Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 38 Complete Novel

*ASM Bk2038*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

 

 

 

…….Da k’yar taja k’afafunta ta koma kan kujera ta fad’a da6as duk jikinta yay weak ta kasa gane wannan bak’in Abubuwan da yake mata na miye, bai jin komae yanzu yake ta6a ta ga wani irin kallo da yake mata wanda ada sam ba irin shi yake mata ba, shiru tay kamar mai nazari can wata zuciyar ta ayyana mata kodai son ta yake tunda ada da bai mata hakan ai ba son ta yake ba kuma ko Fanan da tazo itama yana ta6a ta lokacin kuma soyayya suke can kuma wata zuciyar ta tuno mata da labarin Fauzy wanda itama ai tace Mujaheed na ta6ata kuma k’arshe ya yaudareta, rasa tunanin ainihin dalilin canzawar Haisam d’in tay k’arshe jiki a sanyaye ta mik’e ta d’auki laptop d’in bayan ta kashe hasken parlon ta nufi d’akinta don ta san tuni gwaggo tay bacci, kayan jikinta ta cire ta sa na bacci ta haye gado sam tunanin Haisam yak’i barinta wani iri take ji ran ta sai bata yake ko dae da gaske son nata yake in kuwa haka ne da zata yi farinciki to amman mizai sa sai yanzu zai so ta bacin yana da mata wata zuciyar ta k’ara raya mata nan fa ta shiga wasi wasi k’arshe ganin tana neman harmutse kwakwalwarta da tunane tunane ta bar ma ran ta ba son ta yake ba kawae, Fauzy ce ta fad’o mata a rai tay tunanin ko ta kirata ta sanar mata game da zuwan shi sai kuma ta ayyana kamata yay ta bata surprise suje tare da shi to amman ya zata yi wata zuciyar tace in kince ya kai ki ai zai kai ki ne, d’an murmushi kawae tay k’arshe ta jawo d’ayan pillow dake gefen kanta ta rungume shi sosae ta lumshe ido a haka bata san lokacin da bacci ya kwashe ta ba, Haisam na komawa part d’in shi ya nufa duk da bai dad’e da yayi wanka ba da zai je gidansu saida ya k’ara watso ruwa ya fito d’aure da farin towel a k’ugun shi ya nufi press don saka sleeping dress, yana gamawa ya nufi switch ya kashe hasken d’akin kafin ya kunna bedside lamb guda d’aya ya haye gado ya kwanta yana facing sama da alama dae Haisam ya d’aura aure da tunani yana haka wayarshi ta fara ringing ya kai hannu gefen shi ya d’auka sunan Lovely Wife ya bayyana wato Fanan ce ta kira picking yay yasa speaker ya aje wayar kusa da kan shi cike da k’auna ta fara Magana tana nuna yadda tay missing nashi shima yace yayi nata ta tambaye shi ya akai bai bacci ba ko rashin ta by his side ne ya hanashi yi d’an murmushi kawae yay sai kuma yace mata Yeah, haka suka cigaba da hiran yawanci itace mai Maganar shidae saidae yay murmushi mai d’an sauti ko ya bata amsa a tak’aice daga baya sukai sallama har tana ce mashi zata zo a cikin dream d’in shi tayi mashi duk abunda ya kamata yana murmushi ya furta mata Ok had’i da take care, yana cire wayar ya aje akan bedside ya koma yana facing sama kaman da farko had’i da lumshe ido saidae bansan ko duniyar tunanin ya k’ara tafiya ba ko kuma baccin ya yi ba.

 

Washe gari sai wurin k’arfe 10 na safe Fatuu ta tashi tunda weekend ne ba school, bayan tayi breakfast ta fara gyara gidan zuwa k’arfe sha d’aya da rabi ta gama komae taje tayo wanka ta shirya cikin short skirt da yar vest zaman school ya koya mata sa guntayen kaya dama kuma zafi ake, saman gado ta haye ta d’auki wayarta ta fara lallatsawa nan ta fara doubting na kota kira Haisam d’in tayi mashi Maganar zuwa gidan su Fauzy ko kuwa ta k’yale shi,to in ta Kira kawae sai tace tana son ya kaita gidan k’awarta ita bata iya zuwa ne dole zai ya kaita haka tay ta wasi wasi can dai ta yanke kiran nashi lokacin da kiran ya shiga yana zaune a Parlor bai jima da gama yin Breakfast ba anan part d’in na shi don ko kayan ma ba’a kaiga zuwa an d’auke ba yanata Operating system jikin shi sanye da farar jallabiya jin ringing d’in wayar yasa ya kai hannu gefenshi ya daukkota ya kalli screen d’in kafin yay picking yasa speaker ya aje ta agefen laptop d’in d’an shiru sukae Fatun ce ta fara cewa “Ya Haisam ina kwana an tashi lpy” amsa mata yay da “Alhamdulillah and how was ur night?” Itama tace Alhamdulillah sai kuma tay shiru shi kuma yana ta lallatsa computer d’in gabanshi rasa ta yadda zata fad’i mashi tay sai kawae tace “d..dama na kira in k’ara maka godiyar Laptop” jinjina kai yay tamkar tana gani sai koma ya furta is Ok suka k’ara yin shiru can taji ya furta “then What else?” d’an gwale ido tay jin ya gano akwae abunda take son fad’a cikin yar inda inda tace “d….dama so nike in ba damuwa ka kaini gidan wata k’awata zaku gaisa da ita na ta6a bata labarin ka” shiru yay ita kanta sai taji kaman she sounds stupid da ta fad’i mashi hakan can taji yace “Magana ta kike da wasu kenan” rud’ewa tay bata zaci zai fad’i hakan ba cikin shaky voice tace “a…a wllh Ya Haisam kaji na rantse ni ba Maganar ka nike yi ba ita kadae ce itama don k’awata ce sosae kuma saida taga pic d’in ka a waya na ne ta tambayeni na fad’a mata kai yayana ne shine…shine…” sam ta rasa mi ma zata ce, shikam d’an ta6e baki yay fuskarshi d’auke da d’an murmushi can taji ya kira sunanta “Zarah” kaman zatayi kuka tace “Na’am” yace “unhun am listening shine what” abu ta had’iya da k’yar tace “na fad’a mata lokacin baka K’asar kayi Aure, kawae dama don ku gaisa ne amman a bashshi ma” still murmushin yake yi kafin yace “by what time?” d’an waro ido tay had’i da yin d’an murmushi tace “duk lokacin da yayi maka ni yau ba abun da nike yi” taji yace “is it Ok by 4:00?” Da sauri tace eh yayi yace Ok till then tayi mashi godiya kafin ta kashe wayar yaci gaba da latse latsen shi, murna ce ta lullu6eta bayan ta gama ta fad’a saman gadon harda su mirgina mirgina can kuma a fili ta furta “Ya Haisam kai na daban ne wllh I so much luv u” ta rungume hannayenta a k’irji had’i da runtse ido. Misalin k’arfe hud’u saura kwata ta gama shiryawa har Salla tayi kaya kawae ya rage ta saka tay tsaye gaban wardrobe d’inta tana tunanin wanda yakamata ta sa, in ta janyo wannan sai taga bai yi ba ta maida ta fiddo wasu sai faman ruwan ido take k’arshe dai ta fiddo wasu riga da skirt na atampa da bata ta6a saka su ba cikin kayan da Chairman ya bata, atampar na da zanen flowers army green da kuma light green ba k’aramin amsarta kayan sukai ba dama kuma saida aka aunata kafin aka yi su, yar light make up tayi tasa yan kunne da sark’a silver sai Agogo haka gyale da jaka da takalma duk mahad’in kayan ne takalman half cover ne masu tsini jakar ma mahad’insu ce bata sa turare sosae ba don gwaggo ta hana ta iya roll on ta goga sai ta shafa Humra a jiki kayan kuma dama suna sakin kamshinsu sakamakon turaren kaya da suke amfani dashi, k’arfe hud’u saura yan mintuna da basu wuce 2 ba sai ga kiran shi yace in ta gama yana waje tace to, bayan ta fito saida ta lek’a d’akin gwaggo don yi mata sallama dama tun lokacin da tay Magana da Haisam d’in ta sanar mata, sosae gwaggo ta hau yabon kyaun da tay tana ce mata sai kace Amarya ita dae Fatuu sai dariya take har waje gwaggo ta biyota ta tsaya a bakin kopar d’akinta tana kallon Fatun cike da jin dad’i har ta fice sannan ta koma ciki, tunda ta fito ya kai idonshi kanta ta zagayo ta gaban Motar ta zo d’ayan side d’in duk idonshi na akanta saidae ita bata gani don glass d’in blacktinted ne, bud’e kopar gaban tayi ta shiga bayan ta rufe ta juya da murmushi ta gaida shi shima kallonta yake ya jinjina mata kai kawae wani abun mamaki sai kace yasan kayan da zata saka don kuwa shima wani d’anyen Voile ne army green ya saka sumar nan tasha gyara hatta Agogo da takalman kafarshi duk army green ne sosae kayan suka fito mashi da farin shi ita kanta Fatuu a cikin ranta saida tay mamakin kalar kayan ganin sun hau dana jikinta sosae, saida suka hau hanya idon shi akan titi ya tambayeta ina zasu tace mashi Goruba road yaci gaba da tafiya ba tare daya ce komae ba, tsit kake ji ba wanda ya k’ara cewa uffan Fatun ta juyar da fuskarta tana kallon hanya yayin shi kuma yake driving saidae akai akai yake d’aga ido ya kalleta ta cikin mirror a haka har suka iso ita ta rink’a nuna mashi hanyar da zai bi har suka k’araso gaban gidan ya parker, da murmushi tace mashi zata shiga tay mata magana ya d’aga mata kai ta fita idon shi akanta, da sallama ta shiga Parlon gidan saidae ba kowa a ciki ta wuce d’akin Fauzy ta tura kopar da yar sallama ta shiga lokacin Fauzy na kwance saman gado tayi rubda ciki wayarta ruk’e a hannu da alama wani abu take kallo tana sanye da doguwar rigar material koda ta d’ago taga Fatuu ce mai yin sallamar wata yar k’arar farinciki ta saki ta saukko da gudu ta tarbeta, kama hannunta guda tay tana k’are mata kallo kafin tace “Yar matar nan wai kinga kyaun da kika yi kin wanku wllh sai kace wata Amarya” dariya Fatun tayi Fauzyn ta sake cewa “koda yake in sha Allahu Amaryar ce ta Ya Haisam da zai yi” zaro ido Fatuu tay ta d’an bud’e baki tace “ki rufa Asiri kar Aunty Fanan ta ji mu” yar dariya Fauzy tay tace “to sai me in Allah ya k’addaro ai bata isa ta hana ba wllh duk min kishinta” Fatun tace “amman dae Fauzy ai ana barin halak ko don kunya ko” wani kallon kina da hankali tay ma Fatuu tace “Halak….Kunya, ke yanzu idan yazo yace yana son ki zai aure ki sai kice a’a kenan duk da son da kike mashi Saboda matar shi?” Fatuu tace “Uhmm Fauzy mubar Maganar nan tunda bai ce ba d’in, ni kinga zo muje waje zaki gaisa da wani ne” da mamaki ta maimaita wani kuma Fatun tace mata eh still da mamakin ta sake ce mata wanene tace tazo dai suje ta gani ta juya taje ta d’aukko gyale ta dawo suka nufi waje tana ce ma Fatun kodae Sabon saurayi tayi ita kuma tay murmushi tace suje dae, tunda suka fito take bin Motar da kallo duk ta k’agu taga wanene a ciki a tare suka isa driver side d’in yana ganinsu a bakin kopar Motar glass d’in ya fara sauka slowly lokacin da fuskarshi ta bayyana mutuwar tsaye Fauzy tay har saida kirjinta ya buga don bata ta6a kawo ma ranta irin halittar da zata gani kenan ba jin saukar muryar Fatuu tay tace “Fauzy ga Ya Haisam ya zo” tana murmushi tay mata Maganar har saida ta had’iye miyau Kutt kafin tay murmushin yake tamkar yar koyo tace “Ina wuni Ya Haisam an zo lafiya” da k’yar ta k’arasa a haka ma ba k’aramin kokari tay ba wurin daidaita Maganar amman duk da haka saida muryarta tay d’an rawa cikin cool voice d’in shi yace “lpy ya School” wohoho Fauzy na ganin Mujaheed ya gama had’uwa acikin Mazan Nigeria to yau ga Kakanshi ta gani wanda komae nashi mai tafiya da mutum ne amsa mashi tay da Alhamdulillah ya jinjina mata kai kawae daga haka bai k’ara cewa komae ba, a hankali ta matso gefen Fatuu cikin rad’a tace “bari in yi ma Aunty Mareeya Magana su gaisa don Allah na bata labarin da muka yi da ke” bata jira cewar Fatuu ba ta juya da sauri ta tunkari gate shi kam bai ma san suna yi ba don ya maida kanshi jikin Headrest, bata dad’e ba ta dawo tun daga bakin gate d’in tay ma Fatuu alamar su shigo ta juya ta kalli Ya Haisam d’in sai ma ta rasa ya zata ce mashi can dae ta kira shi ya juyo da face din shi kanta cikin yar inda inda tace wai zai shiga su gaisa da Auntynta da take zaune wurin ta wani kallo ya bita dashi da sauri ta sunkuyar da kanta k’asa can taji yana kokarin bud’e Motar ta d’ago da sauri sai kuma taja gefe ya fito, alamar suje yay mata da kai tay gaba yana biye da ita suka nufi gidan, lokacin da suka shiga Parlon da yar Sallama ya shiga Aunty Mareeya dake a tsaye da fara’a ta shiga yi mashi sannu da zuwa ta nuna mashi wurin zama ya zauna itama ta zauna gaidashi tay duk da da gani ta girmeshi tayi mashi an zo lafiya ya iyali a nutse ya amsa mata shiru ta biyo baya idonshi a kan carpet Fauzy ta fito ruk’e da k’aton tray data d’auro ruwa da lemu ta d’aura saman c-table Aunty Mareeya ta kalli Fatuu dake zaune tace “Zarah zuba mana” tana niyyar tashi ya dakatar da ita ta hanyar d’an d’aga mata hannu ya furta “am Ok” Aunty Mareeya na murmushi tace ai yakamata yasha ruwan zumunci ko yace bai jin kishi ne can kuma sai ya mik’e yay mata sallama itama ta mik’e tana mashi godiya ya fita, kallon juna sukae su duka ukkun Aunty Mareeya ta d’an gwalo ido har saida ta basu dariya su duka tace “Zarah dama Akwae irin wad’annan Mutanen a Nigeria” Fauzy ta kar6e “wllh Aunty nima lokacin da ya sauke glass nay arba da face d’in shi har tsoro naji nafa san shi a picture amman gaba d’aya ban gane shi ba don sai naga ma ya fi kyau a fili…..” Aunty Mareeya ta sake cewa “Tubarkallah ma sha Allah kai kace hausa bazata fito daga bakin shi ba koda yake ai kun ce ruwa biyu ne koma ace ukku, Zaraah banga laifin ki ba wllh kin yi namijin kokari da kika iya danne son shi baki furta mashi ba ai inni ce wllh ban san lokacin da zan fad’a mashi ba” gaba d’aya suka sa dariya dama Aunty Mareeya yar barkwanci ce anan Fatuu ta gaya ma Fauzy zancen Laptop d’in daya kawo mata ta hau murna tana fad’in su Shar sun yi computer suma Aunty Mareeya ta hau yabon kirkin shi tana fad’in ita ko a labari bata ta6a jin mutum da ya had’a abubuwa irin nashi ba ga kyau ga kud’i ga tsananin kirki k’arshe ta hau yi ma Fatuu Addu’ar Allah ya mallaka mata shi in rabon ta ne Fauzy ta amsa da Amin ita kuma tay murmushi kawae can tace bari taje kada yay ta jiranta Aunty Mareeya harda fad’in yi maza kar ki rink’a 6ata mashi rai kita mashi biyayya har mu samu yazo hannu duk suka kwashe da dariya, tare da Fauzy suka fito lokacin ya rufe glass d’in side d’inshi suka zagaya d’ayan side d’in Fatuu ta bud’e ta shiga Fauzy ta d’an rankwafa tana ce mata sai sun had’u a School ran Monday kafin ta kalli Haisam tay mashi sai anjima da godiya, kud’i ya mik’a ma Fatuu yace ta bata yan dubu dubu ita kanta bata san ko nawa bane lokacin har Fauzy ta juya Fatun ta kirata ta juyo ta mik’a mata tace in ji Ya Haisam waro ido tay alamar mamaki sai kuma ta amsa ta sake lekawa tay mashi godiya kai kawai ya d’aga ba tare daya kalleta ba, a d’an can gefe ta tsaya saida taga tafiyar su sannan ta nufi cikin gidan da gudu a Parlor ta iske Aunty Mareeya bata shiga ciki ba ta nufeta tana dariya ta d’aura mata kud’in saman jikinta tace shi ya bata, hannu tasa ta ruk’e haba Fauzy ta zauna gefen ta da yake saman 3 seater take nan suka dasa hirar Haisam har Aunty Mareeya na cewa wannan dole ma Matar shi ai tay kishin shi. Bayan sun baro Unguwar EE ya wuce da ita tunkan ya tsaya Fatuu ta fara yin Murmushi tunawa da randa ya zo da ita, bayan yayi parking a parking space ya kalleta yace su je a tare suka fito suna shiga entryway ya nufi shagon saida wayoyi Fatuu ta bishi lokacin da suka shiga da fara’a masu shagon suka tarbeshi suna mashi sannu da zuwa ya amsa kafin ya tambayi wanda ke gabanshi ko sun kawo iPhone 15 yace mashi a’a amman in sha Allahu gobe zata iso akwae ma wad’anda suka bada akawo masu zai iya yin payment shima ya fiddo card ya mik’a mashi ba 6ata lokaci ya fitar da kud’in ya bashi receipt yace a zo dashi goben ya furta Ok daga haka suka fito, waje suka nufa wurin packing space ya bud’e ya saka receipt d’in da aka bashi a shagon waya Fatuu na tsaye gefe ya juyo bayan ya rufe Motar suka kalli juna Calmly yace mata yana son shiga gym ko zata jira shi a pack wani kallo tay mashi kafin ta d’an tura baki tace ita mi zata yi a park kaman wata k’aramar yarinya komawa yay ya jingina da jikin Motar ya bita da ido kawae ganin kallon da yake Matan ne yasa ta yamutsa fuska tace “Ko fa da can ma da muka zo ai na girmi wurin balle yanzu” d’an murmushin gefe yay ya jinjina kai kaman bazai ce komae ba sai kuma yace to ta shiga Mota su tafi da sauri ta kalleshi tace ina ya bata amsa da gida tana kallon shi tace ya fasa yin gyming d’in ko zai dawo yace mata yadda ya yuwu ganin zai bud’e Motar duk sai bata ji dad’i ba don sai take ganin kaman zata hana shi yin abun da yake so da sauri ta dakatar dashi ta hanyar fad’in “To muje gym d’in tare mana ba sai in tsaya wurin Aunty Anah ba” juyowa yay ya kalleta Calmly yace “bata nan yanzu” tace tana ina ya bata amsa da dama Service ya kawo ta garin ta d’an zauna yanzu ta koma garin su, jinjina kai Fatun tay tace “Allah sarki Aunty Anah, to ai nasan baka rasa sanin wasu ba sai ka had’a ni da su ba nima inyi exercise d’in dama wllh ina d’an jin nauyin jikina” d’age gira yay yana mata wani kallo tace “bafa zanyi bane da kaina sai a koya man nike nufi” kaman bazai ce wani abu ba sai kuma yace “taya zaki da wannan dressing d’in?” Yay tambayar yana mata nuni da kan shi ta d’ukar da kanta ta kalli kayan jikinta skirt din straight skirt ne yay mata k’yam a jiki ko tafiya da sauri bata tunanin zata iya yi balle kuma exercise d’agowa tay ta bishi da ido kawae ya juya zai bud’e Motar ta sake tambayar shi tafiya zasuyi baza su je gym d’in ba yace ta shigo zasu je su dawo ne tace to ta zagaya ta shiga, yar tafiya sukai bayan sun bar wurin ba mai tsawo sosae ba suka iso bakin wata plaza yace su je ta bud’e Motar, Wani k’aton shago suka nufa wanda kayan sports ne kawae a ciki shak’e, bayan sun shiga ya gaisa da masu shagon ya fad’i masu irin kayan da suke so aka d’aukko masu kamar kala biyar don su za6a da kai ya nuna ma Fatun yace ta d’auki wanda take so ta bishi da kallon mamaki don bata yi zaton inda zasu zo ba kenan k’arshe ta zabi wasu riga da wando rigar tight long sleeve ce sai wandon ta shigen wanda Fanan ta ta6a sawa a gabanta, bayan ya biya su aka saka masu a babbar leda mai tambarin wurin suka fito, within Few minutes suka dawo EE d’in yace ta d’aukko kayan suka nufi ciki, lokacin da suka shiga gym d’in a bakin bangaren mata ya tsaya ya fiddo wayarshi ya kira wata mai suna Deborah yace ta fito yana son Magana da ita suna gama wayar sai gata ta fito cikin shigar gym tana ganinshi ta washe baki tana gaishe da shi ya amsa, nuna mata Fatuu yay yace pls ta shiga da ita ta taimaka mata tay gyming bata iya ba da sauri ta amsa da Ok ta kai idonta kan Fatuu lokaci guda taga kaman ta san Face d’inta can ta tuna tace mashi kaman itace suka ta6a zuwa ko yace mata yeah sosae tay mamakin ganin girman da Fatun tay ta gaishe da ita ta amsa da fara’a ta kama hannunta suka shiga shi kuma ya wuce side d’in su dama ya taho da jakar shi komae na ciki har kayan da zai canza, bayan su Fatuu sun shiga ne ganin bak’uwar fuska yasa aka fara tambayar Deborah bak’uwa akayi ne tace eh, wad’anda suka dad’e suna zuwa wurin tay masu bayanin kowacece nan fa suma sukai ta mamaki suna fad’in ta girma ita dae murmushi kawae take, wata k’opa Deborah ta nuna ma Fatuu tace change room ne taje tasa kayan tace to ta nufi d’akin after some minutes sai gata ta fito uhmm nasan ko ban fad’a ba kowa yasan kayan zasu yi mata kyau ko don dirinta zo kaga idanu gaba d’aya ta janye hankulan su nan fa aka shiga yabawa ana Maganar shape d’inta duk da kasancewar ta mai k’ananun shekaru gashi dama kanta ba kallabi shima gashin ba’a k’yale shi ba sai da suka tanka ganin abun yayi yawa yasa Fatuu ta rink’a fad’in Tubarkallah a hankali, Sosae tay exercise d’in kuma ta matuk’ar jin dad’i don komae ta iya a nutse Deborah ta kokkoya mata cike da kiyayewa gudun kada a sake samun matsala,Sai lokacin da aka tashi sannan suka dakata ganin kowa na fita a yadda yake yasa Fatuu yin tunanin ba sai tasha wahalar mayar da kayanta ba tunda ga gyale sai tay rolling d’in shi kawae ta shiga ta d’aukko kayan data cire dama ta saka su a cikin ledar kayan, lokacin da ta fito Deborah na tsaye tana jiranta da murmushi ta ce suje H.zakee na nan waje yana jiranta suka nufi hanyar fita, yana d’an can gefe suka fito suka nufe shi idon shi akan Fatuu har suka k’arasa Deborah na murmushi tace mashi gata nan tayi kokari don ta iya komae kuma tayi sosae ya d’aga mata kai kafin ya furta mata thanks tay masu sallama ta tafi, kallonshi Fatuu tay tana murmushi ganin sun yi tsaye tace su tafi tana kokarin yin gaba kawai taji ya kamo hannunta guda yay pulling d’inta back har saida ta d’an bangaji gefen jikinshi, zaro ido tay tana kallon shi lokaci guda hankalinta ya tashi ganin kallon da yake mata ya d’an 6ata rae ta fara tunanin mi tayi mashi a kausashe taji yace “How can u go out like dis!” Sai da yay Maganar ta fahimci laifinta murya na d’an rawa tace “n…naga wai Mota zamu hau ne kuma nasa gyale” kallonta kawae yake wai tasa gyale komi wannan d’in yay mata ganin ta d’an tsorata yasa shi sassauta d’aure fuskar da yay yace “amman haka kika fito gida?” da sauri ta girgiza mashi kai ita sai lokacin ma ta tuna da ba hakan ta fito ba da sauri tace bari taje ta maida kayanta ta juya sam ya kasa janye idon shi daga kanta har ta shige wurin, lokacin data fito ta maida kayanta bata ganshi a wurin ba hakan yasa ta nufi hanyar fita saida ta fita can waje ta hango shi a tsaye jikin Mota yana ganinta ya bud’e ya shiga itama ta k’arasa ta bud’e ta shiga ba tare da ya ce mata komae ba yaja suka tafi…

?

.

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button