Karfe A Wuta Chapter 30 By Ayshercool
A ƙalla ya kai awa ɗaya da mintuna talatin, yana tafiya da ƙafa, bayansa ɗauke da jauhar, wani wurin idan da mutane, ayi ta kallonsa, tun da sauran sahun mutane, har ya zama saura ɗai-ɗai.A haka ya isa gida, ya buɗe gidan, ya shiga da ita ɗakinta ya kwantar da ita, zazzaɓin jikinta ya sauka, sai dai gaba ɗaya jikin nata ya saki.Ya kunna fitilar wayarsa yana haskata.Surutai take yi, wanda tun suna hanya take yi, sai dai ba ya gane me take faɗa sai yanzu.”Allah ka shirya mini mijina, Allah ka sa ya daina abun da yake yi. Ya Allah, Allah ka sa ya shiryu.Allah na san ba zaka kunyata ni ba, Allahumma inni as’alukal jannata wa na uzubika mina narr. Rabbana hablana min azwajina, wa zuriyyatuna ƙurattu a’ayunun waja’alna lil muttaƙina imama. Rabbigfir ummi wa abi, warahamhuma, kama rabba ya ni sagira” ta ƙarasa tana shafar fuskarta, da tafukan hannayenta, hakan ya tabattar masa da addu’aoin ta ne na salla, take maimaitawa.Ya lulluɓeta, ya tashi ya sake fita, sai dai abubuwa daban-daban suna ta cigaba da kai komo a zuciyarsa, ya ji ƙwarai yana son sanin wacece yake zaune da ita a matsayin mata, shi dai ya san ba shi da nagartar da uban kirki zai bashi auren ‘ya, idan ba da wata a ƙasa ba.Cikin gari ya sake ninkawa ya tafi, bai zarce ko ina ba sai gidansu, ya tarar har sun rufe ƙofa.Bugawa ya fara yi iya ƙarfinsa, Abba ya zo ya buɗe, yana ganin Al’amin ya ruga da gudu ya koma, saboda yana bala’in tsoronsa.Ba tare da ya kula kowa ba, ya shiga kitchen, ya dudduba babu komai sun cinye abincin.Rahila ta fito, ta ce “Kai Aminu lafiya ka zo mana a wannan daren? Yaushe aka sako ka?””Shahida” ya ƙwala mata kira, kasancewar ya hangota a falo.Cikin hanzari, ta fito ta ce “Gani yaya”Yayi mata alama ta shiga kitchen, ta shiga ya bi bayanta, ya ce “Dafa mini shayi cikin flask ɗin nan” yayi maganar yana nuna mata flask ɗin shayinsu, family size.”Wai Aminu me ka ke yi haka, dan me zaka sakata girki a wannan tsohon daren?”Bai kulata ba, ya kwaso ƙwai ya zube mata ya ce “Ki soya mini wannan ma”.Rahila ta koma bedroom ta taso Abbu ta ce “Ta so, ga ɗanka can ya zo a wannan tsohon daren, kar ya yi mana ɓarna”.Abbu ya taso ya fito, dan ya fara bacci ma.Ya fito yana faɗin “Kai Al’amin lafiya, ka zo mana a daren nan? Ina matar taka ina gidan naka?”.Shahida ta ce “Abbu ka koma ka kwanta, ba wani abu, girki kawai ya ce na yi masa”.”Kuma a daren nan, ina matar ta sa?”.Abbu yana ta ɓaɓatu, Amma Al’amin bai kula shi ba, sai ma ɗaukko ledar viva, ya buɗe fridge ya kwashe lemon ɓawo ya zuba a ciki, kankana da sauran abubuwan da ya gani a ciki har da su madarar ruwa.”Ka yi masa magana, wannan kayan da yake ɗiba ina zai kai su?”.Al’amin ya kalli rahila ya ce “Da kuka aura mini ‘yar mutane, ai kun san bani da abun yi, in bari yunwa ta kasheta ko na fara satar kayan mutane ne na kula da ita? Ba ta da lafiya dan haka dole na fito na nemi abun da zan kai mata ta ci”.”Da can kai da me ka ke riƙe kanka, ba sai ka nema ba, kuma saboda lalacewa da abun kunya, daga gidanku ne za a ciyar maka da mata? Al’amin ya waiwayo a fusace, ya nunata da yatsa ya ce “Ki kiyayi lokacin da haƙurina zai ƙare a kanki”Shahida ta ce “Yaya gashi na gama, ka ga akwai su maggi ma a nan, tayi maganar tana buɗe drower tana ɗaukkowa. Ta buɗe wata ta ɗebo su taliya da macaroni ta ce “Ka haɗa da su”ya girgiza kai ya ce “Ban da wannan, wannan sun isa”Ta sake cewa “Yaushe zan zo gidanka, ina son kan na koma school na zo muku ziyara, tun da ba ma nan aka yi bikinka, samu zo mu dubata”A taƙaice ya ce “Sai kin zo”.Ta ce “Wannan ɗin sun isa, ko kuna buƙatar wani abun?”Ya ce “A’a, sun isa. zo ki rufe muku gidan” ya ƙarasa maganar yana kwasar kayan, ya nufi hanyar ficewa.”Al’amin” Abbu ya kira sunansa, ya tsya cak bai waiwayo ba.”A tunanin auren nan da aka yi maka nutsuwa zaka yi, ka daina wasu abubuwan da ka ke aikatawa, amma abu ya ci tura, ka sanya ‘yar mutane a tasku da tashin hankali, meya kai ka ta’amalli da hodar iblis?.Lokaci yayi da yakamata ka daina wasu abubuwan, ko dan kare mutuncinka da na iyalinka. Ko dan ka ga ka sameta a ɓagas ka ke nema ka wahalar da rayuwarta””Kaga Abbu dan Allah ka daina jan maganar nan, ya tafi kawai su je can su ƙarata, dama ai ba ji take ba ita ma, daidai da ita ne”Wani abu mai nauyi ya haɗiye, ya saka kai ya fice, ba tare da ya sake cewa uffan ba.Bayan ya tafi, Shaida ta ce “Mama dan Allah ki daina tayar da hankalinki a kan yaya, idan yana wannan abubuwan ki zuba masa ido, tun da ba kullum yake zuwa ya yi ba. Abu ɗaya kawai yake buƙata yayi iko da kayan mahaifinsa a matsayin sa na ɗa, kamar yadda muke yi, kin san fa ke da shi, ba kwa jituwa ki din ga kawar da kai a wasu abubuwan da yake yi, yana ɗaga miki ƙafa fa kar yayi miki wata illar”.Abbu ajiyar zuciya ya yi, maganganun shahida gaskiya ne, amma shi babban takaicin sa, Al’amin ba ɗan da za a haɗu a rufawa kai asiri bane ba, miyagun halayensa ya sanya ba ya son ya zo ko in da yake. Gaba ɗaya auren da aka yi masa bai sanya ya nutsu ba, kodayeke da sauƙi tun da ya san ya fito ya nemi abun da zai bawa ‘yar mutane.Ya koma ɗakinsa, Rahila ta bi bayansa, Amira ta ce “Ohh yau ni nake ganin tsiya, yanzu fa sai a ce ciki ne da ita ko?”Shahida ta ce “Ba abun mamaki bane””Taɓ, a wannan muzuran da tashin hankalin nass har ta ɗau ciki, iko sai Allah”Al’amin ya sake ninkawa, ya koma gida ya shiga ɗakinta, ya tarar tana ta baccinta, kamar ya tashe ta, sai ya fasa, ya koma ɗakinsa ya kwanta.Bai farka ba, sai wajen tara na safe, a gaggauce ya yi sallar asuba, ya fito falo, ba ta nan ya shiga ɗakinta, tana kwance ta takure wuri ɗaya.”Kin tashi?” Ta jinjina masa kai almar eh.”To taso ki karya ki sha magani”Ta ce “To, bari na yi wanka nayi brush”A hankali ta lallaɓa jikinta, ta shiga ta yi wanka, ta canza kaya ta fito falon.Ba tare da ta kalleshi ba ta ce “Ina kwana?””Lafiya ƙalau, bari na kawo miki abinci”Kitchen ya je ya ɗaukko kofi, da shayin da ya zo da shi a flsk, da uban ƙwan da ya saka shahida ta soya masa.Ya ajiye mata a kausashe ya ce “Gashi nan ki karya, ki sha magungunan da suka baki. Saura ki ƙi ci wani ciwon ya kuma kama ki”Ta na fara ci ta ji ta ƙoshi, amai ma take ji.”Wai ba kya so ne ki ke jagwalgwalawa?”Ta ce “Na ƙoshi ne””A ɗan abun da ki ka ci ne har kin ƙoshi” ya taɓe baki, ya miƙa mata magungunan ta karɓa ta sha.Ya bata wayarsa ya ce “Saka mini lambarki, idan da wani abuk sai ki kira ni fita zan yi”Kallonsa tayi da mamakin yana sane ko wulaƙanci ne, ya sanya yake tambayarta lambar waya.”Bani da waya” ta amsa kanta a ƙasa.Ya mayar da wayarsa aljihunsa ya ce “Shikenan, maganar da nayi miki, ki yi tunani a kai, a ɓangarena ni ina ganin hakan shi ne mafita kawai, amma ki yi tunani abun da ki ka yanke, ki sanar da ni”.Dummm ƙirjinta ya buga, kenan haryanzu yana kan bakansa? Ba ta ce masa uffan ba, ya fice.Rasa abun yi tayi, duk da ba ta da tsarki, tayi alwala ta zauna ta kalli gabas, tayi ta addu’a a kan lamarin rayuwarta.Can wurin su Walid ya tafi, in da suke zama su yi shaye-shaye, su naɗa wiwi.Walid ya kalli Al’amin ya ce “Maza lafiya kuwa? Yanayinka ya nuna kamar akwai damuwa”.Banza ya yi wa walid, dan haka shi ma ya share shi, ya cigaba da aikin gabansa.Sai kuma can ya ce “Mai laya””Na kiyayi mai zamani, ya aka yi?””Dama yara matasa suna hawan jini ne, ba sai tsofaffi ba?”Ya ce “Eh to, na ji an ce akwai wanda ake haifar su da shi ma, amma hawan jini a matasa, maybe damuwa ce ko gado”.Ya jinjina kai.Liti ya ce “Maza ko kai hawan jinin ke damu? Kana da ‘yar madara, ai ba zaka yi hawan jini ba”Tsuke fuska ya yi, jin liti ya kira jauhar da ‘yar madara.Gidansu Al’amin, Abbu ya shirya zai fita ya kalli rahila ya ce “Yakamta idan an janye yajin aikin nan, ku je ku duba matar yaron nan”Rahila ta ce “Taɓ haka kurum, su dai yaran su je ni in je ya illata ni a banza? Su dai su je”Abbu ya ciro kuɗi a aljihunsa ya ce “Amira, ga kuɗi nan ku hau mota, ga dubu biyar ku saya mata fruit ku kai mata, na ji an ce zuwa jibi in Allah ya kaimu, za a janye yajin aikin, sai ku je ku duba jikin nata, kafin na samu na je nima”Ta amsa da to Abbu. Sai dai bayan fitarsa Amira ta ce “Na samu na saka data, dan ba za ta ci 5k ɗin nan ba”.Shahida ta ce “Wallahi kuwa da sai na gaya masa, ai ba haka ake yi ba” haka suka cigaba da faɗan su na sakonni.Jikinta ya ɗan yi sauƙi, sai dai ba ta daina ciwon kai ba, ga damuwar abun da Al’amin ya sake nanata mata, kenan yana nan a kan bakansa na rabuwa da ita.Kusan kwanaki biyu, ba ta bari su zauna wuri ɗaya, saboda kar ya sake tayar mata da maganar.Ya gama karyawa, yana kallonta tana ta shirin dutsenta, karyawar ma ba ta yi ba, kamar yayi magana kawai ya shareta, ya tashi ya fita.Su halimatu suka shigo, suka tayata aikace-aikace, sannan suka koma gidansu.Tana falo tana karatunta tana shirin dutse, aka yi sallama a tsakar gida.Ta amsa tare da bayar da izinin a shigo, ‘yan mata ne da zasu girme mata su biyu, suka shigo falon.Jauhar ta faɗaɗa fara’arta tayi musu maraba.Suka gaisa da ɗayar, ɗayar kuwa sai hura hanci take yi.Shahida ta ce “Kin gane mu kuwa?”Jauhar ta ce “Na gane wannan ranar da na je gidan, mun haɗu da ita ai, ƙannensa ne ko?”Shahida tayi murmushi ta ce “Kin canka””Sannunku da zuwa, baku taɓa zuwar mana ko sau ɗaya ba”Shahida ta ce “Ai da yake ba ma zama a gari saboda school, shekaranjiya ya je gida ya ce baki da lafiya, Abbu ya ce lallai mu zo duba ki kafin ya zo shi ma. Ya jikin?””Jiki Alhamdilillah na warware””To Allah ya ƙara afuwa, ko mu ce Allah ya raba lafiya, ya kawo mana baby lafiya” Shahida tayi maganar tana murmushi.Buɗe baki Jauhar tayi ta tashi da sauri ta ce “Bari na kawo muku ruwa”Ta kawo musu ruwa, lokacin ta hura gawayi, ta ɗora girki.”Wancan ba tea flask ɗin mu bane?” Amira tayi maganar tana nuna flask ɗin.Jauhar ta ce “Ina ga naku ne, shi ne ya zo da shi, ina ta so nayi masa maganar na waye, yanayin jikina ya hana, amma tun da Allah ya kawo ku shikenan”.Suka cigaba da hira da shahida, yayin da Amira ke ta harare-harare itakaɗai.Shahida ta ce “Yaya muka ji da abun da ya faru da yaya na rufe shi da aka yi, Ubangiji Allah ya tsare gaba”Jauhar ta ce “Amin ya Allah, sharri ne ma aka yi masa, amma duk da haka a tayamu da addu’a dan Allah, duk zai daina wataran sai labari. Ina mama?””Haka ne, ana nan ana yi, mama tana nan ƙalau, tana gaishe ki”Shahida ta sake cewa “Nikam wai dan Allah ya aka yi kuka haɗu da yaya ku ka yi aure, har ya taka ya je gida, sha biyu fa ta wuce, ya ce na yi masa girki matarsa ce ba lafiya na ce wace ‘yar baiwa ce haka? Kin san a rayuwarsa ta duniya mata ba sa gabansa mu kanmu yadda ki ka san dodo haka yake a wurinmu”.Jauhar za ta yi magana, Amira ta ce “Kin jiki da wata magana shahida, a ina kuwa za su haɗu?, Tallarta fa aka kawo masa ba ta ji, ta fanɗare a gida an rasa yadda za ayi da ita, aka haɗa su, aka jogana masa, da yake shi ma ba sanin ciwon kansa yayi ba, ko ke baki san zancen ba? Kin zauna kina ta zuba ni ina da wurin zuwa” ta ƙarasa maganar tana tashi tsaye ta ɗauki jakarta tayi waje.Gaba ɗaya jauhar ta yi sak, jikinta yayi shock, yayi wani irin sanyi da mamakin maganganun Amira.Cikin dirircewa shahida ta ce “Dan Allah ki yi haƙuri, wallahi ƙarya take yi, ina zuwa” ta lallaɓa ta ɗauki takalmanta cikin tsananin jin kunya ta bi bayan Amira.Biri yayi kama da mutum, duba da yadda aka yi auren cikin gaggawa ko wata guda ba a rufa ba, ashe abun da aka gaya musu kenan a kanta?A take ta ji ciwon kanta ya tsananta, ta fara tunanin wace irin muguwar ƙiyayya ce tsakaninta da ‘yan gidansu har haka.Gidan su jauhar, Hafsa ta shigo daga zance, ta zauna a tsakar gida, Yaya saifu ya shigo, ya kalleta ya ce “Daga ina ki ke?””Zance” ta bashi amsa kai tsaye.”Wurin wa?” Tayi shiru tana kallonsa.Ya ce “Wallahi kun yi asara, yanzu dama Saboda hafsa ta auri mutumin nan, da yake son jauhar shiyasa ku ka aurar da ita ga mutumin banza, wallahi ba ku kyautawa kanku ba, kuma da ikon Allah sai Allah ya saka mata”.Mama ta ce “Saifu maganar me ka ke yi ne ban fahimta ba?” Ji yayi kamar ya gayawa mama baƙar magana, sa’arta ɗaya mahaifiyarsa ce, babu yadda zai yi da ita, kawai ya fice.Mama ta ce “Zakiyya, da gaske mutumin nan ne yake zuwa wurin Hafsa?”Ta haɗa rai ta ce “Ni ma ban san zancen ba sai yanzu”Mama ta ce “To meye abun ɓoyewa ban da abunki, ai abun farinciki ne a gare mu baki ɗaya. Dama ai jauhar ɗin ce ba ma son ya aura, wallahi nayi murna haƙanmu t cimma ruwa”.Sai kuma ta ɗan saki ranta ta ce “Wallahi ina ta son na gaya miki, abubuwa ne sun sha mini kai, kuma ba gama daidaitawa suka yi ba””Ai bakomai, Allah ya tabattar mana da alkhairi” suka gama maganar ta shiga ɗakinta, ta jinjina kai ta ce “Hmm zakiyya kenan, baki da wayo da ni ki ke zancen, duk wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi, zaki gane kuskurenki”.Yau tun la’asar ya dawo, kwana biyu ba ya yin dare, saboda rashin lafiyarta sai dai fa ba zai ce mata sannu ba.Ya kasa gane kan yanayinta, ta zuba masa abinci, ta koma gefe ta yi shiru.Ya gama ya tashi ya tafi ɗaki, zai ɗan kwanta ya huta, kasa jurewa ta yi ta tashi ta bi bayansa.Ta ssme shi, yana ta watso kayan wardrobe ɗin sa da ta gyara da ƙyar.”Master””Yeah” ya amsa ba tare da ya kalleta ba.”Ƙanneka sun zo ɗazu baka nan””Ok” kawai ya ce, amma ƙasan zuciyarsa mamaki yake yi, tun da ƙannensa ta ce, da ƙanwa ta ce ya san shahida ce kawai.”Dan Allah abu nake son tambayarka, na san kai ba ma’abocin ƙarya bane ba, na san ba zaka fara a wannan karon ba” bai amsa ba, dama ba tayi tsammanin hakan ba, ta ce “Da gaske tallata aka kawo maka, wai ba na ji na fanɗarewa iyayena shi ne aka aura maka ni?”Ya ɗaga rigar hannunsa yana kallo kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce “Eh, haka na ji”Cikin rauni ta ce “Kuma ka yarda?””Kusan haka, dan na san ba yadda za ayi a aureni haka kurum babu dalili, a abun da bai wuce sati biyu ba”Yayi maganar yana ajiye rigar, ya ɗauki wata, sautin da tayi na ƙwacewar kuka ne, ya sanya shi ɗagowa a tsorace yana kallonta.Cikin kuka ta ce “Wallahi ni ba lalatacciya ba ce, ban fanɗarewa iyayena ba, dama kallon da ka ke yi mini kenan, kallon da ‘yan uwanka da sauran mutane suke yi mini kenan” da ƙyar maganarta take fita, saboda numfashinta da ya fara sama.Ya ƙaraso gabanta ya ce “Wai ke ba kya gajiya da kuka ne? Komai kuka?”Hannunta take fifitawa kusa da hancinta, alamar numfashi yana bata wahala, da sauri ya ɗauketa ya fita da ita tsakar gida, ta lumshe idonta hawaye na bin gefen fuskarta, sai dai ƙirjinta sai ɗagawa yake yi yana sauka, alamar numfashin da ƙyar take yi.”Ko mu koma asibiti? dama sati ɗaya suka bamu mu koma”Ta girgiza masa kai.”Ba zaki daina kukan ba?” Maimakon ta daina, sai ma wata sheshsheƙa da ta zo mata, ga numfashinta yayi nauyi.Ya ciro wayarsa a aljihun wandonsa, ya kira liti.”Maza ya ne?”Viper ya ce “Kana ina?”.”Na shiga area raba kaya”.”Samo adaidaita sahu, ka zo gidana zan mayar da ‘yar madara asibiti””An gama mazaje”Zai ajiye wayar, ta fara vibrating, ya ɗaga bai yi magana ba.”Honorable ya dawo, akwai taron gaggawa da zai yi, yana son ganinka””Na ji””Dan Allah kar ka ɓata lokaci sosai, ka san zaɓe yana ƙara gabatowa”Ras jauhar ta gane muryar waye, muryar P.A ce, a take ta jinjina rashin kunya irin na ɗan siyasa.”Dan Allah kar ka je, idan ka tafi mutuwa zan yi””Allah ya jiƙanki”A sanyaye ta ce “Amin, amma dan Allah ko na mutu kar ka je ba na son ka din ga zuwa wurin ‘yan siyasa””Ki yi mini shiru, idan ba haka ba zan tashi na bar ki””Yi haƙuri” ta faɗa tana haki.A hankali take iya takawa, saboda numfashinta, ya sakata a napep ɗin da liti ya zo da ita, sannan ya shiga, liti ya zauna a gefe suka tafi Asibiti.File ɗin ta aka kai wa likita, shi da ita suka shiga, liti kuma yana can waje.Likita ya ce “Ka ƙi yadda ayi mata gwajin ciki, gashi tana ta fama da an duba dai”Ya ce “To duba”Jauhar ta ce “Ni bani da komai”.”Shikenan, ki na da athma ne dama, wannan hakin da ki ke yi?” Ta jinjina masa kai ta ce “A’a allergy ne, shi ma kuma tun ina yarinya ne”Al’amin ya kalleta, likitan ya sake cewa “Akwai magani da ki ke sha ne? Ai kusan duk abu ɗaya ne, allergy ɗin da athma”Ta girgiza kai ta ce “A’a ai na daɗe ba na shan magani, addu’a nayi ta yi, ya daina tashi, tun ina ƙarama sosai ban kum jin alamun sa ba”Likitan yayi murmushi ya ce “Masha Allah, ka ga ‘yar baiwa, to a din ga sakamu a addu’ar mu ma, amma dai yanzu zan rubuta miki magani, sai ki kiyayi hayaƙi, ko kin shaƙi wani abun ne?”Ta ce “A’a kuka na yi kawai na ji na kasa numfashi sosai”Likitan ya jinjina kai, ya ce “Bari na duba bp naki na gani”.Shi dai gogan bai ce komai ba, likitan ya duba bp ɗin ta sannan ya ce “Zahra kina shan magungunan da na baki kuwa?””Ta jinjina kai alamar eh”.”A iyayenki akwai mai hawan jini?”Ta ce “A’a”Ya kalli Al’amin ya kalli jauhar ya ce “Akwai abun da yake damunki ko?” Tayi yaƙe ta girgiza kai.”Zahra, ita rayuwar duniya haƙuri ake yi. Malam ka zauna da matarka ku tattauna idan a cikin aurenku matsalar take, a magance ta, idan ba haka ba, hawan jinin nan zai iya taɓa mata zuciya, idan wani abu ka ke yi mata da ba ta jin daɗin sa, ku tattauna dan Allah ku fahimci juna, amma tayi ƙanƙanta da wannan ciwon””Zahra” likita ya kuma kiran sunanta, kamar yadda ya gani a jikin file.”Idan kun je gida, ki zauna da mijinki, idan damuwa ce da ke, ki gaya masa, ki cire koma menene a ranki, mijinki da kuma al’umma baki ɗaya muna buƙatar ki a raye” kawai ta sunkuyar da kai sai kuka.Al’amin ya ce “Rubuta mana magungunan kawai mu tafi”Ya rubuta maganin, ya bawa Al’amin yana kallon jauhar cikin tausayawa.Al’amin ya kalleta ya ce “Mu tafi? Ko yau ma goyakin zan yi?”A hankali ta tashi tsaye, ya ce “Kin daina hakin?”Ta ce “Ya ragu”Ya saka hannunsa ya riƙe nata, suna tafe a hankali har suka fito wajen asibitin in da pharmacy yake, ya saya mata maganin suka hau napep ɗin da ya kawo su zuwa gida.Shi dai bai iya rarrashi ba, bai ma san ta ina zai fara ba, amma gaba ɗaya yanayin da jauhar take ciki, bai yi masa daɗi ba, ya san fiye da rabin damuwar ta shi ne sila, ya ce su rabu kuma ta cigaba da kuka.Tana kwance a kan kujera, tayi lamo, shi kuma yana zaune a ƙasa, yana kaɗa ƙafa.”Master””Mmm””Kana ta ɗawainiyar asibiti da ni, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, ya ƙara arziki””Amin”Ta sake cewa “Master”Ya ɗago yana kallonta. “Dan Allah da gaske kallon mara ji wadda ta fanɗarewa iyayenta ka ke yi mini?””Haka aka ce mini ai”Ta ce “Aishikenan, shiyasa ka ke so ka sake ni?”.Ya ce “A’a kina takura mini ne kawai, kin isheni yanzu ina zaman zamana ba zan fita ba, sai dai na zauna kula da ke”Ta ce “To ka yi haƙuri, dan Allah kar ka fita yanzu, ji nake kamar kana fita zan mutu” idan tayi zancen mutuwar nan, gabansa faɗuwa yake yi, amma ya maze ya ce “To zan hanaki mutuwa ne?”.”A’a, amma dan Allah ka daina yi mini kallon mutuniyar banza, dan Allah ka gaya wa ‘yan gidanku, aje ayi bincike ma a kaina, wallahi ba mutuniyar banza ce ni ba” ɗago ido yayi yana kallonta, kenan zuwansu ne suka gaya mata wannan maganar, yayi shiru ya cigaba da latsa wayarsa.”Master”” ‘yar madara” ya amsa bai kalleta ba.Likita ya ce “Ka daina yi mini abun da na so, ka tambaye ni abun da nake so ka daina yi mini”Ya ce “Tom” ɗan murmushi ta yi, yau tayi sa’a ana amsa mata ma.”Yaushe zaka sake nin?”Ya yinƙura ya tashi ya ce “Na fasa yanzu, sai an kwana biyu, idan aka yi yanzu ina ga warewa zaki yi”.Wata irin ajiyar zuciya ta sauke, ya shiga ɗakinsa.Cikin ikon Allah, washegari ta tashi jikinta da sauƙi, sai dai damuwar cewar ita fanɗararriya ce, ta kasa barinta.A tsakar gida ya taso, ya tarar da ita, tana aiki.”Ina kwana””Kin warke ne?”Ta girgiza kai ta ce “A’a, bayan ba ka zauna mun yi maganar da likita ya ce ba””Akwai abinci ne?”Ta ce “Eh shinkafa na dafa amma akwai sauran buredi in dafa tea”Ya ce “Zubo mini, ke ki sha tea ɗin”Ta zubo abincin ta kawo masa, ya kalleta fuskarta duk ta faɗa.”Amma yau ba zaka fita ba ko? Ka zauna ka kula da ni”Murmushi ya yi da gefen bakinsa, ta sake cewa “Idan ka gama cin abincin zan gaya maka abubuwan da nake son ka daina yi mini, ko sannu baka yi mini bama”.Tayi ta zuba, amma yayi gum.Wayarsa da take ringing ya ɗaga ya ce “Ina sane zan zo yanzu”Ta haɗe rai ta ce “Amma ba fita zaka yi ba ko?”Ya ce “Fita zan yi””Ni dan Allah ka zauna ka kula da ni” shagwaɓa da rikici kawai take yi masa tsakanin jiya da yau, kamar yau an cire mata tsoron sa.Ta tashi ta ɗauki kwanukanta, ta tafi kitchen cike da takaici. Ko ba zai kulata ba, tana son ganinsa a gida.Sosai ta ji ranta ya yi mugun ɓaci fitar da zai yi, ɗan tattalin da aka yi mata jiya zuwa yau yayi mata daɗi, duk da ana yi ana haɗe mata rai.Tana cikin ƙunƙuni, ya fito da sauri hannunsa da wayarsa a kunnensa, hannunsa ɗaya da makamin da yake kira da iraƙi.Ya ce “Gani nan, ka duba bayan nan, russiata da sweazland suna nan, ka ɗaukar mini su, kar ku bari su motsa, gani nan zuwa” hannunsa ɗaya yana soke makaminsa iraƙi a cikin ƙugunsa.Ya ce “Fitar gaggawa ta kama ni, idan nayi dare ban dawo ba, ki rufe ƙofa, duk wanda ya buga kar ki buɗe, idan na dawo na hauro”Banza tayi masa, ta cigaba da yanka albasarta.”Ke ba magana nake yi miki ba?” Shiru ta sake yi masa.Ƙoƙarin leƙawa yake yi, ya ga ko lafiya.Kawai ya ga ta jefo masa murfin tukunya, a zatonsa ko ba ta san me tayi ba, kawai ya ga ta sake jefo masa rariya.Saroro ya tsaya cikin mamaki, ta cigaba da zaro kwanuka tana jefa masa tana kuka, bai ƙara tsinkewa da lamarin ba, sai da suka haɗa ido ta jefo masa ludayin hannunta a ƙirji. Ayshercool 08081012143
