Uncategorized

Za a rufe shiga gasar Gamayyar Marubuta Jihar Kano (GAMJIK) nan da kwana Uku masu zuwa.

Za a rufe shiga gasar Gamayyar Marubuta Jihar Kano (GAMJIK) nan da kwana Uku masu zuwa.

Hakan na nufin daga ranar Lahadi 13/3/2022 da misalin ƙarfe 12 na dare, ba za a sake karbar wata kungiya don shiga gasar ba.

Wannan sanarwa ce daga kwamitin gasar, inda suka bayyana cewa yanzu haka anyi nisa wajen ƙoƙarin fara shirya gasar. 

Akwai kwararru alƙalai da kwamitin gasar ya naɗa da za su yi aikin tantance hujjojin da kowacce kungiya ta bada, su yi tankade da rairaya inda kungiyoyi biyu da suka fi samun maki za su fito daga ko wanne rukuni, a cewar shugaban kwamitin gasar wato Mukhtar Musa Karami.

Yadda gasar take shine kowacce ƙungiya zata kara ne sau biyu da haka za a duba adadin yawan makin da kowacce ƙungiya ta samu, wacce tafi kowacce yawan maki itace ta ɗaya, sai mai biye mata ta biyu, ƙungiyar da tayi ta uku banda ita.

Bayan an gama karawa gaba ɗaya ƙungoyi 16 za su rage shi ake cewa zagaye na sha shida.

Daga shi kowa zai ta karawa da kowa har zuwa final.

 Manufar wannan muhawara ita ce, domin zaburar da matasan narubuta, wajen bincike da gabatar da ingantaccen rubutu nai ma’ana.

 A kokarin wannan kungiya ta Gamayyar Marubutan jihar Kano (GAMJIK) na bunƙasa Adabin Hausa, wannan kungiya ta shirya gudanar da gasar muhawara ga kungiyoyin marubuta a kan batutuwan a suka shafi Adabi da rayuwa.

KYAUTUKAN DA ZA A BAYAR 

  1. NA DAYA 50,000 
  2. NA BIYU 30,000
  3. NA UKU 20,000 
  4. NA HUDU 10,000 

 Daga na daya zuwa na hudu kowacce kungiya za ta samu kyauta manyan littattafai, tare da kambun girmamawa. Akwai tsarin kyautuka na littattafai, ga kungiyoyin da suka tsallake zagaye 16.

 Akwai dokoki da ƙa’idojin muhawarar za su zo a cikin jadawali na jerin ranaku da za ayi, kamar dai yadda aka yi muhawarar da ta gabata a 2020. 

Har yanzu ana kan tattara kungiyoyi, ga masu bukatar shiga wannan gasa ta muhawara sai a tuntubemu ta wannan lambobin; 08138131990  08138873799 08144692542  08149741554  08037442582

Za ku iya bibiyar group ɗin mu na Facebook ta hanyar danna bulun rubutun dake ƙasa Gamayyar Marubutan Jihar Kano (GAMJIK)

Back to top button