Hausa novels

Halysaah Page 100 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 100…Hajiya Zaliha na rike da hannun Khaleesat ta fito da ita daga parlon Babanta bayan ya gama yi mata duk nasihar da zai yi mata, ya so a wannan gabar ya sanar mata wanda zata je Bauchi ta tarar a matsayin mijinta amma Nenne tayi bake bake a parlon kamar ta san niyyarsa kenan, ganin hakan sai bai yi ma Khaleesat maganar ba har dai Hajiya Zaliha ta fita da ita daga parlon zuwa dakin Ummanta, nan ma dai Nenne na biye da su a baya, ita dai Umma kasa cewa komai tayi bayan Khaleesat ta duka gabanta, after some seconds Umma ta dafe kanta cikin sanyin murya tace “Allah Ubangiji ya maki albarka Jiddah, ta haka ne zaki samu aljanna, Allah ya sanya wa auren ku albarka” Khaleesat dai kuka kawai take a hankali, Nenne tace “Ameen, addu’ar uwa ai baya faduwa kasa banza, in sha Allahu zata zauna lafiya da mijin da zata je ta tarar da izinin Allah kuma zata zame masa sanyin idaniya, bamu da shakku akan tarbiyyar da muka mata mun san bazata kunyata mu ba, in Allah ya yarda sai ta zamo abar alfahari a babban gidan nan, Zaliha dagota ku fito ga can motoci na jira a kofar gida kar a bata masu lokaci” Hajiya Zaliha ta dago Khaleesat dake kuka ta rungumeta jikinta, ita dai Umma bata yarda ta kalleta ba don daurewa kawai take ita ma, a ranta kuwa addu’a take Allah ya sa gidan zamanta ne, Allah ya sa shi din mijinta ne na har abada da za su tara zuri’a, kada Allah ya maimaita masu irin auren Abdul, a haka Hajiya Zaliha ta fita dakin tare da Khaleesat Nenne dake biye da su tana nata nasihar, sai a sannan hawayen dake makale idon Umma ya zubo ta bi su da kallo. Tun da Khaleesat suka iso Emirate din Bauchi take jin gabanta na faduwa ta rasa dalili, zuwa yanxu ta dena kukan da take sai addu’a da ta dinga yi a ranta ko zata samu nutsuwa a zuciyarta, tarba iya tarba aka masu a Emirate din kafin aka sauke su a inda aka tanadar domin sauke su a babban gidan, Hajiya Shafa’atu sai da ta tabbatar they are very comfortable don ita ce ma silar irin tarban da aka masu na girma, daga bisani ta fita daga bangaren don barin su suyi sallahn magrib da ya gabato, ko kafın su idar da sallah abinci kala kala da drinks aka cika masu a masaukin nasu, ga kayan marmari iri iri masu kyau, Baaba Gaje na kallon Hajiya Zaliha murya can kasa tace “Banda ma magariba tayi Hajiya ai tun da muka kawo masu amarya ina ga kamata yayi ace yau mun juya mu je gidansu Murja mu tafi mu kwana, duk da bamu san ya al’adar su take ba” Mama Salame tace “Wannan gaskiya ne Baaba Gaje, abun ka da gidan sarauta kada mu yi karanta bamu san ko ba a yi masu haka ba” Mama Shatu ta wani kallesu tace “Sai kace ana koranmu daga kawo amarya sai kama hanya, ai rashin wayewa ne wannan, yo ko kwana biyar za mu yi in dai wannan babban gidan ne ina ruwansu, baza kuma su gaji da ciyar da mu ba, gidan sarauta fa aka ce” Hajiya Zaliha tayi murmushi, can ta kalli Baaba Gaje tace “Ai babu komai don an kwana washegari mun tafi Mama, ai ba shigowar wuri muka yi ba, wannan ne ma yasa har aka bamu babban masaukin nan, in sha Allahu gobe za mu bar gidan nan in dai ba su suka tsayar da mu suka ce za su yi wani taro ba” Baaba Gaje tace “To shikenan” Aunty Farida ce tayi serving kowa abinci a parlon, sannan ta debi abincin ta kai ma Khaleesat dake daki tare da Lamisah da Sakinah yarinyar Hajiya Zaliha, Aunty Farida na kallon Sakinah tace “Don Allah ku saka ta ci abincin nan dole, tun safe babu wani abun kirki da ci” Sakinah tace “To Aunty Aunty Farida ta kwanta a dakin don duk ta gaji rabonta da baccin kirki tun shekaranjiya. karfe bakwai da rabi sai ga Hajiya Shafa’atu da Hajiya A’isha, sai Hajiya Sumayya sun shigo bangaren, sannu da hutawa Hajiya Shafa’atu tayi ma su sannan tace “Ga Fulani matar Mai martaba zata shigo yanxu ku gaisa” Sai ga Aunty ta shigo parlon cikin shiga ta alfarma tana taku dai dai fuskarta babu yabo babu fallasa, daga bayanta jakadiyarta ce da Cousin sister dinta Hajiya Nafisah, ban da Mai martaba da ko kusa da bangaren nan bazata zo ba haka ta dau alwashi, amma munafuka Shafa’atu sai da ta hadata da sarki, a iya saninta a bangarenta ya kamata ace an sauke Amarya, danginta kuma sai su zauna a masaukin da aka basu amma don a nuna mata iyakarta a nuna mata ba ita ta haifi Junaid ba shi ne aka ki sauke amarya a bangarenta, wanda tasan duk shirin Shafa’atu ne wannan, a sanda take kasar waje da mijinta uban wani ne ya rike Junaid din da dadi babu dadi, shi ne vanxu dọn ta dawo Nigeria har zata fara mata shisshigi haka, Aunty ta kai zuciya nesa ta zauna saman kujera Mama Shatu da su Baaba Gaje da Mama Salame sai jero mata gaisuwa suke babu kakkautawa Ita kuwa tana amsawa da kyar cikin isa da gadara tana bin ko wannen su da kallo, Hajiya A’isha tace “Ina Amaryan” Baaba Gaje ta mike da sauri ta tafi dakin da su Khaleesat suke tana cewa “Bara a fito da ita ranki shi dade” Haushi kamar ya kashe Hajiya Zaliha a inda take zaune don ta ma ki cewa komai, Aunty Farida ta sa Lamisah ta dauko ma Khaleesat wani Alkyabban dake ta kamshi don an turara sa ta saka mata, Aunty Farida dake kwance ta kalli Khaleesat tace “Saura ki je kina tura kai kasa kamar wawiya” Baaba Gaje tace “Haba Parida, cikin nasiha zaki mata magana ba da fada ba, Khaleesah ai yarinya ce” Baaba Gaje na rike da hannun Khaleesat suka fito babban parlon, ita dai Khaleesat kanta na kasa. Mama Salame tayi caraf tace “Hauwa’u ce” Hajiya A’isha tace “Maa sha Allah” Ita dai Aunty bata fasa kallon Khaleesat ba, gashi ko gaisuwarta bata amsa ba, after some seconds ta mike tana kallon wa enda suka rakota tace “To naga amarya mu je ko….” Jakadiyarta ta hau jero mata kirari a haka har ta fita daga parlon suna biye da ita, Hajiya Shafa’atu dai ta bi ta da kallo don ko kadan bata ji dadin attitude din da tayi displaying a parlon ba, gashi ko sallama bata yi ma su Hajiya Zaliha ba tayi tafiyartaq. Karfe tara Hajiya A’isha ta shigo parlon ta sanar ma su Hajiya Zaliha za a kai Khaleesat wajen Mai martaba ta gaishesa, Hajiya Zaliha ta tashi da kanta ta tafi dakin da su Khaleesat suke, kara shiryata tayi ta saka mata Alkyabbarta sannan ta kamo hannunta suka fito daga dakin, Hajiya A’isha tace “Maa sha Allah, to ina ga fa daga haka sai da safe kenan don bangaren Fulani zata kwana, in ma da abinda zata bukata Hajiya Shafalatu zata shigo ta daukar mata” Hajiya Zaliha tace “Toh hakan ma babu laifi Hajiya, Allah ya tashe mu lafiya gaba daya” Sosai Khaleesat taji jikinta yayi sanyi, nan da nan hawaye ya cika idonta, Hajiya A’isha na rike da hannunta suka fita daga parlon, tafiya me nisa suka yi kafın suka iso babban parlon sarki, yana zaune parlon nasa tare da Aunty, Hajiya A’isha ta zaunar da Khaleesat kan Carpet, bayan tayi ma sarki Barka da hutawa ta juya ta fita daga parlon, Khaleesat ta daga kai ta kallesa a hankali ta gaishesa, ya sakar mata soft smile with calmness in his voice ya amsa gaisuwarta, she felt so comfortable with him, ko don ta taba qaninsa har… time around a mai martabansa take kallonsa, unlike the other time da bata san wanene shi ba, addu’a sosai Mai martaba yayi mata kamar yanda zai yi ma er cikinsa, ita dai kanta na kasa tana wasa da Alkyabbar jikinta tana jin hawaye na taruwa idonta, Aunty kuwa sai kallonta take babu ko kiftawa, kwata kwata bata san Khaleesat ta kai har haka ba, ko don bata wani kare mata kallo bane a Amurka, sannan hoton da Mami ta nuna mata shi ma bata tsaya kare mata kallo ba, yanxu kuwa ga ta zahiri tana kallonta, sosai take jin abu ya tokare mata a makogwaro, duk da sanyin Ac da ya cika parlor wani zafi kawai take ji, sai yanxu take kara tabbatar da tayi babban kuskuren biye ma Mami don daga karshe ita ta kwana ciki, wai Junaid da mata, matar ma irin wannan, amma Mami ta cuceta ta ruguza mata tsari and this means starting afresh, ita kuwa Mami tsabar bakin ciki har yanxu bata je gun dangin Khaleesat dake gidan ba tana bangarenta taki fitowa kamar bata san abinda ake yi a gidan ba ma… daga karshe cikin nutsuwa Sarki yace “Allah Ubangiji ya baku zaman lafiya da zuri’a ta gari Jiddah, if there is anything you can meet me anytime and feel free to speak to me, Allah ya maki albarka….” Khaleesat dai bata dago kanta ba sai da taji an bude kofar parlon don tana zaune opposite din kofar ne, ido hudu suka yi da Ajay da ya shigo parlon, taga ya sauke idonsa, Mai martaba ya juya ya kallesa, juyawa yayi zai fita Sarki yace “Come in Ahmad” Aunty dai ta tsuke fuska, har Ajay ya karaso cikin parlon kansa na kasa, Khaleesat dai kallonsa kawai take, bata taba ganin yayi shiga irin ta Yarima that he is ba sai ranan, and he looks totally different from his normal self, zaunawa yayi kasan carpet har sannan bai yarda ya dago kai ba ya gaida Mai martaba sannan ya gaida Aunty, Aunty ta amsa sannan ta kalli Mai martaba tana dan murmushi tace “To ranka shi dade, bari in karasa bangarena da ita tun da ka gama yi mata magana ko? Don nasan akwai gajiya tare da ita, tana bukatar ta huta” Sarki yana kallonta yace “Ohk, akan me kenan?” Aunty ta kwantar da murya tana murmushi tace “Ka mance al’adar ta mu ce ranka shi dade? Tun asali ma ai wajena ya kamata ace ta sauka, sai tayi kwana uku. Sarki yace A’a i don’t think that is necessary he should take her to her abode kawai, babu wannan al’adar” Aunty tayi shiru tana kallon Mai martaba don ta ma rasa me zata ce ga wani tukuki da zuciyarta yake, Sarki ya kalli Ajay yace “Take her with you, sai da safe” Khaleesat ta daga kai ta kalli Sarki sannan ta kalli Ajay, har sannan ko da wasa bata kawo komai a rai ba, A hankali Ajay yace “Sai da safe ranka shi dade” Daga haka ya mike, sarki ya kalli Khaleesat calmly yace “Sai da safe Jiddah” Kanta a kasa tayi masa sai da safe sannan ta mike tana tafiya a hankali ta bi bayan Ajay da yaki kallonta har Ikcn, Aunty taji kamar zuciyarta zai buga don bakin ciki, ta yaya sarki zai yi mata haka, bata taba tunanin zai ce haka ba, duk nufinta a wannan kwana ukun ta samo solution din gaggawa, sai da Ajay ya tsaya ya jira Khaleesat ta fito sannan ya kullo kofar parlon, yana wondering inda zai kai ta kamar yanda Sarki yace ya tafı da ita, at this point ta fara tunanin why is she still yet to meet Jay, tafiya kawai Ajay yake amma gaba daya hankalinsa baya jikinsa, don ganin komai yake kamar a mafarki har wannan lokacin, at times sai yayi tunanin zai farka daga mafarkin amma kuma the dream is taking too long, walking slowly ya wuce bangaren Jay, ita dai Khaleesat na bin sa a baya just that ta gaji da tafiya duk ta kagu ya kai ta inda aka ce ya kai ta…..

Back to top button