Hausa novels

Harijin Sarki Page 36 Romantic Hausa Novel

A can nesa cikin duhu Ameer yana tsaye gaban madubin ƙaddara.Madubin ya nuna masa yadda Rayyan ke haskakawa har cikin idanu.Ya harare shi, muryarsa ta canza ta zama mai nauyi “Yaron nan yana ɗauke da alamar haske, amma zan same shi ta hanyar mafarki Duhu ba ya mutuwa, sai haske ya yarda” Ya ɗora hannunsa jikin madubi ya furta sunan jaririn “Rayyan…” Madubin ya motsa, ya nuna fuskokin mutane daban-daban wasu kamar bayin fada, wasu kuma kamar masu sihiri.“Ku shirya,” Ameer ya ce cikin ƙara, “za mu shiga cikin mafarkinsa kafin ya kai shekara ɗaya”Daren yazo da sanyi.Samha ta kwantar da Rayyan tana yi masa lullubi da addu’a, har ta lumshe ido.Cikin bacci, ta ga Rayyan tsaye a cikin fili mai haske yana kiran ta Ummi, ki bar tsoro Ni ba jariri bane kawai Allah ne ya ba ni hasken da duhu ba zai iya kashewa ba.”Ta ruga zuwa gare shi, amma sai wata murya daga gefe ta ce.“Amma duhu yana neman gadonka, Rayyan Za ku haɗu a mafarki nan gaba”Samha ta farka cikin tashin hankali ta rungumi ɗanta da ƙarfi tace “Ya Allah, Ka tsare ni da shi Ka hana duhu samun hanyar zuwa garemu”Sai ta ji kamar muryar Sheikh Zayyad daga cikin zuciyarta“Haske baya gudun duhu, Samha Haske yana tsarkake shi”Ta share hawaye, ta murmusa cikin ƙarfin imani, ta ɗaga hannu “To in haka ne, hasken Allah ya ci gaba da kare wannan ɗa”Rayyan ya buɗe idanunsa hasken ya sake cika ɗakin, sannan ya rufe ido yana murmushi kamar yana jin addu’ar da aka yi masa.Daren nan, rana ta rufe duniya da duhun da taurari suka ɓace.Ameer yana cikin ɗakin tsafinsa, madubin ƙaddara a gabansa yana ta fitar da hayaki mai duhu kamar gubar da ke ƙonewa a iska.Ya miƙe cikin keken zinare, hannunsa ɗaya riƙe da zoben da aka sassaƙa da lu’ulu’u daga ƙasan Baharain — zoben da ya haɗa jinin sarki da jinin bokaye “Rayyan…” ya kira cikin murya mai cike da ƙiyayya “Jaririn haske, yau zan ziyarci mafarkinka. Zan rufe muryar haske da sautin duhu!” yana gama faɗar haka iska ta motsa, madubin ya faɗi ƙasa, ya fara juyawa kamar ana katantawa dashi Ameer ya rufe idanunsa, ya shige cikin duhun mafarki.Cikin duniyar mafarki wuri ne mai hasken sama kamar alfijir, Rayyan yana zaune kan dutse yana wasa da takobi a hannunsa.Samha ta bayyana daga gefe, cikin farin rigar nur, tana kallonsa da murmushiAmma sai iska ta canza, gajimare ya rufe sararin samaWata ƙarar tsuntsaye masu baki suka cika sararin su ne aljannun Ameer.Sai Rayyan ya ɗago kai cikin natsuwa, yace da su:“Na san kun zo da duhu, amma ku tuna duhu baya iya rufe rana”Ameer ya bayyana daga tsakiyar ƙura, fuskarsa ta cika da annuri mai ɓarna. “Kai ne jaririn da ke yin dariya da haske! Amma yau zan kashe muryar dariyarka har abada” Ɗaga hannunsa yayi ya miƙe madogaran tsafi, ƙasa ta fara girgiza.Wani dodo mai fuskar azaba ya fito daga ƙasa yana ɗauke da wuta mai launin baki.Sai Rayyan ya juya, yana kiran:“Ummi!”Cikin ɗan lokaci, haske mai kamar rana ya bayyana Samha ta bayyana a cikin mafarkin, cikin tsarki da addu’a.Ta ɗaga hannunta tana karanta“A’uzu billahi mina sh-shayṭanir-rajīm!Bismillahir-Raḥmānir-Raḥīm!”Haske ya watse kamar walƙiya, ya bugi dodon, dodon ya yi ƙara kamar an hura ƙaho, ya watse zuwa gawayi. Ameer ya firgita, ya yi ƙoƙarin gudu, amma ƙasa ta kama ƙafarsa.Ya ga Rayyan yana kallonsa da idanun da ke cike da haske yace “Me yasa kake tsoron haske, Babana Ameer?”“Saboda haske yana nuna min fuskata ta gaskiya!”ya faɗa yana ƙara, jinin idonsa ya rufe.A lokacin, Sheikh Zayyad wanda yake addu’a a zahiri a cikin gidan Samha, sai ya ji iska ta motsa.Zanen da ke kan ƙasa, wanda yake rubutun “Wa maa hum bidhaarreena bihi min ahadin illa bi idhnillah” (Al-Baqarah:102), ya fara haskakawa.Haske ya bi ta madubin ƙaddara inda Ameer yake, ya bugi fuskarsa da ƙarfi.Ameer ya yi ihu mai ban tsoro, madubin ya fashe ya watse gida-gida, hayaki mai wari ya cika ɗakin, wata murya daga sama ta ce cikin tsoro tace.“Ka taɓa abin da ba naka bane, Ameer. Haske baya mutuwa.”Ameer ya faɗi ƙasa, hannunsa na rawa.Zobensa ya narke ya koma toka.Kafin ya rasa hayyacinsa gaba ɗaya, ya ji muryar Rayyan tana ratsawa cikin kunnensa yana cewa “Ka nemi gafarar Allah kafin ka rasa damar komawa duniya” A gefe guda Samha ta farka daga mafarki cikin zufa, tana riƙe da jaririnta da hannaye biyu,Rayyan yana barci cikin nutsuwa murmushi a fuskarsa kamar mai nasara.Rashid da Granny suka shigo da hanzari suna tambayar “Me ya faru?” Samha tace cikin murya mai taushi“Haske ya kare kansa yau Kuma duhu ya rasa ƙafafunsa” Sheikh Zayyad ya shigo cikin nutsuwa, yana kallon Rayyan.“Alhamdulillah… wannan jaririn ba kawai al’amari bane. Shi ne sakon da Allah ya ƙaddara kafin sarauta ta fara. Kuma daga yau, duhu zai fara jin tsoron mafarki”Sai iska mai sanyi ta buso, fitila ta yi walƙiya,ƙamshi me daɗi ya sake cika ɗakin……..

Back to top button