Mejo Najeeb Page 39 By Autar Alheri
“Tace “mikukeyi a kitchen ne?? “Girki mukayi muku Hajiya umma, Ummi tabata amsa. “Girki kamar yaya? Wayasaku? “Bakowa kawai anty Maryam ce tazo zatayi Sena tayata…wani mugun kallo Hajiya umma tayiwa Ummi kamin tashigo kitchen ɗin duka tana abin kayanda tagani ciki da kallo cikin mamaki takebin komai ɗaya bayan ɗaya kamin tace”wai duk ina kayan abincin gidannan? Kuma wayakawo wannan? Cikin tsoron yanayinta ummi tace “yah munir ne yakawo wannan bansan ina yakai wanda yakwasheba. “What?? Shi munir da kanshi ne yakwashe kayan abinci yakawo wasu? Duk yoshe Alhaji yasa aka kawo wannan dahar za’abanzatar dasu? Tukunnah ma uban waye yasakashi?? Tafaɗa cikin fishi,, wanda yayi bala’in tsorata ummi…isseta kuwa da tun shigowar Hajiya umma tashigo batace komaiba seyanzu taɗago tana kallon Hajiya umma da murmushi kwance akan fuskarta tace “ayya Hajiya sorry please nicenan nasakashi domin ban yadda da kayanba shiyasa nasa yafitar dasu yakawo muna wasu kuma naje natambeki miza’adafa bansameki a part ɗinki ba shiyasa kawai narage miki aikin kafin kizo kinga har mun gama……tunda isseta tafara magana Hajiya umma kebinta da wani wulaƙantaccen kallo hartakai ƙarshe cikin kakkausar murya tace “ohh mikike nufine? Kinanufin karyamin doka zakiyi agidan daga zuwanki shekaran jiya har kin isa kisaka ayi abu agidannan batareda nasaniba? Tukunnah ma akan wanne dalili? Dawanne matsayi kike taƙama dahar zaki zartada abu agidanan. Bada saninaba? “Humm Hajiya kenan matar babban yaron gidan mana kinga kuwa inada damarda zanyi komai ayadda nakeso tunda gidan mijinane, tafaɗa tana murmushi….ido ummi tawaro ganin yadda isseta keyiwa Hajiya umma magana babu tsoro balle fargaba kuma babu girmama amma bada rashin kunya ba.Maganar Hajiya umma ce tadoki kunnenta inda take faɗar karki sake shigowa kitchen ɗinnan kinji nagaya miki kuma kidena taƙama da auren najeeb kibari har idan yakarɓeki tukunnah tunda nasan kinada labarin ku biyu ne aurenku yake kanshi doline da wadda yazaɓa zezauna kuma baze zaɓi wadda ban amince da itaba amatsayina na mahaifiyarshi sabida hakan doline kibi umurnina agidannan kamar yadda kowa yakebi indai kinason zamada ɗana, kuficemun dagani, tafaɗa cikin bada umurni….batace mata komaiba tajuya tareda nunawa ummi wata Warmer dasuka zuba soyayyen nama tace “ummi ɗauki wannan muje…bamusu ummi taɗauka jiki narawa tafice daga kitchen ɗin.Tana fita isseta tayi wata irin juyiwa tana fuskantar Hajiya umma idonta gabaki ɗaya sunjuye ga dukkan alamu tunɗazu da suke magana da Hajiya umma ba ita bace kauda ido ne..kafeta da ido Hajiya umma tayi kogizau baba….itako cikin Issa da izza taƙaraso dabda ita yadda zasu iyya jiyo numfashin juna tace “Jamilaah, takira asalin sunan Hajiya umma…cikin mugun mamaki Hajiya umma ke kallonta amma bata nuna hakan afiliba, domin itama kallonta takeyi yadda itama take kallonta, babu ko ɗar azuciyarta. “Gyara tsayuwa Isseta tayi kana tace”Jamila inamiki kashedi akan kifita harkar Maryama babu ruwanki da duk abinda zatayi domin kuwa baki isa kidakatarda itaba kuma abincin gidannan yanzu tafara harse ta tsabtace ƙazantar dake gidannan tukkuna kozata dena yinshi kuma kisani idan baki saka mata idoba kikace zakiyi jayyaya da ita to wlh kasa ce zata tono wuƙar yankata kisani nasan komai Jamila kuma bana barin bashi domin banacin nakowa sabida hakan wlh duk wanda yaci nawa seya biya kije kitambayi mushrikin tsohon dakike taredashi kiji wacece gimbiya mardeeya idan kunne yaji jiki yatsira, tana gama faɗar hakan tanufi ƙofar zata fice anan sukayi karoda Hajiya mama zata shigo kitchen ɗin sabida Ummi tafaɗa mata abinda ke faruwa dudda cewar bataga lokacinda gimbiya mardeeya keyiwa Hajiya umma gargaɗi ba…dasauri gimbiya mardeeya taja baya tamkar isseta ce tareda cewa sannu da fitowa mama..”yawwa sannu Maryam lafiya kuwa? Tatambaya gudun kar wani abun yafaru daga baya. “Lafiya qalau mama sallah zanje nayi..to shikenan yimaza kije domin kam lokaci yayi. Tana gama faɗar hakan tajanye Isseta tawuce zuwa pert ɗin mejo……da kallo tabi Hajiya umma datayi tsaye kamar andasata kafin tasaki wani shi’umin murmushi tajuya tareda barin wurin….Hajiya umma kuwa tadaɗe tsaye a kitchen ɗin kafin tafito tanufi nata part kamar zata tashi sam, kida tashiga tadubi lokaci setaga ba lokacinda yadace tashiga wancan ɗakin bane tsaki taja kawai tajuya zuwa bathroom ɗinta..South AfricaYana fitowa daga wanka yashirya cikin ƙananun kaya yafito perlor sedai yaga bakowa,, wayarshi yaɗauka yakira general Faruk yafaɗa mishi inda suke,, okay kawai yace tareda yanke wayar yafita….ababbar hidikwatar sojoji dake ƙasar yasamesu inda wani commander kemusu bayanin yadda suke neman wannan ƴanta’addan suma domin su yiwa ƙasar muguwar ɓarna amma sunkasa samunsu duk inda sukaji labarin su koda zasuje sesu tarar sun gudu…..shiru dukkansu sukayi kowanne da abinda yake tunani kamar daga sama sukaji Muryar wani saurayi yace “Ni nasan inda suke domin nagansu idan kunaso kuzo zan kaiku….dasauri duk suka ɗago suna kallonshi matashin saurayine kyakkyawa wanda baze wuce shekaru 22 ba….wannan commander ɗin ne yafarayin magana cikin jin daɗi yace “that’s good my buy yanzu bara ashirya runduna semu tunkaresu zuwa gobe, yafaɗa tareda zaro wayarshi yana ƙoƙarin kira. “No base anhaɗa runduna ba mukadai zamu iya kawai aje yanzu. Muryar mejo najeeb tadoki dodon kunnensu. Da mamaki wannan commander ya kalleshi kana yayi murmushi irinna manya yace “kakuwa san wakake nufin zamu tunƙara mukaɗai? Kasan haɗarin dake tattare dasu? Ɗan cije lips ɗinshi na ƙasa yayi kafin yabuɗe blue eyes ɗinshi akan commander ɗin yace “yes zamu iya kowanne irin haɗari sukedashi zamu tunkaresu da ƙarfin uban giji zamuyi nasara akansu nidai ashirye bakeda tunkararsu ayanzu nida brother’s na yafaɗa kanshi tsaye. “What?? Sedai idan kaine zakaje amma sukan nasan bazasu tunkari wannan haɗarinba kadena yanke hukunci kabari kaji abakinsu tukunnah, cewar wannan commander ɗin. “Humm yasauke numfashi kafin yaɗago yana kallonshi ido cikin ido yace “bayankan hukunci nayiba abinda yakasance ne nafaɗa domin duk abinda naji zan iya araina nasan agun general Aliyu haidar ma hakan abin yake domin bantayin abinda shi baze iyaba sabida yadda bugun zuciyarmu ɗaya bazata saka ɗayanmu abinda ɗaya baze iyaba, hakama general Faruk yaƙullah alaƙa da wannan zuciyoyi namu tun ranarda yaƙullah alaƙa damu, ɗan shiru yayi yaname lumshe kyawawan idanuwanshi kafin yaɗago yana riƙo hannun commander ɗin yaɗora adede zuciyarshi dake bugawa dasauri dasauri…ido duk suka zuba mishi suna kallon yadda yake buɗe idon nashi ahankali yace “kaji yadda zuciyata ke bugawa da soyayyar ƴan’uwana?? Tosuma hakan tasu keyi akaina sabida hakan bazan taɓa bari suyi abinda nasan bazu iyaba koze cutar dasu so we will Reddy to going all, yana gama faɗar hakan yasaki hannunshi tareda juyawa zebar wurin…cikin sauri general Aliyu yamara mishi baya yana faɗar “Yes of course maganar mejo hakan take babuko sirki acikinta..shima general Faruk dakuma su Captain jameel bayansu sukabi,,hakama wannan saurayin….baki sake wannan commander yabisu da kallo kafin yakira wasu mutun ukku daga cikin sojojinsu cikin sauri suka marawa motar su mejo baya….sukuwa kaitsaye inda wannan yaron ke kwatanta musu suka nufa dama kowanensu dashirinshi domin duk sunada bindiga ajikinsu… general Faruk kuwa baƙaramin mamaki kalaman mejo kebashiba domin yaga sahihiyar gaskiya a idonshi kuma abinda yake gani a idonshi shiyake gani a idon general Aliyu tabbas sunayiwa junanso na haƙiƙa shiko mizeyiwa Allah inba godiyaba daya haɗa shi abota da waƴannan bayi nasa, yanacikin wannan tunanin suka ƙaraso wurin inda sukayi Perking ɗin motarsu nesa da wurin kaɗan duk suka fito kowanne ya fidda bindigarshi suna fitowa motarsu commander na isowa hakan yasa suka tunkari wurin gadan gadan babu tsoro balle fargaba sunrigada sunshiryawa tunkararsu ko sukashe ko akashesu(Allah sarki sojojin Nigeria dama nawasu ƙasashen musulmi Allah ya tsareku aduk inda kuke yakareku da kariyarsa😢) ahakan suka tunkari wurin cikin dakiyar zuciya gasu dukkansu basu wuce mutun 9 ba amma hakan suka nufi mutanenda sunfi 40 suna zuwa suka fara musu ruwan wuta tako ina babuzato babu tsammani kawai sukaji saukar harbi….cikin mugun mamakin yadda akayi jami’an tsaro sukasan inda suke suka shiga neman kayan aikinsu, amma cikin iyawar uban giji kafinma susamu nasarar barin wurin su mejo sun ƙararda fiye da rabinsu, hakan akarinƙa musayar wuta babuji babu gani kusan awa ɗaya ana ɗauki ba daɗi dakyar su mejo suka samu nasarar kama duk wanda sukeso sukama acikinsu hadda shugabansu gabaki ɗaya datemakon wannan saurayin,,,hakan suka taso ƙiyarsu agaba suka dannasu mota sojojin South Africa se jinjinawa ƙoƙarin sojojin Nigeria sukeyi domin sunyi abinda sojojin ƙasashe mabanbanta suka kasayi….ababban kurkuku suka kaisu suka rufe dazimmar gobe zasu wuce dasu Nigeria sabida ayanke musu hukunci…haka su mejo najeeb suka fito a jigace suka nufi masaukinsu cikin matsanancin farin cikin samun nasara cikin sauƙi, tun fitowar su suke neman inda wannan saurayin daya temaka musu yashiga amma basuganshi ba ko me kamadashi basuganiba, har suka ƙarasa masaukinsu kowanne yanufi bedroom ɗinshi domin susamu suyi wanka sugasa cikinsu. Tofa abinda su mejo basusaniba wannan saurayin daya temakesu bakowa bane face gimbiya mardeeya itace tazo musu amatsayin wannan saurayin tatemakesu domin suyi saurin gama wannan aikin sukoma Nigeria ayita taƙare.👍aikinki nakyau gimbiyar mata🥳LagosIsseta nashiga bedroom ɗin mejo gimbiya mardeeya takwantarda ita akan bed ɗin tukunnah taficewarta kusan minti 10 tana ahakan kamin tamiƙe ganinta kwance yabata mamaki sosai amma bata kawo komai arantaba tanufi bathroom kawai domin tayi wanka tayi sallah…..bayan tafito daga wankan tashirya kana tayi sallah tana ganawa ummi tazo kiranta aci abinci hakan yasa tabita suka fice general perlor ɗin inda suka samu kowa ya hallara a dining table harda Hajiya umma dasu Munir su juwaira kowa ya fito…kujera ummi taja mata tazauna bayan tagaidasu Hajiya umma da Hajiya mama sedai tayi mamaki sosai yadda Hajiya umma ta’amsa mata gaisuwar….itama su sajad da auta siyana suka gaidata suna santin girkinta tun basuciba sabida Ummi tabasu labarin itace tayi girkin…munir kuwa tunda yagaidata bekoma cewa komaiba domin Allah yasani yanzu yarinyar tsoro take bashi.Ummi ce tayi saving kowa awurin hadda isseta ɗin se alokacinne kowa yakulada babu mansura Hajiya mama ce tace “Ummi ina mansura baki kirata bane? “Wlh mama nanemeta bangantaba..”eh fa inaga bata gidannan domin ɗazu dazan shigo naga fitar motarta cewar Munir….. okay kawai Hajiya mama tace amma Hajiya umma komai bataceba….hakan a kafara cin abincin inda mutanen gidan seyaba girkin isseta sukeyi suna santin amma anty hawwa da juwaira harma Hajiya umma bawanda yace komai kuma ba wanda yakulada kowa,,,sedai isseta ce gabaki ɗaya hankalinta naga hannun Hajiya umma tana kallo taga kizataga wannan zoben nata amma bata ganshiba hakan ya tabbatar mata dacewar wancan ɗin dai natane, tana zaune tana tsakurar abincin zuciyarta fall tunani har aka gama cin abincin *(inda akabawa ƴar amanarmu ragin da sukayi ita da team teemah p r v🥳 suka cinye suna wawaso dasantin girkin isseta..ohhhh su inna kwaɗairu ƴar amana aci sannu🤩🤩)* suna gama cin abincin kowa yatashi wasu suka nufi perlor wasu kuwa shiga gyaran wurin yayinda Hajiya umma tanufi bathroom ɗinta bayan taduba agogon hannunta. tana shiga bedroom ɗin tanufi wannan lungun babu sallah balle salati tana shiga tayanjo wani ƙaton madubin tsafi tareda wasu kaya green tasaka ajikinta,,wata ƙatuwar tukkunya tajanyo kana tasaka hula, seda tagama duk abinda takeso tayi tukkunna tazauna tareda saka wannan ƙaton madubin tsakiya tashiga kiran “tsijuju tsijuju tsijuju,, hakan kawai take kira kusan minti 2 kafin wannan mushrikin tsohon yabayyana agareta yana wata irin mahaukaciyar dariya. Ido nazaro arikice ina dubansu dagashi har ita cikin mugun mamaki ganin ashe Hajiya umma ce ketarayya da wannan mushrikin tsohon domin awancan lokacin hular datasaka tahana aga kowacece lokacinda wannan tsohon yabata labarin gimbiya laweesat. “Baki tabuɗe zatayi Magana cikin sauri yadakatarda ita ta hanyar faɗar “karkice komai Jamilaaaa domin duk abinda zaki faɗa nasani sedai abinda zance miki anan shine dai wanda nasaba gaya miki kiyi hankalida gimbiya mardeeya kamar yadda tagaya miki domin kuwa tafi gimbiya laweesat haɗari sabida ita da kanta takeyi bajira takeyi ayi mataba kuma ayanzu tashiryayin fito nafito dake tashiryawa karya alƙadarinki kisani tabbas bazaki iya takon saqa da itaba domin ita ɗin tamkar guguwa hakan take abu ɗaya ne zesa kiyi nasara akanta shine samun haɗin kan najeebullah akan biyan buƙatarki domin tabbas duk ranarda yakwanta dake to komai zeƙare kuma burinki zecika batareda wani yashiga tsakaninki da hakanba amma kisani muddin kikayi sake gimbiya mardeeya tarigaki ƙarasa nata aikin to kin rusheeee, yaƙarasa zancen cikin daga murya gabaki ɗaya seda ɗakin yaɗauke…ajiyar zuciya tasauke kana tace “To amma tsijuju akwai matsala fa domin kuwa yarigada yakwanta da wannan tsinanniyar yayinyar kuma kace doline nice zan kasance tafarko gashi tana neman shiga tsakaninada hakan tunda ayanzu wuri ɗaya suke bacci. “Ƙarya yakeyi betaɓa samunta amatsayin ƴa mace ba sedai zesamu idan kikayi wasa abu naƙarshe daya dace kisani shine tsuntsu zekomawa sheƙarsafaaaa hhhhhh hhhhhhhh hhhhhh yafaɗa yana sakin wannan razanniyar dariyar kana yaɓacewarshi….ajiyar zuciya Hajiya umma tasauke kamin tamiƙe tacire kayan tareda maida komai mazaunin shi tafito tana tunanin wanne tsuntsu tsijuju kemagana akai…tana fitowa taga wayarya na ruri ɗagawa tayi tareda karawa akunne…kafin tayi magana mekiran nata yarigata “Hajiya ya’akayi hakan nejeeb yaje South Africa batareda kingayamin ba??…..!
