Hausa novels

Matar Hariji Page 2 Romantic Hausa Novel

MATAR HARIJI Part 02 Tabe baki tayi ta juye indomie dinta a flat sai yanzu ma ya lura da yanda gashinta yake a hargitse shi dama ba kirki ba, kafin yayi mgn tace “dallah malam kauce na wucce” matsawa yayi ta wucce har takai bakin qofar yace “yinin yau banci abinci ba Ina abinci na?” Ko kallon arziqi bai samu ba tayi ficewarta.Ajiyar numfashi yayi ya dauki yourghut da cake ya fita ya nufi dakinsa dake sama abin takaici da mamaki dakin kaca² gadon harda danshi alamun baa dade da tashi akai ba ya ajiye yourghut din ya fara gyara dakin ya gama ya shimfida sallaya yaci abinda zaici ya miqe yayi wanka ya dawo ya dauki laptop dinsa ya fara aikace²nsa sai wajen daya sannan ya kwanta saime?Zuciyarsa taqi hutawa da tunanin Hauwa da zarar ya rintse idonsa kallonta yakeyi matse jikin mota ya hade jikinsa da nata yana sauke mata kiss a kuncinta jikinta na rawa tunaninsa gabadaya ya karkata ya koma Rugar Sambajo qauyen su Jiddoh yasan dai bai barta da matsala ba tunda ya biyata kudin nononta da wautarta tasa ya zubar da haka ya kwana ko cikin baccinsa itace wai tana shafa gemunsa tana cemasa “I LOVE U My Lameer” shikadai yaketa zuba murmushi yana qara qanqame pillow.Hodijam Jiddoh baiwar Allah wannan dare ta daku gurin goggonta har saida ta kumbura mata jiki saboda duka da muburgi fadi takeyi “ni zaki kunyata ki jawa abin hwadi a gari dan ubanki ki rasa wa zakike kulawa kuna shiga duhun dawa dashi yana lalubeki sai kado ashe da gaskene da Madi dan burni yashe yana ganinki kina kaiwa wani dan yankon kayi nono yanayi miki juyensa ya baki kudi da yawa, to daɗa Allah ya nunamin kuɗi har jaka goma a jikinki ɓingel wato kuɗi yake baki yake ƙwaƙuleki ko?”Girgiza kai takeyi kamar zata tsinkeshi tana kuka jikinta na rawa goggo ta sake nufota tana cewa “kina yimun bayani ko sai nasha aradu ani gaton uwarki”Jiddoh bata iya qaryaba cikin kuka ta zayyane musu komai suka rinqa sallalami da tafa hannaye suna hwadin “aradun Allah Jiddoh kin riqa qugunki ya isa daukan bindira tunda har kado ya hwara hwadi maki batun aure to kuwa ai dole baffanki yayi miki aure da Madi dan burni tunda ke shegiyar ya ce” Wata wawura goggonta ta kumayi mata ta zauneta ta bare qafafunta tana kuka tana ihu ta dauki danyan tasshi ta murza Mata ta dagata tace “gobema ki qara bari Kado ya tabaki har ya dambusheki dau uwariyonki aurakiya kawai almura me idon agwagwa”Habawa me Jiddoh zatayi banda kuka tumami da ihun azaba danyan barkono a gatonta sai tsuku yakeyi Mata ita kuma tanata dara tana tumami tana ihu da kuka me ban tausayi.A haka goggonta ta cillo Mata bokatin qarfe tace “tashi dan ubanki kije rafi ki daukomin ruwa kizo kiyi wanka kiyimin wankin daudata ki sukole wadannan kayan naki bazan kwanta dake bukka dai ba babu tsarki yau sai kin qarar da ruwa buta goma” Hakanan tana tafe tana talewa tana kuka taje rafin ta zauna a bakin rafi tanata rera kukanta taji an warce bokitin nata ta dago da sauri zatayi bala’i sai taga Madi a tsaye sai washe baki yakeyi yana turo harshe gaba yace “hegiya Jiddoh yau nayi miki burni ai ya nine nazo nace naganki da Kado a cikin duhun dawa kuna cicin tsuli kuma aradun Allah gobema na ganki kin qara kai mushi nono sai nayi miki sharri da yahi haka tunda ke bakyaji kuma kin rainani aradun Allah bindira ta tahi ta Kado qarhi kuma kizo muje bayan rafi a gwada ki gan….”Qumm yaji an buga masa Abu a goshinsa jini ya balle ita kuma taja da baya da sauri tace “alqur’anin Allah kai tsinanne ne Innan qotai tayi asarar aihuwa shege dan durun uwa danma ka samu nace da Kado ka iya sa agogo to tunda kai Dan iskane na daina sonka ma na tsaneka na tsaneka hege bindirar ka din uwarka an hwadi muka di diyat iskace”Damqota yakai hannu zaiyi ta qara jifansa da bokatin ta kwasa da gudu ta shige cikin duhun dawa tanata bubbuda qafa saboda zafin tasshin da takeji a qasanta har yanzu ta jima a gurin sannan taga yabar gurin ta fito da sanda ta kandami ruwanta ta dora akanta ta nufi cikin rugarsu takai tayi wanka ta wanke gidan dadin sosai Amma har lkcn zafi yakeyi Mata ta shafa versilin a gurin ta rinqa fifitawa har Allah yasa taji relief ta koma daki tayi sallah ta kwanta tanata juyi qasan zuciyarta cike da tunanin Kado tare dajin haushinsa na jamata dukan da yayi a fili tayi tsaki tace “Kado hege ne harda wani hmwah yayimin qaton kawai saikace Bandirawo Iro”…………Washegari tun asuba ya tashi ya fara shirya kayansa cikin trouble bag dinsa kasancewar yasan Koda ya tashi Mubaraka ba lallai ta tashi ba zatace yayi wuri da yawa to shima baiyi yunqurin tashin nataba ya gama shirinsa tsaf ya hada tea dinsa yasha ya kira drivern office dinsa ya daukeshi zuwa airport kasancewar tafiyar bashi daya bane da sauran abokan aikinsa zasuje training din.Yana zuwa babu bata lkc suka daga zuwa South Africa zuciyarsa cike da kewar parents dinsa da yar fulaninsa Hauwa da kewarta take neman zame masa jiki a wannan lkcn haka ya wanzu cikin wata irin rayuwa daya kasa gane wacce iri ce kullum zasuyi waya sau biyu da Mubaraka ya tambayeta lfyrta data yarsa Fadwah amma ya kasa daina kewar qasarsa ta gado musamman Rugar Sambajo.____________Kwananta uku bata dauki tallan nono ba ko dandali ta daina fita duk a qoqarinta na karsu hadu da Madi dan burni yace zai sanya mata bindara tunda taji Indo qawarta da akayi Mata aure tana cewa bindira lubebiyace idan ta shiga bata iya fita saidai ta yayyaga mutum kuma idan ta tashi dane yake tunkudota waje.Shiyasa take masifar tsoron bindira ita har kuka takeyi da tumami idan akace zaa kaita asa mata bindira, tana tafi tana yan waqoqinta taci uwar dammara abinka tayi kwalliya ta rambada kanta kile harda digon india a goshinta da kumatunta tasa kayansu na fulani shudaye tana tafe tana waqar “lula lulaye aluliya zani bikin andi aluliya” batasan binta akeyi ba saida tazo jikin wata bishiya kawai taji an dumbular mata nono an kwasa da gudu.Aikuwa ta dora hannunta akan nononta tana ihu tana burgima tana hwadin “shikenan na mitu na lalashe dan innini na sun tabamin wayyoh Goggo wayyohhhh Baffa wlh bazan yarda ba saina taba nonon uwarsa nima” wasu yanmata ne guda uku sukazo wuccewa suka ganta a kwance duk tayi birgima tayi tumu² suka tsaya suna kallonta tare da tafa hannu sukace “Hamdi imboni Jiddoh meye hakadin?” Miqewa tayi zaune tana karkade qasar data shiga cikin dogo baqin gashinta da ya mulku da manshanu tace “Qur’ani saina mulmulawa uwar Wanda ya dumbularmin Inninina Fura a gatonta”🤣🤣Dariya suka kwashe da ita Lantana ta kalli Jummai tace “kiji doluwa to yau aka fara dumbular inninin naki naga cewa akayi har Kado kike bawa yakesha shiyasa sukayi girma sukayi ruguza ruguza haka” Zabura tayi tace “kutmar dumadu naci hagu naci dama naci tattabatsinin kantalin baqoramar inyaniyar marurun tsohon gwailon uban wanda ya hwadi haka” kafin suyi wani aune ta hade kansu guri guda ta kama jibgarsu hagu da dama tana wani tsalle tana naushi ta ko Ina.Suna ganin haka kowa yaci na kare ta kuwa rufa musu baya a guje fadi take. Yau har bayan tsoho da tsohuwa suna doki doki sai nabi ƴa naci uwar galken ubanta Kaɗon dako mgn bata dameshi ba ina ya iya wannan iskancin shi banda sumba da qaquba babu abinda ya iya kuma qur’ani saina hwaɗí muhi bashi kawo lantarki gidanku”Yanda suka rinqa gudun a daji abin abin dariya kuma sai qara rungume qirjinta takeyi wai kada a qara dumbular mata nono😁Jitayi an riƙeta ta baya taja ta tsaya tana huci tare da waiwayowa zatayi bala’i sai tayi ƙasa luuuu saboda ganin yayanta lawan tasan ta kaɗe har rassanta rirriƙeshi tayi tana kuka tana cewa.”Alqur’an bani na tsokalesu ba sune kawai ina kukana da burgimar tuba sukazo suka tambayeni meye yasani kuka nace adumbili akayimin shine sukace wai ai dama ance ina bawa Kaɗo nono na wannan na jikina bana shanuwa ba yanasha kuma aradun Allah ƙarya sukeyi barima na fito maka dashi ka gani”Hannu ya dora aka yace “honi lawwali ni zaki nunawa dan qaniyarki yar ja’ira tashi muje wuro kiyi bayani” yanayin gaba ta miqe da sauri ta nade zanenta ta kuma kwasa da gudu ta nufi gdan yana kiranta yana komai amma bata tsayaba saida ta isa gdan ta shige dakin kishiyar Goggonta tana mazari Inna Jummah ta miqe da sauri tace.“Wanne niya meye hakadin ubanwa kika taokano” sake qanqameta tayi tana kuka tana girgiza kai yana zuwa ya cake yace “zakici qaniyarki yar kusun uwa”Yana fita ta zube a tsakar dakin tana mayar da numfashi tace “wlh sai nayi qulla ciki akan wanda yayimin adumbuli” tafa hannu jummah tayi tace “gide shiyasa nice da baffanki yayi miki aure” Saurin rufe Mata baki tayi tace qur’ani baniso ance idan akayi wai…Wai….” Saurin daga mata hannu tayi tace “aradu ya isa kuma dole baffanki ya aurar dake shekara sha hudu qawayenki harda yayansu ke kinanan kina bambadanci a gari” Miqewa tayi tace “ai saiki aurar dani din yo aradun Allah guduwa zanyi kamar yanda Ladin Moddibo ta gudu nima na rinqa shigowa daga maraya Ina taunar danqo Ina tafiya qwasqwas.Binta tayi da kallo har ta fice daga dakin ta nufi dakinsu ta kwanta tare dajan mayani ta lullube jikinta dashi yau goggonta da kanta ta fita tallan nono, zuciyarta ce ta tafi tunanin Lameer ta dallawa kanta mari tare da jan tsaki tace “aikin banza ma ko meye gamina dashi.

Back to top button