Karfe A Wuta Chapter 46 By Ayshercool
Wayar Walid ce ta fara ringing, yayi shiru ya cirota daga aljihunsa ya kara a kunnensa ya ce “Ya aka yi?””Oga walid ka yi sauri ka dawo dan Allah, ya fara dawowa hayyacinsa, kar ya dawo gaba ɗaya ka san ba zan iya da shi ba”.Walid ya ce “Gani nan, ka yi iya ƙoƙarinka, kar ka kuskura ya fita, idan ya fita akwai ƙura ka sani, gani nan zuwa” ya katse wayar ya sakata aljihunsa, ya kalli matasan ya ce “Ku mayar da ita kawai” ya juya zai tafi.Cikin azama Nabila da idanunta suka yi ja saboda kuka ta ce “Dan girman Allah ka yi haƙuri, kar ka tafi, ka ƙarasa mini labarin nan, yaya aka yi Viper ya tafi prsion? Shi aka ɗorawa kisan matarsa? Ta mutu ne ma ko kuwa yaya aka yi, ya kuma aka yi ya fito yanzu? Ni abubuwa da yawa ban gama fahimtar su ba, sun cukurkuɗe mini sun shige mini duhu, dan Allah kar ka tafi baka ƙarasa mini ba”Walid ya ce “Ba zan ƙarasa ba ɗin, ba dai ke mara mutunci ba, na ɗauka haɗuwarki da shi, zai zama alkhairi amma ki ka yi mana halinku na mata, laifina ne da na kawo masa ke, Al’amin ya daɗe da cire mata a rayuwarsa, sai zuwan jauhar cikin rayuwarsa daga kawo ki a tashin farko kin mayar mana da hannun agogo baya, Viper ba zai taɓa zama ya bar liti a tsare ba, saboda shi ɗan halak ne”Cikin matsananciyar damuwa ta ce “Na ji, na yi kuskure amma dan Allah ka yi haƙuri ka ƙarasa mini””Ba zan ƙarasa ba, ki je shi ya ƙarasa miki”Cikin hanzari ta sake tarar Walid ta ce “Dan Allah ka sake yi mini jagora, ka kai ni wurinsa na nemi afuwarsa, na yi kuskure kaina ne ya riga ya gama kullewa na faɗawa lamuran a gaggauce cikin duhun kai, amma a shirye nake na gayara kuskuren da nayi”Walid ya ƙare mata kallo ya ce “Kin riga kin aikata abun da ba zai gyaru ba, kuma kar ki sake yin gangancin zuwa in da yake, idan ba haka ba, ko bai kashe ki ba ni zan kashe ki. Ku ɓatar da ita daga gabana”.Suka saka Nabila a gaba, suka tasa ƙeyarta zuwa cikin napep ɗin da suka kawota, tana ta kallon walid tana yi masa magiya, amma suka ja babur ɗin suka tafi da ita.Suka mayar da ita hanyar law firm ɗin su, suka bata wayarta suka tafi, wani abun hawan ta tare, ta nufi gida, zuciyarta sai bugawa dake da sauri da sauri, cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, ga matsanancin tausayin Al’amin da ya mamaye zuciyarta, lallai an yi wa rayuwarsa yankan ƙauna mafi munin da har ya mutu ba zai manta da shi ba.A falo magajiya take ce mata sumayya ta zo har gida tana nemanta, duk an kira layukanta ba sa shiga, ko akwai matsala ne, gashi yau ta daɗe sosai ba ta dawo ba.Ai har baba magajiya ta gama maganarta, ba ta fuskanci komai ba, ta tafi ɗakinta ta rufe ƙofa, wayarta na ta ringing ta duba, missed calls ɗin sumayya sun fi ashirin, ga na Nasir, ban da barrister Habib, ta kashe wayar, ta cillata kan gado, ta shiga banɗaki tayi alwala ta fito ta yi sallar azahar da la’asar.A kan daddumar ma haɗa kai da gwiwa ta yi, ta din ga kuka, za ta iya cewa tun da ta buɗe ido a duniya, ba ta ji labari mai ban tausayi da tsayawa a zuciya ba kamar na Al’amin.”Why Nabila kin yi garaje, why would you judge the book, according to cover? Why?” Ta tambayi kanta cikin tsananin takaicin abun da ta aikata.Ta kifa kanta a kan gadonta, wani abu tsananin ɗaci yana yi mata zafi a tsakanin ƙirjinta. Gaba ɗaya ta ji ta tsani kanta, wani mugun haushin kanta ya isheta.”Ko yaya yake ji a zuciyarsa yanzu? Dole ya zama bugagge gaba ɗaya, amma idan aka bar shi ya cigaba a haka, to tabbas zai haukace, amma yanzu yaya za ayi na samu ƙarashen labarin nan? Ta haihun ko mutuwa tayi, kuma wa ya kashe aka kai shi prison? Wait, to yaya ma aka yi aka sake shi daga prison ɗin, yana yawonsa idan ya ga dama har ya je yayi ɓarna, kuma still a haka wai nansa ake yi. Wai wannan wane irin lamari ne mai sarƙaƙiya haka? Kar na je na haukace a banza mana” tayi maganar kamar za ta haukace ɗin.Ta cigaba da sintiri, tana ƙirga yatsunta, tana lissafi.”Kai dole na samo ƙarashen labarin nan, ko da kuwa me zai yi mini, ko dai wanda ya fara ya ƙarasa mini, ko kuma shi Vipern ya ƙarasa mini, no matter how and what it takes sai na ji ƙarshen labarin nan, kuma sai na yi wani abu a kai. Haba dan Allah What a pitful life of his? Kai, to ita meye nata ma da za ayi mata haka? Me ta yi she don’t deserve this at all” tayi maganar tana fashewa da kuka iya ƙarfinta.Bugun ƙofar ɗakinta ake yi, amma ko gezau, da ta gaji da jin bugun ma, sai ta tashi ta tafi banɗaki, ta rufe ƙofa ta kunna fanfo, ta cigaba da kuka da tunani.Ƙarfe takwas na dare Abba ya dawo gida, Nabila ya fara tambaya tana ina, Mama ta yamutsa baki ta ce “Ta dawo”Ya jinjina kai, ya tafi sashensa, har ya fara cin abincin dare, ya ajiye cokalin ya kalli mama ya ce “Kirawo mini ita, ina ga ba ta san na dawo ba”Haushi ya ƙule mama, ta tashi ta fita, ta je ɗakin Nabila, ta tarar da ƙofarta a rufe, ta din ga jijjiga ƙofar tana bugawa, amma ba ta buɗe ba.Magajiya ta ce “Hajiya tun da ta dawo fa ta rufe kanta a ɗaki, taƙi buɗe wa, ba yadda ban yi ba taƙi buɗewa”Mama ta yi tsaki, ta koma ta ce wa Abba, “To ka ji tun da ta dawo, ta rufe ƙofa taƙi buɗewa””Kuma lafiyarta ƙalau?””Ƙalau take, tsagwaron iskanci ne”Ya girgiza kai ya ce “No, ko an ɓata mata rai ne, a wurin aiki ko a gida, ƙyaleta na ganta da safe na ji menene, ko kuma rigimar ce ta motsa” yayi maganar yana murmushi. Wani malolon takaici, ya ƙule mama, yadda yake lallaɓa Nabila, yana bin ta kamar wata uwarsa.***Abdul kuwa ganin ramma taƙi mayar da hankali ta ci abinci, hakan ba ƙaramin ƙular da shi yayi ba.Ita kuwa jikinta ne babu daɗi, ga kewar gidansu, tana tunanin mama, ga baƙin cikin abun da yake aikata mata, gashi ya sakata a gaba duk sai ta kasa cin abincin.Tana cikin zancen zuci, ta ji hannunsa a kan fusarta, ta tsorata ta ja da baya, ya tsuke fuska ya ce “Meye haka ne?” Ya buɗe idonta, ya ga she’s still pale.”Solomon” ya ƙwalawa kukunsa kira.Solomon ya fito tare da cewa “Yes sir””Kana da kayan miya ko?”Solomon ya jinjina kai alamar eh.”Kawo mini tumaturi manya guda uku, da wuƙa ka haɗo mini da Apple ja guda biyu”Ya ce “Ok sir” ya cigaba da kallon ramma, da ta ajiye cokalin, ta hau jan rigarsa da take jikinta, tana rufe ƙafafuwanta.Mintuna kaɗan solomon ya dawo, da plate biyu, ɗaya ɗauke da tumatir, ɗaya kuma Apple sai ƙaramar wuƙa guda ɗaya.Ya karɓa, ya matsa kusa da ita, ya ɗora ƙafarsa ɗaya a kan cinyoyinta, ta ɗago cikin rauni idanunta sun tara hawayen takaici, ya yanka tumatirin ya miƙo mata. Ta tsaya tana kallonsa tana kallon tumaturin.Miƙa mata yayi bakinta, ta kawar da kanta ta ce “Ni ba zan iya cin tumatur a haka ba””Zaki karɓa ko sai na burma miki wuƙar nan a ciki?” Yayi mata maganar cikin tsawa. A tsorace ta buɗe baki, ya din ga bata tumaturin nan, tana taunawa da kyar.A zatonta zai bata tuffar, ta washe bakinta da ta ci tumatur, amma ya hau yanka tuffar yana ci, yana yi mata tauna a fuska, yana kallonta ga ƙafarsa a kan cinyoyinta da tayi musu nauyi.Ya gama cin Apple ɗin sa, ya taɓa wuyanta ya ji babu zazzaɓi, ya ce “Haryanzu kina zubar da jinin ne sosai?” Tayi masa banza kamar ba da ita yake ba, ya harzuƙa ya ɗaga hannu zai kwaɗa mata mari, ya ga ba ta motsa ba, sai hawaye da yake bin kuncinta.Ya janye ƙafarsa daga kan cinyarta, ya ce “Ki cigaba da ina yi miki magana kina kallona, ki yi mini banza kashe ki zan yi a banza” tayi shiru ba ta tanka masa ba.Jin ana knocking ɗin ƙofar falon, ya sanya ya tashi tsaye, ya ce “Tashi ki tafi ɗaki, za a shigo”. Ga mamakinsa ko gezau ba ta yi ba, ta cigaba da zama tana zubar da hawaye.Zuba mata ido yayi, cike da tsananin mamakin shegen taurin kai a wurin kucakar ‘yar ƙauyen yarinyar.Tashi tsaye yayi, ya fizgi hannunta, amma ta faɗi a wurin, saboda dama jikin babu ƙwari, ga jiri tana ta fama.Ya durƙusa ya ɗauke ta, ya nufi bedroom ɗin da ita, a bakin ƙofa ya dungurar da ita ta ciki, ya ja ƙofar ya rufe, ya koma ya buɗe ƙofar falon.Wata matashiyar budurwa ce a tsaye, sanye cikin doguwar rigar material, sai hula a kanta, hannunta riƙe da Jakarta.”Ko wata ce a ciki ne? Ina ta bugu amma baka buɗe ba?” Bai yi magana ba, ya bata hanya, ta shigo ta ajiye jakarta ta nemi wuri za ta zauna ta ce “Abdul, staining ɗin jini nake gani a kan kujerar nan”Cikin ko in kula ya ce “And so?””Mace ka kawo gidan nan?””Eh, akwai magana ne?”Cikin takaici ta ce “Abdul don’t try me, ka sanni ka san halina, ba zai yiwu nayi dumping guys ɗina just because of you ba, and ka din ga rough play da ni ba”Yayi murmushi ya ce “Nina, ki na da matsala, saif ne ya yanke hannu da wuƙa, yana cin Apple, yayi bleeding sosai, amma ba abun da ki ke tunani bane ba” tayi ajiyar zuciya ta ce “Yauwwa ko kai fa, har hankalina ya tashi, i so much miss you” tayi maganar tana rungume shi.Gaba ɗaya sai ya ji banbarakwai, kamar ranar ya fara rungumeta, haka ya lallaɓata suka tafi ɗaya ɗakin sheƙe ayarsu, sai dai hankalinsa na kan ramma, kuma gaba ɗaya ya ji bai samu abun da ya samu a tattare da ‘yar ƙaramar baƙauyyiyar yarinyar ba.Duk yadda ya so mazewa, sai sa Nina ta fuskanci hankalinsa a ba a kanta yake ba da tayi magana sai ya ce mata ba shi da lafiya ne.***Har washegari, Nabila ba ta ci abinci ba, ta dai buɗe ƙofar cikin dare da zafi ya isheta, ta fara numfashi da ƙyar.Ta ɗaukko wayar Viper, ta din ga kallo, kamar shi ne a gabanta, ta rintse idanunta tana tuno kamanninsa, a zahiri suffarsa ta ban tsoro ce, amma a baɗini abun tausayi ne.Ƙarfe takwas na safe, yaran gidan na ta zuwa gaida Abba, sai da sauda ta shigo ta gaishe shi, ya ce “Sauda duba mini Arfa ko ta buɗe ƙofar, ki ce mata ina bata haƙuri idan laifi nayi mata, da ya sanya tun jiya ba ta neme ni ba, yau kuma ba ta zo ta gaishe ni ba” Sauda ta tashi, ranta a ɓace ta tsani yadda Abba yake sakata a shirgin Nabila ta girmeta gashi ba shiri suke yi ba, amma ayi ta zubar mata da girmanta.Ta je ta tura ƙofar ɗakin taga ta buɗe, taga Nabila a kwance a kan gado, ta kwanta a kan hannunta, ta murɗe jikinta.”Ke! Malama ki taso Abba yana kiranki” sai dai shiru Nabilan ba ta motsa ba.Walida ce ta shigo ɗakin tana faɗin ta ga dama ta buɗe ɗakin kenan, sai dai tana ganin irin kwanciyar da Nabila tayi ta ja ta tsaya.A fusace sauda ta tafi ta ɗala mata duka Walida ta ce “Yaya sauda kina ganin irin kwanciyar da tayi, da ƙyar idan ba iskokai za ta yi ba” da sauri Sauda ta ja da baya ta ce “Taɓ wallahi ba zata dake ni a banza ba” Nabila ta saka hannayenta, ta toshe kunnuwanta dan ta daina jin maganar su.Sauda ta koma ta gaya wa Abba, cewar Nabila iskokai ta tayar.Abba ya taso yana yi wa sauda faɗa, a kan cewa ya hana cewa Nabila tana da da iskokai, takura ce kawai ba ta so da ɓacin rai.Ya ƙarasa ɗakin yana kiran sunan Nabila.Ya ɗagota daga kwanciyar da ta yi, jikinta yayi wani irin mahaukacin zafi, har wani huci take yi.Idanunta sun kumbura sun yi suntum, ga wani irin ja da suka yi, ga wasu irin siraran jijiyoyi da suka kwanta a saman goshinta.Sai da Abba ya razana da yanayin da ya ganta, “Arfa, meyasame ki haka? Meyake yi miki ciwo”Ta buɗe baki za ta yi magana, amma bakin ya din ga karkarwa ta kasa furta komai, hawaye ya din ga bin gefen idonta.Ya kalli walida ya ce “Bani bedsheet a rufe mata jikinta” ta duba ta ɗaukko masa, ya rufe wa arfa jikinta, ya din ga tofa mata addu’a.Wani abu mai nauyi, ya tokare mata ƙirji, ya hana numfashinta fita yadda yakamata, a ƙalla Abba ya kai awanni biyu, yana yi mata addu’a yana tofa mata, sai bin sa take yi da ido, amma ta kasa magana, sai can wani irin nananuyan bacci ya ɗauke ta, dan ba ta yi bacci ba jiya gaba ɗaya.***Walid ne yake ta kokowa da Al’amin, a kan lallai sai ya fita ya kai kansa wurin ‘yan sanda, a sakar masa liti, shi a kama shi, amma kafin nan sai ya fara kashe Nabila.”Ita wannan da tayi maka abun da bai taka kara ya karya ba zaka kashe, ko kuma zaka fuskanci indabo da madaki ne ka bar maganar wannan ƙaramar alhakin?”.Viper ya ɗaga rinanun idanunsa jawur da su ya ce “Zuwa yaushe? Zuwa yaushe mutane za su daina cutuwa a dalilina? Ba zan sake gangancin da na yi a baya ba, dole a saki liti, in dai kai kaina zai saka a sake shi””Is a minus case, dole zai fita, amma bama buƙatar a sake kama ka, ka gane mana, dole mu shirya ɗaukar fansar ka”Viper ya sake kallon Walid ya ce “Sai na kashe yarinyar nan fa””Indabo yakamata ka kashe da Madaki, wani tunanin yakamata ka yi a kan wannan yarinyar ba wannan ba””Tarko aka yi mini da ita, ko ba ka gani?”Walid ya girgiza kai ya ce “Haryanzu bamu da tababcin hakan, amma ba ka da wani sharhi ko tunani a kanta?””Babu, idan na sake ganinta kuma sai dai wata ba ita ba” ya bashi amsa kai tsaye.”Shikenan, yanzu dai zan fita in ga me za ayi a sako mana liti”.Viper yayi shiru bai ce masa komai ba, sai da ya yinƙura zai tashi, Al’amin ya riƙe shi. Walid ya juyo ya kalleshi ya ce “Ina alƙawarin da ka yi mini?”Walid ya ce “Ina sane, haryanzu kayan ba su sauka bane ba, ka san yanzu hanyar akwai tsaro sosai ba irin na da bane ba””Bani wanda ka kwashe ka fita”Cikin damuwa walid ya ce “Wai dan mai zamani so ka ke yi sai ka haukace ne gaba ɗaya hankalinka zai kwanta, wannan uban ƙwayoyin da ka ke jibgaw kanka ba abun da suke yi maka, jikinka duk ya riga ya bujire, ka yi haƙuri mu bi a sannu””Mai laya…..Walid ya ce “Mai zamani””Ka yi mini abun da nake so, ai na riga na daɗe da gama haukacewa, ka bani idan na cigaba da zubawa na san za su yi mini”Walid ya girgiza kai ya ce “Da za su yi maka, da tuni sun yi, ka yi haƙuri ka bani lokaci”Al’amin ya waro masa idanunsa ya ce “Ka fara kaini bango, baku san fa me nake ji ba, bana bacci, ƙwaƙwalwata so take ta tarwatse, sonake komai ya shafe daga cikin kaina, ko da hakan yana nufin zan haukace””Fansar ta ka fa””Zan ɗauka” Walid ya yinƙura zai fice ya bar Al’amin, amma ya sake riƙe shi, Walid yana ƙoƙarin ƙwacewa, hakan ya ƙara tunzura Al’amin, ya fara ƙoƙarin shaƙe Walid.Babu yadda Walid ya iya, duk da yadda Al’amin yake zuba wa kansa kayan maye, amma yafi ƙarfin sa, ya dunƙule hannu, ya daki jijiyar wuyan Al’amin, ya silale ya faɗi ƙasa.Yayi sauri ya durƙusa a kansa, ya ga Al’amin yana ta ƙifta idanunsa, bai kai ga suman ba, jikinsa ya saki gaba ɗaya.Walid ya dafe kai yayi shiru, abubuwa na neman su ƙwace musu, gashi alamu sun fara nuna ƙwaƙwalwar Al’amin na nema ta fara taɓuwa.Ya dafa kafaɗar Al’amin ya ce “Ka ƙara bamu lokaci ɗan uwa, zamu kawo ƙarshen komai, da yardar Allah” ya tashi ya fice.***Abba da magajiya sai anty, su ne suka yi ta ɗawainiya da Nabila, har ta ɗan samun nutsuwa, take ta uban bacci, tana tsaka da baccin sumayya ta zo, dan jiya hankali a tashe ta kwana, ta jirata har ta gaji, taje can wurin aikinta an ba ta je ba, ta zo gida an ce ba ta zo ba, ga lambobinta ba sa shiga, ta din ga fargabar Allah ya sa ba su indabo ne suka yi mata wani abun ba, gashi suka din ga kiranta suna tambayarta ta gaya musu me suka tattauna da Nabila.Yanayin da ta ga Nabila, ya tsoratata, gaba ɗaya kamar ba ita ba, duk ta yi wani iri. Cikin ikon Allah ta farka daga nannauyan baccin da ya kwasheta, da sumayya ta fara tozali, cikin kulawa sumayya ta ce “Sannu” ta jinjina mata kai kawai.Duk shegen surutu irin na Nabila, sai bakin ya mutu, ta kasa cewa kowa uffan.Sai da suka kaɗaice, sannan sumayya ta ce “Nabila ki yi magana mana, meyafaru da ke? Kiran me ki ka yi mini kina so mu haɗu? Kuma na neme ki na rasa jiya, yau kuma na ganki a haka ko wani abun ne ya faru?”Nabila ta ƙura mata ido, yanzu ita ta ina za ta fara yi wa Sumayya bayani ma, wataƙila idan ta bata labarin abun da ya faru ma ƙaryata ta zata yi, ta ce mata ba ta da hankali, ta san babu lallai ta bata goyon baya, a kan abun da take niyyar yi. Ba wannan ba shi kansa Nasir idan ya dawo, ta ina za ta bi ta warware mugun ƙullin da tayi, muddin ta yarda aka kama Viper a sanadinta, ta zama azzaluma duk da ba ta ji ƙarashen labarin ba, amma yin hakan shiga hakkinsa ne.Sumayya duk yadda ta kaɗa ta raya, fafur Nabila taƙi cewa komai, hasali ma zancen zuci ta din ga yi taƙi kulata.Abba ya din ga yi wa Nabila faɗan yawo ba ɗankwali, jin kaɗe-kaɗe da kuma yawan kwalliya.Walida ta shigo da waya a hannunta, ta miƙawa Nabila ta ce “Gashi Yaya ne zai yi magana da ke”Nabila ta girgiza mata kai, ba zata karɓa ba.”Me zan ce masa to?”Sumayya ta karɓi wayar suka gaisa da Nasir ta ce “Yaya mutuniyar jikin ba daɗi, taƙi magana ma gaba ɗaya, ka yi haƙuri ko zuwa anjima mu gani idan zata yi”Ya ce “Shikenan, hanklina ne a tashe, ban ji ɗuriyarta ba ai, na sake kira anjima”. Suka yi sallama ta kashe wayar.***Kwanaki kusan uku ramma na fama da jikinta, kafin ta ɗan ji ƙwari, a kwanaki ukun nan, Abdul bai kulata ba, zai dai ba ta abinci ya bata magani, sai a kwana na uku da ya ga yi ƙwari, har tana salla.Tun da rana ta fara ganin take-takensa dan haka hanklinta ya ƙi kwanciya, da daddare ta kasa bacci sam, aikuwa kamar yadda ta yi tsammani, sai gashi ya shigo ɗakin, yana miƙa yan kallonta. Cikin hanzari ta tashi tsaye. Ya mayar da ƙofar ya rufe ya ce “Ina zaki ne?”Ta hau ja da baya, ya nufota gadan-gadan kawai ta ciro wuƙar yanka fruit, ta ce “Wallahi ka taɓani sai na caka maka, sai na kasheka azzalumi mara imani kawai”Ya ce “Ohh wow, in ajiyeki ina ciyar da ke, ki ɗauki wuƙa ki ce zaki kashe ni, ni da ki ka samu ban kashe ki ba? Dole na canza taku.Ya danƙota sai ga wuƙar a hannunta, amma ta kasa yi masa komai da ita, ba ta wuƙar yake yi ba, ya fara ƙoƙarin yi mata abun da ya saba, taƙi sakin wuƙar, garin kokowar ƙwatar kanta ya yanke shi da wuƙar hannunsa. Sakin wuƙar ta yi ta ce “Na shiga uku” ya tsaya yana kallonta, hannunsa na zubar da jini.Tayi sauri ta saka hannunta, ta danne wurin da yake ta zubar da jinin, ta ga hakan ba zai yi ba, ta kama rigar jikinta tana dannewa tana cewa “Ka yi haƙuri” ya ƙura mata ido, gaba ɗaya sai ta rikice.”Ni zaki kashe ko?””A’a ba kasheka zan yi ba, sonake kawai ka ji tsoro ka ƙyaleni, ka yi haƙuri” ya fizge hannunsa ya fice, ta samu wuri ta zauna hankalinta rabi a tashe, rabi kuma tana gode wa Allah da ya saka ya ƙyaleta.Nabila ta warware, sai dai gaba ɗaya walwalarta ta ragu sosai da sosai, ba ta iya bacci, tunaninta da lissafinta kawai yaya zata ɓullowa lamarin.Ta sake ɗaukko wayarsa tana jujjuyawa, ta tuna abun da Walid ya ce mata “Sai dai ki je shi ya ƙarasa miki”Tayi ajiyar zuciya ta ce “Dole zan je, zan neme shi, sai na ji ƙarshen labarin, for now dole na tsayar da aikin DSP, na kamo bakin zaren nan, dan gudun kar a haihu a ragaya.Ranar monday ta kunna wayarta, ta shirya ta ce wurin aiki zata tafi, ana ta zancen Nasir zai dawo, sai dai ko a jikinta, dan ba ta shi take yi ba, ta shirya ta fice.Da ƙafarta take ta tafiya, dan kar ta hau abun hawa tayi saurin zuwa wurin aiki, ba ta gama tunanin da take son yi ba, wataƙila ko za ta samu mafita a haka.Kamar an ce ta waiwaya, ta ga wata baƙar mota, na ta bin ta sannu a hankali, tun da ta fito titi kuma ta ga motar, ta basar ta cigaba da tafiya, bayan wasu mintuna ta ƙara waiwayawa ta ga motar still tana bin ta.Tsayawa tayi ta juya ta nufi motar, sai aka tsaya aka yi parking aka daina bin ta, glasses ɗin motar tint ne, dan haka ba ta ganin na ciki. Ta ƙarasa ta hau ƙwanƙwasa glass ɗin, amma ba a sauke ba.Ta gaji ta tari abun hawa, ta tafi.Ta shiga reception kenan, ta tarar da wasu matasan mata su biyu, a cikin tashin hankali.Ba ta damu ba ta wuce su, ta tafi office ɗin ta, ta ajiye kayanta ta sake fita harabar wurin, ta gansu a tsaye suna kuka.Har ta gota su ta dawo, ta kallesu ta ce “Lafiya kuwa?”Ɗayar ta ce mata “sannu”Nabila ta ce “Yauwwa meyafaru ne?””Dama babanmu aka yi wa sharri, an kai shi wurin ‘yan sanda ma, wai kotu za a kai shi, an ce mu ɗaukar masa lawya mai zaman kansa, mun ji ba zamu iya ba, abun da tsada sosai”Nabila ta ce “Sharrin me?””Gadi yake yi a wani gida, sai ɗan wan matar gidan ya yi wa mai aikinta fyaɗe ya gudu, su suka fara kaita asibiti, da shi mai wankin gidan, shi ne daga baya aka kama su, wai su ne suka yi mata”Nabila ta yi shiru tana nazarin maganar ta kalli ɗayar ta ce “Yayata kin tabatta, ba na shiga case ɗin mutumin da ba shi da gaskiya, kar na yi bincike na tarar da saɓanin abun da ku ka gaya mini””Wallahi ba ƙarya muka yi miki ba”Ta ce “Well, yanzu ina da tarin ayyuka a office ɗina, personally zan taimaka muku, ku zo gobe in Allah ya kaimu ƙarfe tara na safe, zamu je wurin mahaifin naku, na ga abun da zan iya yi a kai”Godiya suka din ga yi mata, tamkar za su durƙusa mata, yanayinsu kawai ya nuna suna fama da matsin rayuwa.Ta so haɗuwa da barrister Habib, amma bai shigo ba, ya tafi gudanar da wasu shari’oi dan haka ta zauna ta gudanar da nata ayyukan.Sha biyu na cika, ta ɗauki jakarta ta fita, kiran Nasir ya shigo wayarta, kamar ta share, sai ta ɗaga tayi sallama.”Barrister, kina office ne na biyo?””Ka dawo kenan?”Ya ce “Eh ina cikin kano”Nabila ta ce “No, zan yi wata shri’a ne, ka je gida ka huta na kusa dawowa nima” ba ta jira mai zai ce ba, ta saka wayar a Flight mode, ta tari abun hawa, ta nufi unguwar da Viper yake. Ayshercool 08081012143
