Kanwar Matata Complete Document
Description/Story:
Kanwar Matata! Complete Hausa Novel Document Written By Fateema S. Omar
Description
🌻🌻 *KANWAR* *MATATA* 🌻🌻
Story and writing
by
*FATEEMA* *S* *OMAR*
Alhadullih Allah ya bani ikon Nakammala *DR* *AMEENA* lafiya kuma Allah yasa sakon da nake son isarwa ya isa gareku kuma xakuyi anfani dashi
yau ina dauke da sabon labari me suna
*KANWAR* *MATATA*
Allah yaba ikon rubuta alkari aciki ameen
*PAGE* *1* *-* *2*
*BISMILAHI* *RAHAMANIR* *RAHIM*
————📖Wata budurwa ce ta fitu daga bed room tana sanye da pink shirt sai trouser black iya kuwa yayi mugun kamata ko hula babu akanta
kyakykyawace sosai sade ba fara bace sosai
*MA’ISHA* ke nan budur war da baxata huce 17 years ba
kai tsaye kitchen ta nufa
ta had’awa tea tafito parlour ta xauna akan canter carpet ta aje cup d’in a ta fara danna phone d’inta
tana danna phone tana shan tea a hankali
sada ta shanye tea d’in tas san-nan tashi ta kuma bed room
tana shiga ta tadda *SAFNA* ta fito daga toilet tana daure da tawol ajikinta kalonta
*MA’ISHA* tayi tace “sister har yanxu baki shiryaba ko tu indai ya *MA’IN* ya dawo kinsan baxaki fitaba” murmushi *SAFNA* tayi tace ” hhmm inbanda abunki *MA’ISHA* ai fitata taxama dole sabuda kinsan jiya kwana nayi ina xaxxab’i kuma dai kinsan ba’a son masu ciki dayin xaxxab’i” “hhmm nidai inaso inga ranarda xaki haihu sister tunyanxu yana k’arami ma ana wan-nan rawar kan inada anhai feshi ra nar sai Allah ciwon mai iyali” dariya aunty Safna tayi tace “kedai bari y’ar uwa nima na k’agu naga na haihu inga wai nice da baby ranar sainayi kukan dad’i” “to Allah ya kaimu time d’in”
haka sukaringa hira har aunty Safna ta gama shirinta tsaf ta tafi huspital
bata dad’e da dafita ya *MA’IN* ya dawo a parlour ya yada xangu
ya ciro phone d’in shi yakira Safna tace mishi ita bata dawoba saida sukasha hirar *love* san-nan sukayi salama
kira ya k’ara dannawa amma harta yanke ba’a d’auka ba
tsaki ya ja yak’ara danna kiran amma shiru ba adaukaba dan haka yafara kiranta ahankali *MA’ISHA* amma bata amsaba ba tsaki k’ara ja yamike yanufi bed room d’inshi saida yayi wanka ya sauya kaya ya k’ara fitowa parlour amma ba mutsin mutun a cikin gidan
room d’in aunty Safna ya nufa kai tsaye
baiyi tunani komaiba ya kutsa kai ciki
tana kwance akan bed tayi d’aid’ai tana baccinta hankali kwance
ajiyar xuciya yasauke ya k’arasa kan bed d’in yafara k’iran sunanta ahankali *MA’ISHA*
cikin bacci taji ana kiranta ahankali ta bude white eyes d’inta tayi manya dasu ta xuba mishi wani irin sihirtaccen murmushi yayi yace “baby kinaji ina kiranki amma ko ki amsa ko” wani dugun tsaki taja tamike xaune tana laluben hijab d’in da xatasaka
ta d’auko xata sake nan yayi saurin riketa ya kwace hijab d’in ya mannata da jikinshi yana cewa “haba baby me kike kok’arin rufewa bayan kinsan cewa duk wata gab’a ta jikinki mallakinace nan gaba to mexaki b’uyemin bayan duk kayanane” tureshi tafara kokarinyi amma sai ya k’ara rungumeta sosai ta kasa kwacewa kalonshi tayi idonta taf da kwalatace “waikai wanne irin mutunne da kaje islamiyya ba dasainace jahilci ne yake damunka amma kanada hankali kanada ilimi amma kake abu irin wadda ko axamanin jahiliyya banji tarihin wadda yayi irinshi ba” sakinta yayi tayi saurin mikewa ta tashi daga kan bed d’in ajiyar xuciya ya sauke yace “Allah ne ya jarabeni da sanki *MA’ISHA* bayi kaina bane kuma duk da ke *KANWAR* *MATATA* ce amma inada tabbacin xan malakeki kuma karki manta cewa nida Safna auren xumunci akai mana ba na soyayyaba ke kad’aice burin raina inaso ki bani had’inkai ki karb’i soyayyata nikuma namiki alkawarin aurenki”
hara rarshi tayi tace “inkai idonka yarufe akan soyayya kanason sab’awa Allah to nida hankalina kuma ni ba jahila bace danhaka baxan iya karb’ar soyayyarka ba saidai in itace sanadin mutuwarka to Allah ya jikanka”
wani irin murmushi yayi xaiyi magana phone d’inshi tafara ruri
xarota yayi a aljihu ya kara akunne yace “hellow, ok ganinan xuwa” yana gama fad’in haka ya kashe wayar ya dubeta yace “baby duk kincinyemin time ku abinci banciba amma bakomai ganinkima ya kusar dani to kixo in miki kiss na bye bye ko” wani irin kalo tayi mishi
yayi murmushi yace to shike nan xamu hade ne yanxu sauri nakeyi yana gama fad’in haka ya fice daga room d’in
ajiyar xuciya ta sauke ta kuma kan bed d’in ta xauna tayi ta gumi tana tunani irin abunda xai faru in aunty Safna tasan abunda ke faruwa gata damugun kishi hhmm “Allah ka taima keni” ta furta a fili
4:30pm aunty Safna ta dawo gida ta tadda *MA’ISHA* axaune tayi ta gumi ku shigowarta bata ganiba
dafata tayi tace sister me yake damunki figigit ta dawo daga duniyar da tatafi
xama tayi kusa da ita tace “haba sister baki tab’a b’uye mini komaiba amma wan-nan karan kina b’uye min wani abu”
kai ta xirgixa tace” walahi bakomai aunty kawaidai bana jin dad’ine sosai” “ayya to sannu kitashi ki je kikwanta ki huta” kai kawai ta gyada ta mike ta shige room d’inta Safna ta bita da kalo
danjinta kawai tayi amma duk time d’in data fita unguwa to haka take xuwa ta tadda ita
time d’in da ya *MA’IN* ya dawo har *MA’ISHA* taware sunfara hira da aunty Safna
a parlour ya tadda su sunata hira harda dariya
k’arasowa yayi kusada aunty Safna ya rungumuta jikinshi yanacewa “my lovely darling hira kukeyi keda kanwartawa” ya k’arasa maganar yana kalon *MA’ISHA* yana wani murmushi da shi kad’ai yasan ma anarsa
kauda kaitayi cike dajin haushisa
aunty Safna ya kala yace jeki had’omin tea xansha
mikewa tayi tanufi kitcking
tashi yayi yadawo kusada *MA’ISHA* yakamu hannunta yace “baby me yasameki naga duk kin had’ade rai konine namiki laifi innaimi afuwa” tsaki taja ta kwace hannunta ta tashi
dasauri ya jawota ta fad’a jikinshi
wani irin duba tamishi xatayi magana sukaji salamar aunty Safna……….!
karku manta yanxu aka fara
File Name | Kanwar Matata… Hausa Novel Doc. |
Title | Kanwar Matata Complete |
Author | Fateema S. Omar |
Group | Ai Hausa Novels |
Genre | Fiction Story |
Published Date | 17/07/2024 |
File Size | 113KB |
Format Size | TXT |
Book Price | Free |
Phone No |
Download Yaroma Namijine Complete Novel Document By Aisha Aliyu Garkuwa
Click the below green button to read the novel online
Proceed with your download by clicking the below button
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.