Hausa novels

Ruwan Zuma Page 25 Hausa Novel

(25) Laila ta jima tsaye a cikin d’akin sannan ta bi Haydar falo bayan ta tabbatar ta saisaita kanta. A kan kujeran dinning table ta sameshi yana danna wayarsa, jin motsinta da yayi yasa ya ajiye wayar ya zuba mata idanu har ta iso ta mik’a mishi rigarsa. “Ka saka rigarka don Allah.�? “Zafi nake ji.�? Yace da ita ba tare da ya kar6i rigar ba. “Haydar.�? Ta kwa6eshi tana ajiye masa rigar a kan cinyarsa. “Ki tambayi Ammi ko a gida bana son saka kaya.�? Rolling idanunta tayi kana ta zauna shi kuma ya mayar da rigar kan cinyarta. “Yanzu don bani da kunya sai in samu Ammi in tambayeta ko kana saka riga ko baka sakawa?�? D’age kafad’arsa yayi yana murmushi bai ce komai ba. Da haka ta fara saka mishi abincin yayi saurin dakatar da ita wai ya isheshi. “Seriously haka kake baka son cin abinci? Ko dai kulaku kake mini?�? Ta fad’i hakan cikin zolaya amma rashin cin abinsa ya fara damunta. “Yanzun ne bani da appetite. Kinci abinci kuwa?�? “Nima banida appetite ne.�? Ta zuba mishi miya kan shinkafa da waken. “Ki k’ara mini abincin.�? Yace da ita yana d’aukan wayanshi. Murmushi tayi mai k’ayatarwa kana tace, “Har na fara jin haushi domin ni nayi girkin da kaina. In k’ara?�? Ta dubeshi taga d’aukanta yake yi a hoto. “Haydar.�? Tayi kiranshi cikin kwa6a tana rufe fuskarta. “Kina yawan kiran sunana. Da gaske na lura yana miki dad’i ne.�? Ya fad’i hakan yana ajiye wayarsa a gefe. Murmushi kawai tayi kana ta zuba cabbage a wani k’aramin bowl wanda aka had’a da tumatir ta ajiye a gabanshi. “Yanda kake da shafaffen tumbin nan nasan Ammi na fama da kai wajen cin abinci.�? “Laila kenan.�? Yayi ‘yar dariya kana yace, “Me ya kai idanunki tumbina?�? Kawar da kanta tayi gefe cikin kunya tace, “Kaci abincinka.�? Bata yi aune ba taji ya jawo kujerarta k’iii ya sakata a tsakanin k’afafunsa. Ita kuma tsorita tayi ta rik’o hannunshi gamm tana zare ido. “A tunaninki ban lura da cewa kema bakya son cin abinci bane? Yanda tumbinki yake a shafen nan Ina son yayi k’ato ya kai haka.�? Ya gwada mata da hannunsa. “Sai ka fara k’ok’ari.�? Tace dashi tana murmusa cikin jindad’in kasancewarsu tare. Matso da bakinshi yayi saitin kunnenta ya fara magana a hankali tamkar mai rad’a. “Kin k’i bani dama ne amma da tuni na nuna miki k’ok’arina.�? Tuni jikin Laila ya d’auki sak’onshi ta lumshe idanunta kana ta bud’esu taga ya koma baya yana mata murmushin cin nasara, kana lokaci d’aya fuskarsa ta zama so serious ya d’auki spoon ya d’ebi abincin yace, “Oya bud’e bakinki in baki abinci, idan kuma kinyi gardama in d’auko bulala kuma da gaske nake ina zane marasa jin magana. Haaa.�? Ba k’aramin dariya hakan ya bata ba ta toshe bakinta har kwalla na taruwa a idanunta. Abunda yafi bata dariya shine yanda ya tamke fuska tamkar da gasken zaneta zai yi. “You are funny.�? Sake fuskarsa yayi shima yana murmusawa ya k’ara mik’a spoon d’in bakinta yace, “Yanayin adadin spoon d’in da kika yi yanayin adadin nawa. Idan kin tsaya nima zan tsaya. Bud’e bakinki.�? Ba musu ta bud’e bakinta ya saka mata abincin tabi da hannunta ta saka sauran tana son yin dariya. “Baka iya bawa mutum abinci ba.�? Ta fad’i hakan bayan ta had’iye na bakinta. Loma ya kai bakinsa yace, “Ki barni in koyi komai a kanki.�? Ya k’ara mik’a mata wani spoon d’in ta kawar da kanta gefe domin maganarsa ta k’ara hargitsa mata lissafi. Shin yasan halin da yake sakata kuwa? Komai ya fito daga bakinsa sai ta masa fassara, fassaran ma dirty one. “Mun k’oshi ne?�? Ya tambayeta yana lek’en fuskarta a ransa kuma farin ciki yake yi domin plan d’insa na tafiya yanda yake so. Dolenta haka ta k’ar6i abincin suna ci tare, har sai data k’oshi ta shafa tumbinta tace, “Don Allah haka ya isa.�? “Nima na k’oshi.�? Ya fad’i hakan yana ajiye spoon d’in. “Better.�? Ta fad’i hakan tana mik’ewa tsaye. “In fad’a miki wani abu?�? Ya dawo da ita ta zauna tana kallon cikin idanunshi. Kad’a kai tayi yace, “Kin iya girki sosai. Thank you.�? Wani dad’i ne ya lullu6eta ta k’ara mik’ewa tana tattara kwanukan tace, “Welcome.�? Da haka ta d’auki used plates d’in shi kuma ya d’auki kulolin ya bita kitchen dasu. A can ya samu ta bud’e ledojin daya dawo dasu tana ajiye komai inda ya dace fuskarta d’auke da annuri. “Kamar kasan sune abubuwan da bamu dasu a gida. Allah ya k’ara bud’i.�? “Ameen.�? Ya amsa yana bin bayanta da kallo. “Ohh dama baka manta da Agwalumana ba? Thank you.�? Ta ajiyesu a gefe ta cigaba da adana sauran kayan abincin. Sai data gama ta juyo tana kallonshi taga kanshi a k’asa. Girgiza kai tayi kana ta sunkuya ta bud’e drawer ta d’auki cup da spoon. D’agowan da zatayi ta jishi a bayanta ya zagaye hannunsa kan tumbinta yana tura kanshi cikin wuyanta. “Haydar.�? “Just a moment.�? Seconds goma da haka ya saketa da sauri ya fita daga kitchen d’in. Itama halin daya shigan ne take ciki, jikinta a sanyaye ta fara 6are agwaluman tana sakawa a cikin kofi. Sai data gama ta zuba sugar kad’an ta dama sannan ta fita falo ta sameshi yana kallo. “Zaka sha?�? Ta fad’i hakan tana zama a kujera mai kallon nashi. “Mutum sai rowa. Sha kayanki.�? Ya fad’i hakan yana mik’ar da k’afafunshi kan 3 sitter. Murmusawa tayi kana ta fara shan abunta tana lumshe ido. Binta yayi da kallo kana yace, “Zo kiji.�? D’an zaro idanunta tayi tace, “What?�? “Zan nuna miki wani abu ne.�? Girgiza kai tayi tace, “Bana so.�? Zai bud’e baki yayi magana aka kwankwasa k’ofar falon tare da turowa aka shigo. Sabrin ce idanunta jawur tare da mijinta Salman yana rik’e mata da jakanta. Ganin Haydar ba riga yasa tayi saurin juyawa shi kuma ya tashi ya shiga d’akinsu ya saka jallabiya ya fito. Yana dawowa falo ya samu Sabrin a jikin Laila tana kuka, ita kuma tana buga bayanta tana cewa tayi shiru. “Lafiya?�? Ya tambayesu cikin d’aurewar kai. Salman ne ya mik’a mishi hannu suka gaisa cikin mutunci sannan suka maida hankalinsu kan mata biyun. “Mama kiyi hak’uri ki yafe mini.�? “Nace ya isa haka na yafe miki duniya da lahira Sabrin. Ki daina kukan nan haka, tashi ki share hawayenki.�? Da haka ta mik’ar da ita zaune Salman yayi saurin mik’a mata handky ta kar6a tana goge fuskarta. Yarensu na shuwa Sabrin ta fara yi Laila na girgiza kanta. “Ya wuce, kinji?�? Ta kad’a kanta tana goge hancinta kana ta dubi Haydar wanda shima su yake kallo tace, “Ina wuni.�? Zai iya rantsewa Wannan shine karon farko da magana mai dad’i ya ta6a shiga tsakaninsa da Sabrin. Murmusawa yayi yace, “Lafiya kalau, Hamdallah. Kuna lafiya?�? “Lafiya kalau.�? Da haka kowa yayi shiru a d’akin kana Haydar ya mik’e yace, “Zan fita.�? Laila zata tashi ya dakatar da ita yace, “No, kiyi zamanki.�? “A dawo lafiya.�? Tace dashi kana ta maida dubanta kan Sabrin wacce ke son yin magana tun d’azu. “Amm Uncle Haydar kayi hak’uri kan abubuwan da nayi maka a baya.�? Ta fad’i hakan tana sunkuyar da kanta k’asa. “Babu komai Sabrin.�? Da haka ya fita daga falon Salman ya bishi a baya ya tsayar dashi suka fuskanci juna. “Sunana Salman, thou nasan ka ganeni. What I want to say is; I’m not against your marriage illa ma murna da nake yi da yasa Mama tayi aure. Mutumiyar kirki ce bata aikata abunda ake zarginta dashi. Sai dai yau dana duba naga an cire hotunanku da duk wani batu da akayi a akanku.�? Ba k’aramin dad’i hakan yayiwa Haydar ba, domin saboda gudun 6acin rai yasa ya daina shiga duk wata social media da yake yi. “Kun gani kenan?�? “Yes.�? Ya bashi amsa yana kad’a kai. Haydar ya mik’a mishi hannu yana cewa, “Mun gode.�? “Anything for Mama.�? Da haka suka yi sallama Salman ya shiga motarshi ya tafi shi kuma Haydar ya isa bakin titi ya tari achaba ya nufi gurin abokinsa kwalli d’aya tak, wato Nasir. Bayan fitan mazan ne Sabrin ta k’ara kwaye fuska tace, “Mama ki gafarceni don girman Allah kar Allah ya kamani da laifin saka mahaifiyata kuka.�? Ta fad’i hakan wasu hawayen na taruwa a idanunta. “Na fad’a miki na yafe miki Sabrin. What change your mind cikin k’ank’anin lokaci haka? Na d’auka ai kin rabu dani ne.�? Share hawayen fuskarta tayi kana tace, “Har duniya ta nad’e bazan ta6a samun wanda zai soni kamarki ba Mama, kuma bazan ta6a canjaki ba. D’azu Uncle Mas’ud yaje gidana ya bani labarin da ban sani ba game dake, dama uwa tana iya sacrificing farin cikin rayuwarta don ‘yayanta? Ashe haka kika wahala damu har muka kawo wannan lokacin Mama? Wallahi bamu miki adalci ba da muka kasa baki goyan baya akan abu guda da kika nuna kina so ba. Ki yafe mana don Allah.�? Shiru Laila tayi domin itama hawayen ne a idanunta ba tare data bari sun zuba ba, can tace, “Kina da labarin Abul?�? Gyad’a kai Sabrin tayi kana tace, “Yana can gidan abokinsa Micheal, munyi waya dashi yace kar na bawa kowa numbernshi. Kar ki tayar da hankalinki Mama, yana nan lafiya kuma monday zai je school.�? Laila ta godewa Allah a zuciyarta tana jin sanyi a ranta. Kenan Abul d’inta yana nan cikin k’oshin lafiya ba tare da yaje ya yiwa kanshi illa ba. Da haka suka cigaba da hiran tsakanin uwa da d’anta cikin farin ciki, domin kaso sittin na damuwar Laila ya kau babu shi. Burinta da fatanta har gobe bai wuce ace ‘yayanta na jikinta tana ganinsu ba. Sai bayan isha Salman yazo ya d’auki matarsa suka tafi. A nan Laila ta samu kanta ta fara tunanin ina Haydar ya shiga. Wayarshi ta kira ya d’auka yana cewa, “Matar Haydar.�? Murmushi tayi ta zauna tace, “Ina ka shiga?�? “Kina tsoron a sace miki ni ne?�? Wani murmusawan ta sake yi wato yasan duk yanda zai yi ya sakata nishad’i. “Ka dawo gida.�? Tace dashi kana suka yi sallama. Bayan ya dawo sun ci abinci take bashi labarin abunda ya faru, yanda yaga take farinciki da sanin inda Abul yake ya tabbatar ba k’aramin so take yiwa ‘yayanta ba kamar yanda Mas’ud ya bashu labari. Suna cikin hiran Mas’ud yayi sallama ya shigo da Naana wacce ke kumbure-kumbure kamar bata son zuwan. “Amaryar ka d’auko ka kawo? Baza ka bari gobe inje gidan naku ba?�? Laila ta fad’a cikin mamaki. Domin d’azu ta rana ya shigo take Fad’a mishi cewa gobe zata je taga gidansa da amaryarsa yace to. A nan take tambayarshi key d’in sashensa yace bai san a ina ya ajiye ba. “Na kawo miki ita ki ganta ne domin baku ta6a had’uwa ba.�? Ya fad’i hakan yana zama kusa da Naana. Da haka suka gaggaisa ita dai Naana fuskarta sam babu fara’a, ko da Laila ta lura da hakan sai ta raya a ranta cewa ko dai jikin ne irin nasu na Amare, domin kuwa yarinya ce wacce bazata wuce shekara ashirin zuwa ashirin da biyu ba. Haydar da Mas’ud hiransu suke yi akan wata sabuwar cuta data 6ullo wai Corona Virus wacce a kanta har gwamnatin Nigeria na cewa zata rufe makarantu, kasuwanni da duk wata ma’aikata. “Ni ban yarda da wannan cutar ba.�? Fad’in Mas’ud kenan in conclusion. Laila k’ok’ari take yi taja Naana da tad’i amma sai ta nok’e tak’i ta sake da ita. Basu jima ba Mas’ud ya tashi wai zasu tafi. “Don Allah Mas’ud gobe ka zauna a gidanka karka dawo nan. Yau sawunka uku gidan nan.�? Fad’in Laila cikin fad’a. “Zan dawo sai dai karki bud’e mini k’ofa.�? Yana fad’in hakan yaja hannun matarsa suka fita yana dariya. Laila har bakin k’ofa ta musu rakiya kana ta koma ciki. Su kuma suna shiga mota Naana ta 6ata ranta sosai tana kumburi. Ko da Mas’ud ya lura da hakan yace, “Yaya dai Amarsu?�? Bata kulashi ba har suka iso gida yana cakalarta da tsokana sai basarwa take yi. Tana fita daga motar shima ya fito yayi saurin isa gurinta yana jawota jikinshi. Da k’arfi ta fisge jikinta tana cewa, “Don Allah ka barni.�? Daya lura da gaske take sai ya saketa suka shiga falonsu a haka, a nan ne ya nemi ta zauna zasu yi magana, taso ta mishi musu amma data dubi kwayar idanunshi sai taga shima babu wasan a fuskarsa. “Mena miki Naana? Naga lafiya kalau muka fita amma tun muna can na lura kamar wani abu ya 6ata miki rai.�? “Jiya-jiya aka d’aura aurenmu amma yau sawunka uku gidan yayarka ka kasa zama a gidanka. A yanda kowacce amarya ke samun hankalin mijinta ni ban samu ba Mas’ud, da safe ka fita ka barni sai da kayi awa biyu kafin ka dawo, da rana ma haka ka fita ka barni kaje gurinta sai la’asar ka dawo gida. Yanzu kuma kazo ka tilasata mini akan sai mun je gidanta na gaisheta, nifa Amarya ce, kamata yayi ni za’a zo gidana ba wai ni in fara bin gidajen mutane ba. Na rasa meyasa gabad’aya hankalinka baya kaina.�? Shiru yayi yana tunani sannan can ya d’ago yace, “Naji ban kyauta ba kiyi hak’uri amma na fad’a miki da safen karyawa naje d’auko mana.�? “Zaka iya yin order ba dole sai a gidanta ba.�? Ta bashi amsa cikin hargowa. Runtse idanunsa yayi na wasu sakanni kana ya bud’e yace, “Bai kamata daga aurenmu har mun fara samun sa6ani ba Naana, sannan Kalti da kike magana da ita na tashi na rayu a matsayin abokiyata kuma yayata, gaskiya bazan ji dad’in tun daga farko ki fara nuna bakya sonta ba.�? Yana fad’in hakan ya shige d’akinsa ya barta a nan cikin mamakin wai wani irin so mijinta yake yiwa yayarsa? Bayan tafiyarsu Mas’ud Laila ta koma falo ta samu Haydar ta kira sunanshi ya juyo yana kallonta. Sai data zauna sannan tace, “Dama d’azu ne Alhaji Abdul ya kirani muka yi magana.�? Yana jin ta ambaci sunan fuskarsa ta canja, shiru yayi bai ce komai ba. Ganin hakan yasa taci gaba da magana cikin sanyi. “Ya fad’a mini ya kiraka yace ka koma bakin aikinka kace baka so, shine yace in fad’a maka cewa in ma jin nauyinshi kake yi ka daina ka koma bakin aikinka domin ya yarda da k’addara yasan ni ba matarsa bace.�? “Duk wannan maganan shi ya fad’a kuma kina saurarenshi? Kuma yaushe na fad’a mishi ina jin kunyarsa?�? Ya tambayeta yana zuba mata ido amma ita kanta ta gane ranshi ya 6aci. “To ya zan yi? Kar yace na wulak’antashi.�? “Bana son ki k’ara d’aukan wayarshi Laila.�? Ya fad’i hakan gaba gad’i wanda yasa ta dubeshi da kyau ko wasa yake yi. Ganin da gaske yake yi yasa itama taji ranta ya fara 6aci, yana nufin juyata kenan zai yi? Zai dinga k’afa mata sharud’d’a tana bi? Data lura zasu iya yin fad’a sai ta tashi ta shige d’akinta ta rufe, kamar zai bita amma ya fasa yayi zamanshi a gurin yana kallo amma hankalinshi na kanta. Sai da yayi awa d’aya zaune shi kad’ai sannan ya tashi ta rufe musu gidan ya kashe wutan falon ya shiga d’akin nasu. A saman gadonta ya sameta ta kwanta jikinta sanye da farar doguwar riga ta bacci mai tsantsi, a yanda ya lura da ita tana son saka fararen kaya. Shimfid’inshi ya gani a k’asa ya tsallakeshi ya isa bakin gadonta kana ya tu6e jallabiyarsa ya bar boxers kad’ai. Hawa gadon yayi a hankali ya kwanta kana ya jawota jikinshi yana cewa, “Ni mijinki ne Laila, ina kishinki sosai yanda bakya tsammani. Karki manta tun kafin in aureki na bar aiki a gurin saboda ganinshi kad’ai zai iya saka mini hawan jini idan na tuna cewa ya sameki ni ban samu ba. Yanzu ma ko sunanshi bana son ana kira, so kiyi hak’uri ki daina d’aukan wayarshi, shi ba danginki bane balle ace ya zama dolenki, kamar yanda kika yanke huld’a da duk zawarawanki haka shima ya kamata ki yanke dashi. Kina jina?�? Kad’a mishi kai tayi bata ce komai ba. Sumbatar kanta yayi ya k’ara rungumeta yace, “Yauwa Matata ta kaina. Nasan kina tayani kishin kanki.�? “Amma da sharad’i d’aya.�? Ta fad’i hakan kai tsaye. Gyaran murya yayi kana yace, “Wani sharad’i kenan?�? Juyowa tayi ta fuskanceshi kana tace, “Zaka koma gurin aikinka domin ka sameni Haydar shi kuma bai samu ba. A k’arshe idan ka koma aikin ma kai kayi winning bashi ba. Fargaban me zaka ji idan ka ganshi alhali kasan ka bar matarka a gidanka? Shine sharad’ina.�? Shiru yayi yana kallon sama tana jiran amsarshi. Ganin zai iya fand’arewa yasa ta d’aura hannunta kan sajen fuskarshi tana shafawa a hankali. “Haydar look at me.�? Ya sauk’o da idanunsa yana kallonta amma ta gane ta fara samun kanshi. Cigaba tayi ta isa har kunnenshi tana shafawa a hankali ta fara magana, “Yanzu kai idan ka sake wannan aikin naka wanne zaka yi? Karka manta kai kake ciyar da Ammi, ga kuma nima na zama iyalinka. Wallahi tun farko bana sonshi, wannan karon ma pressure yasa na amince da aurensa har Allah ya ku6utar dani my knight in shinning armor yazo ya aureni a lokacin da nake tunanin na rasashi. Ka koma aikinka in yaso duk lokacin da ka samu wani sai ka barshi. Kaji?�? Ta shafo tsakar kanshi ya lumshe ido yana rik’ota. “Baka ce komai ba Ruwan Zumana.�? Bud’e idanunsa yayi yana murmushi mai bayyana hakwara yace, “Say it again.�? Dariya tayi kana ta matso ta bakinta saitin kunnenshi ta hura kad’an tace,“Ruwan Zumana.�? “Shikenan, zan koma.

Mum Fateey 👌

Back to top button