Hausa novels

Abban Sojoji Chapter 67 Book 2 Complete Novel

Abban Sojoji Chapter 67 Book 2

The Father Of Soldier

Written By Hafsat Bature

*Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za’a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata  zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari*,

Wuraren ƙarfe 4:30 gaba ɗaya matasan gidan sun hallara a baban falon gidan wanda yasha decorations abun ba’a magana,yayi kyau over tamkar wani babban  hall na taro,an ƙawata shi sosai hada wasu kujerun aka ƙaro,an tsara komai na wurin anyi table arrangements,kowane table yana zagaye da Kujeru guda uku uku wadanda ke dauke da seat cover haka ma tables din,a jere Ayaan da Jahan irfan da khaleed da kuma jabeer da fawan,suka shigo main palour ɗin kowannansu ya ɗau wankan tsadaddiyar shadda ajikinshi,bayansu sae kanal yousouf shima ya fito cikin nashi wankan,ba ƙaramin ƙyau sukayi ba,sai hotuna suke ɗauka da wayoyinsu,kafin camera man ɗinsu wato junaid ya kammala shirin nashi ya fito ya ɗauke su hotuna,dama shine maiyi masu hoto duk in suka shirya walima irin haka,acikin gida,

 

Lokacin da Abbansu ya fito jikinshi sanye da shadda fara taji aiki ajikinta,koda sukayi arba dashi da sauri suka ƙaraso wurinshi suna yaba wankan daya ɗauka,

“Abba harka fi mu yin kyau wlh,gaskiya bamu yarda ba Abba,’

Dariya sosai Abban nasu yayi yana kallonsu one by one,wani irin farin cikine ya lullu6e shi ganin ƴa’ƴan nashi gaba ɗayansu agabanshi,duk da ba wasu acikinsu,amma yasan duk zasu hallara ne suna ciki suna shiryawa,

“Abba,bari mu fara ɗaukar hoton tare dakai kafin Baby junaid ya ƙaraso,”

fawan ne yayi maganar yana kanga wayarshi saitin fuskar Abban nasu,

dakatar dasu Abba yayi yana tambayar ina Abusufyan yake ne?bai fito bane?

Kanal yousouf yace”naje bedroom ɗinshi lokacin yana acikin toilet ɗinshi,amma ina da tabbacin zuwa yanzu ya kammala wankan ƙila ma harya shirya shima,”

Jinjina kai abban nasu yayi tare da cewa”Gaskiya sae dae kuyi haƙuri to,babu wanda zanyi hoto dashi har sae naga ɗan uwana akusa dani,dashi nake son na fara ɗaukar hoton nan,don haka ku jirani yanzun nan zamu fito tare,”

Bashi wuri sukayi ya wuce ɗakin Abusufyan,tura ƙopar yayi yasa kai ya shiga ciki,a lokacin Abusufyan yana tsaye gaban dressing mirror yana maƙala links ɗin hannun rigar shaddar daya sanya,madarar kyau,gezner ce ajikinshi green colour,sae faman salƙi takeyi,yayi kyau Over,ta cikin madubi ya hangi shigowar yayan nashi,

Ƙayataccen Murmushi ya saki tare da cewa”Yaya hossein,yanzu nake shirin fitowa nima,wlh bacci ne ya ɗan dauke ni bayan mun dawo daga sallar la’asar,shiyasa na makara ban kimtsa da wuri ba,”

Ƙarasawa ciki Abba yayi yana cewa”tun ɗazu nake ta baza idanu inga 6ullowarka,amma bangani ba,shine nace bari ni nazo da kaina na janyoka mu fita tare,don na sanar dasu cewar babu wanda zan ɗauki hoto dashi har sai naga ɗan uwana mun fara yi dashi ,’

juyowa Abusufyan yayi a lokacin ya kammala sanya links ɗin ya kalli abba yace”yaya hossein bansan da wasu kalmomi zan iya bayyana maka irin farin cikin da nake ciki ba,wlh sai yanzu nake danasanin yin nesa da ƴan uwana,domin kuwa babu abunda yafi kasancewa tare da ahali daɗi aduniyar nan,’

Abba yace”ae bazan ƙara yin gangancin barinka kabar ƙasar nan ba,wancen lokacin ma satar hanya kayi ka gudu batare da saninmu ba,amma wannan karon zan sanya tsaro sosai akanka,ko nan da bakin gate zaka je sai da izinina,zan sanya security guards ɗin da zasu dinga bibiyarka a 6oye,”

Dariya sosai Abusufyan yayi kafin ya tsagaita da yin dariyar yace”Ya hossein nima bazan ƙara maimaita kuskuren da nayi ba,na tafiya nabarku,nasan ban kyauta ba,wlh naji ba daɗi sosai lokacin da junaid ya ƙankame ni yana murnar zuwana hada hawayenshi,sae naji wani iri araina,na tafi na barshi yana ƙarami bai mallaki hankalinshi ba,amma yanzu dana dawo na same shi ya girma sosai,a waya ne kawai nake jin muryarshi,iya wannan shaƙuwar da mukayi ta waya itace tasa ya ruƙe ni sosai aranshi,insha Allah bazan ƙara tafiya nabarku ba,nayi alkawarin hakan,”

Ba ƙaramin farin ciki Abba yayi ba,da jin kalaman ɗan uwan nashi,ruƙo hannunshi yayi acikin nashi tare da janyo shi suka fito daga cikin bedroom din,

Kamar jira suke Abban nasu ya fito tare da uncle Abusufyan da sauri suka nufesu fuskar kowannansu ɗauke da farin ciki mara misaltuwa,nan fa suka shiga ɗaukar hotuna,

 

💋Boss Bature💋

 

Tabarakallahu ahsanul khaliqin!Azmee ce ta ambaci hakan yayin da take kallon sehrish dake tsaye,sanye cikin tsadadden cord lace red colour yasha adon duwatsu ajikinshi,riga ce har guiwa sae zani,azmee da kanta ta ɗaura mata ɗankwalin golden colour tamkar gwargwaro haka ta ɗaure mata shi a kanta,fuskar nan tasha make-up ɗan light ba over ba,ta gyara jagirar idanunta duk da ta ƙara zana ta da eye pencil brown colour,ta ko’ina kwalliyar ta fiddo mata da zunzurutun kyawun fuskarta,hancin nan yayi tsayi,ga bakin nan nata yasha jan janbaki,yadda kasan wadda zata gasar sarauniyar duniya haka ta fito ɗass da ita,wasu matsiyatan takalma ƴan ubansu azmee ta ɗauko mata daga cikin shoe rack dinta,ankle strap masu tsinin gaske golden colour ne suma,launin head dinta,wayyo Allah bournvitar kyau just imagine it,

Wuyanta na sanye da ziririyar sarka golden colour,haka earrings dinta,da kuma rings ɗin da ta zura a hannunta duk launi ɗaya ne,

Kai jama’a!,ga zanen fulawar da azmee tayi mata a hannunta na jan lalle,yayi mata kyau sosai hannun nata kamar a lashe don kyau,

 

“Juya a hankali ki kalli madubi,”Azmee ce tayi mata maganar tana faman sakar mata murmushi,

Ajiyar zuciya sehrish ta sauke tare da juyawa awani slow ta kalli kanta acikin mirror ɗin,

Gabanta ne taji yayi wani irin bugu lokaci guda,zuba ma kanta ido tayi tana kokwonton Anya itace kuwa!?

Yarfa hannu tashiga yi aruɗe take cewa”Aunty azmee wai dagaske ni ce!dama haka nake da kyau kamar macen aljanna! Am just speechless oh my God!! 🤣😂

Maganar sehrish ba ƙaramin dariya taba Aunty azmee ba,kama hanyar fita tayi daga cikin ɗakin tana cewa”Bari naje na fara jera abincin a falo,pls kada ki fito yanzu sai nan da 15 mins nake son ki fito saboda inason inga reaction ɗin matansan gidan idan sukayi arba dake,”tana kai ƙarshen maganar ta fuce,

Ƙayataccen murmushi sehrish ta sakar ma kanta tana kallon kyakkyawar fuskarta acikin madubin,lokaci guda Sgr ya faɗo mata acikin ranta,lumshe idanunta tayi tare da buɗesu a hankali tana ƙara bin jikinta da kallo,

Sae ta dinga jin kanta tamkar amarya a wannan lokacin,amaryar kuma ta Sgr,

“Ya Allah ka nuna min wannan ranar da nake ta mafarkin zuwanta,ranar da zan kasance mallakinshi,shi ma kuma ya kasance mallakina,a wannan ranar nayi ma kaina alkawarin cewa ko bacci ba zanyi ba,zan kwana ina sallar dare,ina miƙa godiya ta ga Allah daya cikamin burina,a washe garin ranar kuma zan tashi da azumi,’

ta ƙarasa zancen zucin nata tare da samun wuri saman kujerar gaban madubin ta zauna,

 

Gaba daya duk sun zazzauna saman kujerun yayin da table din ke shaqe da kayan ciye ciye iri²,Abusufyan tare da Abban nasu sae junaid suna a zaune wuri daya,Ayaan da jahan da kuma fawan suna zaune suma a wuri daya suna cin abincinsu,Irfan da jabeer sae khaleed suma suna zaune a table daya,

Kanal yousouf ne ya buɗe masu taron da addu’o’i,kafin su fara kulu washarabu hani’an,sunyi haje haje da naman kaji,farfesu iri iri da sauran kayan maƙwalashe,

,kowa ya mayar da hankalinshi akan abincin dake gabanshi,

“Wai ni ina Rafayet da Omar ne?naga kowa amma bandasu,”Abusufyan ne yayi ma Abba maganar a yayin da yake ɗaukar cup na lemu,yakai bakinshi yana kur6a,

“Ina tunanin suna ciki suna shiryawa,kasan su fa manya ne nasu wankan ba irin namu bane,nasan shiyasa suka jima aciki basu fito ba,”a cewar abbansu,

“Naga alama,amma ni ko ina so na tambayeka yaya,wai har yanzu Sgr da Omar basu fara soyayya bane “?yayi tambayar yana kallonshi,

Murmushi Abba ya ɗanyi kafin yace”Omar dae ya sanar dani cewa akwai yarinyar da yake so,kuma ashirye yake daya aureta,amma shi rafayet har yanzu fa babu wani sauyi yana nan yadda kasan shi,amma kwanan nan na fuskanci kamar akwai wani abu atsakaninshi da yarinyar gidan nan,wadda na faɗa maka cewa tana taya Azmee aiki,kamar akwai soyayya atsakaninsu,duk da dae bani da tabbacin hakan,”

tunda suka soma magana junaid baisan me suke tattaunawa ba,saboda hankalinshi na can wurin tunanin abu biyu,rishi ɗinsa da kuma zuwan mommynsu a takure yake,gaba ɗaya ya gaza samun natsuwa saboda ya kwallafa rae akan zuwan nata,

 

Abusufyan yace”yanzu me ka yanke shawara agame dasu ne?zaka tunkari Sgr da maganar yarinyar ne ko kuwa”?

 

“A’a,bana tunanin cewa zai amince cewa yana sonta harma ya yarda ayi auren kasan halin shi,yanzu dai akwai wani shiri da nakeyi dama zuwanka kawai nake jira,nan da sati mai zuwa zan sanar dakai insha Allah,”

Murmushi Abusufyan yayi tare da cewa”Allah ya kaimu lafiya,”

Abba ya amsa mashi da Ameeen,

Juyawa abbansu yayi tare da kallon junaid ya ambaci sunanshi,

Firgit junaid yayi tare da aza idanunshi kan abban nasu yace”Abbana,”

..murmushi sukayi gaba ɗayansu,Uncle abusufyan yace”junaid kodae ka fara soyayya ne?tun ɗazu muke magana amma hankalinka na’a wani wuri,”

Murmushi ya ɗanyi tare da sunnar da kanshi ƙasa yana kallon plate dake ajiye gabanshi shaƙe da Chips,tun da Azmee ta zuba mashi bai ko ta6a shi ba,

“Junaid naji kayi shiru kodae dagaske ne abunda Uncle ɗinku yace ka fara soyayya”?Abbansu ne yayi maganar cike da zolaya yana kallonshi,

Duk kunya tabi ta kama junaid,ba wai abban nasu yake ji ma kunya ba,uncle ɗinsu yake ji ma kunya,don ta Abbansu har zancen aure suna yi dashi in wasan nasu ya motsa,

yana ƙoƙarin buɗe baki yayi magana,wayar shi ta shiga ringing,jikinshi na rawa ya zura hannunshi a aljihu ya curo wayar yana duba sunan mai kiran nashi,private number ya gani wato anyi hidden ɗin numbar,kallon abbansu yayi tare da cewa”Abba zan amsa waya,”

amsa amshi yayi da cewa”okey,amma kada ka jima,muna jiranka,don bamu gama hotunan ba,”

Murmushi ya saki tare da miƙewa yabar wurin,sae da yayi nesa dasu sannan ya ɗaga kiran tare da kara wayar a kunnanshi yana jiran jin wanene ke kiran nashi,

Wata sanyayyar murya yaji ta karaɗe kunnan shi da cewa”babyn abbanshi kana ina ne”?

Tunani ya shiga yi kodae mommynshi ce don haka yace”ina a gida ne,”

Matar tace”Idan ba damuwa kazo Airport kadauke ni,na ƙaraso Nigeria amma banaso kowa yasan da maganar,kai kadae kawai nakeso kazo ɗaukana,Kada ka bari kowa ya biyo ka”

da ƙarfi junaid ya ambaci sunan mommy fuskar nan tashi cike da farin ciki yace”mommy am coming right away”

Matar tace”okey,idan ka fito daga cikin gidan ka sanar mun,”

Cike da zumuɗi ya amsa mata da toh,sannan jiki na rawa ya katse kiran tare da zura wayar a aljihun shi,

Gaba ɗaya ya gaza rufe bakinshi saboda tsabar farin ciki,juyawa yayi yana kallon ƴan uwanshi dake zazzaune kowannansu fuskarshi ɗauke da farin ciki,aranshi yace”kodai na sanar masu cewa mommy ta ƙaraso?kuma dae tace kar na faɗama kowa,gaskiya bazan faɗa masu ba,zan basu mamaki ne nasan in suka ga mommy zasu yi murna sosai,amma kuma inason na sanya rishi a idanuna kafin nabar gidan nan,bari nayi sauri naje naga wankanta na yau,

Yayi maganar tare da nufar corridorn ɗakinsu sehrish da sauri da sauri ya ƙarasa kopar bedroom ɗin nata,

A lokacin tana acikin bedroom din nata sae faman zagaye takeyi,tarasa ya zatayi ta fita,kunya take ji su ganta da kwalliyar jikinta,

Jin kwankwasa ƙopar ɗakin nata yasa ta cewa”wanene,”

daga waje junaid ya amsa mata da cewa”Mijinki ne insha Allah,”

Murmushi ta saki tare da cewa”ka samu iznin shigowa ciki,daga matarka insha Allah,”

tura ƙopar yayi tare da sanya ƙafa ya shiga cikin ɗakin,koda yayi arba da sehrish nan take yaji gabanshi ya faɗi,kokwonto ya shiga yi yana tambayar kanshi Anya wannan sehrish ce kuwa?

matsawa kusa dashi tayi tace”meya faru junaid naga ka toge anan?

“Reesh,kinyi kyau Over,”cikin sanyin murya yayi maganar,don ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,

Ƙayataccen murmushi ta sakar mashi tare da cewa”saboda kai nayi wannan kwalliyar,launin lips dinka red colour ne,shiyasa nima na sanya jan lace don inyi anko da kai,to ya kaga wankan”?

tayi maganar tare da jujjuya mashi bayanta don ya kalla da kyau,aikuwa ba ƙaramin ruɗashi tayi ba,gaba daya yabi ya susuce,

Kamar yakai mata runguma haka yaje ji,amma ba halin yin hakan jikin shi sae faman kerma ya keyi,

juyawa tayi tare da nufar bedside drawer dinta,ta ɗauko wayarta tare da dawowa saitinshi ta ɗaga wayar tare da cewa”ka shirya in ɗauka?’tayi maganar tana jiran jin amsarshi,

Jin hannunshi ta gefen waist dinta yasa ta ɗan razana kaɗan,sosai ya ruƙo qugunta tare da kwantar da kanshi saman kafaɗarta yace”ki ɗauka,”

Zuba mashi ido tayi ta cikin camera ɗin tana kallon fuskarshi,hakanan ta dinga jin zuciyarta nayi mata wani irin bugu,muryarta akasalance tace”junaid ka buɗe idanunka,taya zan ɗauka dakai ido a rufe”?

Murmushi yayi tare da buɗe idanunshi yana cewa”Reesh,ƙamshin turaran nan naki,kashe mun jiki na yake yi,ba kiji yarda nake ji ba,don Allah reesh,kada ki guje ni kinji”?

Martanin murmushin ta mayar mashi sannan tace”junaid banda hankaline da zan guje ka?angaya maka kai irin mazan da ake gudu ne?kai fa na musamman ne junaid,tun farkon ranar dana fara zuwa aiki gidan nan,dakai nafara cin karo,a lokacin da nayi arba da wannan kyakkyawar fuskar taka mai ɗauke da wannan tsadadden murmushin,lokaci guda na rasa samun natsuwa,kasan Allah junaid da ace siyar da wannan murmushin naka kakeyi da ba ƙaramin ciniki zakayi ba Allah,”

Fashewa da dariya junaid yayi saboda jin kalaman sehrish akanshi,ba ƙaramin hura mashi kai tayi ba,kuma ta samar da farin ciki acikin zuciyarshi,

ɗaukar hoton sehrish ta shiga yi,style iri iri suka shiga yi ita da junaid,hada wanda ya manna mata kiss a gefen fuskarta,da kuma wanda ta lotsa yatsanta acikin dimple dinshi,hotunan sunyi kyau sosai,

Sae da suka kammala hoton sannan ta lura da zoben diamond ɗin dake hannunshi,sae faman ƙyalli yake yi,

Waro ido waje tayi alamar mamaki tace”wow junaid wannan fa,waya siya maka shi!”

“Mommy azeema ce ta bani shi,dama ɗazu na sanar dake cewa zan nuna maki gift din da takawo mun,to itace wannan,’

Ya ƙarasa maganar yana nuna mata zoben da Wrist watch din,

“Junaid sunyi kyau wlh,musamman daya kasance kaine ka sanyasu,”

“Thank u reesh,sunyi mun kyau amman idan ke kika sanyasu sae sun fi yi maki kyau,bari na ciro maki su ki sanya,nafison su kasance a hannunki,”

cikin sauri tace mashi”no junaid that’s impossible,Auntynku azeema ce ta baka shi,muddin ta neme shi a hannunka bata ganshi ba zata nemi jin ba’asin inda ka kai su,kuma ma in banda abun ka junaid wannan ae irin naku ne!kamar diamond ne fa,nida ko zoben azurfa ban ta6a sanyawa a hannu ba,balle diamond!

Kafin ya buɗe baki ya bata amsa wayarshi ta shiga ruri,nan take ya tuna da abunda mommynshi ta sanar mashi na cewa ta ƙaraso nigeria tana a Airport yaje ya ɗaukota,

Jiki na rawa yayi ma sehrish sallama tare da fucewa daga cikin bedroom ɗin,

Junaid bai sanar ma kowa ba,ya shige motarshi tare da janta yabar gidan gaba ɗaya,ya miƙi hanyar zuwa airport din cike da zumuɗin son ganin Mommyn tashi.

 

💋Boss Bature💋

 

A hankali sehrish ta sanya kafarta tare da fitowa daga cikin bedroom ɗin nata,a natse take tafiya yayin da takalman kafarta ke bada sauti kwas,kwas duk in ta takasu ƙasa,cike da fargaba ta tunkari babban falon gidan,

Jin takun takalmanta ne yasa matasan dake zaune acikin falon dawo da hankalinsu akanta,koda su kayi arba da sehrish,lokaci guda sukayi tsit yarda kasan mutuwa ta gifta,babu mai magana acikinsu ba don komai ba,sae don kallon da suka bita dashi,

Abbansu ne yayi ƙoƙarin cewa”Masha Allah my daughter,irin wannan kyau haka kamar sarauniyar kyawun duniya”?yayi maganar fuskarshi ɗauke da murmushi,

Ita ma murmushin ta shiga sakar mashi tare da ƙarasawa wurin table dinsu don ta gaishe dashi,a lokacin Abusufyan yabar wurin saboda kiran wayar da akayi mashi,yaje ya amsa kiran ne,

“Ina yini Abba,”

Lafiya lou daughter,tun ɗazu nake jiran fitowarki amma ban ganki ba,har azmee na tambaya ta sanar dani cewa kina nan zuwa,

Ya ƙarasa maganar tare da cewa”kinyi kyau sosai,da ace ƴa’ƴana zasu bari dana yi ta biyu dake……’yayi maganar cike da zolaya yana satar kallonsu fawan da suka ƙure ta da ido suna kallonta,koda suka ji abunda Abban nasu yace nan take suka ɗaure mashi fuska alamar basu son zancen,hakan ba ƙaramin dariya ya bashi ba,

 

Sehrish kuwa sunnar dakai ƙasa tayi tana wasa da yatsun hannunta cike da jin kunyar Abban nasu,

“Have a seat my daughter,”yayi maganar tare da nuna mata empty chair din da junaid ya bari,

Janyo kujerar tayi ta zauna har lokacin ta gaza sakin jikinta,

Muryar fawan ta jiyo yana cewa”Sister idan an kammala,zamu yi pic atare,”

Jahan yace”tunda tayi kwalliya ae dole ka nemi yin hoto da ita,mayen mata kawai,waccen dae tafi ƙarfinka Allah,ko kallonta ka cika yi sai Abban mu ya tuhume ka,don na lura da yadda yake ji da ita kamar mommynmu ce ta haife ta,”

. Dariya su kayi gaba dayansu,

Fawan yace”wai ni ina wannan tsinken sigarin take?

Atare suka haɗa baki wurin cewa”wa kenan”?

Irfan dake zaune a next table ɗin da ke akusa da nasu yace”yana magana ne akan wannan ƴar moli-molin da ke yawo acikin gidan nan,”

Kamar zautattu haka suka fashe da dariya,har sae da Abbansu ya tambayesu ko lafiya,suka ce mashi babu komai,nishadi kawai sukeyi,

 

adaidai wannan lokacin Abusufyan ya dawo wurin da suke,da alama ya kammala wayar da yake yi,wuri ya samu ya zauna yana fuskantar sehrish,daga ita har shi ba wanda ya lura da wani,

Gyaran muryar da Abba yayi mashi ne yasa shi ɗagowa yana kallonshi yace”meya faru ne yaya”?

Da ido yayi mashi nuni da sehrish yace”baka ganta bane,”

A hankali Abusufyan ya mayar da idanunshi kan sehrish dake zaune tana faman wasa da yatsun hannunta,gabansa ne yayi wani irin mugun bugu ji kake daram!!!a gigice ya miƙe tsaye hankali tashe yake kallonta,

Miƙewa Abba yayi yana kallonshi ganin yarda ya tsorata da ganin yarinyar,

Sehrish kuwa tuni ta firgita da ganin yarda Abusufyan ya razana da ganinta,hankali atashe itama ta miƙe tsaye tana kallonshi ido cikin ido,

Gaba daya fa kowa na falon ya miƙe yana kallon ikon Allah,duk atunaninsu uncle din nasu ya kamu ne shiyasa ya firgita da ganinta,

jikinshi har kerma yakeyi wurin nunata da hannunshi,ƙoƙari yake yi ya ambaci sunanta amma sam ya kasa faɗin sunan,saboda ya kakare mashi,wata irin zufa ce ta shiga gangarowa daga gafen fuskarshi,wannan abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,

 

Adai dai wannan lokacin Sgr da Marshal Omar suke saukowa down stairs atare,Omar ne agaba jikinshi sanye da shadda maroon colour,yayin da Sgr ke sanye cikin riga da wando na lallausan voile baƙi,wa’iya zubillah wato tsayawa bayyana irin yarda yadin yayi mashi kyau ma 6ata baki ne,don zan iya karashe littafin nan gaba ɗayanshi wurin kwatanta haɗuwar da sgr yayi acikin boyel ɗin wanda akai ma dinkin Senator style,irin style din da rigar bata karasa kaiwa gwiwa ba yayin da wuyan ke a matse sannan hannun rigan ya dan wuce gwiwar hannunshi kadan,yayin da takalman kafarshi da agogon hannunshi duk launi ɗaya ne da boyel ɗin jikinshi,bai sanya hula ba akanshi,sai dae ya ɗaure sumar kan tashi,a tsakiyar kanshi,hakan ba ƙaramin kyau ya ƙara mashi ba,wani irin daddaɗan kamshi ne ke fitowa daga saƙo da lungu na jikin kowannan su,fuskar nan tashi kamar ya aza mata makeup saboda tsabar kyan da tayi,yadin ba ƙaramin fito da hasken fatar shi yayi ba,yayi fari sol dashi,kamar asace don kyau,yarda kasan diamond haka ya koma,tauraro mafi haske acikin taurari.

cike da wannan tafiyar tasu ta majiya karfi suka ƙarasa saukowa daga saman benen,

Adai dai lokacin wayar Omar ta shiga ruri,hannu ya zura tare da curota daga cikin aljihun wandon shaddarshi,ganin sunan major ya bayyana akan screen din wayar yasa shi picking call ɗin ya kara wayar a kunnan shi tare da cewa”kun ƙaraso ciki ne?

On the other hand major yace”Eh,yalla6ai yanzu haka mun ƙetaro babban gate din gidan tare dasu,yayi maganar yana kallon su hosana dake zaune a back seat ta cikin mirror din gaban motar,fuskokinsu dauke da farin ciki yau zasu ga Sehrish ɗinsu,

Omar yace”Okey,ka shigo dasu kawai,”yana fadin hakan ya katse kiran sannan ya bi bayan Sgr suka ƙarasa cikin main palour din.

Domin Sauke cikakken Littafin ku danna inda kaa saka Download 👇👇

 

Back to top button