Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 55 Hausa Novel

Suna sama ita da maigidan suna ta hirarsu cikin kwanciyar hankali, sai waje karfe tara sannan Anti Wiyya ta fito daga dakin baki ta ga wankin. Tayi matukar mamaki musamman da ta tambayi Afaf ta tabbatar mata Habib din ya fice bai dauki wankin ba. Nan ta koma daki ta kirawo Naja a waya wadda ta sauko, ta nuna mata wankin sannan tayi mata bayanin cewa a nan ya fice ya barsu.Yaran suna kallo ta tsuguna ta tsince kayan ta bar kala daya da hijab guda daya sannan Anti Wiyyan ta koma daki ita kuma ta haye sama.Jimawa kadan Mustapha ya sako yana tambayar Afaf ina kaninta.‘Abba ban ganshi ba, ficewa kawai yayi ba tare da yace komai ba.’ Ta bashi amsa.A fusace ya murda kofar dakin Habib din ya shiga yana kiransa, sai dai ga mamakinsa Habib din baya cikin dakin. Ya fice wajen Baba Maigadi inda ya tabbatar masa bai san inda Habib yake ba, ya kara da cewa ‘Bana jin ma fita yayi, don tun da aka ce ya zo kana kiransa ban sake ganin gilmawarsa ba. Sai dai ko da ina sallah ne ya fice ban sani ba.’Ya koma cikin gidan ba tare da yace komai ba.Yana shiga parlor din ya dubi kayan yace ‘Nasreen zo ki kwashi kayan nan ki mayar mata, yayan naki zai zo ya same ni.’Ya haye saman inda ya tara da Naja a zaune a parlor ita da Rukayya, ya sami waje ya zauna sannan ya dauki wayarsa ya dannawa Habib kira. Ba karamin mamaki yayi ba da yaji wayar Habib din a kashe, sai dai yayi tunanin kashe wayar Habib din yayi don ya san bashi da gaskiya. Don haka sai kawai ya sauko ya sanar da Baba Maigadi cewa idan Habib ya shigo gidan yayi masa waya.……..Tun yana sa ran shigowar Habib har abun ya fara bashi tsoro; yaran duk sun tafi sun kwanta har sha biyun dare ta yi amma Habib bai shigo gidan ba, gashi sai kiran wayarsa ake yi a kashe. Yana son ya kirawo Hajia ko Habib din yaje can amma kuma baya son ya daga musu hankali.A karo na babu iyaka motsin shigarsa dakin ne ya farakar da ita daga bacci, ta gyarawa Baby Maryam kwanciyarta sannan ta dubeshi tace ‘Wai bai dawo ba.’A jigace yace ‘Eh, wallahi har abun ya fara bani tsoro. To ina Habib zai tafi? Ina ma ya sani a garin nan shi da ba wani yawo yake ba?’Tace ‘Ya zaka ce ina ya sani yaron da yake level 1, kuma yake tafiya makaranta da kansa. Ai yanzu ba kamar da bane, tsaf ya san ko ina.’‘To ina zai tafi a wannan daren? Gashi Baba Maigadi ma yace ko fitarsa bai gani ba kuma gidan nan babu inda bamu duba ba baya nan.’Tace ‘To ka dai yi hakur ka zo ka kwanta tunda ka ga yanzu dayan dare ta kusa, zuwa wayewar gari sai a nemoshi a bashi hakuri a gaya masa ya barwankin.’‘Mtseww! Wai kin san me kike fada kuwa? Na zo na kwanta saboda ke kin kwanta ko?’ ya sake jan tsaki sannan ya fice daga dakin ya rufe mata kofar da karfi, rufe kofar da sai da ya farkar mata da Baby daga barci.Ta juya a fusace tana gunguni ta dauki yarinyarta ta saka mata nono.Yanda yaga rana haka yaga dare, yana zaune a parlor shi kadai. Sai dai idan bacci ya daukeshi yayi firgigit ya farka, ya sake buga lambar Habib amma a kashe. Yana fara jin kiran sallar asuba ya kirawo Alhaji ya sanar da shi ba a ga Habib ba.A shirye ya fice masallaci, bayan an idar da sallar asuba ya sanar da su bacewar habib. Yana dawowa gidan ya dauki mukullin motarsa ya fice ya nufi gidan Hajia.Suma a tsaye ya samesu cikin tashin hankali, nan suka zauna suna jira gari ya kara wayewa suje police station su sanar.Suna zaune a parlor din Alhaji cikin tashin hankali Hajia ta dubi Mustapha tace ‘Kuma ka tuntubi kakanninsa, can gidan su Ma’u da ma ita Khadeejan ko wajensu ya tafi?’Ya gyara zama yana cewa ‘Khadeeja dai na tambayeta itama bata ganshi ba, amma gidan mama ma ni na manta da su. Bari na kirawosu na ji.’Kafin ya gama laluben lambar suka jiyo bugun kofa, gaba dayansu suka nufi kofar saboda Alhaji ya bada sanarwa a masallaci yayi zaton ko an sami wani labari ne.Ga mamakinsu Kawu Auwal ne wato kanin Ma’u tare da Habib din. Suna hada ido Mustapha ya kai masa duka yana cewa ‘Shine zaka fice ba tare da ka gayawa mutane ba saboda raini ko?’Alhaji yace ‘Ka barshi mana ya zauna yayi bayani.’Suka karasa cikin gidan suka zauna a parlor din Alhaji.Bayan sun gaggaisa Kawu Auwalu yace ‘Wallahi nima da asuba Mama ta kirawoni tace na zo na dawo da shi, itama ta yi zaton an san yana gidan shi yasa ma bata nemi kowa ba. Sai dazu bayan sallar asuba Antinsa Khadeeja ta kirawota tana cigiyarsa. Shine ta kirawoni tace na kawo shi nan nayi bayani.’Alhaji yayi masa godiya sannan ya dubu Habib yace ‘Mutumina ya haka kuma? Me suka yi maka a gidan da zaka bi dare ka gudu? Kuma madadin ka zo ka gaya min sai ka tafi ka dagawa Mama hankali.’A nan ne ya sami dama ya gayawa Alhaji abinda ya faru, sannan ya sanar da shi irin zaman da ake yi a gidan.Hajia tace ‘Dama Aminan Jidda ta fada, tace wancan zuwan da suka yi gidan basu ma ga Najan ba. Kamar yaran suna kasa su da mai aiki suna rayuwarsu ita kuma tana sama ita da nata yaran, kuma yanda ya fada haka Aminana ta fada tace shi kanshi Mustaphan yaran basa ganinshi sai dai idan ya sauko.’Shima Auwalu ya tabbatar musu da cewa duk wadannan maganganu yaran sun dade da yiwa Mama bayani, sai dai da yake ta dauka ba huruminta bane shi yasa ma bata ce komai ba. Amma dai gaskiya da akwai matsala, tunda ai da ba a taba samun matsala irin wannan ba.’‘Hakane, in sha Allahu za a duba kuma a dauki mataki.’ Alhaji ya fada.Suka karasa tattaunawa Auwalu yayi musu sallama ya tafi.Shima Mustapha ya mike ya sa Habib a gaba don su tafi, sai dai shi habib din ya nuna ba zai koma don ya fi so ya zauna a nan wajen Hajia. Alhaji ne ya saka shi a gaba da nasiha yana nuna masa gara ya zauna saboda kannensa, kada ya tafi ya barsu su kuma bai san me zai faru da su ba.Sai wajen karfe tara sannan Hajia ta shirya suka kama hanya tare da Habib din da Mustapha suka koma gidan.A cikin tashin hankali suka sami yaran, Nasreen da Shukra suna sanye da uniform dinsu; don saida suka fara shirin makaranta sannan Naja ta sauko ta sanar da su ba zasu makaranta ba Habib ya bata Abbansu kuma ya tafi nemansa.Babu wanda ya ji shigowarsu gidan saboda Mustapha a waje ya ajiye motarsa saboda Hajia tace yanzu zata fito ya mayar da ita. Da sallama suka shiga parlor di, Nasreen ce da Shukra suna zaune a parlor din da flask din shayi a gabansu da katon bread. Sai dai sun kasa shan sahyin sun yi tsuru-tsuru.Da gudu suka mike, Shukra ta fada jikin Habib tana dariya yayinda Nasreen ta matsa kusa da Hajia. Suka karasa ciki suka zauna.Hajia tace ‘Ina Afaf?’Nasreen tace ‘Tana dakinmu.’‘Antin fa da Rukayya?’Nasreen ce ta sake sunkuyar da kai tace ‘Basu sauko ba.’Hajia tace ‘To kije ki kirawo min ita kice ta zo.’Shukra tace ‘Yanzu fa ta leko kuma tace kada wanda ya hau mata sama ya dameta, ko menene a jira sai ta sauko.’Hajia ta jijjiga kai, ta kalli Mustapha.Ya dan diririce sannan yace ‘Hajia tasowa zakiyi muje saman ai.’

Back to top button