Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 19 By Ayshercool

Cike da ƙwarin gwiwa, zakiyya ta tafi gida, tare da hasaso daular da za su shiga, idan hafsa ta auri Alhaji mu’azzam.Al’amin kuwa yana zaune ya miƙe ƙafarsa, da ta sha bandeji, hannun sa ɗaya riƙe da kofin shayi yana sha a hankali.Walid ya miƙa masa buredi ya ce “Wai yaya aka yi har yaran nan suka samu suka sareka ne? Ni fa haryanzu mamaki nake yi”Al’amin ya ce “Liti suka rufarwa da sara, shi na je karɓowa, saboda sun ga suna da yawa, shi ne nima suka yi tunanin za su yi mini taron dangi” yayi wani irin murmushi yana kallon walid.”Murmushin me ka ke yi kuma?”Ya ajiye kofin ya ce”swizalan ɗina ta sha jini sosai, wannan yankanma, ban lura yaron ya taho ba ne, yadda nake ji na anya ba wasan dambe zan fara ba walid. Idan na kwana biyu ban motsa ba, idan na tashi motsawar ba na iya riƙe kaina fa”.Walid shi ma yayi murmushi ya ce “Ai ƙarfi ya yi maka yawa aminu, ka shiga dambe abun ba zai yi mana kyau ba, daga karate zuwa dambe, amma da sauƙi jikin ai ko?”Ya kalli ƙafar ya ce “Alhamdilillah, da sauƙi sosai, jibi za ayi aikin honorable, zai je campaign fa”Walid ya ɗan tsuke fuska ya ce “Akwai hatsari fa a aikin nan”.”Ai ban ce wani ya tayani ba, nikaɗai zan yi abuna”Walid ya girgiza kai ya ce “Sorry, ba zaka yi kai kaɗai ba, amma da rauni a jikinka, ba ka warke ba”.”Ba ruwanka da ciwona, zan yi abuna a haka” walid ya girgiza kai, dan ya san ko me zai ce, bai isa ya hana Al’amin abun da yayi niyya ba.***Kamar zakiyya za ta tashi sama dan sauri ta ƙarasa gida, saboda rahila na bata shawarar nan, ta ji shawarar ta kama zuciyarta, kuma taga hakan ne kawai mafita, ayi ayi jauhar ta bar gidan kafin Allhaji mu’azzam ya dawo, wataƙila ita ke tsokanewa samarin kirkin ido, ba sa ganin nasu ƴaƴan sai ita.Ko da ta koma gida a can ta tarar da mama, ita har ta dawo tuni.Ta ja ta ɗakinta, ta ce “Na samo mafita fa, amma ban sani ba ko zata yi miki?”Cikin zaƙuwa mama “Wace mafitar ce, ina jinki””Me zai hana mu san duk mai yiwuwa, a aurar da jauhar, kafin Alhaji mu’azzam ya dawo, tun da dama sai ya dawo, za a tsayar da lokacin bikin”.Mama ta ce “To wa za a aurawa kafin ya dawo ɗin?”.Anty ta ce “Ba zai gagara ba, sai dai shawo kan Alhaji ne aiki””Wane irin aiki kuma? Babu wani aiki, ni a wurina ba aiki bane ba, wa ki ke gani yakamata ta aura”.Zakiyya ta muskuta ta ce “Kin san dai muka bari ta auri wani mai danshi, daga ni har ke babu wanda za ta saurara, tun da bamu muka haifeta ba”.Mama ta ce “Na sani””To, kin san yaron nan da yayi suna a ƙofa, mai dogon zamani?””Eh ina jin sunansa sosai””To mariƙiyarsa, ƙawata ce tare muka yi boarding ai rahila shehu, kwana biyu bamu haɗu ba, kwatsam na je ƙofar na’isa na ga ɗan ta, ya rakani har gidan, to ita ma haka take fama da shi, ta rasa sukuni, kullum cikin tashin hankali take, neman maraba take da shi, uban ya kore shi, amma yaƙi barin gidan, kin ga idan aka aura mata shi, mun huta, a fake da fyaɗe aka yi mata, kuma dai ga tambarin da ki ka yi uwarta na maita, kawai dai ki lallaɓa maganar, kin san yadda zaki yi dai sabgar nan ta yiwu, wallahi muddin ba ta bar gidan nan ba, bana tunanin za a din ga kula namu, kuma wallahi ta auri mai kuɗi, kashinmu ya bushe, ai kin san riƙon da muka yi mata”.Mama tayi ajiyar zuciya ta ce “Maganarki duka gaskiya ne, kar ki damu, wannan shawarar ta yi, kuma na aminta da ita, yadda muka kwashi baƙincikin uwatta, ita ma ba zata ji daɗi ba. Duk da wasu lokutan tana bani tausayi tana da biyayya, amma idan ba haka ba, namu ba zasu auru ga irin wanda muke so ba, ki gayawa ƙawartaki azo a nema masa aurenta, zan ji da komai”Anty ta washe baki ta ce “Alhamdilillah, magana ta ƙare”.Jauhar kuwa, ba ta san me ake  ƙulla mata ba, ita lissafinta yadda za ta mayar da jarinta, dan tun da ta farka a asibiti, da ta dawo gida sai jakarta babu kuɗin cinikinta, dan ma mai shirin dutse ta yafe mata.Duk yadda take jin nauyin yin roƙo, haka ta cire kunya, ta tambayi yaya saifu ya taimaka mata da jari, ta cigaba da sana’arta, kuma cikin ikon Allah ya bata, saboda ta hannun daman sa ce sosai da sosai, aiki duk yawansa duk wahalarsa babu ƙyuya take yi masa, gyaran ɗaki, wanki guga idan baya nan tayi girki, ta zuba ta kai masa ɗakinsa, idan ya gama ci ya bar kwanukan a ɗakin, ta kwaso ta gyara masa, dan haka baya jin ƙyashin kyautata mata sam.***Abbu yana daga kwance ya kammala azkar, ya juya zai yi bacci, rahila ta shigo ɗakin, ta nemi wuri ta zauna a kan gadon ta ce “Tun da idonka biyu tashi mu yi magana”Ya juyo ya ce “Ina jinki””Magana ce mai muhimmanci, a kan Aminu”.”Aminu dai Aminu dai, me kuma ya faru wannan karon?””Menene ma bai faru ba, tun da an mutu an bar mini jaraba da masifa, kullum hankalina a tashe, nan aka zo ana bayar da labari, sun je ya tayar da tarzoma, har an yanke shi a ƙafa, rashin mutuncin sa kullum ƙara gaba yake yi””To, na ji, maganar kenan ki sake maimaita mini abun da yake aikatawa? Wannan ai wani abu ne da na riga na sani”.”Ba shi ne ba, magana ce a kan mafita game da abun da yake yi”Ya tashi zaune ya ce “Wace irin mafita?”Rahila ya gyara zama ta ce “Akwai wata ƴar ƙawata, yarinyar rashin ji take yi, tana neman fanɗarewa, gashi ba ta da wani tsayayye, na ce tun da shi gashi, kuma akwai wannan kangon gidan da ya gada, a gyara masa ka nema masa aurenta, ta je su ƙarata ko zai yi hankali idan ya ajiye iyali”.Abbu ya ɗan yi shiru sannan ya ce “Too, ikon Allah, banda abunki wane mai hankalin ne zai bawa Al’amin auren ƴar sa, yadda suanansa ya yi shuhura, a kan rashin ji”.”To ai yarinyar na ce maka fitina take yi ita ma””Kuma sai ayi gyaran ɓarna da ɓarna? Sai a aura masa wadda ba ta ji?”Rahila ta ce “To shi ɗin menene? Shi na kirkin ne?ko Jin yake yi? Sai su rufawa juna asiri, amma aka ƙyale shi a haka, nan da shekara ashirin, kana ganin zai yi nutsuwar da zai kula wata mace da sunan zai aura, tsabagin wauta da kayen maye ne kawai a cikin kansa”Abbu ya numfasa ya ce “Maganarki haka take, amma kamar yayi ƙanƙanta ma da auren shekara ashirin da bakwai, ga ba sana’a yake ba sai ɗaukar magana, da yaya zai riƙe auren? ga faɗa da faɗin rai”.”Idan ya san ya ajiye mace, dole ya nemo ya ba ta ai, tun da morarta zai din ga yi, ko kuma kana tunanin zafin rai da faɗin ransa zai hana shi, mu’amala da ita ne namiji ne fa”.Abbu yayi murmushi, har sai da haƙoransa suka fito, ya ce “Na san ɗa na kamar yunwar cikina, ban san meyasa mata ku ke tunanin maza, bamu da wani tunani idan ba wannan ba, Aishikenan”.Ta kwanta ta ce “Aikuwa idan haka ne, da sai an dangana da nema masa magani, idan baya wannan tunanin”Ya kwanta a kusa da ita ya ce “Zuwa da safe in Allah ya kaimu, sai ki yi mini kwatancen gidan su yarinyar, na samu mahaifinta”.Ta ce “Yauwwa Abbu ko kai fa”****Jauhar ta dawo daga makarantar dare, ta tarar da Baba da baƙo a waje, ta durƙusa ta gaishe su, sannan ta shiga cikin gida.Baba ya nuna wa Abbu ita, ya gaya masa ita ce jauhar ɗin da suke maganarta, Abbu sam bai ga alamar rashin ji, a tare da jauhar ba sai ma nutsuwa da kamala, hatta muryarta mai sanyi ce, yayi mamakin da rahila ta ce masa wai ba ta ji, fanɗararriya ce, sai dai bai yi magana ba, suka cigaba da magana da Baba a kan nemawa Al’amin auren jauhar, ya sanar da baban jauhar Al’amin ɗin ba ya ji, sai dai bai gaya masa irin rashin jin ba, ya zata Baba ya san komai, saboda yadda rahila tayi masa bayani.Baba ya ce “Babu damuwa, Allah ya tabbatar musu da alkhairi, na san iyayen nata ba za su zaɓa mata abun da zai cutar da ita ba”.Suka taɓa hira, ya tambayi Baba ko akwai wani shiri da za su yi? Baba ya ce idan sun shirya kawai su kawo abun da suke da shi, ayi komai a wuce wurin.Suka gama magana, Abbu ya tafi gida yana farinciki, tare da fatan Allah ya sa ƙarshen matsalar Al’amin ce ta zo, Shi ma Baba ya shiga gida, can ƙasan zuciyarsa yana ta kokwanto da wasi-wasi, amma ya kasa ayyana hakan a zahiri.Sam  bai iya tambayar menene rashin jin da  Aminu yake yi ba, bai tambayi menene sana’arsa ba da sauran su, kawai shi dai ya tsinci kansa da amincewa, bayan da mama tayi ta jaddada masa idan har Alhaji mu’azzam ya dawo, ya ji ƴan daba sun yi mata fyaɗe za ta wulaƙanta, ba zai aureta ba, shi gaba ɗaya ma ya manta da batun ya karɓi kuɗin auren Jauhar.Abbu na komawa, Rahila ta tare shi, tana tambayarsa yadda suka yi, ya ce “Ya amince zai ba shi ita, amma ni da ya nuna mini yarinyar, ba ta yi kalar marasa ji ba”.”Ban da abunka Abbu, dama a goshi ake gane marasa jin? Kai dai kawai ayi sha’ani”.”Amma anya ban yi ganganci ba kuwa, ban sanar da shi ba na je na nema masa aure, idan ya bujire fa”.”Au sai ma ya yarda? Ashe na kabari zai dawo duniya idan shi ne zai yadda, ka yi iya yinka a matsayin ka na uba, kar ma ka sanar masa, sai ka kai kuɗin, kuma ku saka lokaci kaɗan, kar ya tafka wata tsiyar, ba akwai gidan da ya gada na wurin babarsa a chiranci ba, aje a ɗan gyara masa, ya zauna”.Abbu ya jinjina kai ya ce “Shikenan Allah ya yi mana jagora”.Kwana huɗu, Abbu ya kira baba, ya ce za su zo, su kawo dukiyar aure.Ko da Baba ya sanar da wanda za su karɓi kuɗin Jauhar ɗin tare, sun yi mamaki, suka din ga tambayar sa, meyafaru da waccan saka ranar, ya ce musu matsala aka samu.Dubu ɗari uku da hamsin, aka kai kuɗin komai da komai, har da lefe da sadaki da kuɗin aure, wai bayan sati biyu za a ɗaura aure.Mama ta fito tsakar gida ta din ga rangaɗa guɗa, suna Allah ya sa za su gani, gaba ɗaya sai jauhar ta zama confused, wane irin abu ne haka? Alhaji mu’azzam ne ya dawo? Ko kuma yaya aka yi, aka kuma karɓar wani kuɗin. ta ji ana zancen wani Al’amin shi kuma daga ina? Ta tambayi kanta.Sai dai tsananin kunya, da kawaicin jauhar, bai sanya ta yi magana ko ta tambaya ba.Su surayya suka din ga yi mata dariya, wai ta ga samu ta ga rashi, from grace to grass.Duk wani shirin auren, Mama ce take yi, ita ke karɓar kuɗin a hannun Baba wani abun ta saya mata mai kyau, wani akasin haka, masu kyan ma tana saya ne, saboda kar a yi mata gori, ta riƙe yarinya shekara goma sha shida za a shiga sha bakwai, amma ba ta yi mata abun kirki ba.Aminu kuwa tun kan a kai kuɗin, yayi ɓatan dabo, dan rigimarsa ba ta ciwo shi ya zo gidan ba, dan haka tilas Abbu ya fara bin dabar da yake zama, da duk in da ya san zai ganshi, amma babu shi babu labarin sa, haka ya din ga bayar da cigiyarsa, kamar wani kuɗi, kowa ya tambaya sai ya ce masa bai ganshi ba.Rahila ta ce masa ya cigaba da shirin sa, duk in da ya tafi ma zai dawo.A gidan su jauhar kuwa, hankalinta ne ya tashi, da ta ji Anty na yi mata iƙirarin wai nan da sati biyu za a ɗaura mata aure, da angonta Al’amin.Saifu ya kasa jurewa, ya samu Baba ya tambaye shi, wai meke faruwa da auren jauhar ne?.Baba ya ce “Eh, nan da sati biyu za ayi””Amma na ga kamar sau biyu aka kawo kuɗin, wancan an ce Alhaji mu’azzam, yanzu kuma an ce Al’amin wanne ne gaskiyar lamarin ne?”Baba ya ce “Maman ka da Antynku, ne suka yanke shawarar a aura mata wani, wancan za a iya samun matsala, ta ɓangaren zakiyya ma aka kawo wannan ɗin” cike da takaici yake kallon Baba ya ce “wace irin matsala kuma Baba? Meyasa wanda aka kawo ɗin ba za a haɗa shi da wata ba, sai jauhar? A ina yake, kuma menene sana’rsa? Yazo ya ganta ta ganshi, yayi mata?”Baba ya sunkuyar da kai tare da girgizawa ya ce “No, amma na san ba za su zaɓi abun da zai cutar da ita ba, kuma jauhar yarinya ce mai biyayya”Takaici ya ishi Saifu, ya tsani yadda matan gidan suke shirya wa Baba abun da suke yayi, kuma yayi babu musu mussaman a kan jauhar.Kawai ya tashi ya fita tsakar gida, ya tarar da ita, tana ta uban wanke-wanke, gefe ta jiƙa kayan wankin uniform ɗin ƙanan yaran gidan.Ya ja kujera ya zauna a kusa da ita ya ce “Waliyiyya, wai saura sati biyu aurenki?”Tayi yaƙe ta ce “Haka na ji, amma dai Baba bai gaya mini ba”.”Wanda zaki aura ɗin kin taɓa ganinsa ne? Ki na son sa?”.Ta sunkuyar da kai tana murmushi ta ce “Ko ban ganshi ba, tun da an ce su mama ne suka zaɓa mini shi, kuma Baba ya amince na san ba zai cutar da ni ba””Baki taɓa ganinsa ba kenan?” Sai ta kasa amsa masa, ta cigaba da durza tukunyar hannunta cikin ƙarfin hali.Can kuma ta ce “Dan Allah yaya, ka roƙi baba, ya ce masa dan Allah ina son ƙarasa makarantata, ko WAEC na yi”Saifu ya girgiza kai ya ce “Ki kwantar da hankalinki, na san juriya kawai ki ke yi, amma in sha Allah, ba zaki ji kunya ba jauhar”.Mama ce ta fito ta ce “Kai saifu, uban me ka ke gaya mata, hure mata kunne zaka yi?”Ya tashi tsaye ya ce “Ko na hure mata kunne, ba zai huru ba, kawai ina tausayin sauran ƴan matan ne, saboda komai nisan jifa ƙasa zai dawo”Ta ce “Saifu ni ka ke gaya wa haka? Me ka ke nufi?””Mama kin san fa me nake nufi sarai, Allah ya haramta zalunci a kan kansa, babu wanda zai yi ya tsira wallahi” ya ƙarasa maganar yana ficewa.Cike da takaici da son hucewa, mama ta rarumi takalmi, ta jefi jauhar da shi a fuska, aikuwa ya tsokane mata ido.Ta zauna ta din ga mutsutsuka idon, sai da idon yayi taruwar jini.Ƴan unguwar su jauhar sai ganin invitation suka yi na bikin jauhar, suka din ga zuwa gulma da jin ba’asi, wane irin aure ne haka faka-faka ko lefe ba a nuna musu ba, da yake ba su san ma zancen kawo kuɗin auren farko ba.Mama da zakiyya, suka din ga cewa saboda ayi a rufa mata asiri, ake son ayi gaggawa a aurar da ita, sadakarta aka bayar babu ko kayan lefe.Saboda cin fuska a gabanta, suke faɗar hakan. A gabansu sai ta jure, tayi kamar ba ta ji ba, idan ta ɓuya kuma sai tayi ta kuka.Al’amin kuwa, honorable Indabo ne ya saka aka kai shi asibiti ta ƙarfin tsiya, saboda ciwon ƙafarsa an sake fama masa lokacin da ya tayar da rigima a wurin campaign, a haka yake lanjarata, ya tafi nasa wuri, saboda soyake Aminun ya warware sosai, kafin lokacin zaɓe kuma, yadda zai yi masa aikinsa yadda yakamata.Yana shiga arearsu, aka sanar da shi cewa, babansa yana ta yawon nemansa, mamaki ya kama shi, dan idan zai kwana nawa bai ganshi ba, babu ruwansa da in da yake, dan haka cikin gaggawa ya nufi gidan, domin jin dalilin neman nasa.Sai dai da ya je ya tarar da Abbun yana shirin fita.”Kai baka iya sallama bane Al’amin, sai dai mutum ya ga ka bayyana kamar wani shaiɗani?””To meye marbarsa da shaiɗanin?” Tayi maganar ƙasa-ƙasa.Sarai ya ji ta, amma ya yi shiru, ya samu wuri ya zauna ya miƙe ƙafarsa ya ce “An ce kana nema na””Ba an ce bane, nemanka nake yi, ka dawo daga gantalin kenan? Kodaye ba yau ka fara ba, ka buɗe kunnenka da kyau ka saurare ni”Yayi shiru bai ce komai ba.”Daga nan ba kasuwa zani ba, Abba ne zai je ya buɗe shago, gidanka na chiranci, na gado zan je, za ayi masa wasu ƴan gyare-gyare, ba ni da kuɗi sosai a hannuna, za a yi masa abun da ya sauwwaƙa, kai ka ƙarasa gyarawa daga baya”.Ya yi shiru yana wasa da zobensa, kamar yadda ya zame masa ɗabi’a, idan ba ya son yin magana.Abbu ya cigaba da cewa “Kuɗin aure na kai maka, next week za a ɗaura maka aure”Lanƙwashe ƙafarsa ɗaya yayi, ya koma wasa da yastun ƙafarsa, yana kallon wani wurin daban.Rahila ta ce “Taɓɗijan, lallai gagare”.Abbu ya ce “Al’amin da kai nake fa”Ya ɗago idonsa ya kalli Abbu ya ce “Wai ni ko wa?””A’a da ubanka nake ba kai ba, ni da waye a wurin nan?”Al’amin ya ce “Ni fa yau ban sha komai ba, garau nake balle ace a buge nake ban ji dai-dai ba, wannan kawai zance ne, ni da ake cewa gagarrare haihuwar asara, wa zai bani wani aure? Ni bana buƙata, idan kuma ba haka ba, duk abun da ya biyo baya ba ruwana idan na kashe yarinya, ko na yi mata illa, kar a zo ana yi mini ƙanan maganganu, ba na so bana buƙata”.Ya yinƙura zai fice, Abbu ya riƙe shi ya ce “Umarni nake baka, ba shawararka ko ra’ayinka nake nema ba, dole ne wannan, aurenka wani satin, na kai kuɗin aure da komai, dole ka nutsu ka shiga hankalinka, idan ka illata musu ƴa ko kasheta kuma, zan sallamawa duniya kai, wannan shi ne hukuncin da na yanke”A fusace ya ce “Meyasa zaka yanke wa rayuwata hukunci, ba tare da amincewata ba bayan ka daɗe da sallamawa duniya rayuwar tawa? Ka yi hakan ne saboda farincikin matarka ko? Ta daina ganina na gusa na bar mata gidan nan ita da iyalinta. Da zan iya wallahi garin zan bar muku na ɓacewa ganinku ku samu cikakken kwanciyar hankali kamar yadda ku ke buƙata, amma ba zan iya ba.Ka sani ina ta’amalli da miyagun ƙwayoyi, da gaske zan iya kashe ƴar mutane, ko na illata ta, sai dai ba na fatan na fi haka lalacewa, idan ka yi mini baki, zan ƙara lalacewa ne zan bi umarninka, amma duk abun da na yi mata da ni da kai zamu ɗauki nauyin zunubin. Saboda ni babu mata a tsarin rayuwata, miyagun halittu da babu Allah a ransu, bana fatan raɓar su, saboda yadda tasirin kaidinsu ya kassara rayuwata, kassarawar da ba za ta gyaru ba, mace ɗaya da nake wa kallon rayuwata, uwata kenan na rasata a yanzu babu wata mace mai sauran kima da mutunci a idona, nayi alƙawarin nesanta kaina da mata, nesantawa mai nisa ta har abada, amma ka karya mini alwashi, ta hanyar janyo mace rayuwata, ina sake nanata maka, duk abun da ya biyo baya, tare zamu ɗauki nauyin zunubin”.Ya saka hannu, ya cire hannun Abbu da ya riƙe masa riga, ya saka kai ya fice.Har ya bar gidan, babu wanda ya sake magana, daga ita har Abbu.Gaba ɗaya aka hana jauhar fita daga gida, ana ta shirin biki, ita kuma tana rama kamar ana tsotseta, duk ta fiƙe sai farar fata da idanuwa.Maƙwabciyar su ta din ga cewa “Gaskiya mama ban so a aurar da jauhar yanzu ba, na so a bari maƙerin budurci ya gama ƙere mana ita, wannan kyawun da gidan wani hamshaƙin ya dace”Anty ta ce “Wannan ma hamshaƙin ne”.A gida mama ta saka su surayya sa walida, suka dinga kwaɓe-kwaɓe suna murzawa jauhar da sunan gyaran jiki.Malam jamilu ya shiga matsananciyar damuwa, da samun labarin auren jauhar, dan har ga Allah yana matuƙar sonta, tsoron kar ta daina ganin mutuncinsa, ya sanya ya ɓoye mata.Gidan jauhar da aka je jere, yana da girma, sai dai tsakar gidan tsurar ƙasa ce, cikin ɗakuna babu floor, sai dai an yi plasta a ɗakunan, falo ɗaya da ɗakuna uku a ciki, kowanne da banɗaki, sai kitchen a tsakar gida da tsakar gida mai girma.An yi wearing ɗin wutar lantarki, a gidan.Sai buhunhuna, aka shimfiɗa a ƙasa, sannan cikin ɗakunan aka saka leda, falo kuma aka shimfiɗa carfet, saboda duk turɓaya ne.Tagogin duk babu na kirki, sai kame-kame da faci.Sai kujerunta, ƴan gida masu kyau, ɗaki ɗaya an saka furnitures, ɗaya kuma sai aka saka ƙatuwar katifa da wardrobe mai biyu, abun saka takalma. Duk da haka gidan ya yi kyau.Amarya ta din ga fargaba da tunanin, waye mijin nan, da haryanzu za ace, bai taɓa ganinta ba, kuma ba ta taɓa ganinsa ba? Kuma ya amince da zai aureta.Dogon gashinta baƙi, aka gyara mata shi, aka yi mata lalle ja da baƙi.Haka kurum take tuna Alhaji mu’azzam, a haɗuwarsu biyu, yadda yake nuna yana sonta, ba ta son ya zai ji ba, idan aka ce masa an yi mata aure.Kodayeke ita ba ta san dalilin fasawa da shi ba.Su liti suka lura da shirun Al’amin ya ƙara yawa, duk da ba mai yawan magana ba ne dama, sai ya zauna yayi shiru yana zancen zuci.Walid ya ce “Baaba, wai dan Allah kwanan nan meyake faruwa ne? Kamar ka na cikin damuwa” tabbas ba dan Walid ya tambaye shi yanzu ba, ba zai gaya masa ba.Ya karkace ya ɗaukko invitation a aljihunsa, ya miƙa wa walid.Wani irin ihu walid yayi, haɗi da kururwa, yayi katantanwa a ƙasa ya kuza uwar ashariya.Sannan ya ce “Allah dai ya biya maza, dama zaka afkawa sabgar nan, ka yi mana shiru haka? Ba ka gaya mana ba, balle mu shirya saura kwana uku fa”.Sauran matasan da ke wurin suka miƙe suna tambayar Walid ko lafiya?.Ya miƙa musu invitation ɗin, take suka hau shewa suma, suna dara.Kawai ya dafe kansa, yayi shiru.Walid ya ce “Wai tsaya, auren dole za ayi maka ne? Na ga baka murna, kuma shi ne ba ka taɓa kai mu ehhh, mun gaisa da antyn namu ba, iya wuya mun samu mai dafa mana abinci””Walid, Abbu ne ya shirya komai, ni ko ganinta ban taɓa yi ba, kuma ba na fatan na ganta, kuma ba kowa ne ya shirya wannan abun ba, sai wannan shaiɗaniyar matar ƴar haramun, ya ce umarni yake bani ba shawara ba, ni kuma na yanke guduwa zan yi, ba abun da zai haɗani rayuwa da wata mace, ba za a mayar da ni nusari ba, kalli yadda mace ta yi silar rushewar farincikin rayuwata gaba ɗaya”Walid ya zauna kusa da shi ya ce “A’a maza, duk lalacewar naka naka ne, kai ka san albarkar dattijan ke riƙe da mu, ka daina kallon abun da yake yi maka na rashin jin daɗi, idan yayi maka baki ƙara watsewa zaka yi.Duk da lokaci ya ƙure, dole ayi celebration, zamu gayyaci gayu a sha shayi a babbaka hayaƙi, abun farin ciki ya same mu” ya ƙarasa maganar suna shewa, ban da Al’amin da zuciyarsa kamar ta yi bindiga.Hatta kayan da Al’amin zai saka na aure, sai da Abbu ya saya wa Al’amin,  dan ko ganinsa bai sake yi ba, sai dai ya fita yawon neman sa.Ƙarfe goma na dare, su Walid suka shirya party, aka dafa shayi aka raba lemuka, da kayan shaye-shaye.Gogan yana gefe, yana zancen zuci, har ga Allah so yake ya gudu, amma ya san ya gudu alaƙarsa da Abbu za ta ƙara tsami. Kuma ya san ko ya gudu sai ya dawo, ba zai iya barin Abbun ba.Tunani yake kowace mai tsautsayin da ba a so, ce haka, aka zaɓi a aura masa oho.Ana tsaka da walimar hayaƙin, faɗan daba ya kaure, Al’amin kuma ya koma gefe ya ƙi magana, ƴan sanda suka yi wa wurin dirar mikiya, saboda rahoton da ƴan unguwar suka kai wa jami’an tsaro, ai kuwa suka kame su har da shi suka tafi da su ana gobe ɗaurin auren da bai san wacece matar ba.

Ayshercool08081012143

Back to top button