Mijin Marigayiya Page 51 Hausa Novel
Kafin ya bata amsa tuni Khadeeja ta ja akwatinta ta fice daga parlor din. Shukra wadda ta karasa ta fada jikin Abbanta ta rushe da kuka; saboda ta kasa fahimtar me yake faruwa su da aka ce za ayi tafiya har Abbansu a barsu da Anti kuma Antin ta fara tafiya.Ya dubi naja yace ‘Cewa tayi na saketa kuma na saketa, tunda ita ta nema.’Ta dan firgita ta dafe kirji, bata san lokacin da yawun da yake bakinta ya wuce ba tace ‘Saboda me? Kai kuma ka biye mata?’‘Saboda bakin cikin zan tafi dake Hajji ban tafi da ita ba.’ Ya fada cike da adcin rai.Ya karasa ya zauna a kan kujera a jigace kamar wanda aka tura.Sukayi cirko cirko suna kallonshi.Habib ya shigo a guje ko sallama bai yi ba, yana cewa ‘Abba na ga Anti tafi. Me yake faruwa ne? waye zai zauna damu?’Ya mike a jigace yana cewa ‘Maza kowa ya debo kaya ko kala daya ne mu wuce, sai na ajiyeku gidan Hajia. In ya so ko gobe sai ku dawo da Yaya Jidda ku debi kaya. Antin ta tafi.’Ya fice batare da ya sauraresu ba Naja ta rufa masa baya.Nasreen ta kalli Habibi ta kare gefeb bakinta kamar me rada tace ‘Ya saketa.’Ya zaro ido zai yi magana suka jiyo muryar babansu daga kafar bene yana cewa ‘Maza fa ku sauko.’Suka mike gaba daya suka shirya suka fice.Ba karamin mamaki Hajia da Alhaji suka yi ba da Mustapha ya gaya musu ya saki Khadeeja.Shi kadai ya shiga da yaran don ita Naja ma cewa yayi ta zauna a mota saboda kada ta bata musu lokaci. Suna shiga yaran suka wuce cikin gida shi da Hajia da Alhaji suka tsaya a parlor yana musu bayanin abinda ya faru.Alhaji yace ‘To kai wane irin rashin hankali ne wannan? Ai don mace tace a saketa ba a sakin nata. Zuciya ce ta kwasheta kuma sai daga baya zata zo tana nadama. Da ka sani ka barta da aurenta idan ma tafiyar zata yi ta tafi idan ka dawo kalau zaka ga ta dawo.’A fusace yace ‘Alhaji yarinyar ce ta kureni, ita kullum sai dai ay mata yanda take so amma ita ba zata yi yanda ake so ba? Taje idan mutuwar aure dadi ne ai ta samu sai ta dana ta fi shiga hankalinta.’Hajiya tace ‘Ai shikenan tunda haka ta zaba. To yanzu in Hammad din da Rukayya? Ban gansu tare da ‘yan uwansu ba.’‘Shi Hammad dama yana gidansu, ita kuma Rukayya gidansu ta kaita.’‘Ai shikenan, Allah ya sauwake. Idan ka dawo a san yanda za ayi domin dai aure bai kamata ya mutu saboda kujerar hajji ba.’ Alhaji ya fada cike da nadama.Mustapha ya dubi Hajia yace ‘Mukullin gida yana hannun Habib in an jima Baba Sani abokina zai zo ya kaisu shi da Afaf su debo kayansu su rufo gidan. Idan sun dawo sai ya bawa Alhaji mukullin gidan ya ajiye min. akwai ATM card din a hannun Afaf idan ana bukatar wani abu na kudi sai taje ta ciro ta bayar.’Yayi musu sallama ya fice zuciyarsa cike da damuwa.……….Zuciyarta fayau ta fito daga gidan tana addu’ar Allah ya sa iyakar zamanta kenan da Mustapha tunda ta san saki daya yayi mata. Sun tsaye a bakin titi ita da Hafsa suna jiran mota ya zo ya wucesu a guje a tashi motar. Ta bi bayan motar da kallo tana murmushi; ta tuna lokutan da yake zuwa ya wuceta a titi zata tafi makaranta amma ba zai iya rage mata hanya ba. Tayi murmushi ta kawar da kai. Jimawa kadan da wucewarsu ta sami mota, suka hau suka nufi gidan Mommy.Tana tura gate din gidan Baffa ne a tsaye yake rufe motarsa, da alama dawowarsa kenan.Suna hada ido dashi hawayen da ta kasa fitarwa ya kwace, ta saki akwatin da take ja. Ahmad wanda yake tsaye a kusa da shi ya karasa ya rike akwatin yayinda ita kuma ta karasa ta fada jikin Baffa wanda yake binta da kallon mamaki. Ya rungumeta sannan ya dafa kanta wanda ta kwantar a kirjinsa yana cewa ‘Subhanallahi! Me ya faru da ku Khadeeja?’Ta kasa magana sai kuka kawai take har da shessheka.Baffa ya fara shafa bayanta yana cewa ‘Ya isa haka, ya isa, ki gaya min me ya faru?’‘Ya sakeni.’ Ta fada a cikin shesshekar kuka kamar mai rada.Take fuskar Baffa ta canza, ranshi yayi matukar baci. Yace ‘Mustaphan ya sake ki?’Ta daga masa kai.Ya sake shafa kanta cikin yanayi na lallashi yana cewa ‘To shikenan, ya isa haka.’Ya ja hannunta suka shige gidan; da yake Mommy tana dakinsa kai tsaye can ya wuce da Khadeeja. Mommy tana kokarin yi masa sannu da zuwa ta kula da Khadeeja, tace ‘A’a, Baffa a ina ka samo wannan?’Ya zaunar da ita a gefen gadonsa yace ‘Mustapha ya saketa.’‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Saki kuma? A yau din? Na dauka ce min kika yi yau jirginsu zai tashi?’Ta share ragowar hawayenta ta ajiye jakar hannunta sannan tace ‘Eh, kafin su tafi airport din ne ya sakeni saki daya.’‘Lallai Mustapha, to me kika yi masa ya sake ki? Ko kuwa dai tsabar wulakanci ne yaga gara ya sakeki kafin ya wuce yayi ibada?’ Mommy ta tambaya tana daga tsaye.Bata yi tunanin wata amsa da zata bayar idan an yi mata wannan tambayar ba, amma dai tana jin gara ta fadi gaskiya don ma kada ya zo shi ya bada amsa da ta bambanta da tata. Ta daga fuskarta suka hada ido da Mommy sannan ta sunkuyar da kai. Mury kasa-kasa tace ‘Ni nace ya sakeni.’Saura kadan wayar da take hannun Mommy ta kufce ta fadi, ta rike wayar sannan tace ‘Kika ce ya sake ki Khadeeja? Saboda rashin hankali ko saboda me?’Baffa da yake tsaye a gaban wardrobe dinsa yana rataye babbar rigarsa ya zagayo ya zauna a kusa da ita yana kallonta yace ‘Dije me yasa kika ce mijinki ya sake ki?’Kafin ta yi magana Mommy tace ‘Saboda wulakanci mana, ko kuma saboda yace ba zai je da ita aikin Hajji ba sai ya je da amaryarsa.’Kallonta kawai Baffa yayi ta yi shiru, ta gyara tsayuwarta tana binsu da kallo. Ya dubi khadeejan ya sake cewa ‘Deeje me yasa kika ce mijinki ya sake ki?’Ta kalleshi suka hada ido sannan ta sake sunkuyar da kai tace ‘Baffa na gaji, wallahi Baffa baka ga zaman da muke yi a gidan nan ba. Tun kafin ya auri matarsa Baffa dama hakuri nake, matsayina a gidan da kadan ya wuce matsayin ‘yar aiki. Kuma bayan ya aurota ma ya kara tabbatar min da hakan; duk wani abu na walwala da jin dadi da ita ake yi amma wallahi idan aiki ne da wahala Baffa ni zai kawowa kuma dole na yi. Ita kanta matar tasa haka yake saka ni nayi mata aiki babu sannu bare na gode. Shi yasa kwanaki da nace ba zan yi ba ya zo ya kawo maka karata. Wallahi Baffa a lokacin sai da nayi wata takwas ina mata aikin gida da girki da kaomia kuma kullum shi a wajenta yake kwana.’Ta sake sunkuyar da kai ‘Na gaji Baffa, baya sona, wulakancin da yake min suna da yawa, gara na hakura kawai shi yasa nace ya sakeni.’Ya kama hannunta wanda take wasa da shi a kan cinyarta ya kalleta suka hada ido yace ‘To ya isa, kuka ya isa haka. Ki je ki kai kayanki daki ki huta mayi magana wani lokacin.’Ta gyada kai ta mike ta fice daga dakin.A fusace Mommy ta bi bayanta, cikin sauri Baffa yace ‘Zo mana.’Ta juyo a daidai lokacin da Khadeejan ta rufe kofa, ya nuna mata inda Khadeejan ta tashi ta zauna. Sai da ya dauki lokaci yana kallonta sannan yace ‘Ki bita a hankali tunda dai kin ji bayaninta. Ni da na bashi aurenta ai ba ‘yar aiki na bashi ba ko? In ya dawo ya zo yayi bayani in ya so sai a san matakin da za adauka. Shi a zaman aure ma wani lokacin hutu kawai mutum yake bukata; kada ki je ki daga mata hankali. Ki barta ta huta karshenta in ya dawo sai dai kiji da kanta tana gaya miki ya mayar da ita zata koma. Da-Allah kada ki daga mata hankali tunda dai ita ta kawo mutumun nan tace tana so ai ba laifi bane idan ta dawo tace bata son shi. Ki bata lokaci ta sami nutsuwa tukunna.’Ta sauke numfashi sannan tace ‘To.’Ta tashi ta fice ta barshi a dakin.………
