Fentin Zina Page 6 Hausa Novel
Kamar baza tace wani abu ba.Ya dube ta cikin kulawa yace, kiyi magana ina jinki kada kiji komai fadi abunda ke ranki.Tadan numfasa tace inaso kamun alkawarin duk rintsi, ko wani irin yanayi muka shiga bazaka juya mun baya ba.Shiru yayi na dan lokaci sannan yace, bazan juya baya a gareki ba kima daina wannan tunanin soyayyace ta kaini ga auren ki ba kiyayya ko auren hadi ba, ko yanzunma da zanyi wannan auren bawai don kin gaza ta ko wace fuska bace a’a, ra’ayin ne kawai ya shigeni ba tare da ni kaina na shirya wa hakan ba, bana bukatar ki tashi hankalinki akan wannan batun kinji ko?Ta gyada kai sannan tasa hannu ta lakuci hancinta tace insha Allah bazan zame maka cikas akan batun aurenka ba ina fatan Allah ya hada kanmu ya kuma baka ikon kwatanta adalci.Ameen yace kana ya mike ya mikar da ita suka shiga ban daki, wanka ya taimaka mata tayi don ya tabbatar batayi ba, suka fito ya mata duk abunda yasan tana yi kafin kwanciya bacci yaja ta suka fada gado duk bata da kuzari a jikinta.Suna facing juna yana mata murmushi yace muyi bacci ko?Ta gyada kai tana lumshe ido.Sai daya tabbatar bacci ya dauketa tayi nisa ya lallaba ya fita zuwa falo ya kunna datar shi ya samu sakonni da yawa kan WhatsApp din yabi su daya bayan daya yana amsawa karshe ya tsaya kan number maryam inda take cewa “haba sweet baby inata jiranka baka kirani ba kuma ka hanani kiranka ka kirani kajiii”.Murmushi mai sauti yayi yana girgiza kai yace, maryam rigima kenan. Kafin ya kara cewa wani abu saiga kiranta ya shigo ta voice call yayi received yasa kara don bai cika son sa waya a kunne ba.Hello baby ya kake?.Lafiya kalau nike kefa?Ina lafiya sai kewar ka data addabeni a zuciya.Kada ki damu kin kusa zama tawa daga nan sai yadda kika ga damar yi dani ko?.A’a wane ni rufa mun asiri kaifa mijin wata ne kuma dai tare zamu raba ka, idan na tuna hakan sai inji babu dadi dama ni ka fara aura ba ita ba.Ki daina fadan irin wannan maganar ke kinsan ina sonki and then idan kika zama matata har akwai abunda zai hanaki rabata ne?.Baby kasan fa yadda nike kishinka zanfi so ka raba mu kada ka hadani gida daya da matarka.Banida wannan ra’ayin a yanzu saidai zuwa gaba,.Kasan tanadin danayi maka kuwa? Daka sani daka amince da bukatata.Kada ki damu ai nan dinma duk dayane zakiyi duk abunda kike so babu mai hanaki.Ameena tun sanda ya fita ta farka ta bishi da ido tana mamakin ina zaije, saida taji maganar shi a falo ta tashi ta nufi kofa ta tsaya tana sauraren abunda yake cewa hankalinta ya soma tashi sosai ta koma saman gado ta zauna ta dafe kai ba tare da tasan me zatayi ba.A haka ya shigo ya sameta, sosai ya fahimci zaman me takeyi amma saiya fuske yace lokacinda yake zama kusa da ita a gefen gadon.Lafiya kika zauna kodai ciwon kanne har yanzu?.Kallo ta jefa masa wanda sai daya tsargu.Meke damunki ne?Babu kawai banji dadin kwanciyar bane saina farka.Ok toh ki daure ki kwanta zaki samu sauki zuwa da safe sai muje asibiti.Batace komaiba ta hau ta kwanta tana tunanin yaune ya tsiri yin waya da dare koko dacan yana yi yau dinner dai ta ganshi? Tana ta sake sake har bacci ya dauketa.Washe gari kamar yadda ya bukata Abba ya dauki amininshi suka tafi can gidan su maryam din domin neman auren ta wa Abdul.Babu laifi sun samu tarba amma yanayin tarbiyyar gidan da Abba ya lura sai yaji wani iri, sun kammala abjnda ya kawo su suka koma ya kira Abdul tun kafin su iso ya mishi albishir da an bashi auren maryam harma sun biya sadaki don dama sun tafi da kudi idan an bukata sai su bada.A office kuwa koda Abba ya kirashi zuna zaune shida maryam ya shaida mishi yadda sukayi, murna suka hau yi daga shi har ita abunma harya so baiwa maryam din mamaki domin bata dauka zaiyi farin ciki irin haka ba taso ta tambaye shi sai kawai ta fasa suka cigaba da abunda sukeyi duk akan yadda zasu tsara bikin.Daga yadda ya shigo gida Ameena ta farga da abunda ke faruwa domin Allah ya mata baiwar fahimtar kadan daga cikin yanayin mutane da kuma dabi’unsu, sannu da zuwa ta mai ya amsa cikin sakin fuska yana zolayarta, bata nuna komai a fuska ba amma kasan zuciyarta kishine fal ke cinta don har ji take makoshinta ya dan bushe ga kanta dake sara mata kamar zai rabe biyu.Bai fada mata maganar saka ranan ba domin ya lura bata warke daga ciwon kan ba, yauma a dakinta suka kwanta saida tayi bacci kamar jiya ya zame ya koma falo ya cigaba da waya da sahibarsa.Yaukam kasa jurewa tayi ta fito ta same ahi a falon, ya diririce daya ganta yana cewa la…. Lafiya? Ya kashe wayar.Bata amsa shiba ta zauna saman kujera kusa dashi ta juyo tana kallon shi fuska da fuska ta sauke ajiyar zuciya tace, bai kamata ba, cikin gidanka, dakina, falona, bai kamata kazo kana mun waya da wata ba duk da aurenta zakayi amma sam ba daidai bane domin har yarzu bata halasta gareka ba wannan hurumina ne dan Allah na rokeka ka daina kada ka raunana mun zuciya bayan ina kokarin kwarara kaina, amma kayi hakuri idan abunda na fada ya bata ranka ba nufina kenan ba, ta fada tana mai sunkuyar da kanta.Murmushi yayi ya girgiza kai yana cewa abunda nayi baikai ko digon kwayar zarra ba idan aka danganta da naki, bata halasta a gareni ba amma shi ai ya halasta a gare ki a wancan lokacin, waima tsaya kodon kinga ina lallabaki ne ki dauka tsoronki nikeji? Duk abunda nayi niyyar yi kedai baki isa ki hanani ba, duk wannan ciwon da kike karyar yi saboda kishi bashi zai hana ni yin auren nan ba, ki sani dole ne in kawo wata cikin gidan nan daidai da muradina, in banda ke butuluce ma har zaki yi maganar dacewa anan? Indai dacewa ne tun farko nine ban dace dana aure kiba.Bata tsaya karasa jin me zaice ba tayi daki da gudu ta kife a gado ta shiga rera kuka tana kara tsinewa Ahmad albarka don shiya jefata a wannan halin, daba don shiba da badon yaudarar daya mata ba da yanzu tana rayuwar aure mai kyau mai dadi, ta fara magana tana kuka Allah ya isa tsakanina daa kai Ahmad Allah saiya mun sakayya bakin mugu azzalumi bazan taba yafe maka ba, Allah kasa inci wannan jarabawar daka jarabceni da ita ya Allah!.Shiko Abdul cigaba yayi da wayarshi a nufin saiya koya mata hankali ya lura barinta da lallabata da yakeyi na neman kawo raini a tsakaninsu, yana sonta amma bai kai son ya auri budurwa yaji yanda masu auren budurwa suke jiba, yana so ya zama mutum na farko daya fara keta ‘yan matancin matar shi to bai samu akanta ba kuma bazai iya hakura ba ya riga yasa abun a rai sosai.Har tsawon kwana biyu basu kara wata mu’amala mai fasali ba amma zatayi dukkan ayyukanta data saba sannan bata fasa mishi abubuwan da take mishi ba illa rashin sakin fuska da basuyi wa juna, a nashi bangaren hankalin shi kacokam ya raja’a kan bikin shi da duk wasu shirye-shirye domin hidima akeyi sosai a can gidan mamarshi kamar yadda ta bukata a gidanta za’ayi bikin.Tana zaune a falo ta lula duniyar tunani sosai saidai taji fadowar abu kanta, figigit ta dawo daga duniyar tunanin data fada taga shureim a gabanta yana mata dariya cike da farin cikin ganinta, fateema na tsaye daga dan nesa kadan tana kallon yayar tata cikin tuhuma.Am fateema karaso mana kika tsaya daga nan kamar bakuwa? Ta dago shureim jikinta tana cewa kai shureim wannan nauyi daka kara haka me inna take baka kana cine?Cikin dariya yace tuwo da taliya da kifi da shinkafa da kunu da kosai jiya ma munci nama.Good boy Allah ya maka albarka ya shirya mun kai tafarkin addinin musulumci.Ameen fateema ta fada tana zama kusa da Ameena tace, Adda ina kwana?Ta juyo ga fateema tana kara boye damuwarta tace lafiya kalau fateema sai yau, tunda kikace zakizo nake ta duba hanya.Adda kenan kema kinsan baba malam dakyar fa ya yarda nazo saima da inna tasa baki a hakan ma ba don yaso ba.Murmushi tayi tace Allah sarki baba malam da gaskiyar shi wannan killacewar da kikaga yana miki shine alkhairi a rayuwarki don haka kada kiga laifinshi nice wacce na karya mishi zuciya na warware yardar shi garemu bana fatan ko a mafarki abunda ya faru dani ya faru dake fateema.Adda kamar kina cikin damuwa na gani.Ajiyar zuciya ta sauke kamar bazata fada mata ba sai kuma taga bata da wacce ta fita nan ta kwashe komai ta fadawa fateema har ta diga aya.Fateema tace cikin tausayin ‘yar uwarta, innalillahi wa inna ilaihi raji’un Adda kiyi hakuri amma hamma Abdul bai kyauta ba, bai kamata ya dinga amfani da kaddarar ki gurin jefan ki da munanan kalamai ba, bai kamata yake tuna miki abunda ya wuce ba, duk na mijin kwarai bazaiso tarwatsa rayuwar gidan shi saboda wani kuduri nashi da bayada tushe ba.Ameena ta kalleta, ban gane kuduri ba, har Abdul zaice zaiyi aure saboda wani kudurine.Murmushi fateema tayi tace Adda ke matar aurece sannan abubuwan da kika facing a rayuwa yaci ace kin fahimci duniya yanzu, Amma wanna auren da hamma Abdul zaiyi na manufa ne da kuma son cimma kuduri, abunda yasa nace haka shine ita wacce zai aura din budurwace don ke bai same ki budurwa ba shiyasa zai huce a ganin shi kenan idan ya auri budurwa.Dafe kanta tayi tana salati.Fateema tace kada ki damu idan yayi da niyyar ya cutar dake ko ya bakanta miki Allah mai kowa mai komai yana kallonsa bazai samu nasara ba kuma kada kisa tunani a ranki don idan wani abu ya sameki bafa asarar shi bane, mune zamu ji jiki da danki.Fateema ya zanyi nasan idan Abdul ya auri budurwa shikenan zai daina sona ya juya mun baya daga nan kuma tawa ta kare a cikin gidan nan yanzuma ya na kare.Ta fada kamar zatayi kuka.Kiyi hakuri Adda hakan bazata faru ba insha Allah, bazai samu wata nasara ta rabaki da farin ciki ba.Allah yasa, suka mike suka shiga kitchen dukkansu suka soma hada hadar daura girki.**** *****Amarya maryam zaune da kawarta baby suna tattauna abubuwa game da bikin.Baby tace amma kinsan cewa matar Abdul tana da dan shege kafin suyi aure da Abdul din?.Kamarya ban gane abunda kike fada ba, Abdul din dana sanshi da bala’in kishi har zai auri wacce take da dan da fatiha kuwa, anya kin bincika da kyau baby?.Tsaya nan kina wasa daga majiya mai karfi na samu wannan labarin ban kuma fada miki ba har saida na tabbatar domin kuwa har unguwar su naje na bincika kuma an tabbatar mun da gaskiya hakane.Ayyururuiii….Maryam ta rangwada guda tana tafa hannuwa, lallai naji dadin wagga batu ke kice inada makami yanzu a hannu na saitawa shegiya hanya ba tare da shan wahala ba Allah dai ya kai damo ga harawa.Amma dan Allah kada ki mishi maganar ya tambaye ki inda kika ji kice nice.Haba baby kike magana kamar yarinya taya ma zan tare shi da irin wannan maganar ai saima yace ya fasa auren nawa kinga nayi asara.Ai kuwa nima bazanso ba kinda jima zaune bakiyi aure ba har gara nima tunda nayi fitowa dai nayi.Biki yanata matsowa, ango da amarya sai shiri sukeyi yayinda ya rage baifi saura sati ba inna ta kira Ameena a waya lokacin ta gama aikace aikacenta na yamma tana zaune a falo tana kallon tashar sunnah wayarta tayi kara data duba taga innace sai tayi murmushi tace inna kenan ta daga ta sa a kunne.Assalamu alaikum ina yini inna ya aiki?.Inna same zaune tana yanka alayyahu fateema na zaune a gefenta tace, wa’alaikissalam lafiya kalau Ameenatu ya hakurin rayuwa kuma.Tayi murmushi tace inna lafiya kalau Alhamdulillah.Yauwa masha Allah, kina jiba!.Eh ina jinki inna.Ki kara hakuri a game da lamarin nan ki kara kaimi wajen kai kukan ki ga Allah babu dare baby rana koda bakin wasa ban amunce ki cutar da mijinki ko abokiyar zamanki ba koda da kalaman bakinkine, ki koyi kawaici da juriya da maida komai ba komai ba insha Allah nasara taki ce, mamarku zata taho ina jin zuwa jibi kuma a gidan naki zata sauka kinsan yadda take kaunar ki, sannan malam ya baiwa fateema izinin tahowa gidan naki itama jibi amma bazata zo da shureim ba don haka ki kara hakuri kinji.Toh inna nagode Allah ya saka da alkhairi.Ta sauke wayar tana jinjina kai tace, ni kaina bazanso zuwan shureim a yanzu ba.



