Hausa novels

Fatalwar Delu Part 4

Fatalwar Delu Part 4

 

🤡 FATALWAR DELU 🤡

 

Part 4

 

Kingboy Isah 👑

 

Short story

 

 

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION

 

 

Rokon addu’a ga duk wanda ya karanta page din nan, ga mahaifin Hussaini Atk Tanko, da ma iyaye da yan uwa wanda suka rigamu gidan gaskiya, Allah ya haskaka makwancinsu sannan ya yafe zunnubansu. 🤲🏼

 

 

 

A haka na koma na kwanta ina cizon lebe, jimawa kadan bacci bai gama kwasata ba na sake jin wani sabon marin. Wannan karon ma da sauri na tashi zaune domin ganin mai marina. Kamar dazu Bukar dai ya jingina da bango sai bacci yake, jaririn kuwa ina haskashi na ga idanunsa biyu mun hada ido. Ina so na gaskata cewa jaririn ne ya mareni amma zuciyata ta kasa amincewa da hakan, wannan dalili ne ma yasa na kama hannun jaririn na duba ciki da bai, tabbas wannan dan hannun bai isa yayi mun mari da zan ji zafi har haka ba. A fusace na fara tashin Bukar daga bacci, a dan razane ya tashi da alama har lokacin a tsorace yake, bayan na tambayeshi dalilin da yasa ya mareni ya nuna min alamun baima san zancen ba. Da na kara mai bayanin maruka biyu da nasha, ina kallon fuskarsa ta canza kamar zaiyi kuka ya ce, “Ai dama na fada maka, wannan yaron duk inda ya fito ba mutum bane, domin ko mai shigen-shigen kamarsa babu a garin nan. To yanzu gashi nan sun fara taba lafiyar jikinka, ni dai fatana Allah ya sa mu kai gobe da rai”.

 

 

Dariya naji ta zo mun domin Bukar da gaske a tsorace yake sai kara dalla fitila yake kan fuskar jaririn. “Wai Bukar dama haka kake da tsoro ban sani ba, kai sai kace ba namiji ba. To ni ko da ace fatalwa gaske ne idan zan ganta ido da ido ba zan tsorata ba balle in razana. Nasan ba abinda ta isa tayi mun, kai sai dai ma taji tsorona ba ni inji tsoronta ba”. Ya tsaya kallona na ƴan dakiku kana yace, “Ka ga malam nasan kai dan rigima ne ga karambani da rashin tsoro, amma ka sani mutane ake wa wannan ba aljannu da fatalwa ba”. Na danyi murmushi tukun na ce, “Ni ai har fatalwar in tayi mun ba raga mata zanyi ba”. Yace, “Wai dame kake takama ne, in dai karfi ne a wajen fatalwa ba zaiyi aiki ba”. “To in karfi baiyi aiki ba ai sai mu sa ayar Allah mu da muke da kursiyyu”. Da jin haka yayi shiru bai kara cewa komai ba.

 

Fatalwar Delu Part 4

 

Ni kuwa na mike na je jikin jakata na zaro cable na cajin wayata. Bukar na bina da ido hala ya zata cajin waya zanyi a powerbank, ni kuwa ina zuwa na linka cable din biyu na daga na shafdawa jaririn a kafafu. Ina ji ya fashe da kuka, tuni na kara dagawa na lafta masa a karo na biyu. Nan da nan Bukar ya tashi da gudu ya rikeni yana fadin “Innalillahi Nura ka haukace ne? Kana da hankali jariri ne fa kake duka haka kamar ka sama sa’anka”. Ido na bishi da shi daga bisani na ce, “Sakarni ai na gama dukan nashi”. Nan ya sakeni yana mun wani irin kallo da har dariya ya bani, domin a tunaninshi ba a hayyacina nake ba. Shi kuwa jaririn sai tsala ihu yake, na ce, “Wai ba cewa kayi fatalwa ne ba? To fatalwa kamar wannan ai bulala biyu ba abinda zaiyi masa”.

 

 

Bukar ya ce, “To dan na ce fatalwa ne ya zama lalai fatlwa din ne ai nima zargi ne nake. To yanzu da ka fara dukansa in mutum ne fa”. Na ja tsaki na koma ina can bangaran katifa har na kusa kwantawa sannan na ce, “Ah to in mutum ne ta tabbata kenan kaine ka mareni ba shi ba”. Nan naji ya fara rantsuwa wai wallahi bai mareni, nima na ce “To jaririn nan ne ya mareni kuma na rama da bulala mari biyu dama akayi mun”. Ina fadar haka na koma na kwanta da nufin yin bacci, amma wannan jarababben jaririn ya ki daina kuka. Jin hakan ya sa na tattara bargon Bukar na dora masa a saitin kai, ko ba komai da nayi haka sautin kukan ya dan ragu dama na juya kaina dayan gefen. Bukar dai har a lokacin kallona yake cike da mamaki har na koma na kwanta yana tsaye bansan lokacin da ya zauna ba, haka zalika bansan lokacin da bacci ya daukeni ba duk kuwa da kukan jariri.

 

 

Abun mamaki tun daga nan kuma ban sake jin an mareni ba. Da asuba wayata ce ta tayar da ni, dan haka na tayar da Bukar wanda har a lokacin a tsakar shagon na ganshi jingine da bango da alamu a haka ya kwana rike da fitila, na ce ya shiga gida ya debo mana ruwan sallah. Amma yana tashi abinda ya fara tambayana shine ina jariri, ni sai a lokacin ma na tuna da shi. Nan fa na shiga daga bargo amma wayam babu jariri babu alamarsa. Na kalli Bukar hade da cewa, “Baka bayar da jaririn nan ba kuwa lokacin da ina barci”. Bukar ya ce shi wallahi tunda ya samu bacci ya dauke shi ma bai sake farkawa ba sai yanzu. Na ce ya dai tuna ko yarinyar nan ta dawo ya bata jaririn ya ce bai fa farka ba ma. Na ce to ai shikenan ka ga mun huta da cigiyar uwarsa da safe.

 

 

Ya kalleni kamar zai rufeni da duka “Wallahi Nura ni dai zuwanka bai kareni da komai ba sai wahala, ji yadda kake magana kamar komai bai faru ba, jaririn fa yanzu ta tabbata dai ba mutun bane aljanine ko kuma fatalwa tunda ni dai ina sane wallahi ban bude dakin nan ba kuma kaima kace haka, to shi jaririn da kanshi ne zai bude dakin ya fita? To idan ma ya iya budewa ya fita to wa ya kuma sa kuba daga ciki?”. Na yi kwafa hade da cewa, “Oho watakil hannu ya zuro ta tsakanin kofa ya saka kubar”. A kufule yake kallona na tabbata da akwai dama sai ya mammake ni, amma na lura a halin da yake ciki ko dukan nawa yayi hakan ba zai rageshi da komai ba. Can na juyo muryarsa yana fadin, “To wallahi ba zai yuyu ba, daga yau ba zan sake kwana a dakin nan ba in dai ba tabbaci na samu cewa Jaririn fatalwar nan ya bar dakin ba. Haka kawai wa ya sani ko yana nan ya boye da dare suke fitowa in zo in kwanta a shakeni”.

 

 

Nayi yar dariya hade da cewa, “Ka ga malam muna makara kaje ka debo mana ruwa muyi alwala muyi sallar asuba, batun jariri kuma ai kun fi kusa tunda dan garinku ne, ni dai karfe takwas nayi zakaje ka nemo min mashin ya kaini bakin titi inda zan samu mota. Yau a gidanmu zan kwana in ya so daga yau ka rushe dakin ni ba ruwana”. Ina iya hango wata muguwar harara da yayi man kafin ya wuce daga dakin. Da safe bayan mun karya da dumamen tuwo miyar masara na shiga muka gaisa da mahaifansa sannan nayi musu sallama. Shi kuwa Bukar mun rabu yana ta mitar jariri dan lokacin da na shiga su Innarsa ma sai da sukayi mun maganar na nuna musu kawai tsoron Bukar ne, duk da dai basu gamsu ba amma na samu na ci darajar bakunta sun bar zancen a haka. Ba dadewa sai ga Bukar sun dawo da mai mashin, na ce mai na gama sallama da su Inna wucewa kawai zanyi. Jakata na daukko a shagon nasa, aka saka a gaban mashin muka hau domin ya ce zai rakani in munje sai su dawo da mai mashin din.

 

Amma me mashin na slow muna ina hawa mashin ya mutu, yayi juyin duniya ya tayar amma mashin din yaki tashi har bugawa yayi amma bai tashi ba. Nan muka saukko da nufin a tura, ai kuwa ana turawa ya tashi, a karo na biyu muna sake hawa za’a murza kenan mashin ya sake mutuwa…………….

 

 

Zan cigaba.

 

 

Back to top button