Hausa novels

Zakuna Biyar Page 35 By Princess Teema

DEATH OR LIFR (DOL)🔥Sai ya nufi hanyar bakin ruwan, har ya É—an yi step 2 sai kuma ya juyo, kai tsaye ya nufi cikin É—akinsu Arya É—in. A tsakiyar É—akin ya tsaya, ya zuba mata idanu, tana zaune saman electric mattress É—insu, ta sanya bluetooth a kunne, dik iskar dake tashi bata da labari.Angelina dake zaune gefenta ne ta taÉ“ata game da cewa. “Ke”. ÆŠago kanta yi daidai lokacin da take cewa. “Kai ma muryanka na da daÉ—i ai causin…….”. Gagara karisa maganar ta yi a lokacin da idanunta suka sauÆ™a a kan angry face É—in Noor. Da sauri ta zabura ta miÆ™e tsaye, wani irin mugun kallo ya dallah mata wanda bai san ya yi ba, in a harsh way ya ce. “Da waye kike waya?”…… Da sauri ta cire bluetooth na kunnenta, hannunta na É—an kerma, dan gabaÉ—aya yadda ya É—aure faska ya razanata, murya na É—an rawa ta ce. “Wani….. Wan…. Wani brother É—ina ne”.Wani kallo da ya wurga mata ne yasa ta haÉ—iyi yawu gwad…… “Ashe kina da brother kenan?”. A faÉ—a…… Kallonsu Angelina da Manassa suke yi, while Manassa na ta faman rikita hankalin Vash dake cikin tantansu, ta gama ce mashi wai ta gani a in da yake ana ruwan sama, kuma zata kawo mashi ziyara daren yau, dik ta rikita bawan ALLAH, wlh ya yarda aljana ce. “No, he’s my Aunty’s son, tare muka yi school, mother É—insa sister É—in dad ne…….”. Hannun da ya É—aga mata ne yasa ta haÉ—iye sauran maganar. Cikin fushi ya ce. “Kuma kike cewa he have a sweet voice ko?”..Tsuru-tsuru ta yi da idanu, dan bata zaci ya ji ba, kuma wlh ita ba da wata manufa ta faÉ—a ba, kawai guy É—in ya ce mata your voice is so sweet shi ne ita ma ta ce naka ma da daÉ—i, kun gane irin wannan abin ai? Wai ka É—an mayarwa mutum magana mai daÉ—i, ashe sarkin kishi kuma lover boy É—inmu ya jita. Jama’a watau family É—in Noor duniya ne, lovers ne, ga kishin balai da iya shagwaÉ“a.Kai ya É—an jinjina. “Your voice is so sweet”. Ya maimaita yana É—an jinjina kai……. Zata yi magana daga cikin wayar guy É—in ya ce. “Vanisha are you okey?”.Ta É—an zazzare idanu a kan face É—in Noor kafin ta ce. “Nothing Yosif”….. “I hear like kina magana da wani, who’s he?”……… Ƙara zazzaro idanunta a kan Noor ta yi. Daidai lokacin su Angelina suka mimmiÆ™e tsaye suna kallonsu. Wani irin kallo Noor yai mata like ki bashi amsar da waye kike magana!.ÆŠan tattauna lips É—inta ta fara yi. “Yosif bye”. Tana faÉ—a ya katse kiran. Muryarta na É—an rawa ta ce. “My Romeo…….”. Bai jira jin me zata ce ba, waje ya nufa cikin fushi.Da gudu ta rufa mashi baya, a tsakiyar wajen tantin nasu ta tare gabansa, kamar zata yi kuka ta ce. “Please my Romoe, isn’t what you’re thinking……”.In a harsh way ya ce. “How do you know that I’m thinking something? Or you’re hiding something for me right?!”…… Kai ta fara girgiza mashi, kawai tasan yadda ya fita nan ne zai yi tinanin ko soyayya take yi da wani, shiyasa ta ce isn’t what he’s thinking, amma ya sake fassarata ta wani sigar.RaÉ“awa gefenta ya yi zai wuce, a lokacin ruwan saman ta fara karfi sosai. Da gudu ta juya, ta ruga ta faÉ—a bayansa, ta Æ™anÆ™ame shi tightly, hakan yasa dikkan sojojin dake kallonsu suka yi Æ™asa da kai dan girmanawa a garesa. Tsalle ta yi ta haye bayansa, ta saÆ™alo wuyansa. Aikuwa cikin fushi ya dawo da ita ta gabansa, da karfi ya yakiceta daga jikinsa, ido cikin ido ya kalleta, ga ruwa na zuba a kansu, a fusace ya ce. “Kada ki sake taÉ“ani, ina baki wannan umarni ne ba amatsayin masoyinki ba, sai a matsayin oganki!!”. Yana gama faÉ—in hakan ya saketa tare da tureta gefe, ya wuce ya nufi bakin ruwa. Abinku da bata taÉ“a faÉ—a da shi ba, durkushewa Æ™asa a wajen ta yi, kuka ta fara yi, ALLAH sarki bata san komai ba sai soyayyansa, slowly ta kifa kanta a Æ™asa, wani irin kuka ne ya kubce mata. Da gudu Angelina da Manassa suka yo waje. Angelina ce ta watsa da gudu ta yi kanta, a cikin ruwan ta je ta rungumota tana bata hakuri.Takaici tamkar Arya dake tsaye a bakin tantin ta rufesu da duka, sun zubar mata da mutunci a cewarta, siririn tsaki ta ja tare da komawa ciki abinta. Daidai lokacin Unays ya fito, ganin Angelina a cikin ruwa ne yasa ya yi gaggawar shiga ciki shi ma, ya isa daidai lokacin da Angelina ta É—ago V, sai dai V na ta famar langwaÉ“ewa tana a barta a cikin ruwan ita kam. Sai hakan ya zamana kamar ta fi karfin Anglina ta gagara É—agata.Ganin hakan yasa Unays ya ce. “Let me help you, bari in kai maki ita É—aki”. Ya faÉ—a yana matsowa zai É—auketa wai irin shi zai taimakawa Angelina ko zai zamu ya sace zuciyarta, taÆ™i kulashi ne, yana ta neman dama……. Matsawa baya Angelina ta yi tana faÉ—in thanks………. Hannu yasa zai cicciÉ“i V, sai kuma ya tsaya cak, da sauri ya ja da baya daga kusa da ita kallonsa a kan Noor dake nufosu tamkar wani zaki, shi da Leo duns bubbuÉ—e kamar zakuna, ya nufo wajen yana dallahwa Unays É—in wani irin mugun kallo mai kama da ka taÉ“ata kaga yadda zan yi da rayuwarka.”Ki É—auketa kawai”. Unays ya faÉ—a yana Æ™ara ja da baya game da mai da kallonsa a kan Angelina É—in. Ta yi mamakin jin ya fasa taimaka mata, ita kanta V mai kukar ta yi mamaki. Slowly ta É—ago kai karaf suka yi 4 eyes da Noor. Ƙara É—aure fuska tamau ya yi, ya É—auke kallonsa daga kanta, ya zo ya wucesu tare da Leo.Angelina ta gane karatun, watau Noor ne ya hana Unays É—aukar V, ya ALLAH kaga wata soyayya da kishi ga fushi a gefe, kai Noor akwai rigima wlh, ya dai yi fushi, amma ba zai bari wani ya kusantota ba…….. Sai dai ita V É—in bata gane ba, ta zaci ya daina sonta kenan, shiyasa take ta faman kuka.Arya kuwa tana komawa ciki ta hau aikinta na duba drone da suka tasa a wannan daji, ta share su V, a cewarta basu da hankali sam-sam.Tantin Leo suka shiga shi da Noor, a saman electric mattress É—in Leo suka zauna, Noor ya yi Æ™asa da kai tamkar mai tinanin wani abu, kallo É—aya Leo yai mashi ya É—auke kai tare da faÉ—in. “What are you thinking?”……. Nisawa ya É—an yi. “My Jeliet, na wuceta tana kuka, zuciyana tamkar ba zai iya É—auka ba”. Wani kallo Leo ya wurga mashi like baka da aikin yi, daga nan yai shiru bai yi magana ba. A daidai lokacin Arya ya faÉ—o É—akin bakinta É—auke da excuse, sai da ta faki idanun Leo ta dallah mashi harara kafin ta Æ™ame ta sara mashi. Noor ya ganta sarai, a cikin ransa ya ce. “Ban san me yake tsakaninsu ba, kullum sai Arya ta harari brother É—ina, anya ba son shi take yi ba?”.Shi kuwa Leo yana zaune shiru bai motsa ba bare ya É—ago ya kalleta, a dake ta ce. “Sir, there’s something you should come and see!”. Kai kawai ya É—an jinjina ba tare da ya É—ago ba. Juyawa ta yi ta fita, amma kafin nan sai da ta dallah mashi mugun harara.Tana fita ya miÆ™e tsaye, kayan jikinsa ya fara ragewa, shi kuwa Noor ya gyara ya kwanta cike da tinanin V a ransa. Pjs jade color kalar idanunsa Leo ya sanya a jikinsa, ya tara kitson kansa ya É—aure da kyau kafin ya sanya winter coat a saman pj’s É—in, sannan ya sanya beanie, beanie wata hular sanyi ce irin mai laushi sosai É—in nan. Bayan ya kammala ya fita ya nufi room nasu Arya. A lokacin Angelina ta yi ta maza ga É—auki V sun shige cikin tantin nasu.Zaune ya isko Arya gaban laptop É—inta tana duba dajin da kyau. Jin kamshin perfume É—insa yasa ta É—ago kai, zuba mashi idanu ta É—an yi, while shi kuma yana kallon gaban screen na laptop É—inta.Gently ya taÆ™o ya Æ™ariso, dik É—akin natsuwa tsit suka yi, Manassa da Angelina suka zubawa Leo idanu, V na kife saman mattress É—in har yanzu tana kuka. HakiÆ™a Manassa ta ce Leo yana yi mata yanayi da Vash, musamman idan zai yi magana, sai ka zaci Vash ne yake motsa baki yake magana a wajen, dimple É—insu iri É—aya, sharpe na eyes É—insu iri É—aya, dan dai idanun Leo jade ne, kuma kamar sleeping eyes haka suke, na Vash kuma a waje suke gulu-gulu, amma shape É—in É—aya.Saitin in da Arya take ya tsaya, slowly ya É—an sunkuyo kanta kaÉ—an, zubawa dajin idanu ya yi for 2 mins, sai kuma ya ce. “Wannan ai hayaki ne?”. ÆŠagowa da kallonta a kansa ta yi, sai taga ba ita yake kallo ba, shiru ya É—an sake yi, can kuma ya kai hannunsa saman mouse É—inta, ya É—an yi Æ™oÆ™arin yin gaba da drone É—in, amma sai abin ya ci tura, ya yi iya yinsa abin yaki yiwa.Slowly ya dawo da kallonsa a kan, while ta tsaye Æ™ashin wuyan nan nasa da ya fito sosai da kallo, kunga ya sunkuyo kanta ne, so tana iya kallon wuyansa sosai. Ganin ya dawo da kallonsa a kan face É—inta wani irin rass gabanta ya faÉ—i, gagara kallon cikin idanunsa ta yi, cikin zafa ta yi Æ™asa da idanunta. “Meyasa drone É—in yaki yin gaba?”. Ya faÉ—a in a cool way. Sai da ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, ta saita natsuwarta kafin ta ce. “Nima ban san meyasa ba, amma na fi tinanin akwai gagarumin abin da dake bayan dogayen bishiyun da hayakin ke fitowa daga wajen ne”. Tana magana muryanta na É—an rawa, dan gabaÉ—aya ganinsa a dab ita ya rikitata, har take jin kamar numfashinta zai É—auke.Daidai lokacin Zaynish ya shigo hannunsa rike da bindigarsa, yana sanye da army waterproof jacket, ya yi kyau matuÆ™a, a kusa da Leo ya Æ™ariso ya tsaya, zuba mashi idanu su Angelina suka yi, a dake ya sarawa Leo kafin ya rage tsawonsa, ta É—an sunkuyo yana kallon wajen.A daidai lokacin Noor ma ya shigo, dan jin Leo shiru. Yana shigowa V ta miÆ™e zaune tana kallonsa, shi kuwa tamkar bai san da zamanta a wajen ba, a É—ayan gefen Leo ya tsaya, ya zamana Arya da Leo suna Tsakiya. Zubawa hayakin wajen idanu suka yi. Hayaki ke bakinkirin yake tashi a tsakiyar dokar daji, gaba daji baya daji, waje mak sunkuru da cikowar itatuwa, waje ne da ba zaka taÉ“a yarda halittar É—an adam tana rayuwa a wajen ba, akwai alamar ban tsoro a wajen, ga wasu manyan tsaunuka da koguna a wajen.Noor ne ya ce. “Idan muka yi duba da tsuntsayen dake shawagi a sararin samaniyar kewayen hakan na nufin akwai tabkeken reku a wajen! Idan kuwa haka ne lallai ba shakka wannan teku dake kusa damu ta ratsa ta wajen”..Jinjina kai Leo ya yi alamar haka ne, in a cool way sosai ya ce. “Idan kuwa akwai taku a wajen to tabbas akwai wutar lantarki a waje, dik yadda aka yi akwai igiyoyin wuta sosai a wajen wanda su ne suka haka drone É—in nan wucewa, lallai muna buÆ™atar sanin menene a wajen cikin gaggawa, dan ga dikkan alamu gagarumin abu ne a wajen”……. Jinjina kai Zaynish da Noor suka yi, su kuwa matan gabansu ne ya yi mummunar faÉ—uwa jin batun da mazan ke tattaunawa.Zaynish ya ce. “Idan muka yi duba da hayakin dake tashi ba hayaki ne na yau da kullum ba, lallai wannan hayaki gagarumin abu ne ake Æ™onawa, ku yi duba da yadda yake tashi sama, a maimakon ya yi sama gabaÉ—aya, sai yana watsewa a cikin dajin, alamar abin da ake Æ™onawa yana É—auke da guba”.Kai suna jinjina alamar haka, ba shakka a zancen Zaynish….. Jama’a ku tafawa renon AZURE, sun san aiki!.Leo ne ya ce. “Zaynish, Noor, ku kira Vash ina da magana daku a É—aki”…… Da okey sir suka amsa, dawo da kallonsa a kan Arya ya yi. “Keep watching the place, komai Æ™anÆ™antar motsi ki sanar dani”. Yana kai karshe ya miÆ™e daga kanta, cikin zafa ya nufi waje.Bayansa ta bi da kallo, bata iya zare idanunta ba har sai da Zaynish ya zo wucewa, sannan ta É—auke kai. Sunkuyowa kanta Noor ya yi, cikin zola ya ce. “Brother É—ina yai maki kyau ne?”. ÆŠago da kallonta a kansa ta yi, zata mashi tsiwa sai taga yai mata mugun kwarjini, haÉ—iye maganarya ta yi, ta É—an yi Æ™asa da ido. ÆŠagowa yai zai nufi waje raunatacciyar muryar V ta katse shi da cewa. “My Romeo”. Ai Æ™ara É—aure fuska ya yi, ya fice da sauri ba tare da ya kalli in da take ba.Yana fita V ta fashe da sabon kuka tare da kwantowa jikin Angelina tana É—an shessheÆ™a, yau Romeo ya yi fushi mai zafi da ita. Ita kuwa Arya ta cigaba da kallon aikinta, Manassa da Angelina suka zauna yin gulmar Leo da Zaynish, ba su yi gulmar Noor ba saboda kada V ta sauke haushi a kansu. A yayin da a waje kuma ruwan sama na zuba tamkar da bakin kwarya, while sojojinsu guda 34 ciff suka tsaye cikin ruwan kewaye da tantunansu dan bada tsaro, sun sanya army waterproof jacket. To mu leÆ™a sashen jigon labarinmu, mu É—an duba su sister Maya sai mu sake dawowa, watakila kafin mu dawo sun gano wani motsi, su kuma lovers Romeo and Juliet kila zasu shirya. ————————-🔥WS-HOSPITAL.🔥Sister Maya ta bata labarin abin da Dr Kamal ya ce mata, sosai sister Zinta ta tayata murna, suka hau tsara yadda zasu kula da 3D har su samu soyayyarsu sosai!…. Bayan sun kammala hiran, sai suka tashi, suka shiga baiwa jariran madara wanda nurses suke haÉ—a masu suna ajiyewa kowani baby a jikin bed É—insa. Suna baiwa yaran suna murmushi suna cigaba da baiwa junansu shawarin yadda zasu kara sace zuciyoyin 3D.A É—ayan É“angaren kuma, 3D tsaye a cikin SECTION E, a É—akin Drugs factory É—insu. Dr James tsaye gaban wasu injuna, yana sanye da kayan Æ™ariya, yau nose mask dake face É—insu irin manyan nan ne masu É—auke da oxygen, hakan zai sanya ba zasu shaÆ™i numfashin Drugs factory É—in ba, wannan oxygen ya wadatar da su. Dr Kamal ne ya É—auko wannan jini dake bokiti, wanda suka sanya a freezer ta daskarar masu da shi, tin É—azun dama suka ajiyesa a waje mai É—umi, ya narke, a cikin wani tangameme faranti mai zurfi ya zuba jinin, wani karfe dake tsakiyar farantin ya fara jujjuyawa yana kwaÉ“a jinin, engine ne wajen.Almost 10 mins, wannan inji yana juya jinin jaririn, sai Dr James ya É—auko wani ainahin sinadari a cikin kwalba wanda ake cewa collagen peptides ya zuba a cikin jinin jaririn. Collagen peptides sinadari ne dake Æ™arfafa fata, hana wrinkles, da inganta laushin fata.Ya barshi kamar 10 mins injin na mixing É—insa, sannan ya sake É—auko ainahin sinadarin retinoic acid ya zuba a ciki, manyan kwalabe ne sosai fa yake É—aukowa, sinadarin retinoic acid yana sabunta fatar jiki, rage wrinkles, da hana tsufa.Bayan ya zuba injin ta yi mixing like 10 mins sai ya sake É—auko, hyaluronic acid shi ma ya zuba a ciki. Hyaluronic acid ainadarin ne dake hana bushewar fata, yana sa fata ta yi taushi da Æ™yalli tamkar glass, bayan ya zuba dakamar 10 mins shima sai ya sake É—auko kwalbar nicotinamide mononucleotide ya zuba a ciki.nicotinamide mononucleotide sinadari ne dake sabunta kwayoyin halitta, watau cells da kuma kashe alamun tsufa. After 10 mins inji na mixing, suka haÉ—e da juna da jinin jaririn, sai ya sake É—auko resveratrol ya zuba a ciki. resveratrol ana samun shi ne a cikin inabi, yana da tasiri wajen hana tsufa da kuma kare fata daga lalacewa, yana da matuÆ™ar amfani a aikin 3D. Baya ga shi sai ya É—auko coenzyme ya sake juyewa a ciki. coenzyme yana da matukar amfani wajen inganta kuzari a cikin jiki da kuma hana lalacewar fata, bayan shi ya É—auko kwalbar epidermal growth factor ya zuba a ciki. Epidermal growth factor sinadarin ne dake sabunta fata a gaggauce cikin Æ™anÆ™anin lokaci ya warkar da raunuka da dik wani tabo, ki koma tamkar Æ´ar tsana, babu tabo ko kaÉ—an a jikinki.Ya sake É—auko stem cells watau Æ™wayoyin halitta na asali ya zuba a ciki, in jin dai tana nan kunne tana mixing komai ta haÉ—esu su zame abu guda.stem cells yana sabunta fata da gyaran jiki gabaÉ—aya, daga shi sai ya É—auko alpha lipoic acid ya sake zubawa, tsabar yadda injin ke mixing har wani hayaki-hayaki ne yake tashi daga cikin farantin, ga sinadaran da ake ta daddalawa a ciki. To alpha lipoic acid shi ma sinadarin ne dake rage kumburin fata da hana tsufa. Daga shi sai ya É—auko babbansu kuma na Æ™arshensu watau glutathione ya zuba. Wannan sinadarin yana sa fata tayi haske sosai, yana cire wrinkles, komai yawan tamu-tamun tsufarki zai yi fata-fata da shi ya mai da skin É—inki very smooth tamkar yarinyar Æ´ar 13 years, yana da karfi sosai, a take yake cire tamu-tamun, sannan ya fi sauran dik sabonta fata da hana shi tsufa sosai.Yauwa kafin mu wuce gaba, dama na ce maku zan yi maku bayanin kan sinadaran dake cikin jinin jariri dan ku samu Æ™arin ilmi kuma ku fahimta da kyau, dan haka kafin mu ce zuwa gaba ku ji me 3D zasu aikata, bari in baku wannan bayani.A jinin jariri akwai sinadarin hematopoietic stem cells kamar da na faÉ—a a haba, to hematopoietic stem cells sinadarai ne dake samar da sabbin Æ™wayoyin jini red & white blood cells. Ana amfani da su wajen warkar da cututtuka kamar ciwon sankara, sannan suna wanke tsoffin jini. Na biyu a baya na ce a jinin jariri akwai sinadarin mesenchymal stem cells su kuma waÉ—annan Æ™wayoyin halitta suna taimakawa wajen sabunta fata, Æ™ashi, da sauran sassan jiki, dik tsufarka zaka zama sabon matashi mai ji da karfi da lafiya tamkar É—an yaro under age.Na uku a jinin jariri akwai erythropoietin, shi kuma sinadarin da ke taimakawa wajen samar da jan jini red blood cells, kun san jan jini daban yake, masu shi daban suke, da lafiya da karfi.Na huÉ—u akwai fetal hemoglobin. Wannan nau’in haemoglobin ne da ke cikin jinin jariri, wanda ke da Æ™arfin É—aukar iskar oxygen fiye da na manya, idan ka yi amfani da maganin 3D hmmmm, karfi da lafiya kam a dai yi shiru kawai. Na biyar akwai alpha fetoprotein, wannan sinadari ne da ake samu a cikin jinin jariri, wanda ke sabonta garkuwar jiki, idan kin tsufa garkuwar jikinki ta raunata ta yadda kowani cuta zai iya yi maki shigar farad É—aya, to wannan sinadari na sabonta garkuwar jiki, ki zama tamkar yara.Na shidda akwai Interleukins & growth factors, waÉ—annan sinadarai ne dake Æ™arfafa garkuwar jiki da kuma sabunta Æ™wayoyin halitta. To su ne a jinin É—an jariri wanda sai sun razana jaririn suke samo jikinsa ya sakarwa jininsa waÉ—an nan sinadaran ta yadda in sun marÆ™aÉ—a shi sun matso jinin zai zo É—auke da sinadaran!.To mu cigaba da bibiyar 3D yau mu ga abin da ya turewa buzu naÉ—i, amma kafin nan ina da tambaya! Mun gama jin na jini, to shi kuma É“argon Æ™ashin fa? Me suke yi dashi? A gaskiya shi fitina da balainsa ya fi na jini, a hankali zamu iso garesa, zaku ji komai, haÉ—arinsa yawa ne da shi, shiyasa na ware mashi lokaci na musamman.Bayan kamar 30 mins da kammala zuba sinadaran injin na mixing Dr Mark ya tsayar da injin, komai ya haÉ—e sosai. Dr Kamal ya É—auko color É—in da suke buÆ™ata, white suka sanyawa haÉ—in, take da injin ya sake mixing komai ya zama fari tas tamkar farin fenti, ba zaku taÉ“a cewa akwai jini a ciki ba, Dr James ya É—auko fm, sinadarin dake kashe Æ™arnin jini da dik warin wasu sinadaran, ya zuba a ciki, suka É—auko wani powder mai kamshin inabi da sauran kayan itatuwa suka zuba a ciki.Injin ya sake mixing sosai kafin su sake kash injin. Sannan suka danna wani madanni, gabaÉ—aya farantin ya yi sama, ya juye maganin cikin wani abu tamkar ball, daga nan suka kunna wasu injuna dake gaba guda biyu kafin su kunna makunnin wannan ball É—in. Nan take ball É—in ya fara motsawa yana sama ya É—an yi Æ™asa.Matsawa kaÉ—an suna yi izuwa karshen injinan suka tsaya, a wajen akwai wani katon baff a bakin karshen injunan. Sun rungumo hannayensu a saman kirji, idan suna aiki ba’a magana, babu wanda ya ce da wani Æ™ala, kowannensu yana lissafin kan yadda zasu Æ™ara inganta aikin nasu ne.After 30 mins da tsayuwarsu a wajen sai ga bakin injin ya buÉ—e, you can’t believe what i saw my people. Ya ALLAH, a jere drugs suka fara zubowa a cikin wannan baff É—in, yadda kuka ga ake arranging magunguna a cikin saches É—insu, haka waÉ—an nan magunguna suka fito daga cikin injin, ko kasheki za’ayi idan ba’a gabanki aka haÉ—a wannan magani ba ba zaki taÉ“a cewa akwai jini da waÉ—an nan sinadaran a ciki ba, pure magunguna ne a ciki farare Æ™al….. Kin taÉ“a jin maganin hana tsufa? mai da tsohuwa yarinya.To waÉ—an nan magunguna ba komai bane face magungunan mai da tsohuwa yarinya, maganin gyaran jiki, skin É—inki ya zama irin na waÉ—an can na kwana, maganin glowing, lightning, glass skin da sauransu, zai sabonta maki halitta cikin Æ™anÆ™anin lokaci. Shiyasa basa karÉ“ar sperm da eggs na munana sai kyawawan mutane, dan dik wanda ya sha maganin ya zama yaro, ya kuma yi kyau sosai, shiyasa dik nurses dake cikin wannan asibitin suke da mugun kyau, dan sperm and eggs na kyawawan gaske ake É—aukowa! Fatan yanzu kun gane dalilin da yasa dole sai na kyawawa!.To ina matan littafin nan masu shan maganin gyaran jiki? Masu shan maganin Æ™arin haske, su skin care manya! To koma dai me ga abin da kike sha nan, mu munga komai, munga dik abin da 3D suke haÉ—awa, dan haka mu bamu a wannan layin na su glowing, ko ya kuka ce mutanen kirki?….. Watau ni kaina ina kiÉ—imewa idan na tina abin da suke haÉ—awa da wannan É“argon Æ™ashin jariran fa, mun dai ji na jini, ko ya na É“argo da kuma shi kansa garin Æ™ashin da tsoÆ™a É—ika yake? Yanzu shikenan jarirai guda biyar É—in nan sun tafi har abada? Haka zasu cigaba da salwantar da rayuwan jarirai? Suna niÆ™asu tamkar masara! Tamkar ba rai bane da su? Wannan wace iriyar balai ce, rai fa, su É—auka su saka cikin inji ya niÆ™a ya fitar masu da jini daban, garin tsoka da Æ™ashi daban, É“argon cikin Æ™ashi daban, rai fa, ran ma na jaririn da bai ji ba bai gani ba, bai san komai ba, la haula wala Æ™uwata illah billah, allahumma ajirni fi musibatin, wannan musifa ina zamu tsaya da ita? Ba dole jama’a su dinga ganin tashin hankali da musifu ba, ace Æ´an É—an adam akewa wannan É—ibar albarka, ya ALLAH.Bayan magungunan sun gama zuba ne 3D dikka suka É—ebo ruwa a boket duka zuba cikin farantin da ya haÉ—a maganin da farko, sannan suka kunnasa, farantin ya yi sama, ruwan ya zuba cikin ball, daga nan suka sake tsayawa a gefe. After 30 mins sai ga magunguna da basu kai ka farko ba sun fara fitowa, watau marasa karfi sosai aka yi yanzu da É—aurayar inji. WaÉ—an nan marasa karfi sosai É—in sai kun sha sosai yake biyan buÆ™ata, kuma shi ne mai arha daidai talakawa!. A baff daban marasa karfin suka zuba, dan da na farko ya gama fitowa sun janye baff É—in gefe, sai suka sanya wani.Bayan komai ya gama fita sai suka haÉ—a karfi suka cicciÉ“i baff É—in magani mai karfin suka fito dashi wajen É—akin, suka koma suka É—auko mara karfin suna fito da shi waje. (Ni na rasa ma wani irin suna zan baiwa wannan É—aki saboda musifar dake cikinsa, kai ya ALLAH. To bari dai mu bashi sunan É—akin niÆ™a jariran, tin da babban abin da suke yi a ciki kenan.A wajen É—akin niÆ™a jariran suka dire baff dikka biyu É—in, magunguan yana dayawa, ga baff É—in da girma, sai da suka yi da gaske suka iya É—auka. Suna ajiyewa Dr Mark ya kira guards madaka karti su uku suka zo suka É—auki baff É—in, amma kafin su Æ™irasu sai da suka rufe kofar É—akin niÆ™a jariran da matakan tsaronsu na wutar lantarki, babu wani mahaluki da yake shiga masu wannan É—aki, su kaÉ—ai suke shiga, saboda su kaÉ—ai suka san É“arnar da suke yi a ciki. Bayan guards É—in suka bi izuwa wani katafaren É—aki mai girman gaske, kwalayen magunguna ne cike a cikin É—akin, a nan guards É—in suka sauÆ™e baff É—in dikka biyu, akwai ma’aikata mutum 10 a ciki, aikinsu kawai shi ne shirya magungunan a cikin kwalaye Æ™anana kafin a shiryasu cikin manyan cartons.Saman haÉ—aÉ—É—un chairs da aka tanada masu suka zauna, suka zuba idanu suna kallon yadda ma’aikatan nan ke aiki da jikinsu wajen ganin sun shirya komai yadda yakamata a kan lokaci. Suna sanya magunguna marasa karfi a kwali daban, mai launin white and ratsin ash, su muma magunguna masu karfi kwalinsu farine tas.Sai around 10 na dare 3D suka je suka yi wanka, suka shirya cikin shiga iri É—aya, white pj’s, basu ko ci abinci ba suka dawo É—akin aiki. A lokacin ma’aikatan sun shirya cartons 20 na masu karfi, 10 na marasa karfi, kowani carton kuma yana É—aukar kwali Æ™anana na maganin guda 25. Umarni Dr James ya baiwa guards uku da su fitar masu da cartons 30 É—in dikka da aka shirya waje. Cikin Æ™anÆ™anin lokacin suka fitar da shi suka ajiye a tsakiyar SECTION E É—in, sannan suka koma bakin aikinsu. Wayansa Dr James ya É—auka, password na tsaron lantarki dake jikin wani kofa dake fuskantarsu ya cire. Yana cire password É—in shocking na wajen ya mutu, tangameme kofar karfen dake wajen ya wangale kansa.Da kansu 3D suka fara jidan kwalayen drugs É—in suna shigarwa cikin wannan É—akin. Cikin Æ™asa da 10 mins suka kammala, a lokacin 12 na dare ya yi. Bayan sun kammala shigar da komai kaf, sai suka rufe kansu a cikin É—akin, suna rufewa lantarkin wajen ta kawo, shocking ya dawo, dik wanda yakuskura ya zo jikin kofar bushewa zai yi, dan wasu irin mahaukatan shocking ne a wajen. Wuta na kawowa É—akin naga wani haÉ—aÉ—É—en katafaren É—aki ne, ga sofa set, AC, TV, tamkar office na wani hamshaÆ™in muÆ™amin gwamnati, komai na cikin É—aki fari ne tas, an zuba maÆ™udan kuÉ—aÉ—É—e ba karya, ya ALLAH. Dr Kamal and Dr Mark ne suka wuce suka yi zamansu a saman sofas É—in.Shi kuwa Dr James wayarsa ya shiga latsawa kamar na 5 mins, sai ga pop dake É—akin ta gefen hagu ya fara motsawa, jim kaÉ—an wajen ya buÉ—e tamkar kofa, sai ga tsani an juro da shi ciki. MiÆ™ewa su Dr Mark suka yi, suka fara jidan kwalayen drugs É—in suna haura tsanin, kowannensu kwali bibbiyu yake É—auka su haye tsanin. Suna hayewa hudawa suka yi cikin wani É—aki wanda babu komai a cikinsa, tamkar store ne, empty yake, a nan suke shirya magungunan. A cikin É—akin wani babban likita dake sanya cikin kayan aikinsa ne a tsaye, ya rungume hannayensa a kirji yana kallonsu suna shigo da drugs É—in. Wannan likitan shi ya zuro masu tsanin, shi Dr James ya turawa saÆ™on sun iso, shi ne ya buÉ—e wajen ya sako masu tsani dan su haura.Wai kun san tsadar magungunan kuwa? To ko shugaban Æ™asa ba na kowani Æ™asa ne yake iya jurar sayen maganin dik bayan wata É—aya yana sha ba, suna da tsada, dan kwali É—aya Æ™arami mai É—auke da drugs Æ´aÆ´a kwara 6 kawai ya kai 1M, in dai kana son mai da kanka yaro matashi kuwa dole ka dinga sha dik tsadarsa. Amma ai kunga sun yi marasa karfi sosai watau É—aurayar inji, waÉ—an nan basu da tsada sosai, carton É—aya baya wuce 100k, kunga a karton kuma kwali 25 ne a ciki, zai kama kowani kwali 4k kenan, kunga shi da sauÆ™i a kan masu karfi. Marasa karfin ne Æ´an iyayi yaran malan Shehu suke kashe kansu da wahalar sai sun saya su gyara jiki, ayi glowing da lightning, ayi ta zuba kuÉ—i, ba’a ci ba a tsaya dole sai an gyara skin, bayan ga kayan gyara da Manzon ALLAH ya faÉ—a, wanda littafan musulunci suka koyar, dik bai maku ba. Idan baki san kayan gyaran da Manzon ALLAH ya faÉ—a, littafan musulunci suka koyar ba In Sha ALLAH a karshen littafin nan na yi alkawarin zan rubuta!.My people you can’t believe what I saw there. Bayan sun kammala shirya drugs É—in, Dr Kamal and Dr Mark suka tsaya tattaunawa da wannan babban likita dake tsayen, shi kuma Dr James ya nufi kofar da zata fidda shi daga É—akin. Ya ilahi, yana buÉ—e kofar kun san me a wajen?. Katafaren asibiti ne na al’umma a tsakiyar birnin Avaris, babban asibitin gwamnatin na Æ™asar ne! In baku fahimta bari in maku gwari-gwari. Kenan WS-HOSPITAL a tsakiyar al’umma take ba tare da kowa ya sani ba, sai dai tana underground ne, nasan dayawanku suna tinanin a dokar daji WS-HOSPITAL take, aikuwa gata a tsakiyar gari, a garin ma a babban birnin Eldoria, kasar da aka haifi daddynsu Lion, bugu da Æ™ari Æ™arÆ™ashin asibitin gwamnatin Æ™asar, dik wannan haÉ—uwa da tsayuwar WS-HOSPITAL a Æ™arÆ™ashin Æ™asa yake. Jama’a WS sun zarce yacce kuke tinani, manyan kai ne da kamasu abu ne dake kamar wuya, ai tin da kuma ji Lion da kansa ya ce kamasu abu ne mai balain wahala, daga nan zaku game ba Æ™ananan kai bane, sun zarce tinaninku, ku duba yadda suka shinfiÉ—a gini a Æ™arÆ™ashin Æ™asa tamkar ba za’a mutu ba fisabilillahi, suke baiwa Æ™arÆ™ashin Æ™asa wutar lantarki kusan gabaÉ—aya na birnin Avaris, shiyasa a Æ™asar ake wahalar rashin wuta, to ashe ga in da wutar take tafiya, ba’a iya É—auke wuta a WS-HOSPITAL ko na second É—aya, saboda abubuwan da suke sanyawa a freezers irinsu sperm, eggs, blood da sauransu.Dole wuta lantarki tai yawa a wajen, ga nan jama’ar Avaris kullum cikin Æ™orafin babu wuta, da an kawo da an É—auke, kuma Avaris tana daga cikin Æ™asashen da ta fi tsaranta karfin wutar lantarki, suna da uranium, amma ace kullum suna kukan rashin wuta, ashe da in da ake kai wutan a bar jama’a a gantale. Har fa hanyar yadda motoci zasu iya shiga underground É—in a wannan gini an shinfiÉ—ata, sai dai motocin in zasu shiga sai sun yi tafiya mai nisa zuwa cikin daji, a can aka yi wani waje da aka haÉ—a, aka yi shinfiÉ—aÉ—iyar titi har cikin WS-HOSPITAL, ta nan Dr Mark yake fito da motar jarirai idan an saya a wani waje, hmmmm babu wanda zai taÉ“a expecting akwai hanyar zuwa ga 3D palace a cikin wannan asibiti ta gwamnati…… Hmmmmm, shiyasa a wannan asibitin ba ko’ina ake barin mutane su shiga ba, wannan ma iya abin da kuka gani yanzu ne, ainahin labarin yana book 2 jama’a, ALLAH yasa kanmu ya iya É—aukar wasu abubuwa, kai ya ALLAH Æ™azantar dake duniyar nan, ALLAH ne kaÉ—ai zai iya maganin komai! Ni dai yanzu addu’a ta É—aya, ALLAH ka bamu cikawa da kalmar shahada da ni da mutanena na kirki, In Sha ALLAH wlh mutuwar shahada zamu yi my people!. Amma ku daga ganin iya hospital na World system kun san ba mutane ne da zasu kamu ta sauÆ™i ba, basu fito ba sai da suka shirya, kai akwai abubuwa idan muka natsa cikin labarin nan, baku ha komai ba.Cikin asibitin Dr James ya shiga, kewaye ya fara yi yana duba yadda É—akunan da majinyata suke yake, babu abin da zaku É—aga a asibitin nan ku kirasa mai kyau sosai, komai a gurÉ“ace a lalace da yake government hospital ne, amma ku duba irin aljannar duniyar da suka shinfiÉ—a a Æ™arÆ™ashin Æ™asa dan biyar buÆ™atar kansu kawai, ya ALLAH gwamnatin Avarsi ku ji tsoron ALLAH, ita duniya dai wuni muka zo yi, kowa zai koma ga ALLAH, tabbas zaku tsaya ne a gaban ALLAH da abubuwan da kuka shuka a duniya, ku tuba tin kuna da sauran lokaci.Ya jima yana kewaye cikin asibitin nan, wani sashe ma idan ya shiga yawu yake tofarwa saboda lalacewar asibitin, daga karshe ya koma wannan private room É—in, suka koma cikin WS-HOSPITAL É—insu, dan abin da ya kawosu kawowa kenan maganin, daga wannan asibitin kuma za’a fitar da magungunar ne zuwa Æ™asashen ketare, manyan dattawan alhazawa da masu mulki ake sayarwa magungunan.Can na tina lokacin da su oooo suke cewa basu son bakaken fata, wai fararen fata suke so, su jikinsu baya tsufa, bakaken fatanmu su yi ta tada hankalinsu suna damuwa a kan su suna tsufa! Su yi ta sha’awar jikinsu ooo, wai yana da kyau basa tsufa, my sister zauna yadda ALLAH ya ajiyeki shi ne ya fi maki alkhairi, baki san me yake behind rashin tsufar nan ba! MAGANIN MAI DA TSOHUWA YARINYA! MAGANIN HANA TSUFA! HMMMMMMM. Saura mu ji me suke yi da É“argon Æ™ashin da kuma shi kansa garin Æ™ashi da tsokar jariran kuma!.Kai tsaye SECTION D suka wuce, Dr Mark ya koma room É—insa ya kwanta tin da shi babu ruwansa da love.To mu É—an koma baya kaÉ—an a kan su Zinta kafin mu cigaba. Bayan sun kammala baiwa babys É—in nan madara mai É—umi, zama suka yi a gefen gado, sister Zinta ta buga uban tagumi tamkar mai tinanin wani abin. TaÉ“ata sister Maya ta yi tare da cewa. “Tinanin me kike yi?”.Nisawa ta É—an yi. “Darling nike tinani, sister ina jin tamkar bashi da lafiya, anya ba zan fita in je in duba shi ba kuwa? Zan binciko shi a gidan nan, nasan wani É—akin suka kaisa”…….. Shiru sis Maya ta yi, sai kuma da yake soyayyar Æ™anin nasu ya rufe masu idanu sai ta ce. “Mu je mu duba shi, na tabbata yana kusa da mu”. Kai sister Zinta ta jinjina, sai kuma ta ce. “Sister kina ganin da gaske alluran magani suka yi mashi?”. …. Kai tsaye Maya ta girgiza kai alamar a’a kafin ta amsa da. “Wlh ba magani bane, cuta ce, baki ga yanayin kalar ruwan ba? Kin lura akwai chemicals da muka haÉ—a a cikin cutar da yake ikirarin maganin ne?”. Jinjina kai sister Zinta ta yi. “Tabbas cuta ce, amma koma menene zan É—aukosa, zan gwadasa, in dai cuta ce tabbas zan yi mashi magani, ai mu muka haÉ—a chemicals É—in, dik kuma mun san makarin chemicals É—in”. Kai sister Maya ta jinjina. “Ko ni nasan makarin dikka chemicals da muka haÉ—a, kuma zan iya haÉ—a mashi magani”….. Shiru sister Zinta ta É—an yi, can ta ce. “Kina tinanin meyasa 3D zasu saka mashi cuta? Baki tinanin kamar wani mugun abu ake shiryawa? Meyasa muke haÉ—a waÉ—an nan chemicals É—in? Me suke yi da su da kullum sai su je SECTION C sun É—eba? Me kike tinanin ake yi da su?”.Abinku da jinin daddy Haiza’an, shiru Maya ta É—an yi, can ta ce. “Ina tunanin cuta suke kirkira, to anma ina suke kai cutar? Me suke yi da shi?”……. Sister Zinta ta ce. “Kina ganin bai kamata ace mun san me suke yi ba?”. Kai ta jinjina. “Yakamata ace mun sani, to amma ina suke kai dikka waÉ—an nan abubuwa? Baki ganin shi ma yakamata mu sani?”.Jama’a na faÉ—a zan sake faÉ—a, dan jiya na samu tambayoyi a kan abin da na faÉ—a na sake faÉ—a! Dik nurses dake wannan asibitin kyankyasarsu suka yi, basu É—aukar ma’aikata daga waje, su suka kyankyashi kayansu, suka renesu, suka basu ilimi ta É“angaren da suke son su sani, a cikin 3D É—in nan kowanne da abin da ya fi kwarewa, Dr Mark yana da ilimi kan sanin chemicals fiye da yadda kuke tinani, shi ya karantar da su Dr Maya, Dr Kamal yana da sani É“angaren kafiya sosai, shi yakarantar da sauran nurses dake aikin lafiya, waÉ—an da ke duba yaran da ake cire eggs É—insu, su yi treating babys idan basu da lafiya, Dr James ubansu kenan, yana da ilimi da baiwar sani a dikka É“angarorin, dan haka basu É—aukar ma’aikata daga waje, babu wanda yake shigowa wannan asibitin face abin da suke fitarwa, komai da kuke gani a nan asibitin aka kirkiresa, basa amfani da abubuwan waje face kayan abinci da ruwan roba sa ake shigo masu da shi. Haka zalika bayan 3D babu nurses da suke fita bare su je su yi aiki a waje a wani asibitin, ko sperm da suke saye 3D suke fita su É—auko shi, dan haka take note! Basa É—aukar wasu ma’aikatan daga waje, kuma nasu ma’aikatan ma basa fita waje su yi aiki a wani asibitin.”Gaskiya yakamata mu sani, zuciyata ta fara rawa, ina jin kamar akwai wani abin da ya saÉ“a”. Sister Maya ta faÉ—a. Sister Zinta zata yi magana suka lura sauran nurses É—in su suke kallo, da sauri suka ja baki suka yi shiru. Sister Maya ta É—auko wani baby, yana barcinsa, amma saboda tsabar son yara ba zata barshi ya huta ba, ta kwanta tare da kwantar da shi a saman cikinta, tana shafa bayansa, tana jin tamkar ta mai da shi cikin cikinta saboda so, a haka barci ya saceta.Ita kuma sister Zinta shiru ta yi, ta buga tagumi tana tinanin maganganun da suka yi, lallai dole akwai in da suke kai waÉ—an nan abubuwa, kuma tana zargin cuta ce, idan kuwa cuta ce lallai zuwa yanzu darling baya raye, dan kuwa in har waÉ—an can mugayen chemicals É—in da suka haÉ—a dikka aka juye cikin wannan aiki to ba shakka wannan cutar Æ™are dangi yakamata a sanya mata suna.Haka kawai ta ji zuciyarta na raya mata lallai ta fara bincike, lallai ta nemo maganin wannan cuta, tana jin zata iya, kuma tabbas zata iya, dan kuwa in baku manta ba su suka haÉ—a kaso 60 na kwayar cutar, in kuwa ta ce zata yi bincike ta É—auki chemicals da zasu karya waÉ—an can tsab zata iya haÉ—a magungunar, ko bata yi komai complete ba za’a samu kaso 85 cikin É—ari. A haka ta dinga wannan tinani har sister Maya ta farka daga barci around 8 na dare, ganinta zaune shiru yasa ta ce. “Sister, yadda na barki baki motsa ba? Lafiya dai ko?”……. Kai ta girgiza alamar ba lafiya ba, idanunta take suka kawo ruwa taf, murya a raunace ta ce. “Sister dole akwai wani abin da yakamata mu sani a kan darling, ina son ganinsa, yau ba zan yi barci ba, zan jira oga ya zo sai ya kaini wajensa”.Jinjina kai Maya ta yi, tana saÉ“a wannan baby a shoulder É—inta, ta amsa da ita ma ba zata yi barci ba, zata jira 3D. Haka suka kasance, suka dinga hidima da babys É—in har yaran suka yi barci, sannan ne suka zauna zaman hira, ko abinci basu ci ba, da suka ji yunwa suka É—auko crispy chicken É—insu, suka cinyesa su biyu basu tsanwa kowa ba. Haka suka kasance har karfe 12, da yake sister Zinta tasha barcin rana yau, ita kuma sister Maya ta sha na mangrib, sai yazama basa jin barci sam, da karfin hali irin nasu sai da suka jira around 1 na dare, sun fara fidda rai da zuwan 3D, unexpected suka ji an turo glass door É—insu. 3D sun yi mamaki ganin wutar É—akin a kunne, da suka shigo kuma sai suka yi mamakin ganin matan nasu idanunsu biyu, su kuwa suna ganinsu suka É—an miÆ™e tsaye, amma basu razana irin razanar da suke yi a baya idan sun gansu ba, bare ma sister Zinta da ita yanzu gabaÉ—aya ta ji tsoron Dr James ya fara fita a zuciyarta tin da ya cire kayansa gabaÉ—aya a gabanta, ya yi wasa da jikinta, tin daga wannan lokaci take jin tamkar ita da shi abu É—aya ne, and ta fara fahimtar yana sonta sosai, dan haka ba zai yi mata komai ba ko da ta yi mashi laifi. A gabanta Dr James ya tsaya, cikin sanyin murya ya ce. “Me kike yi baki yi barci ba?”……. Murmushin dole ta Æ™aÆ™alo kafin ta ce. “Waiting for you my oga”. Har cikin ransa ya ji wani irin daÉ—i, hannunsa ya ware mata tafukansa game da miÆ™a mata, É—aura nata kyawawan hannun a kai ta yi, tana É—an shagwaÉ“e fuska ta ce. “Ba zaka É—aukeni kamar É—azun ba?”………. Ya ALLAH, wani irin madarar daÉ—in da ya ji ba, baisan lokacin da ya jawota jikinsa ba, ya rungumeta yana É—an shafa bayanta.”Muje side É—inmu ko?”. Ya faÉ—a can Æ™asa……. ÆŠan shagwaÉ“e fuska ta yi kafin ta ce. “Ka kaini in ga darling É—in please”…… Kai ya jinjina mata alamar to, sannan ya rage tsawonsa, cak ya É—auketa suka fito waje. Bai zame da ita ko’ina ba sai side É—insu. A saman katafaren bed É—insa ya direta, zai sauÆ™a Æ™asa ta yi saurin riÆ™o hannunsa. “Baka nuna mun darling É—in ba”. Tana narai-narai da fararen idanun nata ta faÉ—a. ÆŠan riko shoulder É—inta ya yi. “One minute”……. Ya faÉ—a tare da saketa, ya wuce ya nufi wajen laptop É—insa, É—aukota ya yi, a kusa da ita ya zauna tare da kunna laptop É—in. Tana kallon dik abin da yake yi, bai yi zaton tana naÉ—ar komai a kanta ba.Wani folder da aka rubuta new project ya shiga, nan ya yi mata playing video É—in darling a cikin kwalba, a yadda ya É—auke shi video yaron yana kwance shiru tamkar mai tinanin wani abin. Kura mashi ido ta yi, sai ta hau murmushi, rashin sani ya fi dare duhu, da tasan balain da yaron nan yake a ciki da bata yi murmushi ba, amma tana murmushi, ta matsa kusa da laptop É—in sosai, dama ta yi wa desktop computer farin sani, dan a cikinsa aka koyar da su ilimin sanin chemicals, dan haka laptop bai bata mamaki ba.Video É—in ta kare ta sake dawo da shi baya, tana ta murmushi, a tinaninta darling yana cikin farinciki ne, ya sha madara ya Æ™oshi ne ya yi shiru. Dr James ya É—an rungumota yana faÉ—in. “Babynku yana nan lafiya, muna wani gwaji ne, amma zai dawo gareku”…….. Da yake bata ga zahiri ba, a video ne sai ta yarda darling yana nan lafiya, ta dinga murna, har da rungume Dr James, cikin shagwaÉ“a ta ce. “Sir ina son nunawa Maya darling É—inta”. Yana shafa kanta izuwa bayanta ya ce. “Zan sanya Dr Kamal ya nuna mata, ba sai kin je ba”. Ya faÉ—a tare da jawo laptop É—in kusa, ko kaÉ—an bai yi tinanin ta yi wani tinani a kansu ba tare har ya ce ba zai yi wani abin a gabanta ba, a kan idanunta ya turawa Dr Kamal video É—in ta email, ya ce mashi ya nunawa Maya.Daga haka ya kashe laptop É—in, ya É—aura saman side sofa dake kusan da bed É—in. Dik yadda ya yi a laptop É—in ta naÉ—i komai. Jawota jikinsa da kyau ya yi, in a romantic way ya fara sarrafata, yana juyata son ransa. Cikin Æ™anÆ™anin lokacin ya rabata da kayan jikinta, ya cire nasa shi ma, ya dinga wasanni da ita, sai da ya tabbatar da ya gama kiÉ—imata da salonsa, sannan ya saita penis É—in, ya shigeta, dan yau ya yi alkawarin mayar da ita matarsa da gasken kuwa.Sosai ta ji zafi, ta fara Æ™oÆ™arin turesa tana mashi magiyan ya kyaleta, amma bai kyaleta É—in ba, sai da ya mai da ita mace, ta yi kuka har ta godewa ALLAH, ta dinga dukansa tana turesa, amma ina, bai raga mata ba……. Sai da ya gama bidirinsa, sannan ya kwanta tare da jawota jikinsa, ya hau rarrashi yana bata baki, ya dinga lallaÉ“ata har ya samu barci ya É—auketa. Lokaci guda wani irin zazzafar sonta ne ya Æ™ara shigarsa, ya zubawa kyakkyawan face É—inta idanu, yana jin tamkar ya Æ™ara shigarta, dan wani sabon sha’awarta yake Æ™ara taso mashi. Duba time ya yi a wayarsa, karfe 3:30 na dare, dogon numfashi ya ja tare da sauÆ™ewa a hankali, sannan ya sauko Æ™asan bed É—in. Message yai typing wa su Dr Kamal, sannan ya shige cikin toilet. After 30 mins ya fito, a gurguje ya shirya, gaban bed É—inta ya dawo, sumbatar cheek É—inta ya yi kafin ya jawo bargo ya lulluÉ“eta, a gaggauce ya nufi waje dan lokaci na neman Æ™ure masu.Yana fitowa parlo ya isko su Dr Kamal a tsaye, suna haÉ—a idanu Dr Kamal ya ce. “Jammy kar dai ka aikata abin da ka faÉ—a? Naga face É—inka sai wani kyalli yake yi”. Hararansa Dr James ya yi, shi kaÉ—ai yasan irin tsananin farincikin da yake ciki, ya ALLAH, yau ya mori daÉ—insa.Gaba ya wuce ba tare da ya yi masu magana ba, da sauri suka rufa mashi baya. Kai tsaye SECTION D suka nufa, suna zuwa ba É“ata lokacin suka sake É—aukan jarirai guda biyar suka fita da su izuwa É—akin niÆ™a jarirai, biyu daga cikin babys É—in sai feket-feket suke yi alamar suna son yin kuka, sun farka, É—ayan sai buÉ—e baki yake yi, alamar yana jin yunwa, yana son ya yi kuka a bashi madara, da alama sarkin ci ne.Dr James na rike da babys biyu, Dr Kamal na rike da É—aya, Dr Mark na rike da biyu, to na hannun Dr James ne suke ta faman Æ™oÆ™arin fara kuka, ga alamar suna jin yunwa sosai, sai zuro harshe waje É—ayan yake yi.Basu diresu a ko’ina ba sai saman wannan gado na lantarki. Kunna lantarki Dr James ya yi, take yaran suka fara wani irin girgiza kamar yadda waÉ—an can na baya suka yi. Wannan baby mai zuro harshe waje yana son cin abincin nan gwanin ban tausayi, ya Æ™ara zuro harshen nasa waje, jikinsa na wani irin kakkarwa sosai, dadashinsa na garuwa da juna, yatsunsa na wani irin kerma, sun zazzare idanuwansu waje gwanin ban tausayi.Haka wannan shocking ya dinga jansu na É—an lokaci, sannan Dr James ya kashe bayan ya tabbatar jikinsu ya saki waÉ—an nan sinadarai da ake so. Ya danna gadon tai sama da su, wannan jariri dake jin yunwa ne ya fashe da kuka a lokacin da shocking É—in ta tsaya, kuka sosai yake yi, jininsa na É“ari sosai, harshensa ya zazzago waje. Yana wannan kuka suka tura shi cikin wannan ball É—in. Kara fashewa da kuka mai tsanani ya yi, da alama ball É—in cikinsa akwai zafi matuÆ™a. Ko gezau 3D basu yi ba, tamkar ba rai suke gani a cikin mawuyacin halin nan ba. Ya rabb, suna jiyo kukan jariri mai jin yunwar nan a lokacin da suka sanyasu cikin injin nan, yana shiga da suka kunna injin ihu É—aya ya yi, daga nan ji kake É—iff ya É—auke wuta, injin ya murÉ—e mashi wuya kenan. Ya ilahil alamina, wace iriyar musifa ce wannan, ya ji da yunwar ne ko kuwa da azaban nan? Ya ALLAH ka sakawa waÉ—an nan jariran, dik masu sayar da mahaifa da sperm É—insu ALLAH ka walaÆ™anta rayuwansu!.Haka suka É—auki bokitaye suka tari jini, garin Æ™ashi da tsoÆ™a, É“argon Æ™ashi, suka É—auka zuwa freezers room É—insu, suka shiryasu ciki, sannan suka koma side É—insu dan su je su yi wanka su yi shirin fitowa aiki, a lokacin 5 na asuba ta yi!.My people a wannan É—auki É—aiÉ—ai da sukewa jariran kowani dare suna niÆ™asu kuna tinanin one day one time su sister Zinta ba zasu farga bane? Yanzu saura babys 45, watau shiyasa kenan yaran basa taÉ“a wuce 3 months a asibitin, watau irin É—auki É—aiÉ—ai É—in nan ake masu kenan!.Bayan ya yi wanka ya shirya, sai ya tada sister Zinta, da sabon kuka ta tashi mashi, rarrashinta ya dinga yi, da kyar ya samu ta yi shiru, a sanyayye ya ce. “Sorry my wife, zan je office, zan dawo by 1 in duba ki, yau ina da aiki sosai, amma ke yau na hutar dake aiki, ki kwanta a nan ki huta, za’a kawo maki dik abin da kike so”. Cikin muryan kuka ta ce. “Ni ka turo mun sister Maya, ita kaÉ—ai nike son gani”…. Nisawa ya É—an yi, ya sunbaci goshinta kafin ya ce. “Yanzu zan turota, amma ki mun murmushi”…… Din da tana cikin ciwo hakan bai hanata murmurawa kaÉ—an ba, kara sumbatar goshinta ya yi tare da miÆ™ewa, yai mata sallama ya fito.Tsaye ya isko Dr Kamal da Maya a tsakiyar parlon, yana faÉ—a mata ta je ta yi wanka ta fita wajen aiki, sai dare zai sake zuwa ya É—auketa, shi kuma Dr Mark da ba ruwansa da soyayya tini ya yi gaba abinsa.A dake Dr James ya ce. “Maya ki je sama É—akina sister É—inki na kiranki”. Daga haka bai sake magana ba, ya sauÆ™o ya nufi waje. Jawota jikinsa Dr Kamal ya yi, ya rungumeta tare da bata sumbata a goshi. Ya saketa yana mata bye-bye. Sama ta haye tana mashi bye-bye ita ma, sai murmushi take yi. Sai da ya ga hayewarta sannan ya wuce ya bi bayan Dr James suka nufi cikin hospital É—in. ————————–CRYSTAL PALACE.🔥Abba khaiza’an’s House.A yau Abba ya shirya sadaki na alfarma, da misalin karfe 8 na dare, ya shirya cikin shiga ta alfarma, ya sanya thobe and bisht, ya naÉ—a rawani tamkar wani balarabe, amma haskensa kowa ya gani yasan ba balarabe bane. Kai tsaye ya tasa Faryan da Harleen a gaba, dan dole ya ce su rakasa ya je ya kai wannan sadaki, yana son jibi jumma a É—aura wannan aure, ba fa fashi ko za’a mutu. Kai Abba namu na amana.Ga Abba ga grandpa, me kuke tinani a kan wannan kai sadaki?

Back to top button