Mallama Juwariyya

Maganin ciwon sanyi da ke addabar mata (musamman me sanya warin gaba, fitar farin Ruwa da kurajen gaba)

Hakika mata masu yawa suna fama da wannan matsala ta ciwon sanyi wato infection. Idan har kinsa kina fama da ɗaya daga cikin wadannan matsaloli da zamu ambata to yana da kyau ki jaraba wannan maganin da zamu yi bayani, da yardar Allah za a samu waraka.

1. Matsanancin ciwon sanyin mara.

2. Ƙananun kuraje da ke fitowa a gaban mace, sannan idan ana saduwa da ita sai ta dinga jin zafi tamkar gabanta zai tsage.

3. Fitar farin ruwa daga gaban mace.

4. Warin gaba.

5. Ciwon mara yayin da ake al’ada

Duk macen da ke fama da wadannan mas’aloli da muka ambata a sama to, ta samu wadannan abubuwa kamar haka;

Kanwa cokali Uku

Gishiri cokali Biyu

Tafarnuwa dunƙule ɗaya.

Bayan an tanadi wadannan abubuwa da muka ambata, sai ta juye su a ciki tunkiya ta dafa su, bayan sun dahu. Amman ruwan ya kasance daidai yadda zaki shiga baho ki zauna.

Za ki bar ruwan yaɗan sha iska daga nan sai ki shiga tsawon minti goma zuwa sha biyar, daga nan sai ki fice daga cikin sa.

Duk wadda ta yi hakan to lallai zata sha mamakin yadda zata ga cutar sanyi tana fita a gabanta, sannan idan tana son rabuwa da wadancan mas’aloli da muka ambata a sama gabaɗaya, to sai a ƙara da wadannan da zamu ambata kamar haka;

1. Man zaitun kwalba ɗaya.

2. Man tafarnuwa kwalba ɗaya

3. Man kwakwa shima kwalba ɗaya.

Bayan an tanade su sai a haɗasu a tukunya ko kwano a soyasu, amman wajen soyawar za a saka tafarnuwa dunƙule ɗaya, idan ya soyu sai a barshi ya huce sosai, sannan a juye a roba.

Abu na ƙarshe shi ne za a samu auduga a saka ta cikin wannan robar ta soyayyen man nan, za ki dinga saka audigar a gabanki ne har sai za ki yi fitsari ko bayan gida, sannan za a cire.

Lallai duk wadda ta jaraba wannan maganin zata sha mamaki domin duk wani sanyi da ke tare da ita sai ya fito da izinin Allah.

 

Allah Ya sa a dace.

 

 

 

Back to top button