Gargadar So Chapter 92 By M Shakur
Kiraye kirayen sallan magrib yatada Hawwa daga bacci, bude idanunta tayi tabi dakin da kallo tana salati aranta bata bacci haka ba, this house is making her sleep like them, kokarin tashi tayi amman batada karfi kawai saitaji hawaye batada wani wanda zata kira, kannenta duk ta girmesu balle takirasu taji mezatama kanta tasami relief ko yaya akeyi ko haka abin ke zafi, ita batama saniba but she don’t think su Hafsan su dasukai aure sun kira Umma, Ni’ima ce tafado ranta dasauri ta kori tunanin ta dudda ta tuna Ni’ima ta taba gayamata ana wahala but she doesn’t sound like this wahalan, kuma ai kwana uku da bikin saida Ni’ima tasa taje gidansu takarbi magani wajen Mamanta takaiwa Ni’ima agida bataga Ni’ima tai zuru zuru haka kaman ita ba, idanun Ni’ima ko kumbura basuyi like hers ba kodai mugunta Khaleel yake mata? Yanaso ya nuna mata yafi karfinta yanuna mata shi A ne, karan flashing ne yashigo wayanta da kyar ta iya daga hannu tadauki wayan taga Ammi ne idanunta ta lumshe tai dialing number Ammi hawaye na fita daga idanunta daukan wayan Ammi tayi cikeda so tace “Hawwa na!” Tai maganan tana tashi daga inda su Ramla suke tashiga dakinta ta maida kofa tarufe murya chan ciki na asalin rashin lafiya Hawwa tace “Am…mmmi” wlh duk yanda taso ta daure jin muryan Mamanta kawai saita sakinma Ammi kuka ba magana ba komi sai kuka, dan murmushi Ammi tayi irin na manya tace “lafiya kike kuka meya sameki”? Cikin kuka don ita tagaji tace “Ammi kizo ki daukeni wlh Khaleel zai kashe miki ni” Ammi takusan kwashewa da dariya saikuma ta hadarai tace “ke ja chan uwar raki, ni nadauka dakika girma kin daina rakin nan” sai kuma ahankali cikeda lallashi tace “it’s okay abinda kikeji yanzu is normal inhar mace yar arziki ce kamilalla tai aure ko shekara nawa take saitaji abinda kikeji yanzu, it’s normal nan da gobe ko jibi duk ciwon zai tafi Allah miki albarka” Ammi tace “Abinda zakiyi is anytime zaki fitsari ko zaki amfani da bayi kai koma babu abinda zakiyi ki dinga zama a baho kinji zaki warke, Hawwa dan Allah karki karabarin wani abu dazaisa harsai mijinki yakiramu wannan shine auren, idan mijinki ya nemeki ki amsashi hakkinsa ne kikace a’a mala’iku sun dinga tsine miki kenan kinji” “uhm” Hawwa ta amsa ba baki, tabawa Ammi tausayi but she’s happy at least yanzu su ciwon cikin nan datakeyi duk zasu tafi fatanta shine Allah yabawa Hawwa ciki ta haifi yaranta sharp sharp, wannan datakai shekara talatin haihuwa ance yana basu wahala, dasu ciki duk yana bawa mata idan sunkai 30 wahala, kyanshi kafin takai 40yrs ta haifi atleast yara 6 ko 8 dan ita Ammi so take Hawwa ta haihu dayawa, irin iyayyene Ammi da sunyi imani da a hayayyafa, Ammi tace “Allah yasa ki sami ciki da wuri so samu Allah yasa bazama kiyi al’ada agidansa ba” wani iri Hawwa taji da takaicin Ammi taki magana ita tana ta pains Ammi na ta yara, Ammi tace “in sha Allah kodan hakurin da kikayi Allah zai baki ciki da gaggawa Allah karya hadaki da matsalan rashin haihuwa ko wuyan samin ciki ko yawan bari, Ya Allah kabawa Hawwa na juna biyu da gaggawa” baki Hawwa ta turo dan ita bata hararo ko da wasa ta haihu da Khaleel ba, tayi mamaki ma da har yanzu bai saketa ba kuma yanzu yayi har sau biyu, ijiyan zuciya Ammi ta sauke tace “idan kindan ji sauki inaso kije ki gaida iyayen sa, ina miki tuni Hawwa idan kana zaune gida daya da iyayen miji haka akeyi, sannan koda baki girki sau uku kinkai musu ba ko nadare ne ki dinga yi dasu kokuma breakfast, Hawwa ki rike iyayen mijinki babu abinda ban koyamiki ba, ke ko ban koyamiki ba keba yarinya bane kinsan yanda zaki zauna da kowa aduniya” kasa daurewa Hawwa tayi tace “Ammi maman sa bata sona but banda matsala da mahaifinsa” dan shiru Ammi tayi chan tace “make her love you ta hanyar nuna mata ke yar halas ce, idan ta biki da sheri ki bita da alkhairi, ki girmamata, ki darajata, Hawwa aure anyi shikenan dindindin you have to learn to leave agidan mijinki learn to make her ta soki kinji, make a place for kanki azukatan su” Shiru tayi takasa cewa eh sabida tasan yaron nan baya zama da mata zai rabu da ita Ammi tace “bari na barki nayi tunani dama yaje magriba salla saisa namiki flashing nadanyi magana dake kafin yadawo sannu Allah sawake, Allah baki lpy, Allah yasa ciki ya shiga jikinki kenan, Allah kara muku soyayya da fahimtan juna, Hawwa kinyi aure sai arage yawan fada, masifa da yawan fushi, duk suna jawo danasani, nasonki Hawwa na, ki rike aurenki da kyau kinji” kin magana tayi Ammi bata kawo komiba dan taga batada lpy ta katse wayan, ijiye wayan tayi tana wajen tanaso ta tashi takasa wayan Khaleel yayi kara alamun watsapp message hannu tasa ta dauka baiyi hide notification awayanshi ba she was able to see message din from Moh.“Yauma bazaka zo all white party ba Lee”? Abu taji ya tsaya mata awuya sai kawai ta danna ta shiga chats din gabaki daya basuda maganan arziki a chats din saina maganan party ga inda za’ayi party, ga DJ da aka dauko, maganan su shisha, yakarene dasu drinks, dasu giya kawai saitaji ranta yabaci, kirjinta na zafi, wani kalan tarbiya mutanen nan suka bama Khaleel wlh baisan komiba banda party da mata da shaye shaye, ya karanci Dr but harta gane baya aikin komi ko kwanakin baya sabida itane yadinga suntirin asibitin nan, all abinda ke rayuwan Khaleel is party, party, party! Shaye shaye, shaye shaye! Sai mata, mata, mata, he claims yanason Noor koda yace yanason Noor tagani a idanunshi but baisan as a father yakamata yabar rayuwan nan ba, dabi’un nan nashi na bata takaici, tai shiru tana tunani dudda tasan zai iya sakinta anytime ta gwada gyarashi ko ta barshi da halinshi? Tana cikin tunanin aka bude kofa dasauri ta ijiye wayanshi but harya gani yataho da sauri yace “babu matan dake chatting dina up apart from Mom kece the second girl dakeda this my personal number Kulu, me kike dubawa awayana”? Dauke kai tayi da muryanta da baya fita sosai tace “cewa akayi ana jiranka a party” dakatar da duba wayan yayi yakalleta saikuma ya ijiye wayan da sauri yahau gadon yawani juyo da ita.


