Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 49 Hausa Novel

Tun jiya bata jin dadi sai dai bata gane me yake damunta ba, haka take ta fama. Da yake ba itace da aiki ba kuma Hammad baya nan haka ta wuni a kwance. Daf da magriba ta fara gane abinda yake damunta; marata ce take ciwo ga wani amai da yake taso mata amma ya ki fitowa. Haka ta sha panadol ta shige dakinta ta kwanta. Wajen 9pm Mustaphan ya shigo dakin domin sanar da ita ya dawo kamar yanda ya saba. Har ya juya zai fita ya dan tsaya yace ‘Wai ya na ganki a kwance ne? kamar baki da lafiya.’‘Uhm, mara tace take dan ciwo.’ Ta amsa a gajiye.‘Ok, Allah ya sauwake. Ko kina bukatar wani abu?’Tace ‘No ina jin zai daina don na ma sha panadol.’Ya sake yi mata sannu sannan ya juya ya fice.Can wajen 10:30pm ciwon ya matsa mata, tun tana daurewa har ta kasa. Ta lalubi wayarta ta kirawoshi, ba tare da bata lokaci ba ya shigo dakin nata. Kafin ya shigo ma ta riga ta shige bandaki saboda yanda take jin kamar zata yi kashi, kafin ta karasa toilet din abinda yake shirin fitowa daga jikinta ya riga ya fito sai jini da ya biyo baya gaba daya da aman da ya tokare mata kirji.A tsugune ya sameta a bandakin, ya karasa da sauri ya duba halin da take ciki. Ya kamata ta mike sannan ta karasa ta zauna a kan toilet. Tace ya jirata ta wanke jikinta sai suje asibiti.Nan da nan ta wanke jiki ta gyara sannan ta tattare zanin nata da bainda ya fita daga cikin nata gaba daya ta saka a leda sannan ta fito ta shirya suka kama hanyar asibiti. Babu wanda yayi magana sai shi da yake mata sannu lokaci zuwa lokaci; a haka har suka isa asibitin.Ba tare da bata lokaci ba likita ya dubata kuma ya tabbatar da cewa cikin jikinta ya fice gaba daya, don ko wankin ciki ma ba sai an yi mata saboda komai ya fice. Aka rubuta mata magunguna aka sallamesu.Tun a mota ta gane Mustapha bai ji dadin zubewar cikin ba, duk da ita ta fi shishiga damuwa da zubewar cikin; amma dai ta kula ba haka yayi ba wancan lokacin da tayi bari. Har yanzu tana jin ciwon mara don haka ba zata iya surutu ba.Bayan sun dawo gida ta haye samanta ta sake yin wanka sannan ta sha magungunanta ta saka Hafsa ta hada mata indomie da shayi mai kauri ta zauna taci. Sai da taci ta koshi sannan ta kirawo Mommy da Yaya Mama ta sanar da su. A daren Momy ta so zuwa sai da Khadeejan ta hanata ta sanar da ita cewa ta sami lafiya su bari da safe sa zo; don haka suka hakura.Can wajen daya saura ya sameta a dakin; tana kwance a gefen gado tana shirin yin bacci. Ya zauna a gefenta yace ‘Sannu.’‘Yauwa.’ Ta amsa tana daga kwance.Suka yi shiru na dan lokaci, ta san da zance a bakinsa don haka tayi kasake tana jiran taji me zai ce. Jimawa kadan ya gyara zama kamar wani mara gaskiya yace ‘Um wai ni me ya faru ne? Me ya kawo wannan miscarriage din? Ko wani abun kika sha ne?’Tayi ‘yar dariya tace ‘Babu abinda na sha, Allah ne dai ya kawo kamar yanda ya kawo wancan.’Ya dan yi jim yace ‘Allah ya sauwake.’Ya sake yi mata sannu sannan bayan ya tabbatar babu abinda take bukata sannan ya fice ya barta.Washe gari tun da safe Mommy da Yaya Mama suka zo, nan suka zauna suka zube mata kayan dubiyar da Baffa ya aiko mata. Mommy ta ji dadi yanda ta ganta ta riga ta mike kamar ma ba daren jiya tayi bari ba, sai kaiwa da kawowarta take yi ana hira da ita. Har sun fara shirin tafiya suna zaune Yaya Mama tace ‘Kinga idan dai ciki ne zai sa a fasa tafiya dake ai yanzu sai a baki kujerarki ko.’Tayi dariya tace ‘Dama kujera ba tawa bace, babu ruwan ciki niyyar bani ne ba ayi ba.’Mommy ta dafa ta tana dan zare ido tace ‘Khadeeja in ce ko dai ba wani abu kika sha kika fitar da cikin nan ba saboda kujerar Makka.’Ta dan zaro ido ta kalleta suka hada ido tace ‘Mommy! Me yayi min zafi? Wallahi babu abinda na sha, sai kace wata marar hankali? Ai na gaya miki fa ba ciki ne ya sa ba zai bani kujerar ba kawai haka yayi niyya, yanzu kuma barewar cikin ba zata sa ya fasa tafiya da ita ba. Ni ce kawai ba zashi da ni ba.’Yaya Mama tace ‘Haba Mommy, a kan wata kujera zata barar da ciki?’Ta gyara zama ‘To ai abun naku ne sai a hankali.’Suka karasa hirarrakinsu suka yi mata sallama suka kama hanya.Ta zauna tana tunanin dalilin da yasa Momy zata yi wannan tunanin; to ko tunanin da Mustapha ma yayi kenan yake tambayarta me ya faru bayan sun dawo daga asibiti? Allah ya gani babu abinda ta sha, cikin nan ma bata taba kawo masa zubewa ba kuma ko da wasa bata so hakan ba. Kawai dai Allah yayi ikonsa ne kamar yanda yayi a wancan karon, kuma ta san shine zai fitar da ita daga duk wani zargi da zai iya tasowa. Kujerar Makka ma idan dai Mustapha ne zai bata kam bata so ta san Allah zai hore mata taje tunda ita ma tana kan neman kudinta.…….Can da yamma su Hajia suka shigo ita da Yaya Jidda da ‘yan matanta. Bata san da Hajia suka shigo ba don haka ta yi banza da su tunda ta jiyo su a wajen Naja. Jimawa kadan suka hawo saman gaba daya; ta saukesu a nan parlor dinta ta kawo musu ruwa da lemo, suka zauna suka yi mata dubiya da jaje. Suna cikin hirarrakinsu Mustaphan shima ya shigo ya zauna aka cigaba da hirar yana sa musu baki lokaci zuwa lokaci.Yaya Jidda ta dubeta tace ‘Alhazai dai sun kusa tashi balle ma ace za a canza a baki kujera tunda cikin da ya hana ya fice, ko ka canza ne Mustapha?’Ya kalleta sannan ya kalli Khadeejan yace ‘A’a ai an gama wannan maganar, ita zata zauna da yara idan Allah ya kai mu shekara mai zuwa sai aje da ita.’Hajia tace ‘E ai an gama wannan maganar. Allah ya baki lafiya ya kawo wasu yaran masu albarka. Ita Najan sai suje kamar yanda aka tsara.’Ita dai tana zaune a tsakiyarsu amma bata iya ce musu komai ba; to kenan suma zarginta sukeyi da zubar da cikin ko me? To me Mustaphan ya gaya musu har suke mata wannan zargin?Sai da suka gama hirarrakinsu sannan suka yi mata sallama suka tashi suka fice.Bayan sallar Magriba Mustaphan ya sameta a dakinta tana zaune a gegen gado, bayan ta amsa sallamarsa ya karasa ya zauna a gefenta. Tayi masa sannu da zuwa ya amsa suka zauna suka dan yi shiru, jimawa kadan ya kirawo sunanta. Bayan ta amsa ya kakkafeta da ido sannan yace ‘Wai ni me kika yi ne cikin nan ya zube, ko wani abun kika sha saboda ya zube mu tafi dake aikin Hajji.’Tayi ‘yar dariyar takaici sannan tace ‘Mustapha ban zubar da ciki ba, domin kujerarka ta maka bata isa ta saka ni na zubar da ciki ba. Kamar yanda Allah ya kawo wancan cikin ya zube ba tare da nayi wani abu ba wannan dinma hakan ce ta kasance.’Yace ‘To ai kin ce wancan wahala ce da aiyuka suka yi miki yawa ya sa ya zube, ko ba haka kika ce ba? Wanna kuma na ga babu wannan ko?’Ta gyara zama itama ta kakkafeshi da ido tace cikin zafin rai tace ‘Mustapha wai baka ji me nace ba; ban zubar da ciki ba kuma kujerar Makka bata isa ta sani na aikata hakan ba. Na riga na san baka yi niyyar zuwa dani Hajj ba domin lokacin da kake cewa ina da ciki ba zaka je da ni ba itama Najan cikin ne da ita. Ka dai zabi matarka wadda kake so ka tafi da ita ni kuma ‘yar aikin gidanka ka barni na kular maka da gida da yara kamar yanda ka saba. Idan ma kai ne ka gayawa ‘yan uwanka wannan maganar har suke yar min da magana to ka koma ka gaya musu karya ne.’Ya mike a fusace ‘Daga an tambayeki kuma shine zaki yi min rashi kunya kamar yanda kika saba saboda ke ba a gaya miki gaskiya ko?’‘Wannene rashin kunyar a ciki; ganewa da nayi cewa kayi rashin adalci wajen zabar matar da zaka je da ita hajji ko kuwa gaskiyar da na gaya maka?’‘Mtsewwwww!’ Ya ja dogon tsaki ya mike a fusace ya fice daga dakin.Ta zuba fuskarta a tafukan hannayenta, so take hawayenta ya fita ko zata samu taji sanyi a ranta amma hawayen ya bushe kyamas. Kirjinta har zafi yake saboda yanda zuciyarta take turiri; Mommy ce ta fara yi mata wannan zargin gashi yanzu Mustaphan ma da shi da ‘yanuwansa suna zargin ta zubar da cikin ne don yaje da ita Hajji. Tabbas Allah sai ya bi mata hakkinta.Haka ta kwanta zuciyarta na mata zafi saboda takaici; ta so ta kirawo Mommy ta gaya mata ko zata sami salama a ranta, to amma hakan ba zai yi mata wani amfani ba. Tunda Mommy din ce ta fara yi mata wannan zargin. Ta sake fashewa da kukan takaici ta gyara kwanciyarta; yau itace da kwana amma ta san yanda Mustapha ya fice daga dakin nan watakila sai dai idan ya dawo daga aikin hajji sannan ya waiwayeta.………

Back to top button