Hausa novels

Halysaah Page 211 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 211…Babu fara’a Ajay ya amsa gaisuwan Abdul without paying much attention to him yana danna wayarsa, bayan sun nufi ward din da Khaleesat take Ajay ya mike ya fice daga reception din gaba daya, Jay dai ya bi sa da kallo kafin ya tabe baki, ba a dau lokaci sosai ba Abdul da Haiydar suka fito ward din, Jay ya mike ganinsu, Haiydar na murmushi yace “Yallabai Nenne dai ta takura sai na maido ta asibiti, ta kirani kusan sau biyar kenan, kawai na ce mata canza maku asibitin za ayi ma” jay ya dan yi murmuşhi yace “owara da kace mata haka don ta zauna gida ta huta” Haiydar yace “Umma ma bata goyi bayan in dawo da ita asibitin ba®️ Jay yace “Gaskiya kam, Jiya duk sai da mutanen asibitin nan suka san da mu” Dariya Halydar yayi, Jay ya kalli Abdul da yayi shiru yace “Ya aiki Abdallah?” Abdul yana murmushi yace “Alhamdulillah, ya family?” Jay yace “Alhamdulillah, probably za a iya discharging din mu zuwa anjima don jikin nata da sauki” Abdul yace “To Allah Ubangiji ya bata lafiya” Jay yace”Ameen” Har haraban asibitin Jay ya raka su, nan ya ga Ajay zaune a compound din asibitin ya saka bakin spec da ya dauko a mota fuskar nan ta murtuke, duk tunanin Jay barin asibitin ma yayi, Aiay na ganinsu ya juya baya yana facing wani Ajay na ganinsu ya juya baya yana facing wani direction din, dama Jay ne kadai ya kula da shi, Jay ya raka su Abdul har bakin motar Haiydar, yayi sallama da su, yana tsaye har suka fita haraban hospital din sannan ya karasa inda Ajay yake zaune yana kallonsa yace “Ai nayi zaton gida ka tafi kayi bacci* Ajay yaki ce masa komai, Jay ya juya yayi tafiyarsa zuwa cikin asibitin. Ko minti talatin ba ayi da komawar Jay cikin hospital din ba motoci uku suka shigo cikin babban compound din asibitin, Ajay ya dinga bin tsadaddun motocin da ido don motocin gidansu ne gaba daya, he felt relieved ganin babu_ motar sarki, lokaci daya dogarawa dake gaban motocin duk suka sauko, Ajay ya mike ya cire glasses din idonsa ya karasa inda suka yi parking dai dai sanda Mami ta sauko daga bayan mota tare da Kilishi bayan dogari ya bude masu back seat, second car kuma Hajja ta sakko tare da Hajiya Aisha, sai motar karshe Aunty Farida ta sauko tare da Jakadiyarta, Ajay yayi kasa da kai ya gaida Mami da Kilishi don kusa da motar su ya tsaya, Hajja ta karasa kusa da shi tana shafa kansa tana murmushi don ya dawo sak Ajay dinsa unlike sanda za su America da duk yake a rame ga rashin kuzari saboda ciwo, yanxu kalarsa ta ainahi ta fito, he look healthy and y taken care of, cikin kwantar da murya”Ahmad, ya mai jiki fa?” Ya sauke idonsa ya gaisheta yace “Da sauki, Sannun ku da zuwa Hajja…” Juyawa yayi ya gaida Aunty Farida da ladabi, ita dai kallonsa kawai take tana murmushi don ita ma taji dadin yanda ta gansa, a hankali tace “Lafiya lau Junaid, Kun dawo lafiya?” Yana murmushi shi ma yace “Alhamdulillah Aunty” Ya gaida Hajiya Aisha ta amsa tace “Jiya sai muka ji mummunan labari da daddare, to ya jikin nata?” Ya sauke ido yace “She is getting better” Jakadiyar Aunty Farida dake zube kasa tana jiran Ajay ya gama da su Hajja da Aunty Farida sannan ita ma ta gaishesa, kirari ta fara jero masa tare da gaisuwa, yace “Lafiya lau” Juyawa yayl, yayi leading din su gaba daya zuwa cikin asibitin, with no confidence ya nufi ward din da Khaleesat take don tun da gari ya waye bai shiga ward din ba, suna isa kofar ward din yaji kamar kar ya shiga don bai san yanda zata yi reacting ba, amma haka nan ya dake ya tura kofar gently ya shiga, ido hudu suka yi da ita, lokaci daya ta dauke idonta kamar warce taga mugun abu ta hade rai, ya koma gefe bayan ya shiga ward din, su Hajja duk suka shigo su ma, Jay ya mike a inda yake zaune yana welcoming din su, Hadiyah ma ta mike daga kusa da Khaleesat, duk suka nufi kusa da gadon Khaleesat, ita dai Aunty Faridah bata karasa k da gadon ba ta tsaya a gefe, Hajja na ka me jiki, Hajja dai na tsaye kusa da Khaleesat tana ta kallonta, sai kuma ta juya ta kalli Ajay tace “Wai menene ya sameta? Sannan a lokacin da Faridah ta kira ku kunce kuna Abuja, kenan ita kadai ta dawo kano bayan kun san bata da lafiya ko ya aka yi?” Ajay ya sauke kansa bai dai ce komai ba, Calmly Hajja tace “Tambayar ka nake Ahmad” Ya daga ido ya kalli Jay, wani shegen kallo Jay yayi masa ya juya baya don kar ma ya sakasa cikin maganar, Hajja ta kalli Khaleesat tace *Jeeddah ke kadai kika dawo kanon ne?™️ Khaleesat ta daga idanuwanta tana kallon Hajja, a hankali tace “A”a, duk mun dawo Kano, sai su suka koma Abuja” Ajay ya kalleta, Hajja tace *Suka bar ki ke kadal a gidan kike nuft?” Alay dai kallon Khaleesat kawai yake har sai da suka hada ido, a fakaice tayi masa wani matsiyacin kallo ta dauke idonta, murya can kasa tace “Gidan kawata naje, tayi aure sanda bana nan shi ne naje in mata kwana biyu, daga can gidanta ne na koma gidanmu* Hajja ta zauna kan kujeran dake kusa da gadon tana kallon Mami tace “Sam yaran yanxu sun gantalar da sarauta sun maida sa kamar wani abu mara muhimmanci Aseeyah, kwata kwata basu ba sarauta value dinsa ba kamar yanda iyaye da kakanninmu suka yi, daga Junaid din har Jawwad basa halayya inin ta yaran da suka fito gidan sarauta, abu suk kamar wasu gantalallun gari, wani lokacin idansun vi wani abu kai kace taka have kawai muka vi sun yi wani abu kai kace taka haye kawai muka yi a sarautar ma, babu izza, babu nuna mulki babu kamewa, kai ba komai, har gwara gwara Jawwad sau dubu, banda haka ta yaya a matsayi irin na Jeeddah za su bar ta ita kadai a garin nan babu kowa kusa da ita, a kalla ya kamata ace akwai masu aiki biyu da kuma jakadiyarta daya a tare da ita, kawai yayi tafiyarsa wai ya bar ta gidan kawarta saboda rashin sanin darajan sarauta, ina ce jinyar sa ta tafi yi Amurka, to don me zasu dawo yasan ba lafiya ne da ita isasshe ba har ya bar ta gidan kawa ya kama hanya ya tafi wani garin, haka fa na samu labari a Maryland duk ita take aikin babban gidan nan kafin Hadiyah ta je, haba kamar ba warce ke aure gidan sarauta ba wannan ai abun kunya ne a gare mu, tana matar dan sarki ita da sai dai ayi mata komai a bata abinci ta ci, amma ita ke aikin gida da girke girke? dama idan wani ya ga Junaid da Jawwad a hanya ma zai zata wasu yaran Mai unguwa ne ba sarki ba saboda rashin kamewa da nuna izza na ‘ya yan sarakuna, ko fita za ku yi daga ku sai ku a mota babu masu yi maku rakiya a matsayin ku na manyan mutane, ku ke jan motar ma da kanku tsabar gantali da walakantar da mulki” Daga Ajay har Jay babu wanda ya kalli Hajja alamar t don’t have her time, Hajja ta girgiza kai cike takaici tace “In dai jikin nata da dama dama kawai a rubuta mana sallamarta mu koma gida da ita ta samu kulawa da gatan da Allah ya bata, a samu likitocin ayi masu magana su sallameta, daga asibitin nan mu juya mu koma masarauta da ita” Hajja na kai wa nan ta mike tace Hadiyah ta taho mata da jakarta, daga haka ta fita daga ward din, Hadiyah ta amshi jakan Hajja a wajen Hajiya A’isha sannan ta bi bayan Hajja da shi, Mami ta sauke ajiyar zuciya ta juya ta fita ita ma, ita kanta tana mamakin yanda daga Jay din har Ajay suka maida kansu random people a al’umma kamar wasu ordinary persons, babu wani alamar daga Emirate suka fito, shi dayan ma da kyar aka rabasa da dukan mutane a gari, tun asali dama basu yarda wani ya ja su a mota ba ko kuma in za su wani waje a wani yi masu rakiya ana masu fadanci sam basa so, Mami na fita daga dakin Kilishi tace”Gaskiyar Hajja kawai a maidata masarauta tagagata da kulawa, baza a yarda ayi asaran wannan ciki ba yanda aka yi asaran na farko, in aka biye ta mijin nan nata dama shi bai maida mana sarauta komai ba, babu me cewa ma dan sarki ne shi, bai san sarauta wata ni’imace da Allah ke ba wanda ya ga dama ba” Tana kai wa nan ta fita daga ward din, Hajiya A’isha ta bi bayanta, Sai a sannan Aunty Faridah ta nufi kusa da gadon bayan duk sun fita, Ajay ya sunkuyar da kansa ya juya a hankali ya fita daga ward din, bai taba zat Khaleesat bazata fadi ainahin abinda ya faru he was shock at her response, Jay kansa yayi mamaki da ta sakaya zancen he never expect that from her, shi ma ya juya ya bi bayan Ajay ya fita, Aunty Faridah na kallon Khaleesat cikin kwantar da murya tace “Sannu, ya jikin?” Nan da nan hawaye ya cika idon Khaleesat, tace “Aunty ni dai gida nake son in zauna don Allah, wallahi bana son bin ku” Aunty Faridah tayi shiru tana kallonta, can tayi kasa da murya tace “Saboda me? Wani abu ya hada ku da Junaid din ne?” Da sauri Khaleesat ta girgiza kai tace “A’a, kawai wajen Ummata nake son zama wallahi, don Allah ki ce kar a tafi da ni” Hawaye na zuba idonta ta karasa maganar, Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya, kawai sai tayi tunanin salon da wannan cikin ya zo mata da shi kenan na son ta zauna wajen Umma, a hankali tace “Kin san bazan iya ja da abinda Hajja tace ba Khaleesat, sai dai in kira Sarki in gaya masa ga abinda kike so, idan ya so sai shi yayi ma Hajjan magana yace a bar ki a Kanon” Khaleesat ta marairaice tace “Don Allan ki kirasa yanxu Aunty, wajen Ummata nake son tafiya daga nan wallahi” Aunty Faridah tace “Wayar na wajen Ramatu, bari in karbo” Mikewa tayi ta fita daga ward din don karbo wayarta gun Jakadiyarta, gefe ta koma ta kira Mai martaba, sai da kiran ya katse sannan ya biyo ta, ta daga ta kai kunne ta kwantar da murya tana lumshe ido tace “Allah ya taimaki My love” Dan murmushi tayi ta karyar da ka abinda yace…. Hajja ta gama wayar da take y Sarki sannan ta juya tana kallon Ajay dake kallonta don duk ya ji abinda Sarki yace, a hankali yace”To amma Hajja me yasa Abba zai ce mu bar ta a gida?” Hajja tace “To ka dai ji, ni kaina ma ban san hikimarsa ta cewa hakan ba, amma ai tunda bata da lafiya kuma laulayin ciki take yana da kyau mu koma masarauta da ita a bata kulawa na musamman har cikin yayi kwari, ni sai in dawo masarautar ma saboda ita in zauna” Ajay yayi kasa da murya yace “To ai Hajja zaki iya ce masa kar mu bar ta a Kano mu tafi da ita, kin san bazai ce maki a’a ba, don Allah ki kira ki gaya masa haka” Hajja tace “Kasan” bana son yi masa kasalandan idan ya yanke hukunci, gwara dai kay Faridah magana ita sai ta nuna masa gwara mu dawo, masarauta da ita kawai” Ajay ya kasa cewa komai don shi tunda yaga Aunty Faridah bata fito daga ward din Khaleesat ba har yanxu ya ji ya tsargu, Khaleesat ji tayi wani strength ya zo mata ta samu karfi sosai tunda taji Sarki ya amince ta tafi gidansu ta zauna har sanda zata samu sauki, she really mean Ajay sosai ba kadan ba, ita kadai tasan abinda ta shirya a zuciyarta, shi dai Jay na ward din a tsaye yana kallonta bayan anyi discharging dinsu, sarai yasan da biyu take son tafiya gidansu, a haka suka bar asibitin gaba dayan su, Khaleesat da Hadiyah suna mota daya da Jay da Ajay, yanda taki kallon direction din Ajay a motar shi ma bai kalli direction dinta cause he was against abinda Sarki yace, daya mood dinsa ya canza, kawai dai bazai iya ja da mai Maryann ba…

Back to top button