iya karantar yanayin fuskar shi ba ya d’an d’auki lokaci a haka kafin yay yar ajiyar zuciya ya kai hannu ya shafi forehead d’in shi kafin ya juya walking slowly ya koma kan kujera ya zauna, suna hawa hanya Hajiya ta amshi wayar Amadu ta kira saude bayan ta d’aga ta gaishe da ita tace mata taga bata ganta a gida ba ko abu ne na gaggawa ya taso shiyasa batai mata ko sallama ba ta fita Sauden tay Addu’ar Allah ya maido ta lafiya tace ai gata nan ma a kan hanya so take tay sauri ta feraye dankali tay Faten shi yaji Alaiyahu sai kuma ta d’ibi yan ciki tay d’an ferfesu karta 6ata lokaci don Allah da sauri ta amsa mata da to ta kashe wayar, su gwaggo aka fara ajewa kopar gida sukai ma Hajiyar saida safe ta amsa ba yabo babu fallasa aka wuce da ita su kuma jiki a sanyaye suka nufi cikin gida gwaggo taso taga tashin Fatun, bayan sun isa gidan Hajiyan sawa tay dole Abbas ya tsaya har aka gama Abincin don ma ba me d’aukar lokaci bane aka zuba a k’ayatattun Warmers Saude ta bi shi dasu har zai fita daga parlon Hajiya ta tsaida shi tace ma Saude ta je ta daukko mosquito spray bayan ta kawo ta ba Abbas d’in tace gashi nan a fesa a d’akin kar sauro ya ciji Fateema ya k’ara mata wata cutar banda wadda suka jaza mata shi dae d’an murmushi kawae yay yasan harda don Haisam ta bada shi yay mata saida safe ya tafi Saude na biye dashi ruk’e da basket d’in Warmers suka nufi Mota, yana shiga ciki sai ga kiran gwaggo tace ya wuce ne yace mata a’a yanzu dae zai tafi tace to don Allah ya d’an tsaya zata bashi kayan Fatuu akai mata in ta farka sai ta canza yace to, lokacin da ya tsaya horn yay Amadu ya fito ruk’e da yar jaka mai d’auke da kayan Fatuu harda undies da pad bayan ya saka a back seat yay mashi saida safe ya juya shi kuma yaja Motar ya tafi, lokacin da isa Asibitin k’arfe goma ta wuce bayan ya Parker ya fito ya bud’e back door ya fiddo basket d’in kayan Abincin da jakar ya rufe ya nufi ciki, Haisam na zaune kan kujeran ya d’an kishingid’a had’i da lumshe ido Abbas d’in ya shigo da yar sallama ya bud’e idon a hankali ya kalle shi Abbas d’in ya d’an yi mashi murmushi ya nufi inda yake, a gaban kujeran ya aje kayan hannun shi ya zauna gefe idon shi akan Haisam yace mashi sannu ya jinjina mashi kai nuna mashi kayan yay yace ga Abinci nan da kayan matar shi an ce inta tashi ya bata ya kuma taimaka mata tay wanka ta canza kaya wani kallo yay mashi Abbas d’in yay dariya kafin ya juya ya kalli Fatuu ya d’an girgiza kai ya juyo yace ma Haisam wai har yanzu bata farka ba ya d’aga mashi kai yace “Allah sarki Mom Zarah wllh na tausaya mata sosae Allah ya bata lafiya” shiru Haisam d’in yay Abbas yace “bazaka amsa ba ko baka so tay saurin samun sauk’i ka maida bugu nan da nan asamo mana twins” still banza yay mashi fuska a d’aure Abbas ya tuntsire da dariya yace “Serious kasan wani rabon na kore wani fa gashi Mom Zarah na fahimci ba ta wasa bace da an bata take amsa” d’an k’ank’ance ido yay yana kallon shi Abbas d’in sai dariya yake can slowly yace ya tashi ya tafi gida dare yayi Abbas d’in yace wato ya ishe shi kenan daga yana taya shi hira ya rage kad’aici yace mashi ya gode bacci yake ji ne Abbas d’in ya fara kokarin mik’ewa yana fad’in ai shikenan, tare suka fito saida ya raka shi har bakin Mota Abbas ya bud’e ya shige driver seat yay mashi saida safe ya juya ya koma ciki, yana shiga d’akin ya k’ulle kopar ya nufi kujerar ya zauna idon shi akan Fatuu can kuma ya kai hannu ya dauki wayar shi ya fara lallatsawa bayan wani lokaci ya ajeta don bacci yake ji daurewa kawae yake mik’ewa yay ya d’auki bargo ya shimfid’a a saman kujerar kafin ya kwanta saidae bata d’auke tsawon shi ba gaba d’aya a hankali ya fara lumshe ido yana yi yana bud’ewa har baccin ya d’auke shi, Misalin k’arfe sha d’aya da yan mintuna ta fara mutsu mutsun farkawa slowly ta fara bud’e idanuwan ta tana yi tana sake lumshe su a haka har ta bud’e su gaba d’aya akan ceiling d’in d’akin ta k’ura ma Fanka ido tana kokarin gano a ina take, d’ago hannuwanta tay duka jin su kaman ba daidai ba nan idonta ya sauka akan kanular dake a jikin kowanne nan take ta gane inda take, sauke su tay ta fara juya kan ta a hankali tana bin d’akin da kallo har idanunta suka sauka akan Haisam da idanun shi ke a rufe wani irin bugu kirjinta yay ta k’ura mashi ido lokaci guda abubuwan da suka faru suka fara dawo mata har zuwa lokacin data san shi Mijinta ne ta shiga tunanin ashe duk abubuwan da yake mata Saboda wannan dalilin ne ita bata sani ba tay wani tunani na daban a hankali ta saki d’an murmushi tana cigaba da kallon shi zuciyar ta na raya mata yanzun nan shi Mijinta ne wani irin dad’i take ji a cikin ranta can kuma ta tuno da Maganganun da ta gaggaya mashi a G.r.a nan take yanayin fuskar ta ya sauya damuwa ta bayyana tamkar yaji ajikin shi tana kallon shi ya fara motsi yana kokarin bud’e ido sam ta kasa janye idanunta kirjinta sai bugu yake da sauri da sauri a hankali ya bud’e idanun suka sauka akan ta ya bita da kallo suka zuba ma juna ido………..

 

….

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button