Description/Story:
Yar Aikina! Complete Hausa Novel Document Written By Maman Teddy
Description
💕 ‘ *YAR* *AIKINA* …💕
(my house maid…)
Story and written by Aisher moh’d
Maman teddy🧸
*GODIYA*
Ina mika godiyata ga allah wanda yabani ikon fara littafinnan lfy allah yabani ikon gamawa lfy…
Gareku iyayena abun alfaharina ina godiya da tarbiyan da kuka bani tundaga tasowata haryanzu allah yaja kwana yakara budi amen…
*DEDICATION*
I dedicate this page for you Sweat lailah love you so much🥰😘
Wannan labarin kirkirarene ba fasahan wani acikinta…
Wannan labarin na kudine xaka turo #100 mawannan number airtel 08021737594.
______________________________
بسم الله الرحمان الرحيم
Free page
1️⃣➖2️⃣
Kaimashi horo sosain gaske,aina fadama baban shi inhar yakasa sai na ballashi, sannan xaidawo gida.dan haka ku karkaryamun shi saiku kaishi tukur-tukur Zaria.
“cewan captain Anwar abdulrahim”
Ok sir, “cewan sojojin daya basu command”
Nan yajuya hadi dashiga barrack din sojojin.
Yana shiga parking space yadosa hadi da bude motanshi yashi yabata Iska…
Kaitsaye gidan iyayensa ya nufa,bai isa ba sai wurin 12pm.koda yaisa part dinshi yanufa,yana shiga sojojin gidan suka biyoshi dakayansa duda bawasu kayabane.
Umarni yayi masu suka aje suka fita hadi da jawo mai kofa.
Directly bed room yanufa,yanashiga yacire kayanshi na sojoji sannan yayi privacy don ya watsa ruwa.
Bayan yagama alwala yadauro hadi da yin sallah,bayan Ya idarne yabi lfyan gado tare da tunani iri-iri,ahaka har bacci ya kwashe shi…
Dasafe daya yatashi,privecy yanufa hadi da dauro alwala,bayan yagama shiryawa direct part din mom Ya nufa.a hanya ma’aikatan gidan kowa saurin gaishe shi yakeyi tun kan ya karaso inda suke.xakaji ana gaisheshi,kowa na tsoran masifan shi,ahaka yaisa part din mom…
Yana Shiga mom na sakkowa nan tahau cewa sojana saukan yaushe,tana maganan hadi da nuna tsantsan farin cikin ganin dan nata tilo.
Saurin isa inda mom take yayi hadi da hugging dinta,”sai yace”da daddarene mom shiyasa banta shekiba…
Nan tacema house maid da su shiryama Anwar breakfast.nan suka shirye-2,kafin lokaci kadan sungama komai nan suka isar ma hajiya…
Nan”tace” son xomuje kayi break,mikewa yayi tare dabin mom xuwa dinning area..nan tahau serving din dannata ahaka yafara cin abyncin yana ci suna fira da mom,itako mom dadi yahanata cin abuncinnata.
Bayan ya kammalane suka koma dakin mom suka cigaba da fira…
“mom tace”son yaya mimi kaga kariketa tsakani da allah,kacigaba da hakuri da ita,koda mukace ka aureta bamuce ka wulakanta Taba,kodan kaga tana sonka kar yasa karinka wulakanta ta.
Ok mom”cewan Anwar”wanda lokaci daya idon shi yakada,tabbas baxan manta taba arayuwata.maganar mom yakatsemai tunaninshi.
Mom ne”tace”anwar jiya mukai magana da mimi takecemun rabonka da gida kusan wata uku.haba anwar ina ilimunka yake,baidace karinka yiwa mimi haka BA. tafada hadi da kallon anwar da kyau,nan taga kwallah yaciko mai ido,gashi idon shi yaxama kaman gauta saboda jah,tabbas ta tuno ma abunda yake tadamai da hankali arayuwa amma dole ne ingayamai Gary aure bawasa bane… Mom tafada axuciyarta.
Cewa tayi”Anwar kayahakuri wannan dolene in gayama inhar ina kaunarka.
“Anwar ne yace”ngd mom inallah ya yarda xanje kano awannan satin.mom taji dadin magnr anwar dan hakan “tace mai”nayima alkawarin duk inda kaga baby xan aurama koda kowa xai kita,nixan sota.
Anwar yaji dadin maganar mom dan haka yamike yanacewa mom nifah yanxu xankoma barrack.
“mom tace “tun yanxu son, na dauka sai gobe.
“Anwar yace”no mom yanxu nakeso,dama so nake inganki,tokuma naganki mom…
Nan mom tayi ta sama dannata albarka har yabar gidan sannan takoma ciki…
______________________________
*KANO*
Binta…..binta….
Hajiya mimi ne maimagana. Kafin tarufe baki saiga binta,tashigo jiki na bari dan tasan halin hajiyannata.
Gani hajiya “binta tace “hadi da xubewa gaban mimi.
Mimi waya tacigaba dayin charting abunta kaman baita takira binta BA. Sai da ta dau kusan 20minute sannan tadago hadi dacewa”binta yarinya nakeso mai karancin wayewa,kuma ‘yar gidan matsiyatan likis nakeso,wanda xata rinka kulamun da part dina.dakuma aiyukana… “Mimi tafadi” hadi da isa da gadara na masu kudi.
Bintane takuma kwantar da kai kaman xata mawa Mimi sijjada,”tace”hajiya ‘yar shekaranawa kuma wani irin aiki xatayi,don agayamasu…
Mimi tayi shiru kaman bataji mai binta taceba.
Kuluwa dake gyafe ne. aranta “tace “maganinta mujinta yakarinka yimata kaman sarki saboda isa itakuma tana lallabashi wai ita gamai ba so muhimmanci.mtssww.tsaki tayi aciki tana kallon Mimi da sai yanxu allah yayi mata dagowa.
“mimine tace”yarinya nakeso wanda baxata wuce 16yrs ba,kuma xata rika mun girki,gyaran dakina dana husbyna.i think that’s all. Mimi tafadi hadi dayamutsa fuska.nan binta jiki na rawa tace”to hajiya asatinnan inallah ya yarda xansamota.
Ok mimi tace”tare damasu ixinin tafiya.
Koda suka futa kawanta ne”tace”kai mimi kodai kinason yarinya karamane dai kawai.
“mimi tace haba allah Ya kyauta Laura, ‘yar aikina nefah.kuma talaka,kinsan yanda na tsani talaka.mexan da ita huuu,um.husby na yakusa dawowa ma dole in shiryu na kwanakinnan harya koma Tukunna.mimi takaruka maganar hadi da mikewa…
Dan, allah innah kiyahakuri wlh baxan sakeba.
Inna ko sairaran nana Aisha batayi kawai dukanta takeyi.hadi dacewa gobe innabaki talla baxaki kara dawomun dashi baikareba.sai da tagaji dan kanta sannan ta kyaleta.tayi kicin tabarta nan tana matsanancin Kuka..
Ahaka tallalaba tashige dakinta ta dauko wani allo tanaganin rubutun ciki nan ta hau dariya…Allah Sarki nana Aisha kenan dakayimata da yawuce.muyan Inna yakatsemata tunanin da takeyi.
Innane “tafara cewa”toh dan ubanki xama kikayi,baxakiyi wanke-waken ba ne insani.
Nana Aisha tayi saurin mikewa dacewa”innah dan alllah kiyahakuri.tsaki inna tayi hadi dabarin Dakin…
Nana Aisha ne tayi saurin fitowa daga dakin tanufo wajen wanke-wanken, tafara.
Sallaman binta yaka tsemata tunani,amsallaman tayi hadi da saurin bata tabarma.
Innane tafito hadi dacewa sannu da xuwa hajiya binta.
Binta ta amsa da yauwa lantie…
Nana aisha tamike ta basu wuri,takoma yacigaba da wanke -wankenta.
Bintane tace”lanti magana ne mahimmanci yakawoni wurinki.
Lantie tace”inajinki binta.
Binta tacigaba dacewa dama hajiyan danake aiki awurinta ne takeson ‘yar aiki,wanda taiya gyaran daki,girki,dasauran aikin gida,shine tace insamo mata yarinya 16-17.shine naga nana Aisha duk tadauki wannan halin.
Amma mekikace lanti…
Inna tanisa hadi dacewa aina gode binta,ai gomma taje tanimo mana kudun aurensu jidda.tunda ita batada mashin shini,ga kanninta nan saura kwana nawane bikinsu.amma ita kare baitaba xuwa dasusan sontaba.
Bintane ta kalli inda aishar take,nan tga kyau kamar balarabiya.
Aishar doguwace amma basosai ba,er dai -dai gajikin mata, shape hips,duk Sun bayyana,gata da circle fuska afuskanta Beuty point ne duk intayi mgn sai ya loba…kai-kakai kwatan tamaku irin kyaunta baxaiyuwuba sai inbata shafufuka Inayi…
Waigawatayi Inda lantie take axuciyar cewa take anya ba sharri latie keyima yarinyan nanba..
Manage with this banda chajine.
Maman teddy 🧸
File Name | Yar Aikina… Hausa Novel Doc. |
Title | Yar Aikina Complete |
Author | Maman Teddy |
Group | Ai Hausa Novels |
Genre | Fiction Story |
Published Date | 17/07/2024 |
File Size | 145.0KB |
Format Size | TXT |
Book Price | Free |
Phone No |
Download Yar Aikina Complete Novel Document By Maman Teddy
Click the below green button to read the novel online
Proceed with your download by clicking the below button
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.