Halysaah Page 88 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 88…Karfe goma da rabi still that morning Jay ya koma bangaren Mami, zaune ya sameta parlor tayi nisa tunanin da take, ta daga kai tana kallonsa, yace “Lafiya kuwa Mami?” Murmushi tayi tace “Ba komai Jawwad, kawai nazari nake ko in tafi Gomben da nace zan je yau ne ko kuma dai in bari gobe” Yace “Ai da sauran lokaci yau din Mami, karfe sha daya ma bai yi ba, in zaki je kawai kiyi tafiyarki yau din” Mami tace “To bari in shirya, shiru shiru baka dawo ka amshi wayar ka ba” Jay ya dau wayar sa dake gefen Mami, sannan ya zauna yana kallonta yace “Mami kiyi hakuri plss zan bi Ajay za mu tafi Abuja, amma kwana biyu kawai za mu yi mu dawo in sha Allah” Mami tayi shiru tana kallonsa, can tace “Yanxu za ku tafi Abujan kenan?” Jay yace “Eh, amma driving za mu yi zuwa Kano sai mu kwana a can, gobe mu bi flight zuwa Abujan” Mami tace “To ai shikenan, Allah Ubangiji ya kai ku lafiya, ya tsare hanya” Yace “Ameen” Mikewa yayi yace “Let me go and get ready” Tace “Ohk” Daga haka ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita daga parlon ya kullo mata kofa, ta rungume hannunta tace “Tabdi jam” Da yamma Jay ya gama shirin da yake ya fito daga daki yana kallon Ajay dake kwance kan 3 seater yace “Mu je…” Ajay ya daga kai ya kallesa yace “Mu je ina?” Jay ya hade rai yace “Plss ka dena rena min hankali mana” Ajay yace “Dole ne sai naje? Kayi tafiyarka mana” Jay yace “In ka zauna kai kadai a gidan me zaka yi?” Ajay yace “Me nake yi yanxu?” Jay ya ja tsaki yace “Don Allah ka tashi mu je yamma na yi, in ma bazaka shiga gidan ba kayi zamanka a mota mana” Ajay yace “Wai dole ne sai naje gidan da ko shawara ba ayi da ni ba wajen siya? Saboda kana ganin zan hanaka siya ko me? But at least I should have know as a brother, ni bazan taɓa yin abu without ur knowledge Ba no matter what it is” Jay ya ɗan yi shiru, sai kuma yace “Ohk My bad… Yanxu dai ko bazaka shiga ba ka tashi mu je, i don’t want you to start running temperature again, kana ganin an bar ka kai ɗaya kake fara running temperature….” Ajay ya wani kallesa, sai kuma yace “Do I look sick to you now? Ai na ji sauki” Jay ya kamo hannunsa zai dagosa daga saman kujeran with one hand, Ajay yayi wata dariya yace “That is a lie, Kai ka isa” Karfe biyar saura suka isa Tudun Yola, Jay yayi parking dai dai gate din gidan, Ajay dai kallon unguwan kawai yake don manyan gidaje ne kawai a unguwan, Jay ya kallesa yace “This is the House” Ajay ya kalli gate din gidan sannan yace “Allah ya sanya alkhairi” Jay yace “Ameen” After some seconds yace “Yanxu dai bazaka shiga ba?” Ajay yace “Ina jiran ka a nan” Jay yace “Ohk then, Amma kasan kuwa nayi ma Mami maganar Housemate?” Ajay ya kallesa yace “Ohk… ai baka gaya min ba” Jay yace “Yea, i don’t want to stress you with talk duba da baka jin dadi” Ajay yace “Na fa ce maka ni naji sauki, You can see for ur self” Jay ya sauke ajiyar zuciya yace “Mami was so calm about it, and she wish me nothing but what’s best for me, ta amince lokaci daya without prolonging the issue, dama kuma nasan bazata taɓa ƙin abinda na nuna ina so ba I told you that, tunda Mami da Mai martaba sun amince min, i don’t care what others will think or say about this…” Ajay dai kallonsa kawai yake bai ce komai ba, can ya ɗan yi murmushi yace “I am happy to hear that, Allah ya sanya alkhairi” Jay na kallonsa yace “Ameen….” After some seconds yace “Or is there anything you want to tell me but you are not telling me?” Ajay yace “Kamar me kenan? Why did you say so?” Jay yace “Naga kamar har yanxu kai baka yi na’am da batun nan dari bisa dari ba, You are just being neutral about it” Ajay yayi dariya yace “I don’t get you Bruh, idan akwai wani abu ance maka bazan gaya maka bane?” Jay bai sake cewa komai ba ya bude motar ya sauka yace “Bazan dade ba in sha Allah” Ajay yace “Kana wuce minti goma i promise you I am leaving” Jay yace “Ai ba motar ka bace Malam” Bai jira cewarsa ba ya nufi cikin gidan, Ajay ya jinginar da kansa jikin kujeran motar maganganun Mami suna kara dawo masa a kai kamar a lokacin take gaya masa su, rufe ido yayi trying to erase the thought of his mind. Duk da ɓacin ran da Nenne ke ciki mara misaltuwa tana ganin Jay ta watsake lokaci daya ta dinga masa sannu da zuwa cikin fara’a, ta dauko masa rabin ledan pure water ta dire masa a gabansa baki har kunne tace “Ai ni bata ce min kana hanya ba da na bada kudi an amso maka lemon kwalba da ruwan gora nayi maka tuwo da miyar taushe, sai dai kawai matsalar unguwan nan masu kantin barayi ne, komai nasu tsada kamar yan fashi” Shi dai Jay murmushi kawai yake, Umma ta fito suka gaisa da Jay cikin fara’a sannan ta bar parlon, Nenne tace “Amma kuma kace mata zaka zo shi ne ta kama hanya ta tafi Hotoro da kanwar uwar, wai sun je wajen wata wai ita Gaje” Jay na murmushi ya girgiza mata kai yace “A’a ba mu yi waya da ita ba yau, bata san zan zo ba” Nenne tace “To bari in je in sa uwar ta kira mana ita” Jay yace “Zan kirata da kaina Kaka” Nenne tace “To hakan ma ba laifi, sai dai ka zo ina cikin wani bakin ciki wanda rabon da in shiga irinsa har na manta wallahi” Jay yace “Subhanallahi, me ya faru Kaka?” Nenne ta gyara zama rai bace tace “Rimi rimi muka kamo hanya tsakar dare muka dawo gidan nan don bama son kowa yasan inda muka koma saboda tsaro da gudun surutun mutane, amma maganar da nake maka yanxu ɗaiɗai kun ‘yan Mariri ne basu zo ganin gidan ba wai sun zo mana Allah ya sanya alkhairi, gaba daya labari ya baza Mariri an san gidan da muka dawo, to duk ba wannan ba, kasan ba mu dawo da matan Malam Ali gidan nan ba, kai dai kaga irinsu kaga yanda suke rayuwa, yanxu fisabililahi ina wajen da za a ajiye su a gidan nan? shi ne uwar Khaleesat ta munafurce ni ta zaga suna ta kulle kullen yanda kishiyoyin nata za su dawo gidan nan mu gwamutsu….” Jay ya ɗan yi murmushi yace “Kiyi hakuri Kaka, baza a biye ta halinsu ba ai” Nenne tace “Ba halinsu nake gudu ba ɗan nan, wallahi rubar da gidan za su yi ya koma dena ba kowa sha’awa, in don ta mugun halinsu ne ni ina ruwana, babban damuwata kar a dena sha’awar gidan nan gaba, sai kaga yanda ake turuwan zuwa ganin gidan nan wallahi, har da yan unguwan, to aka dawo da su Zubaida ai zance ya lalace kuma” Jay na murmushi yace “Ki dai yi hakuri Kaka, gida in ana gyaransa babu abinda zai yi in sha Allah” Nenne tayi shiru bakin ciki kamar ya kar ta, nan Jay ya dinga lallabata yana bata baki akan ta bar su su dawo kawai ko don Baban Khaleesat, bayan kusan minti goma ta sauke wani bala’e’en ajiyar zuciya tace “Shikenan ɗan nan, ai ka wuce ka ban shawara in ki dauka, kuma babban banza ne baya daukan shawara, zan samu Zahra’un ta kira min Malam Alin mu yi magana ta waya” yana murmushi yace “Maa sha Allah Kaka” Tayi shiru a ranta tana cewa “Zubaida me ‘ya ya rakacaaa dama sai dai ta zauna tsakar gida, kawai ita ta hakura ta bar masu wannan ginin da take cewa nata ne su karata can, parlor daya da kitchen daya da daki da banɗaki ya ishi ita da ‘ya yanta rayuwa, ita kuma Shatu a samu dakin kusa da kitchen a hadata da shi ita ma ta karata da kananun yaranta, su kuma yan matan gidan a basu daki daya su karata su ma, Aunty Farida sai tayi hakuri su zauna tare da Khaleesah kawai tunda haka Allah ya kaddaro masu, ta sauke wani ajiyar zuciya a fili tace “Toh ya iyayen naka?” Jay yace “Duk suna lafiya Alhamdulillah” Ta mike tace “Bari in duba ko da sauran shinkafar in zubo maka, dama Khaleesah ce ta dafa” Bata jira cewarsa ba ta wuce kitchen da sauri. Tunda Khaleesat da Aunty Farida suka sauka daga cikin adaidaita sahu take kallon motar da aka yi parking kofar gidan with the front seat slightly open kuma an kwantar da seat din motar, lokaci daya kawai tasan Ajay ne a motar for some reasons, ta kalli Aunty Farida tace “Kamar Ya Junaid” Aunty Farida tace “Haba” Khaleesat ta karasa har front seat din ta leka cikin motar tana kallonsa, taga idonsa a lumshe, a hankali ta kai hannu zata dau wayar sa dake ajiye lokaci daya ya bude ido, Mikewa zaune yayi da sauri yana komawa baya ta kyalkyale da dariya ta daga nikab din fuskarta don da alama Nikab din ne ya firgitasa cause he was sleeping, sosai ya bata dariya ba kadan ba ganin da gaske ya ji tsoro, shi ko ya hade rai yana kallonta, tace “To guduwa zaka yi da?” Aunty Farida ta karaso gun motar, ya gyara zama suka gaisa tace “To me yasa baka shigo ciki ba Junaid” Ya ɗan shafa kansa yace “Ina ɗan waya ne, amma Jawwad yana ciki” Khaleesat ta ɗan bude ido jin abinda yace, sau uku tana kiran Housemate din nata yau yaki picking call dinta, wanda hakan yasa tun daxu bata da wani walwala sai yanxu ne ma tayi dariya tunda gari ya waye, Aunty Farida tace “To mu shiga tun da ka gama wayar” Ya sauke idonsa bai ce komai ba, Aunty Farida ta nufi cikin gidan, Khaleesat na tsaye har ya sauko daga cikin motar, ya kara hade rai yace “Wai ke mayya ce ne, Kiyi tafiyarki mana” Ta ɗan yi murmushi kawai tace “Ai ko mayyar ce i will finish you first before anybody” Tana fadin haka ta nufi gate kafin ma ya bata amsa, kulle motar yayi ya ɗan tsaya for some seconds before walking toward the gate too. Khaleesat na shiga parlor Jay dake zaune ya daga kai ya kalleta, suna hada ido ta hade rai ta dauke idonta ta karaso cikin parlon ta zauna kasan carpet, Nenne na kallonta tace “Kun samu Gajen ta ku?” Khaleesat tace “Eh” Nenne ta kalli Jay tace “To bari in shiga wajen Zahra’u in yi yanda kace ayi, ai tunda kace inyi hakuri an gama magana kawai” Ya ɗan yi murmushi yace “To Nagode Kaka” Mikewa tayi ta bar parlon, Sai a sannan Khaleesat ta gaishesa ba tare da ta kallesa ba tana wasa da Hijab din jikinta, shi dai kallonta kawai yake babu ko kiftawa, can ya ɗan yi murmushi don yasan fushin me take, sai kuma yayi kasa da murya yace “Should I take my leave?” Sai a sannan ta daga idanuwanta ta kallesa, kamar zata yi kuka tace “Mene yasa baka son yi ma mutum uzuri?” Kamar bazai ce komai ba, sai kuma yace “Uzurin me za a maki Halysaah?” Tace “Da ka kirani jiya ban daga ba ai wayar baya wajena ne Aunty Farida ce tayi waya da shi” Yana kallonta yace “Why didn’t u explain to me on Whatsapp yesterday? Instead you only asked weda I didn’t see ur call and that’s all” Shiru tayi bata ce komai ba, yayi murmushi yayi kasa da murya yace “You know one thing about you Halysaah?” Ta daga idanuwanta tana kallon sa, still smiling yace “Idan kika yi wani action that needs explanation, ignoring explanation din kike kiyi acting as though nothing happened, I called you 4 times yesterday and ur line was busy, da kika min magana ta WhatsApp sai ki bada uxurin ki amma sai kika yi ignoring din hakan” Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace “To kayi hakuri” Shi dai murmushi kawai yake yana kallonta yace “In ban yi hakuri ba ai bazan zo yau ba Halysaah” Ta langwabe kai tana kallonsa, yace “Kun ga Ajay a waje ne?” Ta ɗan bude ido sai kuma ta mike tace “Ina zuwa” Da ido ya bi ta har ta fita daga parlon, a compound din gidan taga Ajay zaune ta tafi har inda yake, ita har ta manta ma da shi, tana kallonsa tace “Baza ka shigo ba ne” juyawa yayi, yayi backing dinta yana kallon different direction yaki tanka ta, dariya ma ya bata, ta taɓe baki ta juya ta koma cikin gidan kawai, ta zauna tana kallon Jay tace “He is sitting outside, kilan bazai shigo ba” Jay yace “Ohk, i think I will take my leave now, dama Abuja za mu tafi gobe so we decided to spend the night in Kano Today” a hankali Khaleesat tace “Ohk, to ko inyi girki sai anjima ka zo ka amsa? May be after magrib” Jay yace “A’a kar ki ba kanki wahala Halysaah, we will get food at a restaurant” Khaleesat ta kalli wayarta dake vibrate alamar shigowar kira sai kuma tayi silencing call din don bata da number dake kiran nata, Jay yace “Wa yake kiran ki”*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah* ur evidence 07087865788
