Hausa novels

Halysaah Page 92 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 92…Jay na zaune parlon Maminsa ta dalilin kiransa da tayi, ko minti talatin basu yi da dawowa gidan tare da Ajay ba don yau ma sun je duba Khaleesat, Mami ta kallesa tace “Ina kuma yake jan ka kuke tafiya duk kwana biyun nan daga safe zuwa dare” Jay ya daga kai ya kalleta, sai kuma yace “Yake ja na kuma sai kace wani yaro Mami?” Mami tace “To ai hakan kake a wajensa, ba kai ne Drivern sa duk inda za shi a garin nan ba” Jay bai sake ce mata komai ba don tunda suka fara zuwa unguwan da Halysaah suka sauka Ajay ne ke driving din, Mami tace “Daxu Me martaba ke gaya min yanda ku ka yi da shi, dama da ban je na samesa ba kawai sai dai inji magana a sama, kai menene dalilinka na ƙin gaya min yanda ku ka yi da shi? Kun je kun yanke shawara har za a zartar amma ni ba a fita hakkina an sanar min ba and you are okay with that” Jay dai yayi shiru don he was only following Ajay’s advice, Mami tace “To ai shikenan, Allah Ubangiji yayi mana me kyau” Jay yace “Ameen” Mami tace “To a tudun yolan wace unguwa suke?” Jay ya daga kai ya kalleta yayi shiru, tace “Ko ba Tudun yola ka ce ba?” Yace “Eh can suke, amma ban rike address din gidan ba ai, any problem Mami?” Mami tace “A’a wai in ji, amma tunda baka sani ba ai shikenan” Wayarsa ne ya fara ringing yana dubawa yaga Mai martaba ke kiransa, ya daga kai ya kalleta yace “Mai martaba na kirana” Mami tace “Ohk” Mikewa yayi ya fita daga parlon, after a while ta tashi zata fita sai ga Aunty ta shigo, dama kuma wajen nata zata je don gaba daya akanta tayi relying all this while tunda tace ta bar mata komai, Mami ta koma ta zauna tace “Kuma gun ki zan tafi yanxu” Zaunawa Aunty tayi tana murmushi tace “Toh albishirin ki, yanxu haka na samo Address din gidansu yarinyar a wajen Mai martaba, ashe daga Kano zai wakilta aje gidan nasu, iyaka mutane biyu ne za su tafi daga nan” Mami tace “Da gaske kin samo Address din?” Aunty tace “Kwarai kuwa, ce masa nayi mijin er uwata dake Tudun yola yace min a basa address din gidansu yarinyar in dai Tudun Yola suke kilan bazai rasa sanin Ubanta ba tunda duk sun san kansu a unguwan, tun da safe muka yi hakan da shi shine ya kira Jawwad din ta waya a gabana ya tambayesa Address din, nan take kuwa ya gaya masa, sannan Mai martaba ya sake nanata min address din, ina komawa parlona na rubuce address din a waya don kar in mance, to na fita ne, sai yanxu na dawo shi yasa ban shigo na sanar maki ba” Mami tayi shiru tana kallon Aunty, can tace “Amma kinsan yanxun nan Yaron nan ya fita a parlon nan ina tambayarsa Address din yace bai sani ba???” Aunty ta taɓe baki tace “Ai ko ya gaya ma Mai martaba daxu da safe” Mami tayi wani murmushi tace “Ki bar ni da shi, in yasan wata ai bai san wata ba” Aunty tace “Ba nace ki fito masa a mutum ba kin ki kina gudun bacin ransa, tun yaushe za ki ce masa bai isa ba kuma hakan ya zauna” Jay na zaune gaban Mai martaba a parlonsa, Mai martaba was quiet for a minute kafin yace “Jawwad…” Jay ya daga kai ya kallesa don sai da gabansa ya fadi cause Mai martaba da serious tone ya kirasa, a nutse Mai martaba yace “Me yasa baka gaya min yarinyar da kake nema ta taɓa aure ba?” Jay ya dinga kallonsa babu ko kiftawa zuciyarsa na bugawa, Calmly Mai martaba yace “Ko ba haka bane?” Sauke kansa ƙasa yayi ya kasa cewa komai at first, shi gaba daya mance Khaleesat ta taɓa wani aure yake yi, lokaci daya yaji jikinsa yayi sanyi sosai, ya dafe kansa da yayi masa nauyi a take, Cikin kwantar da murya Mai martaba yace “Ba hakan zai sa in hanaka aurenta don ta taɓa aure Jawwad, my concern is why did you hide this important thing away from me? Idan da ban sa an min bincike kafin in tura zuwa ga mahaifin yarinyar ba da sai in wakilai na sun je mahaifinta zai sanar masu matsayin yarinyar kenan? Or probably kun ma riga kun hada plan ace budurwa ce duk ban sani ba… kuma duk hakan zai iya yiwuwa tunda har ka iya boye min, Kai ba aure ka taɓa ba Jawwad, this is ur first marriage idan Allah ya tabbatar, ka kuma san yanda al’adar gidan nan yake, tun asali da ka sanar min cewar ta taɓa aure ai sai an fara auren ka da Hadiyah idan ya so ko bayan wasu watanni ne sai ka auri ita wannan din, nobody will question you Jawwad, an sanar min abubuwa da yawa a binciken nan da na sa aka min wanda ina ga babu amfanin in zauna ina zayyano su a nan, har ma unguwan da suka baro kafin su dawo tudun yola na sani, just that I was taken aback knowing so many things…. kawai dai nasan ni bazan hanaka aurenta ba tunda kace kana sonta Ahmad, although bayan binciken nan da aka min akwai abubuwa da yawa wanda na kasa fahimta har yanxu, ban san ko da wani abu da ku ke boye min kai da Junaid ba, ko kuma akwai wani abu da ku ka juya kai da shi akan lamarin nan, anyway… ba hakan zai sa a fasa zuwa gun mahaifinta gobe asabar kamar yanda na tsara ba, sai dai za a fara zuwa gun dangin uban Hadiyah tukunna, so dalilin kiran ka kenan Ahmad, Allah ya maka albarka….” Jay dai ya kasa ɗago kansa don gaba daya jikinsa yayi sanyi qlau, kenan an sanar ma Mai martaba karatun da take a Amurka ma Saurayi ne ke sponsoring dinta tun bai aureta ba, bayan nan ya gano shi da Junaid suka ci gaba da dawainiya da ita a Amurka kenan bayan mutuwar aurenta? Yanxu har labarin prison din da aka kai babanta da dalili duk yaji, ta yaya ma har aka gano tsohon unguwan da suka baro?? Babu abinda ya kara sanyaya masa jiki sai batun gidan da ya siya masu don ya ma san har shi za a gaya ma Mai martaba kawai bazai dai ce masa komai bane, tun da gashi yace yaji abubuwa da yawa, Mai martaba ya katse masa tunaninsa yace “Ko da wata maganar da zaka yi ne Ahmad?” Da kyar ya ɗago kai, cikin sanyin murya yace “Kayi hakuri Abba, nayi kuskure boye maka duk abubuwan nan da nayi tun farko, a gafarce ni Abba” Mai martaba ya ɗan yi murmushi yace “It’s fine Ahmad, i only called to correct you, in sha Allah bikin ma baza a saka lokaci me tsayi ba, kawai asalin mahaifin yarinyar ne ake contemplating har yanxu, ance Kano kuma aka dawo aka ce Bauchi… How true is that? Although ba mu ji daga mahaifin nata ba har yanxu ai, mahaifiyarta kuma aka ce buzuwa ce er Nijar ko?” Da kyar Jay yace “Haka ne, Mahaifinta a Kano aka haifesa amma asalin babansa ɗan Bauchi ne, zama ya maida shi Kano, daxu kakarta ke sanar mana don tana garin nan, har ma tace tana son a kawota ta gaishe ka” Mai martaba ya ɗan yi murmushi yace “A nan garin kakarta take kenan?” Jay yace “A’a zuwa tayi, dama kuma tana zuwa” Mai martaba yace “Shikenan, babu matsala sai ka kawo ta din, zaka iya tafiya…” Jay yayi masa sallama ba tare da ya yarda sun hada ido ba ya mike ya bar parlon, bangaren Ajay ya nufa, ya samesa zaune parlor yana dube dube a laptop, Bayan ya zauna Ajay ya kallesa, Jay ya jinginar da kansa jikin kujera a hankali yace “Kasan Mai martaba ya sa anyi bincike a Kano? And he found out everything, when I say everything I mean Everything Ajay” Ajay ya ɗan bude ido ya ajiye laptop dinsa yace “Really?” Jay ya sauke ajiyar zuciya yace “Dama ai zancen duniya baya buya, but banyi expecting za a gano komai easily haka ba, yau na kara jin tsoron mutum, mutum abun tsoro ne Ajay, nasan har gidan da na siya Abba ya sani yanxu, he was angry but calm at the same time, I wish I told him all this before he find out himself…” Ajay was quiet for some time don shi ma ya girgiza, can yace “To yanxu me yace maka at the end?” A hankali Jay yace “He said it’s fine, I told him about her Grandma da tace zata zo, gobe kenan….” Ajay yace “Ba nace ka kyale wannan tsohuwar ba, sai ta zo ta karasa fada masa abinda ba a fada ba a Kanon hankalin ka zai kwanta, she talks too much shi yasa nace kayi ignoring kawota da tace kayi gidan nan, but you still went ahead and told Abba” Jay ya sauke wani ajiyar zuciyan yace “Bazata yi abinda kake tunani ba, i will bring her tomorrow in sha Allah, don Abba na contemplating asalin Baban Halysaah, an ce masa Kano aka dawo kuma aka ce Bauchi” Sosai Nenne ta nutsu tayi zaman ladabi da biyayya tun da aka shigo da ita babban parlon Mai martaba, don a iya saninta ba kowa ne ke da access din parlon sarki ba, ita a ganinta ba karamin karramata da mutunta ta aka yi ba haka, dama ta baza tsadadden turaren Khaleesat da suka barota a gida, sai zuba uban kamshi take abun ta ga sabon gyale da atamfa a jikinta kai baza ka bata shekarunta ba, zuwa sannan sun kusa minti goma kenan a parlon a zaune, Ajay ne yayi leading dinsu zuwa parlon sannan ya fita, Nenne ta saci kallon Aunty Farida da tayi picking call din da ya shigo wayarta ta hade rai tace “Ke Parida ba nace ki ajiye wayar nan ba, ba fa parlon gidanmu bane nan, ba fa kowa ake ma iso zuwa wannan parlon ba sai wanda ya isa, wannan wani irin kunyata ni kike son yi bayan na yarda dake na jajibo ki, Haba parida…” Ko rufe baki Nenne bata yi ba sai ga Mai martaba ya shigo parlon walking like the king he is, Nenne ta sinne kai irin babban mutum ya shigo, Sau daya Aunty Farida ta daga kai bayan ta gansa ta ajiye wayar hannunta, ya karaso har cikin parlon ya zauna a spot din da ya saba zama yana kallonsu, tuni dama Nenne ta fara jero masa gaisuwa tun bai kai ga zama ba, shi ma ya gaisheta cikin girmamawa, Aunty Farida ma ta ɗaga karamin Nikab din da ta dora kan Abayan jikinta ta gaishesa kanta a kasa, ya kalleta ya amsa sannan ya kalli Nenne yace “Kun zo lafiya Baaba” Nenne tace “Wallahi lafiya lau ranka shi dade, na ce ni dai yau a kawo ni in gaishe ka in sa maka albarka don kai din mutumin kirki ne kowa ya shaida, Allah Ubangiji yayi maka albarka ya kare gaban ka da bayan ka, ya rufa maka asiri duniya da lahira, Allah ya albarkaci zuri’ar ka, ya ja da ranka, ya kara maka lafiya da kwanciyar hankali, Allah ya taya ka riko…” Ya gyada kai with calmness yace “Ameen Baaba, Ameen, dama albarkan irin ku abun so ne gare mu, muna godiya kwarai, Allah ya kara girma, madallah” Nenne tace “Ni dai nayi farin ciki da ganin ka, nace duk yanda za ayi yau dai a kawo ni wajen sarki mu gaisa, shi ne na saka Parida kanwar surkata ta rakoni muka taho tare” Mai martaba yace “Madallah, ai ba a jima ba aka kirani ake sanar min wakilan da na tura sun isa can gidan Alhaji Aliyu, kuma anyi komai lafiya har an tsaida lokaci ban san ko sun sanar maki daga Kanon ba” Nenne da ta bude ido sosai tana sauraron abinda Sarki ke cewa tayi kasa da murya tace “Wallahi ba a sanar min ba, kilan Aliyun zai ce a jira in dawo kafin a sanar min, amma nayi farin ciki da wannan abun arziki haka, ai hada zuri’a da kai Mai martaba abun alfahari ne abun farin ciki ne, nayi murna sosai, Allah Ubangiji ya sanya alkhairi…” Maganar da Umma ta kira Aunty Farida zata yi mata kenan kafin shigowar Mai martaba da Nenne ke tayi mata bala’i, Aunty Farida ta dade bata ji farin ciki irin na wannan lokaci ba, she is finding it hard to believe it, yanxu har an aika neman auren Khaleesah kenan amma ko da wasa daga Jay har Ajay babu wanda yace masu komai all this while, kuma kullum sai sun je can gidan Aunty Murja, Nenne ta nuna masa Aunty Farida tace “Kanwar uwar yarinyar kenan uwar su daya uban su daya, ita kanta bata sani ba banda yanxu da muke ji tare…” Sarki ya jinjina kai yana kallon Aunty Farida yace “To Madallah, ke ya sunan ki…” Nenne ta gyara zama tace “Parida, sunanta Parida Isuhu, tun tana er shekara goma Aliyu ya daukota daga gaban iyayenta a Nijar ya kawota gaban yayarta wato uwar wannan jikar tawa da aka je neman aurenta yau, to Ali ne yayi mata auren fari aka zo zaman babu dadi kuma gashi abokinsa ne mutumin saboda ya yarda da shi ya basa ita ga manema kaca kaca ya hanasu, to daga karshe dai da kansa ya amso mata takardarta ya raba auren ganin tana cutuwa gashi ita ba me baki bane sai dai kuka, to tun sannan har yau tana gaban Ali, duk wanda ya zo neman aurenta sai taki basa hadin kai yau shekara bakwai kenan, duk bayan wasu shekaru za su shirya su je gaida iyayensu ita da yayarta a Nijar, iyayen nasu buzaye ne mutanen kirki wallahi, aure me hada mutanen arziki ga shi ya hada zumunci tsakanin Nijar da Najeriya” Mai martaba yace “Wannan gaskiya ne Baaba” Nenne tace “To tun da har mun samu ganin ka har mun gaisa, to ina ga mu za mu zo mu koma Ranka shi dade kar mu shiga lokacin ka” Mai martaba yace “A’a, ku bari a karasa da ku bangaren fulani ku samu ku ci wani abun kafin ku tafi Baaba, bazai yiwu ku tafi baku sha ko ruwa ba a masarautar nan…” Nenne zata yi declining offer din nasa sai ga kanwar Aunty ta shigo parlon da sallama tana rike da bowl din fresh fruits, tare da Auntyn suke amma ita tana can baya tana tafe tana waya don wani lkcn in har Aunty zata kawo ma Mai martaba abun ci ko sha kanwarta ke rike mata har zuwa parlonsa in ta ajiye sai ta fita, Sarki na kallon Zuwaira yace “Ki shiga da baƙin nan cikin gida Zuwaira, ayi masu duk abinda ya kamata” Zuwaira ta kalli Nenne sai kuma ta kalli Aunty Farida dake kallon direction daban hakan yasa bata ga fuskarta da kyau ba kawai dai tasan fara ce kamar za a latsa ta jini ya fito, kallon Mai martaba tayi da ladabi tace “To ranka shi dade” Ta kalli Nenne ta gaisheta a takaice sannan tace “Mu je” Nenne ta mike bayan ta amsa gaisuwanta, Aunty Farida ta sauke Nikab dinta sannan ta tashi ita ma, hada ido suka yi da Mai martaba, tayi masa sallama ta bi bayan Nenne dake biye da Zuwaira, sun fita daga parlon kenan sai ga Aunty cikin shiga ta alfarma ta sha gwala-gwalai tana taƙu dai dai, daga sama har kasa take kallon Nenne da Aunty Farida dake sanye da Nikab, Aunty ta kalli Zuwaira tana yatsine fuska tace “Su waye wannan kuma Zuwaira?” Zuwaira ta taɓe baki tace “Oho, Mai martaba ne yace in shiga da su cikin gida, a parlonsa na same su” Nenne ta kwantar da murya tace “Ina wuni Pulani, baƙi ne daga Gombe….” Ko amsa gaisuwan Nenne Aunty bata yi ba ta shiga parlon Mai martaba, Zuwaira tana kallonsu a walakance tace “Mu je don Allah ina da abinda zan yi ni kam….” Bata jira cewarsu ba ta ci gaba da tafiyarta, Nenne ta kalli Aunty Farida, sai da taga Zuwaira tayi nisa sannan tayi kasa da murya tace “Parida kira mana Ahamad kice mun gana da Sarki ya fito ya maida mu gida” Ko Nenne bata ce haka ba dama Aunty Farida bata yi niyyar bin Zuwaira ba, haka nan suka canza hanyar da zai sada su da Compound Aunty Farida na kokarin kiran Ajay ta wayarta… Aunty na shiga parlon Mai martaba tana kallonsa tace “Ranka shi dade, wasu baƙi ne wannan aka kawo su har cikin parlon ka? Kuma ni ban taɓa ganinsu ba alamar babu abinda aka hada da su, ita dayar Nikab ma ta saka balle in ga fuskarta, su waye ne su da za su shigo har wannan parlon bayan ga can inda ake sauke baƙi?” Calmly Mai martaba yace “Ina ce kin gaisa da su ai?” Aunty ta ɗan hade rai tace “Eh, wai daga Gombe suke in ji tsohuwar” Mai martaba yace “To haka ne” Mikewa yayi yace “An sanar min ina da baƙi a fada yanxu, zan je in same su Fulani”*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*07087865788Bear with me pls, I am not well

Back to top button