typing📲
🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)
*written* *and* *story* *by*
*Asma’u Muhammad Auwal*
( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)
*WhatsApp me 09065443871*
*Laifin Daɗi qarewa*
*FREE BOOK ZAI ƘARE NE A ƘARSHEN BOOK ONE*
*BOOK TWO DAZAN SHIGA SOON PAID NE,*
*YANA TAFE DA SABON SALO, DA KUMA CAKWALKWALIN CAKWAKIYA, KADA KU BARI A BAKU LABARI DOMIN GANI DA IDO 👀 YAFI JII👉👂*
*MATAR DAMUSAA BOOK 2 PAY ONLY 150👌👇👇👇*
*ASMA’U MUHAMMAD AUWAL,*
*9065443871, OPAY BANK.*
*OR*
*ASMA’U MUHAMMAD AUWAL,*
*2267236949, ZENITH BANK*
*SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER*
👇👇👇
*09065443871*
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________
💫💫 *{{N W A}}* 💫💫
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم
*BOOK ONE*
🅿️ ——->83 & 84 <——-
Ayush tana ƙwance rai a hannun Allah, dole sai anyi mata aiki a cikin cibiyarta sakamakon fincikar zoben da tayi da ƙarfin gaske hakan ya jawo mata tsinkewar jijiyar cibiya, wanda Allah ne kaɗai zai iya tasar kafaɗunta, likitoci ne zagaye a kanta kowa da kalar maganin da yake mata,
wasu sunyi mata operation suna mata aiki a ciki, wasu kuma suna ƙoƙarin ɗaura mata ledar jini saboda ba ƙaramin jini ta zubar ba,
kwana sukayi akan Ayush suna aikin ceton rai…
da sassafe misalin ƙarfe 6 Malam ya shugo Office ɗin Mommy yana ƙiran ta cikin damuwa tareda faɗin “mun bar Gawar Junaid ya kwana ko waiwaya shi ba’ayi ba, yanzu haka ina tunanin ya sanƙare tin jiya da rana..”
Mommy ce ta ɗago hankali a tashe tace “innalillahi wa inna’ilaihi raju’un, hankali na baya jikina wallahi na manta..”
Shima Malam cewa yayi “wallahi kuwa nima ina gida Junaid ya faɗo mun a rai, bansa a raina ya mutu ba,
amma na ƙira malaman da zasu masa wanka wata ƙila mu tarar dasu a gidan..”
da sauri suka shige motar suka fice daga cikin hospital,
A ƙofar gidan suka samu mutane har an taru ga malaman da suke jira suma, har da Doctor Hasheem shima ya samu labarin mutuwar Junaid a gurin Malam, Baba maigadi ne ya buɗe musu ƙofa yana shaftar kuka domin mutuwar Junaid ba ƙaramin girgiza mutane yayi ba,
su Mommy suna shiga cikin gidan saiga jiniyar motar sojoji har guda 10 suma labari ya riske su,
iya waɗanda zasu je ɗakin Junaid sune daga Malam Lawan sai Doctor Hasheem sai kuma wasu malamai su 2 da kuma wasu sojoji suma su biyu haka suka haura upstairs suka nufi ɗakin Junaid, ita kuwa Mommy a falo ta zauna tana sake rera sabon kuka..
shigarsu ɗaki suka tarar da Junaid ƙwance ya kalli sama tareda jan mayafi ya rufe kansa kamar dai yanda aka barshi, sai dai shi a yanzu bacci yake,
Bayan tashin shi ya shiga toilet ya yi wanka ya canza kaya yayi sallah sannan ya sauƙa down stairs ya nufi kitchen cikin sa’a kuwa ya samu abun taɓawa, yaci abinci yayi nakk ya kora da ruwan sanyi, ya kwanta akan sofa har bacci ya ɗauke shi, a falon ya kwana sai da asuba ne ya tashi ya koma room ɗinsa ya ɗauro alwala sannan ya tsayar da sallar asuba, daga nan ne ya haura bed ɗinsa ya lulluɓe kansa da mayafi sakamakon sanyin da akeyi..
kowa da ƙwalla a fuskarsa haka aka yaye masa mayafi za’a ɗauke shi akai shi toilet, wasu suka riƙe hannayensa wasu kuma ƙafafu akayi sama dashi,
a firgice Junaid ya buɗe idonsa yayi wani irin murɗewa ya miƙe tsaye yana faɗin “lafiya kuwa, suwaye kuu..”
Ai kuwa suka ce ƙafa mai naci ban baki ba kowa ta kansa yake, a ɗari suka bar ɗakin ko tsaya sauraronsa basu yi ba, sai gariyar malamai kake gani suna furawa, rawaninsu kuwa duk sun jejjefar a gurin,
suna fita ƙofar gida da gudu sauran mutanen ma suka feffece duk da basu san meya faruba,
toh fah 🤔 sojojin ma anan suka bar motocinsu, iya Mommy kawai aka bari tana zaune kan kujerar falo ta ƙafe guri ɗaya gaba ɗaya ta rasa ƙarfin jikinta ko motsi ta kasa yi…
Junaid ganin haka abun ya bashi mamaki yana maganar zuci “wai meke faruwa ne naga waɗannan mutane haka akaina? kodai akwai abunda ya faru dani ne?…” yana cikin wannan tunanin idonsa ya sauƙa akan likkafani a cikin leda, yasa hannu ya ɗauka tareda cire wa still turare ya sake gani kuma a jikin turaren ga photon gawa a kwance, Junaid ido ya zaro waje tareda faɗin “kenam a matacce suke ɗaukata?”
hankalinsa ne ya koma kan bedsheet ɗin gadonsa yaga duk jini ya ɓata gadon, tin jiya bai lura da shi ba,
ɗaga hannayensa yayi sama yana duban kansa yana kuma cewa “nifa naga lafiyata klau, bana jin komai a jikina..”
ficewa yayi daga ɗakin ya sauƙa down da saurinsa, ganin Mommy yayi a zaune ko motsi babu sai idonta da suka ƙafe alamun dai kamar suma tayi, da gudu ya nufi frig ya ɗauko cool water a jerkan ya since murfin sannan ya fara watsa mata a fuska,
farfaɗowa tayi tana jan numfashi sama-sama, idanuwanta ne suka sauƙa akan fuskar Junaid yana ƙiran sunanta “Mommy! Mommy!! Mommy wake up mana, open your eyes please”
gani yayi ta ƙara sumewa tayi baya yayi saurin tarota yana cigaba da ƙiran sunanta amma shuru,
ruwan goran ya sake watsa mata, a ruɗe ta tashi tana faɗin “taimako jama’a fatalwa, taimakoo…”
ido ta sake haɗawa da shi kuma du sai luuuuu ta ƙara sumewa a karo na uku kenam, ruwa ya sake watsa mata ta farfaɗo ido a rumshe, Junaid ne yakai hannunsa saitin gefen fuskarta, yana faɗin “Mom yau nine kike suma a kaina? Meyake faruwa ne?..”
itama hannu takai saitin fuskarsa tana ambaton “Junaiddd! Junaid kaine? daman baka mutu ba, bakada lafiya to amma ya akayi yanzu ka dawo kana tafiya, ɗaga hannu sama tayi tana hamdala, Allah na gode maka! Yaa Allah lokaci guda ka tayar mun da yarona, Alhamdulillah Addu’a ta ta karɓu, ta ƙarasa maganar tareda rungumarsa tana kukan farin ciki,
ɗagowa yayi yana faɗin “Mom where is my Yushert…?
Mommy tana kuka tace “Ayush tana kwance a gadon asibiti..”
“what? Mom what happened to her?…”
Mommy kasa magana tayi sai kukan da yaci ranta,
“Don’t worry Mom, it’s okay bari naje na gano ta..”
Momy ce tayi saurin riƙe hannunsa tace “karka fita yanzu kowa yasan ka mutu..”
“Please Mommy ki barni naje naga Yushert ɗina, bazan iya juran rashin ganinta ba..”
ya fizgi hannunsa sannan ya haura upstairs da gudu, ya nufi room ɗinsa, farar jallabiya kawai ya ɗora akan gajejen wandonsa ya ɗauki key ɗin mota, sannan ya sauƙo down stairs, bai tsaya duban ta kan mommy ba, kai tsaye motarsa ya nufa ya shige ciki da gudun gaske ya fice daga gidan
sai asibiti…..
Domin sauke CikakkenLittafin Sai Ku Danna bulun Rubutun dake kasa
Matar Damisa Book 1 Complete Novel Document
*WALLAHI BACCI NAKE JI SOSAI SHIYASA NA BAR MUKU IYA WANNAN PAGE, KU BIYONI BASHI NETX PAGE ZANYI TYPING MAI TSAYI*
Some Of Related Hausa Novels
*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500
*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500
*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*
*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*